Cikin sauri ya isa wajen da Idi driver ya fara cin karo yana yashe a ƙasa ko motsi baya yi, zaro idanunsa Al’ameen yayi tare da nufarsa cikin sauri ya sunkuya yana ɗago hanunsa jin hanun da nauyi ya sashi sakin ajiyar zuciya tare da sunkuyawa ya kai kunnensa ƙirjin Idi jin zuciyarsa na harbawa ya sashi fahimtar suma idi yayi, cikin hanzari ya waiga gefen sa ko zai ga Khairi wayam babu Khairi babu labarin ta, miƙewa yayi ya hau dube dube a wajen bai ganta ba, da sauri ya koma motarsa ya ɗauko ruwan faro ya zo ya watsawa Idi, numfashi ya sauƙe idi tare da buɗe idanunsa a firgice zai ƙwala ƙara Al’ameen yayi saurin saka hanu ya toshe masa baki, yana girgiza masa kai tare da cewa.
“Da sunan Allah ya kamata ka farka bada ihu ba, ina Khairi take.?”
Idi zuru zuru yayi da idanunsa tamkar zai danna ihu ya nunawa Al’ameen gefen hagunsa da yatsa miƙewa Al’ameen yayi tare da bin wajen, Idi da sauri ya tashi yabi bayansa, yayi tafiya mai ɗan nisa a wajen kasancewar wajen kamar jeji yake sabuwar unguwa ce wanda mutane ɗaɗɗaya ke cikinta, A kwance ya hangota wurge school bag ɗin ta na gefe, da sauri ya ƙarisa ya sunkuya a kanta yana ɗagota, jin jikinta duk a sake ya sa Al’ameen saka hanu a hancinta, shuru babu numfashi zaro idanunsa yayi a gigice yana ɗago hanunta lagwab hanun ya faɗi ƙasa.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!!!!! Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!!! Allahu ajirni fil musibati!!! Subahanallah!!!! Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”
Abinda ya dinga maimatawa kenan kasancewar sa mutum mai riƙo da ibada da Tauhidi, mawuyacin abune kaga abinda zai fitar da Al’ameen daga hayyacinsa, wayarsa ya ciro tare da dannawa Haidar kira, ringin ɗaya Haidar ya ɗaga, cikin sanyin jiki yaji muryar Al’ameen.
“Kana ina Haidar.?”
Tambayar kawai daya masa, Haidar jin muryar Al’ameen a sanyaye ne ya sashi fahimtar ba lafiya ba.
“Ina Company lafiya kuwa naji muryar ka a sanyaye.?”
Runtse idanunsa Al’ameen yayi zuciyarsa na ƙuna yace.
“Haidar an kashe Khairi wani ya kashe Khairi ta mutu bata numfashi!!! Khairi ta mutu, kaje police station, ka taho da ƴan sanda nan wajen zoo road sabuwar unguwa da ake ginawa ina nan da gawar ta sannan ka kira Papa ka sanar dashi dan Allah karka kira gida ka faɗa musu bana son Ummi taji mutuwar lokaci guda.”
“Whattttttt! An kashe Khairi kace, innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!!! “
Katse kiran Haidar yayi cikin tashin hankali ya zari key ɗinsa shima ya fita, numbern Papa ya kira ya sanar dashi abinda ke faruwa, kamar yadda Al’ameen ya umurce sa haka ya aikata police station yaje ya taho da ƴan sanda, cikin zafin zafin zuciya Haidar yayi parking ya nufo Al’ameen, idanunsa sunyi jajur, kan gawar Khairi ya sunkuya cike da zafin zuciya yace.
“Waye ya aikata mana wannan mungun aikin, me muka tsare masa a rayuwa, me muka tsare masa!!!”
