Skip to content
Part 35 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Tayi maganar tana katse kiran, tare da jan tsuka.

“Aikin banza sai shegen mungun kira, to na fara gajiya da kai gara kawai kayi gaba, yau naga shegen naci na fara gajiya da kai. Al’ameen kawai nake buƙata a cikin rayuwata kuma dole ya zo cikin rayuwata a kwanaki kaɗan.”

Wayar ta ijiye tare da juyawa zata fita Mama ta gani tsaye a gabanta ta harɗe hanu tare da ƙura mata idanu tana mata kallon zargi, numfashi ta sauƙe tare da cewa.

“Nafeesa Haidar ɗin da yake rufa mana asiri kike ƙoƙarin korarsa, so kike ki tona mana asiri, tunda wannan yaron fa ya shigo rayuwarmu kakar mu ta yanke saƙa, muka manta da damuwar rashin yimana da ubanku yake gwada mana shine saboda yanzu tsiyarki tazo gaban goshin ki bara ki tona mana asiri ki koresa mu rasa me bamu ke ga shegiya marar mutunci ko, waye kika samu wanda zaifi ɗan Ahmad Giwa kuɗi?”

Murmushi Nafeesa ta saki tare da neman waje ta zauna tana fuskantar Mama tace.

“Ƙwarai kuwa Mama korar Haidar zanyi domin kuwa bani da mafitar da ta wuce wannan, saboda na samu wanda yafi Haidar kuɗi kuma baya buƙatar kishiya, gashi kuma aurensa zanyi shiyasa zan cire Haidar daga rayuwata zan nemo Soyayyar Al’ameen billion Naira Wanda daga ni har ke zamuyi bankwana da talauci, zamu taka kuɗi harma muyi sarƙa dasu idan munga dama kamar yadda kike burin zuwa American Mama daga zarar na Auri Al’ameen ko sati bazanyi ba zaki ƙetara American kinga laifina saboda na kori Haidar saboda wanda zai yaye mana talauci.”

Dariya Mama tasa tare da tahowa ta zauna gefen Nafeesa tace.

“Kaga ƴar albarka mai ƙashin arziki, ai tun farko da kince min kin samu idanun duniya ne, da bazan ɓata bakina wajen miki faɗa ba, ai kuwa kinyi dai-dai Haidar ɗin banza sanar dani feenata ɗan gidan waye ne shi kuma sabon kamun namu, kinsan idan masunci yaji ragarsa tayi nauyi a cikin tafki to Allah Allah yake ya fito da wannan ragar yaga mai ya kamo dan haka nima ina son sani wani hamshaqin kika kamo mana da ragarki.”?

Dariya Nafeesa tasa tace.

“Kaga Mamana mai sanin darajar arziki, Mama Al’ameen Ahmad Giwa na samu cikakken ɗa a wajen Ahmad giwa ba ɗan kara ba, *MAGAJIN AHMAD GIWA* wanda zaici gadon ubansa, mama ɗan Ahmad Giwa ne na cikinsa, kin fahimta ai.”?

Murmushi Mama tayi tare da cewa.

“Ƙwarai kuwa na fahimta, ɗan uwan Haidar ɗan Baffan sa, shine kika harbo mana to amma na tambayeki mana ƙwallon da kika wurga masa ta shiga ragar kuwa.?”

“Ina kuwa ta shiga mama sai famar bilinbituwa take filin wasan har yanzu bata harba inda ake buƙata ba, da alamu taurin kai garesa baya fahimtar yaren gwari dole sai mun fassara masa da Hausa ko da turanci kafin ya gane.”

“Ai kuwa zamu fassara masa domin kuwa bazamu zuba idanu muna kallo ba muyi asara, dole wannan ƙwallon ya shiga raga ko da tsiya ko da arziki , idan bokaye da malamai basu ƙare ba, to Tabbas kuwa ƙwallon mu zai faɗa raga.”

“Hakane Mama amma bari tukunna mu jaraba sa’ar mu ni da Jamila idan mun gagara dole mu dawo da yaƙin hanunki saboda abinda ya gagari yaro to bazai gagari Babba ba.”

“Shikenan ɗiyata nasan ma zaku iya, bara naje kitchen naga me wannan marar zuciyar take mana.”

Murmushi Nafeesa tasa tare da ɗagawa Mama kai.

Al’ameen da Sallama ya shiga bedroom ɗin Ablah tana zaune tayi shuru cike da damuwa Inna Jumma da Rufaida sun fita, zama yayi gefe tare da cewa.

“Ya jikin naki?”

Kanta ta ɗago ta kallesa tamkar zatayi kuka tace.

“Da sauƙi kaga abinda nake gudu nace ku maidani gida kuka ƙi gashi ana neman rayuwata akan laifin da banji ba ban gani ba.”

