Skip to content
Part 42 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Dariya Abbas ya saka tare da cewa.

“Gaskiya dole zakayi proud da cewa Nigeria zata min zafi, Saboda kana ɗan wakilin Nigeria na ƙasar American, wow hakanma yayi amma karka manta da cewa ni ɗan minista ne mahaifinka baifi nawa matsayi ba, duk inda zaka taka nima ina da himmar takasa, baka da zarrar nuna min ƙarfin iko ka sani kaima kuma kasan waye Abbas.”

Yayi maganar yana shigewa cikin motar sa tare da miƙowa Ablah wata leda ƴar madaidaiciya ta glass ɗin motar Ablah hanu tasa zata amsa Al’ameen ya dakatar da ita.

“Karki amsa domin kuwa bashi da arzikin da zai baki kyauta, Abbas ka fara shiga gonata kayi ƙoƙarin fita da ƙafarka kafin na girbeka.”

Murmushi yayi tare da cewa.

“Indai wannan ne hanyar taka to kuwa zaka girbeni karka manta sai gona tayi kyau ake fara tunanin girbi.”

“Ɗan murmushi Al’ameen yayi yana cije bakinsa tare da cewa Ablah.

“Cewa nayi kibar wajen ko bakiji bane?”

Juyowa Ablah tayi ta dubi Al’ameen murmushi ta ɗan saki tare da cewa.

“Wannan faɗan tsakanin ku ne, ni babu ruwana sannan kuma komai dukiyar mutum baifi ƙarfin amsar kyauta a hanun talakansa ba, bai kamata saboda kana gaba da Mutum ba kace sai lallai wanda ya shafeka shima yayi gaba da maƙiyinka, karka manta maƙiyi kan juyewa ya dawo masoyi haka kuma shima masoyi kan iya juyewa ya dawo maƙiyi, shiyasa ba’a zafafa ƙiyayya da kuma Soyayya gudun juyewa, Abbas ya taimakeni ya ceci rayuwata bazan manta da hakan ba, dole na gode masa kuma na girmamasa, kaima ya kamata ka gode masa bisa taimakona da yayi, bana taɓa tozarta wanda ya min alkairi wannan ɗabiata ce kayi hkr zan amshi kyautarsa badan baka isa dani ba, ka isa dani harma kafi sai dai zan amsa ne saboda duba ga alkairinsa gareni.”

Tayi maganar tana sanya hannu ta amsa murmushi Abbas ya mata tare da kanne mata idonsa Al’ameen bakinsa ya cije cike da ɓacin rai ya juyar da kansa gefe, Ablah cewa Abbas tayi.

“Na gode sosai da taimakon rayuwata da kayi da badan kai ba da yanzu bansan halin da nake ciki ba nida mahaifiyata, sai dai karka manta da alƙawarin da kamin na cewa zaka sanar dani yacce akayi kake bibiyar su amarya, hmmm! Na juma banga mutum mai kyakkyawan hali ba irinka ina sake gode maka.”

Murmushi ya sakar mata tare da cewa.

“Bazan manta da alƙawarin nan ba komai jumawa nasan dole zan sanar miki ko ban sanar dake zaki sani, a cikin kyautar dana miki akwai waya a ciki kisa chaji zan nemeki.”

Kanta ta kaɗa tace.

“Thanks for Care.”

Murmushi ya sakar mata sannan yaja motarsa yabar wajen juyowa tayi taga Al’ameen yayi gaba cikin ɓacin rai da ɗan gudu ta isoshi tare da cewa.

  “Haba rayuwata wai fushi zakayi dani akan wannan ƴar matsalar, nifa Abbas taimakona yayi meyasa zakace na wulaƙanta sa bayan shi yamin alkairi.”

Tsayawa yayi jikin bishiyar umbrella yana ƙare mata kallo cike da tuhuma murmushi tayi tace

“Wannan kallon naka yana tsoratani, wai menene haka bana son kana sauya min fuska, hankalina tashi yake.”

“Dear ina kika kwana a kuma ina kika haɗu da Abbas?”

Tambayar da ya jefa mata kenan fuskarsa a haɗe alamun babu wasa.