Al’ameen ganin Haidar ya zabura yana magana cikin zafin zuciya ga idanunsa tamkar garwashi, yasa ya dafa kafaɗar sa yana girgiza masa kai alamun ya kwantar da hankalin sa, runtse idanunsa Haidar yayi tare da girgiza kansa yana cire hanun Al’ameen daga kafaɗarsa ya saka hanu ya ɗago Khairi ta dawo jikinsa, cikin yanayin damuwa yace.
“Tunda na taso ina Karami har kawo yanzu girmana ban taɓa jin ko ganin muna da maƙiyi ba, tabbas akwai wanda yake bibiyar ahalin mu, amma na rasa fahimtar meyasa har zata kai ga kisa lallai ko waye ya miki wannan aikin ya rabaki da numfashinki, sai mun binciko ko waye sai ya fuskanci hukunci, jinin ki bazai taɓa tafiya a banza ba Khairi.”
Yayi Maganar hawaye na gangarowa daga idanunsa Al’ameen cikin raunin murya yace.
“Mawuyacin abune gano wanda yayi wannan kisan, abune da aka tsarasa kafin a aiwatar Tabbas anyi shiri domin kuwa yanayin mutuwar ta bayyana hakan babu wata shaida ko ɗaya da zai bada damar gane wanda yayi kisan, ko ƙwarzane babu a jikinta, an kasheta maybe ta hanyar toshe numfashi”
Dubansa ya kai ga police ɗin da ke famar dube dube da kuma ɗaukar Khairi hoto gefe kuma har ƴan jarida sun taru, yace.
“Muna buƙatar komawa gida idan kun gama abinda kuke.?”
Yayi Maganar dai-dai Papa ya iso a motar sa shida Dpo, gabaki ɗaya hanya aka basu Papa ya sunkuya gaban gawar Khairi shida Dpo suna nazarin kisan, numfashi Papa ya sauƙe tare da cewa.
“Haidar ɗauki gawar mu koma gida, dpo a tabbatar an kama wanda yayi wannan kisan umarni nake baka, dole ko waye ne ya shigo hanu, bazan yadda da wannan cin zarafin ba, kisa haka kawai na rainin wayo.”
Kansa dpo ya ɗaga tare da cewa.
“Zamu tsananta bincike ranka ya daɗe insha Allah zamu kama ko waye yayi wannan aikin.”
Kansa Papa ya ɗaga tare da shigewa mota yaja, Haidar da Al’ameen motar Al’ameen suka shiga yayin suka bar ta Haidar a wajen ɗan sanda guda ɗaya zai taho da motar, a yayin da ƴan sanda suka kama Idi drever domin shine mutum na farko da suke zargi.
Koda suka koma gida, Papa bai bari su Al’ameen sun shigo da gawar Khairi ba, a mota suka barta kafin suka shiga part ɗin su Ummin, duk suna zaune a falon sunyi carko carko, har su Aunty da momma kowa hankalinsa na tashe, Papa kusa da mahaifiyarsa Inna Jumma ya zauna tare da yin shuru yana duban Ummi, Inna Jumma ce tace.
“Kun sameta kuwa naga kun shigo kun zauna kunyi shuru ina take.”
Papa ne yace.
“Inna dukkan mu musulmai ne kuma mun yadda da ƙaddara mai kyau ko a kasin haka, a rayuwa ba komai bane kake dawwama dashi dole wata rana zaka samu kuma zaka rasa komai matsayinka da kuma ikonka, Allah yana bamu abu domin ya gwada godiyar mu garesa, haka yana rabamu da abinda mukafi so domin ya gwada imanin mu, Allah yana jarabtar bawansa domin ganin ƙarfin imaninsa idan mun samu Allah ne idan mun rasa shima Allah ne, Hajiya Gaji ina so kiyi imani da ƙaddara ki kuma yarda dashi domin kuwa mun tsinci gawar Khairi, Khairi ta mutu dan Allah kar muyi kuka addu’a zamu mata, mutuwar nan ta ɗaure min kai domin kuwa da alamu kashe khairi akayi.”
