Skip to content
Part 46 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Cikin sanyin jiki da damuwa ya shigo cikin falon nasu, suna tsaye carko carko, Inna Jumma sai kaiwa da komowa take cike da tashin hankali, kowa dake wajen fuskarsa cike take da damuwa idanunsa ya runtse yana jin zafin Nafeesa domin kuwa duk itace tayi sanadin shiga damuwar Family ɗinsa, numfashi ya saki cikin sanyin murya yace.

“Saboda wannan ƙaramar matsalar kuke Cmcikin damuwa har yanzu, Inna Jumma kina da hawan jini fa bana son ki dinga sakawa kanki damuwa, Haidar ransa ne kawai ya ɓaci nasan bazaiyi fushi dani ba idan ya huce komai zai daidaita.”

Juyowa Inna Jumma tayi tana ƙare masa kallo tare da tahowa gabansa ta tsaya cikin damuwa tace.

“Aminu ba faɗan ku da Aliyu bane ya ɗaga min hankali yanzu rashin dawowar Ablah ne, tun safe da ta tafi school har yanzu bata dawo cikin gidan nan ba, na sanya idi da Ladiyo suje su dubata ko lafiya sunje babu ita cikin makarantar, sannan shi kansa Isa da ya tafi ɗaukota babu labarin sa hankalina ya tashi ina tsoron kar wani abun ya faru da ita kwatankwacin abinda aka aikatawa Khairi ina tsoron wannan rayuwar.”

Ai kuwa wani irin tsinkewa zuciyar Al’ameen yayi tsoro da fargaba suka ƙara shigar sa damuwar da yake ciki ta ƙara hauhawa karfa a kashe masa rayuwarsa kamar yadda aka yiwa ƙanwarsa Khairi da mahaifiyarsa, abinda ya ƙara basa tsoro harda rashin ganin Isa driver, idan bai manta ba sanda aka kashe Khairi a hanyar school ne, kuma hakane ta faru na rashin dawowarsu har Idi driver tsohon drivern su a wancan lokacin, dafe kansa dake sara masa yayi yana jin Hajijiya na ɗaukarsa, cikin nauyin murya gami da tsoro ya furta.

“Inna kuma kun kira wayarta bata ɗaga ba?”

“Aminu ni ina nasan tana da waya bare nayi tunanin kiranta, wallahi hankalina yana tashe yarinya amanar Allah, idan wani abun ya sameta mai zancewa iyayenta?”

Tayi maganar a ruɗe cikin tashin hankali, Al’ameen yafi kowa shiga cikin damuwa da tashin hankali sai ganin Inna Jumma ta ruɗe ya sashi kama hanunta tare da ƙarasowa da ita kujera suka zauna wayarsa ya zaro tare da dannawa Ablah kira domin kuwa yasan akwai ƙaramar waya a hanunta switch off, idanunsa ya runtse zuciyarsa na bugawa duban Inna Jumma yayi yace.

“Akashe layinta, amma bara na kira Umma ko taje can.”

Yayi maganar yana dannawa Umma kira ringin ɗaya ta ɗaga bayan sun gaisa yake tambayarta Ablah ta iso ne, sai dai bai mata tambayar ta yadda zata fahimci akwai matsala ba, sanar dashi tayi bata iso ba, sallama ya mata ya kashe wayar a wannan lokacin hankalinsa ya tashi ainun a gigice ya miƙe kamar zai faɗi Aunty Amarya tayi saurin taresa tana cewa.

“Subahanallah! Ka nutsu mana, yanzu haka wataƙil ta biya wani wajen ne, amma dai Ablah bazata ɓata ba tunda ba yarinya bace ita, ka ƙyale kawai zata dawo da kan…”

Tsawa Inna Jumma ta dakawa aunty Amarya tace.

“Ina zata biya kin taɓa ganin takai haka a wajena kaji wata maganar banza idan ƴarki ce zaki faɗi haka, na kwana biyu fa da fahimtar bakya ƙaunar wannan yarinyar duk abinda ke faruwa cikin gidan nan ina saka idanuna kuma ina fahimtar kowa, idan bazaki faɗi alheri ba kiyi shiru, kai Aminu jeka nemota Allah yasa tana halin lafiya.”