Shuru Ablah tayi tana kallon sa domin kuwa bata son sanar dashi dalilin da yasa Abbas ya taimaketa ko ta faɗa masa Aunty Amarya tasa a saceta bazai yadda ba saboda sun amince da ita sun bata dukkan yardarsu, muryar sa taji yace.

“Na ce a ina kika kwana meya haɗaki da Abbas?”

Idanunta ta runtse tare da cewa.

“Taimakona yayi kuma a gidan sa na kwana sai dai shi bai kwana a gidan ba da ƴar aikinsa muka kwana.”

Dafe kansa yayi cike da kishi yace.

“Wannan malalacin ne zaiyi taimako kinsan waye Abbas kuwa, mtsss abun takaici wai a gidansa kika kwana, me ya faru dake wanda Abbas ya taimakeki sannan meyasa zaki kwana a gidan namiji gardi wanda ba muharraminki ba ba kuma mata yake dashi a gidan ba, kinsan haɗarin hakan kuwa koda ke kin yadda da kanki wani ya ganki kin fito daga gidan wani kallo zai miki daban karki manta yanzu an daina kiwon dabba mutum ake kiwo, duk inda ka juya idanun mutane yana kanka.”

Numfashi ta saki itama cike da damuwar domin kuwa taga alamar Al’ameen ya ɗauki zafi da yawa, cewa tayi.

“Wasu ne suka taho da mota zasu sace ni,ina gudu suna bina, nayi nisa da gudu harna fara gajiya sai naga motar Abbas ta tsaya a gefena ya buɗe min motar ni kuma ganin bani da mafita shiyasa kawai na shiga, ya kaini gidansa cikin karramawa ba tare daya cutar dani ba, gudun ko suna bibiyata yasa yace na bari har sai gobe kafin na dawo gida wannan shine taimakon da ya min da kuma dalilin da yasa na kwana a gidan sa.”

“Hmmm! Mtss! Abbas kenan maciji baka ramin kanka sai na wani shikenan muje ciki.”

Cike da alamar tambaya Ablah tace.

“Ban gane maciji baka ramin kanka ba, wai meye tsakanin ku da Abbas ne kam da kowa ke kushe kowa?”

Murmushi Al’ameen ya sakar mata cikin kau da zancen yace.

“Ablah kinsan yadda na damu dake kuwa a rayuwata, hankalina ya tashi jiya na kwana banyi bacci ba, ji nake tamkar zuciyata zata bar ƙirjina, bana son kiyi nisa da rayuwata domin kuwa ruhina haɗe yake da naki, kece bugun numfashi na, ina sonki fiye da komai a rayuwata kece komai na, kece ƙwarin gwiwwa ta, idan na kallaki sai naga kamar ni kaɗai Allah ya yiwa baiwar samun mace ta gari, ranar da kika zamo mallakina ranar bansan wani irin farin ciki bane zai ziyarceni i love You Ablah.”

Murmushi take ta zuba masa idanu ita kanta jin Soyayyarsa yana ratsa jikinta, Al’ameen ya zamo numfashin ta, bata jin zata iya rayuwa babu shi, murmushi ta saki cikin sanyin murya ta fara magana wanda bata taɓa zaton zata iya furta su wa ɗa namiji ba.

“A yayin da na zamo bugun numfashin ka,ni rayuwata ka zamo kaine jijiyoyin da suke riƙe dukkan gaɓɓan jikina, JININA yana gudu ne bisa kulawar wannan jijiyoyin da ka riƙe, na damu da kai damuwar da bazan iya jure rashinka ba, yaya Al’ameen yauce rana ta farko da zan furta maka ina ƙaunarka kuma ina begenka, i love You so much, ka zamo gatana ka riƙeni bisa amana kamin alƙawarin bazaka gujeni komai rintsi, idan na rasaka zan iya hauka ina sonka.”

“Idan har zan gujeki to tabbas ba ruhina bane a jikina sai dai idan gangar jikin ne babu ruhina muddun ruhina yana jikina to Tabbas bazan taɓa guje miki ba, zan rayu da ke duk wahala duk daɗi, bazan yarda naci amanarki ba, bazan zalunce ki ba, na miki alƙawari bazan taɓa juya miki baya ba, idan har na cuceki nasan Allah bazai barni ba, ina sonki ƴar budurwata kyakkyawa.”