Wani irin tsinkewa zuciyar Ummi tayi jin maganar tayi tamkar sauƙar aradu cikin kunnen ta, idanunta ta runtse tare da saka hanu ta dafe ƙirjinta tana furta.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!! Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!!! Allah na gode maka Allah na gode maka, Allah ka fini son Khairi shiyasa ka ɗauketa, Allah ka sanyaya min zuciyata Allah ka jiƙan Khairi, Allah ka taushi zuciyata, ina jin zafi a cikin ƙirjina! Ina jin zafi”
Tayi Maganar tana sakin kuka mai ban tausayi, gabaki ɗaya falon babu wanda bai girgiza da jin wannan mutuwar mai kama da almara ba, Aunty Amarya da ƙarfi ta kurma ihu tana cewa.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!!! Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!!! Yau mun shiga Uku, Khairi ta tafi ta barmu, waye ne ya kasheta wani mungunne me muka masa da zai kashe mana Khairi, waye ya cucemu, wa…”
Momma ce cike da tausayin Aunty Amarya domin kuwa da alamu har tafi Ummi ɗimaucewa, a nasu ganin kenan, riƙeta keda wuya sai ta yanki jiki ta faɗi tare da ɗauke numfashin ƙarya ita a dole ta suma, Al’ameen da gudu yazo ya riƙe Aunty Amarya yana jin matar Sosai cikin ransa domin kuwa a duk sanda mummunan abu ya samesu takan fisu shiga cikin damuwa, ruwa momma ta ɗauko aka watsa mata nan ma dai a firgice ta buɗe ido tare da zabura zata tashi tana kiran Khairi,. Al’ameen idanunsa ya runtse cike da tausayin Aunty Amarya tare da kauda kansa gefe, da ƙyar aka samu Aunty Amarya ta nutsu, sai dai fa bata fasa kukan munafurci ba domin kuwa hawaye tamkar ambaliyarsa ake a face ɗin ta, Ummi kam tsabar damuwa da tashin hankali sai sauƙe ajiyar zuciya take, yayin da Inna Jumma ta sata a gaba da lallashi da nasiha, koda aka shigo da gawar Khairi sosai hankalin Aunty Amarya ya ƙara tashi ta ƙanƙameta tana kuka, Haidar cikin nazarin waye yayi kisan ya shiga sai dai duk tunaninsa ya gaza fahimtar komai, zuciyarsa tana cunkushe, Papa da kansa ya sanar da Daddy, Allah sarki tsakanin ɗa da Uba Daddy Sosai yaji zafin mutuwar Khairi, yaso ya dawo Nigeria a ranar, Papa ya hanasa tare da cewa, yayi hkr ya zauna koda yazo babu abinda zaiyi ya mata addu’a daga can zata isketa, Faruq kam harma ya zarce Haidar shiga cikin tashin hankali, domin kuwa koda ya kira Al’ameen gagara Magana yayi sai kuka daya kufce masa, ƙarshe kashe wayar yayi, Al’ameen shine kawai idanunsa bai zubda hawaye ba, sai dai wani irin zafi yake ji a ransa.
Kafin kace me mutuwar Khairi ta karaɗe garin Abuja, gidajen rediyo gidajen tv duk sai sanarwa suke an kashe ƴar *AMBASSADOR AHMAD GIWA* yayin da gidan ya cika da mutane hatta Hajja yalwa mahaifiyar Ummi tazo ita da ƙanwar Ummin Aunty Amina, Allah Sarki Maimu sosai tasha kuka tamkar ranta zai fita, kasancewar dare ya kawo kai yasa aka ce baza’a mata Sallah ba sai gobe da safe misalin 11:00am.
Washegari da safe Inna Jumma da Hajja yalwa mahaifiyar Ummi sune suka yiwa khairi wanka, aka kira Aunty Amarya da Ummi, suka mata addu’a Ummi ta juma a kanta tana mata addu’o’i, kafin ta tashi cikin sanyin jiki.