Kansa Al’ameen ya ɗaga cikin tashin hankali da damuwa ya fita, Aunty Amarya kuwa baki ta sake tana mamakin Inna Jumma tunda take da ita bata taɓa mata tsawa ba sai yau akan wannan tsinanniyar yarinyar maga ta yadda zata dawo lafiyan, tayi maganar cikin zuciyarta tana juyawa a fusace tabar wajen da idanu Inna Jumma ta bita.

Tafiyar kawai yake amma sam baya cikin hankalinsa tunda yake a rayuwarsa bai taɓa shiga tashin hankali irin wannan ba, bai san damuwa ba a rayuwarsa farin ciki da gata shine kawai abinda ya sani sai dai gashi yau baƙon yanayi ya shigesa Idan Ablah ta shiga wani hali ya zaiyi da rayuwarsa (Yadda ka tarwatsa min rayuwata na rantse da Allah kaima saina tarwatsa maka taka rayuwar, ka jira ka gani nan da awa uku sai kayi kuka kamar yadda ka sani nayi).

“Haidar! Ya furta da ƙarfi yana parking a gefen titi, Haidar ne tabbas shine zai ɗauketa domin ya baƙanta min rai domin kuwa yasan akan Ablah kawai zan iya kuka.”

Kansa ya dafe tare da naushin sitiyarin motar.

“Why why! Haidar mtsss bana son nayi mummunan faɗa da kai saboda kai tsagin rayuwata ne bana son mata su shiga tsakanin mu, why Haidar kake neman dole sai na tanka maka.”

Ya juma sosai yana dafe da kansa tamkar zai danna ihu tsabar damuwa da ya masa yawa, motar yaja ya nufi makarantar tasu sai dai a zuciyarsa yana rayawa muddun bai samu Ablah ba to kuwa babu makawa Haidar ne ya sace ta, makarantar yaje babu kowa sai ƴan hostel kawai, ya juma yana bincike cikin makarantar amma bai samu labarin Ablah ba, a wannan lokacin hanunsa har rawa yake, tsabar tashin hankali, bai dawo gida ba sai da ya bincika duk inda yake tunanin Ablah zata iya zuwa amma babu ita da mungun tashin hankali ya dawo gida, Inna Jumma ko da taji babu labarin Ablah hankalinta yayi mungun tashi, take kanta ya hau ciwo, babu wanda bai shiga damuwa ba a cikin gidan sai Aunty Amarya da take dariyar zuci ita a dole burinta ya cika.

“Aminu yanzu yaya zamuyi ko zakaje station ka bada cikiya, Aminu yau bazan iya bacci ba muddun Yarinyar nan bata dawo gidan nan ba, numfashi Al’ameen ya saki shi kansa dauriya yake ji yake tamkar zai faɗi cikin nauyin murya yace.

“Inna babu wani station da zanje Haidar nake zargi da satar Ablah saboda ya baƙanta min rai akan wani dalilinsa na banza.”

“Subahanallah! A’uzubillah! Haba Al’ameen wani irin banzan tunani kake Aliyun kake zargi to Aliyu bazai aikata wannan aikin ba, wai me yake damun kune wacce irin masifa ce wannan da wanne kuke so muji da wannan tashin hankalin ɓatar Ablah ne ko da masifar ku, na rantse da Allah zanci ubanku idan baku kiyayeni ba, idan ku ƴan durun uwa ne to ni ƴar kutumar uwa ne na fiku iskanci, yau naga masifaffu.”

“Haba Inna kina fa ji a gabanki yace sai ya tarwatsa rayuwata cikin awa uku sai nayi kuka da idanuna, to me zai min naji zafi idan ba wannan ba, Inna Jumma Ablah rayuwata ce ina sonta fiye da komai a rayuwata, Haidar da wannan damar zaiyi amfani Saboda ya ƙuntata min, bana neman Haidar da masifa amma na tabbata shine zai tsare Ablah ki fahimce ni Inna.”

“Aminu Haidar bazai aikata haka ba ni na sani, ya furta ne kawai amma bazai iya mugunta ba, dukkan ku nasan halinku nasan abinda zaku iya aikatawa da wanda bazaku iya aikatawa ba, karka masa magana bara na kirasa.”

Tayi maganar tana kiransa a waya ta sanar dashi yazo ya sameta yanzu, haka kuwa akayi bai juma ba yazo, ganin Al’ameen ya sashi haɗa ransa tare da juyawa zai bar falon Inna Jumma tace.