Numfashi Al’ameen ya saki yana kaɗa key ɗinsa yace.

“Banyi zaton akwai wanda zaiyi rashin hankalin nan a gidan nan ba, So koma menene dai kiyi hkr hakan bazai kuma faruwa ba saboda na ɗauki mataki, tun monday ya kamata ace ki fara zuwa school amma hakan bai yiwu ba, ga kuma yanzu an sake samun wata matsala, zan sanar da shugaban school ɗin halin da ake ciki saboda zaki iya kai next week kafin ki fara zuwa, Please bana son ki sanar da mahaifiyarki abinda ya faru saboda bazata ji daɗi ba.”

Kanta Ablah ta kaɗa ta amsa da.

“Shikenan na gode.”

Tayi Maganar a taƙaice miƙewa yayi tare da furta.

“Mun shige office.”

“A dawo lafiya Allah ya tsare.”

Da ameen ya amsa yana fita, baiga Haidar a haraba ba hakanne ya basa tunanin ko dai ya shige Company ne, motarsa ya shiga tare da ja yabar wajen.

Bayan fitar Al’ameen ne Aunty Amarya ta shigo, tare da zama tana saka dariya gami da tafi tare da cewa.

“Na faɗa miki ja dani kuskure ne, amma taurin kanki yasa kike kasa fahimtar haka, kinga abinda ya faru da ke yau, ya kamata ki dawo gareni mu jone har yanzu kina da sauran dama domin kuwa haɗa hanu dani shine kawai zai tseratar da ke daga shiga matsala.”

Kanta Ablah ta ɗaga ta kalli Aunty Amarya tare da cewa.

“Hmmm! Na gwammaci mutuwa da haɗewa da munguwar mace irinki, har abada Ablah baza ta taɓa haɗa kai da Mutum irin ki ba na yarda na shiga ko wacce irin masifa ce da dai na yadda dake.”

Dariya Aunty Amarya ta kuma sawa tare da furta.

“Well jiki magayi, yanzu kuwa zaki fara cin karo da tashin hankalina da masifar da bazaki taɓa iya kauce mata ba, saboda na shirya miki wata babbar kyauta wacce zata tashi da Rayuwarki ta barki ki ƙarasa cikin baƙin ciki da ciwon zuciya.

Kallon banza Ablah ta mata tace.

“Kije kiyi duk abinda kikaga zaki iya amma ki sani bazaki iya min abinda ubangijina bai min ba.”

“Yayi kyau na tabbata zakiyi kuka da idanunki kiji dama baki taɓa haɗuwa dani ba bare mu rayu tare, Ablah ni Amarya na ce miki rayuwarki tana cikin haɗari, kuma nine zan zamo sanadin haɗa wannan hatsarin zakiga masifa iya ganin idanunki harta uwarki sai zuciyarta ya nemi fashewa ki ijiye wannan a zuciyarki.”

Tayi Maganar cikin dariya tare da tashi ta fice da idanu Ablah ta bita harta fita, wayarta ce tayi ringin hanu tasa ta ɗauka tare da karawa a kunnenta, muryar Hafsa taji.

“Ƙawata ya akayi ne, sai yau Allah yasa na samu waya na ɗaura sim card ɗina, ina ta tunanin a wani hali kike ciki.?”

Numfashi Ablah tasa idanunta na ciko da hawaye domin kuwa damuwa ce sosai da kuma baƙin cikin abinda Samira ta mata yake ci mata Zuciya ga tashin hankalin maganganun Aunty Amarya.

“Hafsa nata kiran wayarki bata shiga, na kira Umma itama bata ɗauka ba, kinga Hafsa dan Allah kizo wallahi ina cikin tashin hankali domin kuwa yanzu ma haka kwance nake babu lafiya.”

“innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Subahanallah, Ablah meya sameki ko dai matsala kika kuma samu da wannan Amaryar?”

“Hmmm ke dai Hafsa sai kinzo ki domin kuwa gagarumar matsala ce take kunno min maganar mai tsawo ce.”

“To har kinsa jikina yayi sanyi bana kusa yanzu haka mama ce ta aikeni kasuwa idan na dawo kuma zanyi girki, amma dai insha Allah zuwa Safiya zaki ganni saboda wuni guda yau mama bata nan ba halin na fito.”

Okay to shikenan sai kinzo ki gaishe da Maman.”

Da to Hafsa ta amsa sannan sukayi sallama, tagumi Ablah tasa idanunta na zubar da Hawaye tamkar ta ɗaura hanunta aka ta danna ihu take ji, innalillahi wa’inna ilaihirraji’un shine kawai abinda take furtawa cikin zuciyarta sai dai duk wannan tsoron da takeji bazata bar Aunty Amarya ba dole ta ƙalubalence ta.