Ya ƙarisa Maganar ta sigar zolaya murmushi Ablah tayi tare da cewa.

“Nima ina sonka ɗan saurayina kyakkyawa, kaga ina Inna Jumma na nasan hankalinta ya tashi.”

Dariya Al’ameen yayi tare da cewa.

“Ai kuwa kin ƙwace mana Inna Jumma domin kuwa tafi sonki fiye da kowa, har hawan jininta ne ya tashi saboda ba’a ganki ba cewa fa tayi wai kin fimu.”

Bakinta Ablah ta toshe tana dariya tace,

“Allah sarki uwata Inna bara kaga.”

Tayi maganar tana rugawa da gudu ta nufi part ɗin, Al’ameen da idanu ya bita yana sakin murmushi sai yanzu ya samu sukuni yaji hankalinsa ya fara kwanciya ganin Ablah ta dawo cikin ƙoshin lafiya sai dai yana buƙatar saitawa Abbas hanya domin kuwa bazai taɓa yadda su haɗa gona ɗaya ba.

Papa dake tafe yana waya cikin sauri da alamu wayar da yake mai mahimmanci ne, bangajesa tayi ba tare da ta sani ba wayarce ta faɗi ƙasa, turus ta tsaya tare da zaro idanunta cike da tsoro a mungun ɓacin rai Papa ke duban wayar dake yashe a ƙasa, sunkuyawa tayi jikinta na rawa ta saka hannu ta ɗago wayar gabaki ɗaya wayar screen ɗin ta ya fashe, idan banda rawa babu abinda jikin Ablah keyi cike da tsoro ta ɗago, shi kuwa Papa takaici da haushi duk ya ishesa wannan wani irin rashin hankali ne Mutum zai taho a guje, a fusace ya ɗago da niyar yiwa Ablah masifa suna haɗa idanu Papa ya gagara furta koda kalma ɗaya ce, da kallo yake binta wani irin abune ya tsirga masa daga yatsar ƙafarsa har ƙwaƙwalwarsa, kallon sani yake yiwa fuskar sai dai ya rasa inda ya santa, wani irin ƙaunar Yarinyar gami da tausayinta yaji ya shigesa lokaci ɗaya, ji yake tamkar yasan mai kama da ita, shuru yayi kawai yana kallonta, Ablah cikin sanyi jiki da tsoro itama take tsaye dai-dai isowar Al’ameen wajen, shima tsayawa yayi yana kallon hanun Ablah ko bai tambaya ba yasan waya ta fasa mishi.

“Ablah garin yaya kika yiwa Papa ɓarna haka.”

Cikin raurau da murya Ablah tace.

“Na taho da gudu ne ban sani ba shine na bigesa wayar ta faɗi, ba da sanina bane dan Allah Baba kayi hkr.”

Tayi Maganar hawaye na zubowa daga idanunta murmushi Papa yayi madadin yayi faɗa yace.

“Ba komai ƴata nasan bazaki bigeni da gangan ba karki damu, ban ɗauki hakan wani abu ba.”

Murmushi tayi cike da jin daɗi itama ta ɗago ta kallesa cike da jin daɗi tace.

“Na gode Baba ga nan wayar.”

Tayi Maganar tana miƙa masa wayar amsa yayi yana murmushi har yanzu kallonta yakeyi shigewa tayi abinta tana share hawayen ta, Al’ameen shima murmushin yayi Papa ne yace.

“Al’ameen ya akayi sai famar murmushi kake haka?”

Still murmushin ya kuma saki tare da cewa.

“Babu amm wayar ta fashe ko zaka kawo sim card ɗin naje na saya maka wata wayar sai na biyo Office ɗinku na kawo maka.”

“A’a ka barshi kawai nabi na saya sai na wuce.”

“To shikenan adawo lafiya Allah ya tsare .”

Da ameen ya amsa yana murmushi ya fice, Al’ameen shima shigewa yayi.

Tazo daidai step sukaci karo da Aunty Amarya, murmushi Ablah ta saki yayin da Aunty Amarya ta saki baki da hanci tana kallon Ablah cikin mamaki tace.