“Oh komawa zakayi saboda ban isa da kai ba ni ba uwarka bace ni ba ubanka bane ko, to ka dawo ko naci ubanka shegu ƴan iska marassa hankali kuna zumuncinki zaku kawo hargitsi ciki.”

Dawowa yayi yana huci tare da zama gefe yana jin kamar ya shaƙo wuyan Al’ameen.

“Oh hura ma kake min to zoka shaƙesa nasan bazai wuce shi kake tunani ba, kunji kunya wallahi kunyi asara akan wata can shasha zaku raba zumuncin ku, bara kuga hankalina ya kwanta sai na nemo ja’irar munafuka naci uwarta.”

Shi dai Al’ameen bai ce komai ba sai Haidar daya zauna ransa ɓace Inna Jumma Cigaba da cewa tayi.

“Aliyu ina ka gane min Ablah?”

Ɗago kansa Haidar yayi cike da rashin fahimta yace.

“Wacce Ablah.?”

“Au tambayata ma kake wacce Ablah, Ablah nawa muke dasu a cikin gidan nan naji tambayar banza ina tambayarka kana tambayata, amsa zaka bani ina Ablah?”

“Hmmm! To ai tambayar taki ce ta ɗaure min kai, ni ina zanga Ablah, gaskiya ban ganta ba.”

Al’ameen ne cike da haushin Haidar na raina musu hankali da zaiyi wai bai ganta ba, idan ba shi ba uban waye zai ɗauketa.

“Ƙarya kakeyi Haidar karka raina mana hankali ma kasan inda take domin kuwa babu mai sace ta idan ba kai ba.”

Ɗago idanunsa Haidar yayi a fusace zaiyi Magana Inna Jumma ta rigasa da cewa.

“Uban waye yace kayi magana kaina tambaya, karna kuma jin bakinka, kai kuma Aliyu ka faɗa min gaskiya ka furta cewa zaka tarwatsa rayuwar ɗan uwanka Aminu, zaka sashi kuka nan da awa uku, ka duba agogon hanunka ka gani yanzu awa Uku harda minti 7 da maganarka sai kuma gashi Ablah tayi ɓatan dabo an nemeta an rasa kuma kaine yake zargi, ya sanar dani Ablah itace rayuwarsa ita yake so ka faɗa min gaskiya ina ka kai Ablah domin kuwa ni kaina Ablah ta dawo babban jigo a rayuwata ina sonta fiye daku domin kuwa na tabbata ita bazata ɓata min rai ba.”

Murmushi mai ciwo Haidar yayi tare da ɗago idanunsa ya dubi Inna Jumma yace.

“Kuma ni kuke zargi da saceta ko hmmm! Akan me zan sace Ablah bayan nasan ba ita bace a gabansa yanzu ƙarya yake miki baya sonta ba ita bace rayuwarsa Nafeesa yake hangowa itace rayuwar tasa, to meyasa nasan wannan zan sace Ablah, hmmm! Inna Jumma koda kuwa itace rayuwar tasa bazan yadda na cutar da Ablah ba kona saceta saboda shi domin kuwa yarinyar mutumiyar kirki ce kuma ta ƙwarai idan na zalunceta Allah bazai barni ba, ni ba maci amana bane irinsa, marar gaskiya shine kullum yake cikin tsarguwa da kuma tunani cewa duk abinda ya samesa da hanun wanda ya cuta, ban ɗauki Ablah ba ku yarda dani ko karku yarda dani wannan itace gaskiyata.”

“Aliyu na yadda da kai babu damuwa jeka”

ƙoƙarin tashi Haidar yayi yaji muryar Al’ameen ta daki kunnen sa.

“Haidar nasan ƙarya kake Ablah tana…”

 Marin da Inna Jumma ta daukesa da shine ya hanasa ƙarisa maganar da yayi niyya.

“Nace karna kuma jin maganar ka shine saboda ka rainani bara kayi to ko ubanka Amadu bai isa ina magana yana magana ba, ko na hanasa magana, dole zaiyi shuru har sai na basa umarni bare kuma kai ɗan da ya haifa, na yadda Aliyu bashi ya ɗauki Ablah ba ka tashi kaje ofishin ƴan sanda ka bada report, muma mu cigaba da nema sai ko da wasa karka sanar da mahaifiyarta abinda yake faruwa akwai aminiyarta a unguwarsu Hafsa kaje maza ka duba ko taje wajenta.”