Kansa ya kifa a jikin bed ɗinsa damuwa duk ya ishesa yau Companyn ma baya jin zai iya zuwa domin kuwa kansa ke bala’in sara masa maganganun Nafeesa sunyi mungun ɗaga masa hankali itace rayuwar sa kuma ƙwarin gwiwwar sa, to mesa take ƙoƙarin juya masa baya meke shirin faruwa dashi a fili ya furta.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Why Nafeesa why kike ƙoƙarin juyawa zuciyata baya bayan kinsan kece rayuwata rayuwata bazata daidaita ba dole sai da ke a cikinta?”

Kana jin zafi ne a cikin zuciyarka bai kamata kaji haushi ba?”

Yaji muryar Rufaida dake tsaye bakin door ɗin sa hanunta riƙe da tire ɗin abinci, idanunsa daya kaɗa ya sauya kala ya ɗago yana kallon ta ƙarasowa tayi tare da sunkuya ta ijiye masa abincin ta furta.

“Baka fito kayi breakfast ba shine momma tace a kawo maka hmmm! Ashe kuma damuwar abincin zuciyarka ne ya hanaka fitowa okay Allah ya sauwaƙa dama duk wanda ya ƙuntata zuciyar wani ba lallai tasa ta samu sukuni ba, musamman aka samu karya alƙawari.”

Tayi maganar tana miƙewa ta nufi ƙofar fita taji muryar sa.

“Komai lalacewar da nayi ban cancanci ki faɗa min baƙar Magana ba, okay hakan ya nuna min rashin hankalinki kizo ki ɗauki abincin ki bana buƙatar sa, sannan ki sani har abada zuciyata ta Nafeesa ne, koda zan mutu to da Soyayyarta zan koma ga ubangijina. Nafeesa rayuwata ki sani cewa da Soyayyarta ubangijina ya hallici zuciyata, da’ace ina da iko da zuciyata Rufaida da babu wanda ya cancanta naso sama dake ƴar uwata amma kije ki cigaba da faɗa magana yadda ranki yake so.”

Shiru Rufaida tayi jikinta yayi sanyi tabbas so dashe ne daga Ubangiji to meyasa zataji haushinsa saboda ya ƙi sonta Tabbas ya zamo wajibi gareta ta cire Haidar aka zuciyarta saboda ta fahimci Haidar bazai taɓa sonta ba, juyawa tayi ta fice abinta ba tare da tayi Magana ba, da idanu ya bita harta fice, kwanciya yayi tare da yin shuru yana tunani.

Rufaida tana fita bedroom ɗin ta ta shige da gudu tana kuka Momma dake zaune a falon ne ta ɗaga idanu ta kalli Rufaida da ta shige da gudu cikin tashin hankali, kallon Madina Momma tayi tare da cewa.

“Madina baki fuskanci wani abu ba game da Rufaida da Aliyu?”

Numfashi Madina ta sauƙe tare da duban Momma tace.

“Na juma da fahimtar akwai wani abu tsakanin su, domin kuwa ni nasan matsalar da Rufaida take ciki saboda tare nake kwana da ita nake tashi da ita cikin dare takan tashi ta ta kuka akan soyayyar yaya Haidar, har Sallah take tana kuka tana kaiwa ubangijin ta damuwarta, na tausaya mata ƙwarai domin kuwa da alamun shi yaya Haidar baya sonta.”

Shuru Momma tayi tana sauraron Madina sai da ta kai aya sannan tace,

“Ni kaina tun ranar rasuwar Hajiyar Al’ameen zuwan wannan Yarinyar Nafeesan na fuskanci Rufaida tana son Aliyu, amma idan banda rashin hankali irin na Aliyu meye aibun Rufaida cikakkiyar mace mai diri da zati asali da kyau ni ina ganin babu wanda Aliyu ya dace ya aura sama da Rufaida, amma ba komai zan mawa tufkar hanci dole ya bawa ƴar Uwar sa kulawa, domin kuwa itace ta dace da rayuwarsa kuma itace zata zamo surukata.”

“Amma Momma a ganina Soyayya gamon jini ce, babu ruwanta da usuli ko kyau ko dangantaka, tana shiga zuciyar mutum ne da zarar zuciyoyinsu ya haɗu Momma karki ce zaki yiwa yaya Haidar dole a Soyayya ba’a yiwa namiji dole domin kuwa zuciyarsa bata iya jure ƙiyayya mace ne ake mawa dole saboda tana da rauni zata jure zafin ƙiyayya amma banda namiji dan Allah Momma karkiyi dole ki musu addu’a Allah ya haɗa zuciyoyinsu suso junansu ba tare da anyiwa wani dole ba.”