“Kece!”

Dariya Ablah tayi tare da ɗaga mata kai tace.

“Gashi kuwa kina kallona, kinyi mamakin ya akayi na tsira ko, dafa so kikayi a kira waya ace azo asibiti ankawo ƴar aikin gidan Ahmad Giwa an mata fyaɗe, haka kikaso ko, to Allah ya bai yarda ba, kinga Amarya nake ƙoƙarin kare rayuwar wasu ma bare kuma rayuwata, bazaki iya aikata komai a kaina ba naci dubu sai ceto nan gani nan bari.?”

A razane Aunty Amarya ta zaro idanunta domin kuwa maganganun Ablah sun kiɗimata a ina tasan za’a mata fyaɗe bayan daga ita sai Mansura sai waɗanda suka bawa aikin ne kawai suka sani Kuma tasan kaf cikin su babu mai cin amanar ta ya fitar mata da sirrinta, cike da mungun mamaki tace.

“Waya sanar dake nasa a miki a fyaɗe?”

“Hmmm! Ni kamar aljana nake duk abinda kuke ina sane dashi shiyasa nake faɗa miki ƙarshen ki yazo domin kuwa kin kusa tozarta irinku mutuwar wulaƙanci ne ya dace daku baku cancanci afuwa ko sassauci ba domin kuwa masifa ce ku a duniya.”

Dariya Aunty Amarya tasa tana nuna Ablah da yatsa tace

“Kai! Yaro man kaza, Aljana kike ko to meyasa baki gane ba lokacin da zan kashe Ummi, harma kika gubar da hanunki a matsayin ki na Aljana ai kamata kisan komai kuma ki dakatar amma kin kasa fahimta, ban sani ba kuma ko kin gane kawai kema Ummin ta dameki ne kina buƙatar ta sheƙa shiyasa kawai kika bata gubar.”

Tayi maganar tana kallon Ablah cike da murmushi, shuru Ablah tayi itama tana kallonta cike da tsana sunfi minti 8 a haka Ablah ta buɗe baki kenan zatayi magana taji muryar Al’ameen.

“Ablah ku bani hanya zan shige.”

A mungun razane dukkan su suka juyo suna kallonsa yana tsaye ya harɗe hanunsa a ƙirji, Aunty Amarya ƙirjinta dukan uku uku yake kardai Al’ameen yaji abinda suke faɗi, Ablah ɗan murmushi ta saki tare da cewa.

“Yaya Al’ameen yaushe kazo nan?”

Numfashi ya saki tare da sakar mata murmushi yace.

“Bazaku san yaushe nazo ba saboda kunyi nisa da zance kun tare hanya naga alamar baku da niyar kaucewa shiyasa na nemi parmission ku bani hanya.”

AUNTY Amarya ce tace.

“Al’ameen amm…”

Hanu ya ɗaga mata tare da cewa.

“Hanya kawai nace ku bani.”

Matsawa sukayi gefe yasa kai ya shige da kallo suka bisa har sai da ya shige cikin bedroom ɗinsa, aunty Amarya a tsorace tace.

“Me kika fahimta kardai Al’ameen yaji abinda muke faɗi.?”

Dariya Ablah tasa tare da cewa.

“Zanso ace yaji domin da sai nafi kowa murna, yanzu ma ki saka a ranki yaji sai ki sauya taku alamun rashin Nasara sun fara tabbata a gareki lallai ki fara gudun tsira domin kuwa randa kika shiga hanu HMMM! Kinsan sauran.”

Tayi Maganar tare da juyawa zata shige bedroom ɗin Inna Jumma taji muryar Aunty Amarya.

“Hmmm! Lallai kuwa tare zamuyi gudun tsira wataƙil ma ke ki fini gudu domin kuwa ke rayuwarki ce take cikin hatsari, Mrs Romio ba, Al’ameen shine wanda kuke Soyayya ba, to buɗe kunnenki kiji zaki sha mamaki domin kuwa zaki tsanesa saboda mungun abunda zai miki zakice na faɗa miki Namiji zai zamo miki mungun ƙayar da zata miki sukar da bazai taɓa warkewa ba, ki saka wannan a ranki.”