Haidar bakinsa ya taɓe tare da saka kansa ya fice shima Al’ameen ɗin cike da takaici da damuwa ya fita, unguwar Durmi yaje ya samu Hafsa inda take sanar dashi rabonta da Ablah takai sati biyu, sai ko jiya da daddare sunyi waya, ita kanta hankalinta ya tashi tare suka tafi da Al’ameen duk inda itama take tunanin za’a iya samun Ablah amma ina babu ita babu alamunta, dole tasa Al’ameen kiran Dpo ya sanar dashi tare da tura masa pictures ɗin ta, har ƙofar gida ya sauƙe Hafsa sai dai ya roketa da karta sanar da Umma abinda yake faruwa.

Koda ya dawo gida Inna Jumma na kwance hawan jininta ya tashi, doctor aka kira ya gwada bf ɗinta ya samu ya hau sosai, shi kansa Al’ameen ji yake a wannan lokacin da za’a gwada sa za’a samesa da hawan jinin, rarrashin Inna Jumma da ban baki suka dinga yi, Aunty Amarya suna zaune taji wayarta yayi ringin dubawa tayi Hajiya Mansura, da kallo tabi Al’ameen da Inna Jumma sai Maimu dake zaune da Afnan gefen bed din Inna Jumma, tashi tayi tare da fita tana kara wayar a kunnenta.

“Ina jinki.”

“Akwai matsala fa Amarya Babba ma kaina ya kulle yanzu ajabo ya kirani yake sanar dani basu suka ɗauki Yarinyar ba, yace kwatakwata sun duba basu ganta ba.”

Wani irin razana Aunty Amarya tayi tare da zaro idanunta tace.

“Whattttttt! To waya ɗauketa ina taje har yanzu fa bata dawo gidan nan ba, anyi neman ba’a ganta ba duk inda ake tunanin zataje anje babu ita, abun tambayar nan ina take.?”

“Amma amarya bakya tunanin cewa Haidar ne ya sace ta.”

“Hmmm! Mansura wannan lamarin akwai sarƙaƙiya a ciki domin kuwa zai iya yiwuwa Haidar ne ya saceta amma yace shi ba shi bane.”

“Amarya Haidar zai kasance shine ya saceta saboda Al’ameen tunda kinga ta bayyana Al’ameen yana son Ablah shi kuma Haidar akwai fansa a ransa, to amma meyasa Haidar yake zargin Al’ameen da fashin budurwarsa, gashi kuma shi bisa alamu Ablah ce a ransa ba ita Nafeesa take ko waye ba, Tabbas wannan Yarinyar Nafeesa tana da manufa a ranta idan har tunanina yazo dai-dai lissafi na ya tafi akan tsari ita ke bibiyar Al’ameen sannan take son rabuwa da Haidar saboda dalili ɗaya tayi bincike Al’ameen Mutum ne mai dukiyar gaske ga tasa gata mahaifinsa, Saboda wannan dukiyar take son shiga jikinsa, shiyasa tayi amfani da wannan damar ta shiga tsakanin su, Tabbas idan ba Haidar bane ya ɗauki Ablah to Nafeesa ce, lallai akwai babban matsala ta shigo gonar min domin kuwa tana harin abinda muka juma muna yaƙi akansa, kuma idan mukayi wasa zata zo ta kwashe kuɗaɗen cikin sauƙi ta barmu da ciwon zuciya, a yanzu aiki ne ya ƙaru mana lallai muna buƙatar nunawa wannan Yarinyar ita ƙaramar shegiya ce.”

Jikin Aunty Amarya rawa ya hau yi Cikin tashin hankali tace.

“Na shiga uku Mansura idan har na rasa waɗannan dukiyar wallahi zanyi hauka yanzu meye mafita nayi tunanin Ablah ce kawai matsalarmu a yanzu.”

“Hmmm! Tabbas Ablah matsalarmu ce amma ƙaramar matsala Saboda ita idanunta ba akan dukiyar yake ba sam bata da son abun duniya ita burinta kare rayuwarsu, Nafeesa itace babban matsalar mu, abun yi yanzu shine zan binciko wacece Nafeesan sannan idanma itace ta sace Ablah duk zan gano ki bani nan da awa 24 karki damu zamuyi maganin matsalar.”