Sha ɗaya dai-dai aka yiwa khairi Sallah aka kaita makwancinta, sosai gidan ya cika da mutane, inda Aunty Amarya ta nuna tafi kowa shiga damuwa, Ummi har tausaya mata take.
Hajiya Mansura ma tazo tayi gaisuwa harda kuka, sai basu samu damar keɓewa su biyu ba kasancewar mutane da sukayi yawa a gidan.
Bayan kwana uku da mutuwar Khairi akayi sadaka kowa ya watse amma har yanzu Al’ameen ya kasa sakin jiki tunanin waye ya kashe ƴar uwarsa yake, yana nan zaune a falo Inna Jumma ta sauƙo tare da zama kusa dashi kafaɗarsa ta dafa tace.
“Wai har yanzu bazaka daina wannan tunanin bane Aminu?”
Kansa ya ɗago ya kalli Inna Jumma Numfashi ya sauƙe tare da kwantar da kansa jikin Inna Jumma yace.
“Har yanzu nazari nake akan lamarin kisan Khairi, na rasa me ta tsarewa wani a rayuwa ya mata wannan kisan abun baƙin ciki har yanzu an kasa gane wanda ya aikata mata haka, bana tunanin za’a iya haɗa baki da Idi drever domin cutar da wani a cikin gidan nan, ya kamata a sakesa haka ya wahala ba tare da haƙƙinsa ba, Papa yaƙi bada damar a sakesa amma ni zanje na saka a sake sa.”
Numfashi Inna Jumma ta saki zatayi Magana taji muryar Haidar daga bayansu.
“Ba kowa ake yarda dashi ba a wannan Rayuwar Al’ameen, domin kuwa wanda baka taɓa zaton zai cutar da kai ba, sai kaga shine zai cuceka karkayi gaggawar cewa Idi drever sai ya bar hanun ƴan sanda domin kuwa zai iya yiwuwa daahi aka haɗu wajen kashe ta, ni kaina ina zarginsa dan haka kabar hukuma tayi aikinta Please.”
Ya yi Maganar yana zama ɗaya daga cikin kujerun falon Al’ameen kallon Haidar yayi tare da cewa.
“Ko da wanda kafi kusa dashi zai cutar da kai, ina da tabbacin Idi drever bazai cutar da rayuwar ahalin gidan nan ba, domin kuwa da zaiyi hakan da ya juma dayi karka manta da tun muna ƙananan yara yake gadi a gidan nan ya goye mu a bayansa, ya mana wasa, ya saya mana sweet da kuɗin sa, bana manta ƙaunar da yake mana taya zaka zargi mutum irin wannan, shi kansa a sume na samesa a gefen hanya da alamu sai da aka sumar dashi aka aikata hakan, dole a saki Idi domin kuwa bashi da hanu”?
Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
“Na sani ban manta ba Tabbas ya goye mu a bayansa ya nuna mana ƙauna, ban musa hakan ba, amma hakan bashi zaisa a yarda dashi ba, dole hukuma tayi aikinta, koda Papa ake zargi bazamu saka baki ba, zamu barsa da hukuma bare kuma Idi drever.”
“Hmmm!!! Na fa yanke hukunci dole ne za’a sake Idi domin kuwa bashi da laifi na gama magana kuma sai ya fito.”
Cije bakinsa Haidar yayi cike da ɓacin rai da kuma hasala ya miƙe tsaye cikin tsawa ya cewa Al’ameen.
“Wai mai kake ɗaukar kanka ne a rayuwa Al’ameen, kai kullum idan ka yanke hukunci sai kace babu mai dakatar da kai saboda isa da iko, to wallahi a wannan karon akan case ɗin jinin Khairi baka da iko bazan taɓa bari ikonka yayi tasiri ba bazaka fito da Idi ba, ko da nine bincike ya biyo kaina ko kai to fa dole ne kowa a gidan nan ya gimtse bakinsa har sai gaskiya tayi halinta, ka rage isa da taƙama gami da nuna iko Al’ameen domin kuwa ba’a ko ina iko ke amfani ba ya kamata ka gane wannan.”