Dariya Ablah tasa har sai da dimple ɗinta ya loɓa tace.

“Hmmm! To shikenan Allah ya kaimu lokacin.”

Tayi Maganar tana shigewa bedroom ɗin Inna Jumma.

Aunty Amarya gagara Magana tayi har Ablah tabar wajen sosai ta tsorata sai dai bata tunanin yaji domin kuwa yadda Al’ameen yake da zuciya bazaiji wannan maganar ba yayi shuru, lallai baiji ba.

Tana shiga ta samu Inna Jumma zaune tayi shuru alamun tana cikin damuwa murmushi Ablah tayi tare da zama kusa da ita ta dafa kafaɗar Inna Jumma.

“Ki daina tunani Inna gani na dawo, ina da yaƙinin babu wani mungun abu da zai sameni ina tare da kariyar ubangiji, addu’ar ku kuma tana tare dani ki godewa Allah domin an kawo min hari kuma ya kareni.”

Juyowa Inna Jumma tayi tare da sakin murmushi ta rungume Ablah cikin farin ciki tace .

“Alhamdulillah! Bi ni’imatul Islam, na gode Allah daya kareki, Ablah jikinki nake tamkar jinina meya faru dake.”?

Murmushi Ablah ta saki tare da sanar da Inna Jumma abunda ya faru sai dai bata sanar da ita fyaɗe ake ƙoƙarin mata ba, sun juma sosai suna hira da Inna Jumma kafin ta koma bedroom ɗinta wanka tayi tare da zama ta juye kyautar da Abbas ya bata wayace ƙirar iPhone 11 mai kyawun gaske ash color, sai sim card a cikin kwalin wayar tare da wani kwalin buɗesa tayi taga zoben azurfa mai kyawun gaske, an masa ado da love sawa tayi a yatsarta sai rafar kuɗi 100k katifarta ta ɗaga ta ijiye kuɗin tare da jona wayar a chaji.

Wayarta ƙarama ta kunna sai kace wanda ake jira ta kunna wayar kiran Hafsa ya shigo dariya Ablah tayi tare da ɗagawa ta kara a kunnenta daga can Hafsa tace.

“Malama kin tsorata mu ina kika shiga.?”

Dariya Ablah tasa tare da bata labarin abinda ke faruwa ta ƙarishe maganar da cewa.

“Allah fa ya taimaki rayuwata ƙawata na rasa me Wannan matar take nema a wajena.”

“Hmmm! Babbar Magana, ƙawata ki ƙara taka tsantsan da kula domin kuwa ni ina tsoron sharrin wannan matar, amma kinsan meye zanzo muyi magana babu kuɗi yanzu a wayata naira hamsin ce sun fara min warning.”

“Okay to shikenan sai kinzo ki gaishe da mama da Ummana.”

Da zasuji hafsa ta amsa tare da katse kiran.

Bayan Kwana Uku

Tunda wannan abun ya Faru tsakanin Haidar da Al’ameen kwatakwata Haidar yaƙi yadda su haɗu da Al’ameen kullum Haidar yana cikin damuwa Momma Kanta har damuwar Haidar ya fara damunta duk da bata san abinda ke faruwa ba, babu wanda ya sanar mata ita kanta Inna Jumma tayi shuru ne ta zuba musu idanu taga iya gudun ruwansu sannan tasa a ranta zata kira Daddy ya dawo gida domin haɗa Family meeting akansu.

Zaune suke gaban bokan sun tanƙwashe ƙafa dariya marar daɗin sauraro yayi tare da cewa.

“Nasan abinda ke tafe daku kunzo ne akan wani yaro mai taurin kai ko, uban yaron babban ɗan siyasa ne kuna son a dawo da hankalin yaron kanta.”

Kanta Mama ta ɗaga da sauri tace.

“Ehhh ehhh hakane.”

“Za’ayi aiki kuma zai sota zai dawo gareta sai yadda tayi dasu sai dai akwai waɗanda yanzu idanunsu yake kanta Matar Uban yaron da kuma ƙawarta, aikin ku babban aiki ne sai dai buƙata zata biya zamu kawar da idanun matar Uban nasu daga kanta sannan zamu rufe bakin duk waɗanda zasu kawo mana tseko, dan haka aikinki zai ja kuɗi.”