Momma dankwalon Madina tayi tare da cewa”

“Kinci gidan ku, ni zaki faɗawa Soyayya, to Soyayyar taci uwarta dan ubanki mu zamanin mu munsan wani aure Soyayya ne, to ko ni da ubanku ba Aure Soyayya mukayi ba Asali ma ni bansan mahaifinku ba, ina Kaduna yana Abuja iyaye suka haɗa kuma mukayi biyayya muka amsa, gashi yanzu har an haifeku, meyasa mu bamu bijire ba.?”

“Amma ai Momma zamaninku daban da wannan zamanin, yanzu yanayi ya sauy…”

“Rufe min baki karna kuma jin kin min maganar banza, na fiki sanin abinda ya dace da rayuwarku muddun ina numfashi bazan bari Rufaida tasha wahala akan abinda nake da ikon na mallaka mata ba shasha ashe bazaki yi kishin ƴar Uwar kiba, kin bani kunya wallahi.”

“Momma ni fa bawai kishin Rufaida bane bana yi, kawai tausaya mata nake saboda Auren dole masifa ne haƙuri dashi shi yafi alkairi domin ku…”

“Madina tashi ki bani guri!.”

Momma tayi Maganar cikin tsawa tana nunawa Madina hanya ganin ran Momma ya ɓaci yasa Madina tashi tabar wajen Momma miƙewa tayi tare da haurawa ta shiga bedroom ɗin su Rufaida tana kwance ruf fa ciki sai kuka take tirza sam bata kula da shigowar Momma ba, gefenta momma ta zauna tare da ambato sunanta.

“Rufaida!”

Ɗago idanunta tayi ta dubi Momma saurin saka hanu tayi ta goge hawayenta sam bata so ace wani yaga tana wannan kukan ba, kanta ta sunkuyar ƙasa tare da amsawa.

“Na’am!”

“Meya sameki, daga aikenki ki kaiwa yayanku abinci sai ki fito da kuka meya miki wani abun ya miki ko?”

Shuru Rufaida tayi kanta na ƙasa ta girgiza wa Momma kai.

“A’a Momma babu abinda ya min.”

“Babu abinda ya miki kuma kika fito kina kuka, ɗago idanunki ki kalleni ki faɗa min damuwarki nima mahaifiyarki ne bani da bambanci da Auntyn ki, faɗa min menene zan miki maganin matsalarki.?”

“Babu komai fa Momma ba kuka nake ba kaine ke ciwo.”

Murmushi Momma tayi tare da girgiza kanta domin kuwa ta fuskanci Rufaida bazata sanar da ita komai ba, sai dai tunda tasan matsalar zatayi maganinta, da Allah ya sauwaƙa Momma ta yiwa Rufaida tare da tashi ta fita, da bedroom ɗin Haidar zata shiga sai kuma ta fasa ta shige bedroom ɗinta da niyyar sai dare zata zauna dashi.

Shi kuwa Al’ameen sosai yau yayi mamakin rashin zuwan Haidar Company, duk da idan akwai wata damuwar da zata hanasa zuwa yakan sanar masa amma yau kuma shuru, ga ya kashe wayarsa, ya tuntuɓi Faruq ma yace shima bai ga Haidar ba yau, wayar sa da tayi ƙara ya ɗauka tare da sawa a kunnensa.

“Hello ICO nawa ya akayi bincike ya kammala kenan.?”

Daga can ICO yayi dariya tare da cewa.

“Oh bazan kiraka ba kenan har sai na kammala binciken daka sani ko?”

Dariya shima Al’ameen yayi tare da cewa.

“Kaga ijiye wuƙar tell me?”

“Na gama duk wani bincike akan Yarinyar sunanta Nafeesa Abdullahi Jiji, ana amfani da sim card ɗin a unguwar Mai Tama gida mai Number 12.”

Shuru Al’ameen yayi yana tunanin kaman yasan gidan da kuma sunan Yarinyar.

“Okay ba damuwa na gode Ibrahim zan ƙarisa sauran binciken.”

Sun ɗan juma suna hira Kafin suka katse kiran cikin mutunta juna, tunda suka kashe wayar Al’ameen ya shiga cikin tunani domin kuwa Tabbas yasan inda Ibrahim ya kwatanta masa sai dai ya kwanta masa.

“Unguwar Mai Tama gida mai Number 12 Nafeesa Abdullahi Jiji kamar gidan da Haidar ke neman Mata.

Shuru yayi yana tuno maganarsa da Haidar.

“Nafeesa itace rayuwata, na Tabbata zata burgeka idan ka ganta unguwar mai tama take gidan Alh Abdullahi Jiji, kyakkyawa ce tana da tarbiyya.”

Teburin gabansa ya buga da ƙarfi tare da furta.

“Whattttttt!”

<< Aminaina Ko Ita 34Aminaina Ko Ita 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×