Kansa Al’ameen ya girgiza tare da murmushin gefen baki, sam shi a rayuwarsa ya tsani hayaniya ko ihu a ka, cewa Haidar yayi.
“Ai kai a rayuwarka baka taɓa zurfafa tunani kafin yanke hukunci kana ɗaukar komai ne a yanda yazo a zuciyarka, shiyasa kullum kake kasa gane alƙibilata, saboda muna da bambancin tunani tsakanina da kai, amma ku sani Wallahi duk wanda ya bari aka zalunci wannan bawan Allah, wallahi Allah bazai barsa ba, a kullum nakan tsaya nayi nazari mai zurfi akan abu kafin na yanke hukunci, duk zaman da Idi yayi a hanun police kwana huɗu kenan har yau kaji ance an samu wata hujja da take nuna ga wanda yayi kisan ko kuma hujjar data nuna akwai hanunsa hmmm”
Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
“Kai da bakinka kace ba lallai ne a kama wanda yayi wannan kisan ba saboda bai bar shaida ko ɗaya ba, ba da wuƙa ko bindiga ya kasheta ba, haka babu wani abu nasa daya bari wanda za’a ganesa to ta yaya kake tunanin wannan binciken zai kammala da wuri, amma kuma inaji a jikina wannan makashin asirinsa dole zai tonu dan haka Idi bazai fito ba har sai hukuma ta tabbatar da gaskiyar sa.”
“Hmmm!!! Haidar kenan, jikinka ai kai baya ji maka dai-dai domin kuwa duk wani abu da zaka aiwatar a rayuwarka kana aiwatar wane a makancce bisa umarnin zuciyarka amma ka…….”
Inna Jumma ce ta ɗagawa Al’ameen hanu tare da cewa.
“Ya isa haka kubar maganar, Aliyu ya fika gaskiya mutum ba abun yarda bane, Kamar yadda Haidar ya faɗa Idi bazai fito ba har sai idan hukuma ce ta sakesa, kar kuma ka kuskura ka ce zakaje ka fito dashi ranka zai ɓaci domin kuwa nasan halinka da taurin kai.”
Miƙewa Al’ameen yayi cikin ɓacin rai ya haura bedroom ɗinsa yana cije baki, Haidar duban Inna Jumma yayi tare da cewa.
“Ikonsa yayi yawa Inna, duk iya ƙiƙarina na ganin na sauya masa wannan ɗabiar na kasa, yayi fushi da yawa, bara naje na basa haƙuri, bana jin daɗi idan yana fushi dani sai dai Inna bazan bari yasa a saki Idi ba saboda shine abun zargi na farko.”
Kanta Inna Jumma ta kaɗa masa tare da cewa.
“Karkaje ka samesa yanzu ka rabu dashi sai zuwa anjuma idan ya huce, domin yanzu yana cikin fushi bazai saurareka ba, ka riga kasan halinsa, haka yake da izza tun kuna yara, wannan a jininsa yake ɗabiar sa ne bazai sauyawa ba sai dai ku ku dinga haƙuri dashi domin kuwa Aminu bazai daina nuna iko ba.”
Shima Haidar kansa ya kaɗa tare da miƙewa ya shigo bedroom ɗin Aunty Amarya, zama yayi a falon ta, da take zaune ita da maimu da Afnan, cike da ladabi ya gaisheta su Maimu suma gaishen san sukayi kafin Aunty Amarya tace.