Numfashi Aunty Amarya ta saki cike da tashin hankali dukiyar da ta saka duk wani burin mafarkinta akai shine wata ke ƙoƙarin kawo mata hari numfashi ta saki tare da cewa.

“Shikenan sai munyi waya.”

Tayi Maganar suna katse wayar juyawa zatayi sai taga Al’ameen na ƙoƙarin fitowa daga bedroom ɗin Inna Jumma, cikin fuskar tausayi tace.

“Inna tana cikin damuwa yanzu Al’ameen ya zamuyi idan ba’a ga yarinyar nan ba, kar sunan Familyn ya ɓaci shi nake tsoro duniya tayi zargin mune muka salwan…”

Hanu ya ɗaga mata cikin damuwa yace.

“Ya isa haka Aunty.”

Daga haka bai ƙara cewa komai ba yabi gefenta ya shige, itama cike da tashin hankali ta shiga bedroom ɗin ta.

Al’ameen Tunda ya shiga bedroom ɗinsa cikin tashin hankali yake da damuwa ko wanka ya gagara yi kwanciya yayi yana dafe kansa hawaye ne ya zubo daga cikin idanunsa Tabbas shi yasan Haidar ne ya ɗauki Ablah amma gashi bashi da iko da ƙarfin da zai iya ƙwaco ta, da wannan damuwar Al’ameen ya kwana.

Can part ɗin su Haidar kuwa Momma ganin Rufaida bata dawo ba ya sata kiran wayarta anan take sanar da ita tana family hause ɗin su Auntyn ta, sosai Momma ta mata faɗa meyasa bata sanar da ita ba zata tafi, ita Rufaida haƙuri kawai take bawa Momma daƙyar ta samu ta sauƙo.

Washegari da safe ma cikin tashin hankali suka tashi, babu wanda ya iya breakfast, hatta Inna Jumma ita kamma tafi kowa damuwa, Al’ameen cikin shiri ya fito cike da sanyin jiki, yace musu zaije statin yaji yadda aka kwana, fatan alheri suka masa kafin yasa kai ya fice motarsa ya hau, fuskarsa a haɗe yaja yazo dai-dai first get ɗin Estate ɗin yaga motar Abbas ta danno cikin Estate ɗin wanda aka mata rubutu a bayanta da Mayan harufa *A I B* duk inda yaga motar Abbas yana ganewa.

“ABBAS ISA ABBA meya kawosa gidan nan.”?

Al’ameen yayi maganar cike da mamaki domin kuwa baiga dalilin da zai kawosa cikin Estate ɗin su ba taran gaban motar tasa yayi da tasa motar, murmushi Abbas dake cikin motar yayi domin kuwa yasan Al’ameen ne kawai zai masa haka duban Ablah dake gefensa yayi tare da fitowa daga cikin motar shima Al’ameen a zuciye ya fito ya tsaya tare da sanya hanunsa cikin aljihu, still dai murmushi Abbas yake hanu yasa ya buɗewa Ablah mota, fitowa tayi wanda ganinta cikin motar Abbas yasa Al’ameen razana ya zaro idanunsa, gyara tsayuwarsa Abbas yayi tare da cewa.

“Ka tsorata ko, karfa ka damu ban furta mata komai ba, kuma bana da niyyar furta mata duk da nasamu damar hakan, marar gaskiya gumi yake koda kuwa a cikin ruwa yake, Malam AL’AMEEN AHMAD GIWA ga ajiyar gidanku na dawo muku da ita.”

Yayi maganar tare da sakin dariya, shima Al’ameen dariyar yayi tare da furta.

“Ka kyauta daka dawo da ita domin kuwa daka bari na gano tana hanunka da sai Nigeria ta maka zafi, wato dai shi ƙasƙantaccen dabba baya taɓa gane tazarar sa tsakanin sa da sarkin dawa, hmmm!

Wai mutumin banza shine yake cewa mutumin kirki marar gaskiya wannan shine banbancin ɗan babban gida da kuma ɗan ƙaramin gida.”

Ablah zaro idanunta tayi tana kallonsu cike da mamakin meye a tsakanin su…

<< Aminaina Ko Ita 46Aminaina Ko Ita 50 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×