Mamace tace.

“Boka damu bamu da matsala da kuɗi ko nawa ne zamu kashe muddun buƙata zata biya.”

“Buƙata zata biya yanzu kafin mu fara aikin muna son kuje ku kawo mana abu uku sannan zan fara ai dasu, zaki kawo min ƙasar takalminsa inda ya taka wannan ƙasar zaki ɗiba ki kawo min, sannan da ƙasar ƙofar gidan su, sai kuma guragurbin ƙwai na Kaza, ki tabbatar an samu nan da kwana uku idan baku samu ba karku dawo nan domin aikin ku bazai yiwu babu su ba, ku tashi kuje kar wanda ya ƙara magana.”

Tashi sukayi suka fita da baya baya bayan sun fita ne suka tari adaidaita sahu.

Sunyi nisa da tafiya Mama ta dubi Nafeesa tare da cewa.

“Nafi kina ganin kuwa za’a samu waɗannan abinda Boka ya tambaya.”

Murmushi Nafeesa tayi tare da cewa.

“Za’a samu Mama abubuwa masu sauƙi ya tambaya ni kuwa zan kawo miki su daga gobe zuwa jibi.”

“Shikenan Allah yasa mu dace.”

Da ameen Nafeesa ta amsa ko da suka iso ƙofar gidan su motar Haidar ta hango tsaye, kallon Mama tayi tare da cewa.

“Kin gansa can nacaccen.”

Dariya mama tayi tare da cewa.

“Barni dashi ya kawo kansa lokacin da ya dace kuɗin aikin ma zamu iya samu a wajensa ke dai shige gida ni bara naje nayi magana dashi.”

Bakinta Nafeesa ta taɓe suka bawa mai adaidaita kuɗinsa Haidar tunda Nafeesa ta taho yake kallonta tamkar zai haɗiyeta ya rasa wani irin SO yake mata kullum Soyayyarta ninmkuwa yake a zuciyarsa, kallon banza ta jefe masa tare da jan tsuka ta shige.

Mama kuwa wajensa ta nufo tare da Sallama cike da mutuntawa Haidar ya sunkuya har ƙasa ya gaisheta.

“Haidar kaine tafe dama kuwa kamar kasan ina neman ka, jiya Amnat take sanar dani abinda yake faruwa tsakanin ka da Nafeesa, gaskiya banji daɗin abinda ya faru ba, ai ko ya halinka yake bai kamata Nafeesa ta rabu dakai ba batare da bincike ba, ni nasan sharri ɗan uwanka ya maka ba haka halinka yake ba, ƴan uwan yanzu ne da abokan yanzu duk basu da Amana wai rayuwa tayi lalacewar da ɗan uwanka shine zai tozarta ka, kayi hkr nayi magana da Nafeesa ina ƙoƙarin ganar da ita gaskiya kuma nasan zata fahimta insha Allah muddun nice mahaifiyar Nafeesa bata da wani mijin idan ba kai ba kayi hkr dan Allah ba’a kyauta maka ba sai dai duk laifin ɗan uwanka ne.

“Na sani Mama Nafeesa bazata gujeni haka kawai ba, shiyasa na kasa rabuwa da ita kuma insha Allah nasan zata fahimce ni ta dawo gareni, Al’ameen yamin abinda ko maƙiyina bazai min shiba, amma bazan barsa ba dole sai na ɗauki fansa na gode da ƙoƙarin ki gareni Mama.”

Murmushi mama tayi tare da cewa.

“Shikenan to Haidar ni bara na shige.”

Harta juya zata tafi Haidar yace.

“Mama ɗan tsaya dan Allah.”

Yayi Maganar yana buɗe motar sa rafar kuɗi ya dauko guda biyu ya miƙa mata, amsa tayi tana sanya masa albarka, tare da shigewa cikin gida.

Haidar ya ɗan juma zaune ƙofar gidan ko Nafeesa zata fito sai dai yaji shuru bata fito ba kusan awa biyu hakanne ya sashi fitar da ran zata fito yaja motarsa yabar wajen.

<< Aminaina Ko Ita 41Aminaina Ko Ita 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×