“Ya labarin binciken da hukuma keyi an samu damar gano wanda yayi kisan, hankalina ya kasa kwanciya kullum cikin tashin hankali nake domin kuwa Khairi tana hanani bacci burina kawai a kama wannan azzalumin da mata wannan kisan ko zan samu sauƙi, ina son Khairi fiye da ƴaƴan da na haifa a cikina mun shaƙu da ita shaƙuwa marar misaltawa, kullum tana jikina, amma wannan azzalumin mungu ya rabani da ita rabuwa ta har abada.”
Tayi Maganar tana sakin kuka, Haidar shuru yayi cike da tausayin Aunty Amarya yace.
“Hukuma tana iya kokarinta Aunty Amarya kuma insha Allah za’ayi nasarar kamo wannan tsinannen, sannan ni kaina ina saka idanu gami da bincike akan wannan lamarin baza mubar wannan kisan ya tafi a banza ba, ina da tabbacin duk wanda yake da hanu a ciki wannan zaluncin to fa sai mun ganosa, nan da kwanaki kaɗan ku cigaba hkr khairi kwananta ya ƙare dama ko ba’a kasheta ba, bazata wuce lokacin ta ba, dama nazo na gaisheki ne, bara naje room ɗin Ummi.”
Yayi Maganar yana miƙewa tsaye wani irin sanyi jikin Aunty Amarya yayi take taji tsoro ya kamata, murmushin yaƙe tayi tare da cewa.
“Ya kamata a binciko ko waye, na gode Haidar.”
Kansa ya ɗaga tare da ficewa, Aunty Amarya duban Maimu da Afnan tayi tare da cewa.
“Maimu kuje kitchen ku ɗaura girki keda Afnan maza.”
Babu musu kuwa suka fita, Aunty Amarya ƙirjinta ta dafe tare da tashi ta rufe ƙofar, bedroom ɗinta ta shige tare da kiran Hajiya Mansura a waya tana dagawa babu sallama Aunty Amarya ta fara magana.
“Hajiya Mansura, kin tabbatar da cewa babu wata hujja da Isa Alolo suka bari domin kuwa har yanzu sunƙi barin wannan binciken, yanzu haka Haidar ya fita a room ɗina yana tabbatar min da cewa iya da tabbacin za’a kama duk wanda ke da hanu a cikin wannan kisan gashi har yanzu Idi yana hanun hukuma.”
Dariya Hajiya Mansura ta kece dashi tare da cewa.
“Kai amma dai ke amarya akwai matsoraciyar wallahi, hmmm!!! Wai ke yanzu nan tsoro kikeji kar a gano ki, ta bara kiji da zasu shekara dubu suna wannan binciken bazaau taɓa gano wanda yayi wannan kisan ba, domin kuwa anyi kisan ne ta hanyar toshewa shegiya numfashi kana suka wurgar da ita sukayi tafiyarsu, shi kuma wannan idin da kike Magana, bashi da wata hujja da zaice ga wanda yayi kisan domin kuwa sun rufe fuskokinsu suka sumar dashi kafin suka yi aikin su, dan haka ki sake kiyi walwalar ki baki da matsala, kar kuma ki kuskura ki dinga nuna musu tsoro ko ki dinga tsarguwa ki iya takunki.”
Numfashi mai nauyi Aunty Amarya ta saki tana furta.
“Alhamdulillah! To amma yanzu waye next kuma.”?
“Ina tukunna sai wannan ƙurar ta lafa sun fara mantawa da wannan tashin hankalin sannan zamu ɗaura daga inda muka tsaya amma kafin nan shi babban ɗan nata Al’ameen zamu fara wahalar dashi da kuma tsoratarwa.”
“Ban gane abinda kike nufi ba tsoratarwa kamar yaya.”
Murmushi Hajiya Mansura ta saki tare da cewa.
“Zan sanar dake zuwa gobe, ke dai ki kwantar da hankalin ki.”
“Shikenan Allah ya kaimu.”
Aunty Amarya tayi Maganar tana katse kiran.
Masha allah
I want to read the story