"Abbas nafi ƙarfin ayi maleji dani ka dubeni sama da ƙasa, meyasa kake son furtawa mutum maganar da kaga dama ne, idan har Rabuwar Nafeesa da yaya Haidar zai taimaka min wajen samun Masoyina, to kuwa kai kuma amincewa tsakanin Nafeesa da yaya Al'ameen zai jefaka..."
"Dakata da wannan maganar haka domin kuwa dukkan mu amincewa tsakanin Nafeesa da Al'ameen itace nasarar mu, nasan da hakan shiyasa na ƙyale maganar ina ma laifin kice ta wacce hanya zamubi domin kawo kusanci da yarda da kuma Soyayya ya shiga tsakanin Nafeesa da Haidar da sai nafi amince miki saboda. . .