Skip to content
Part 49 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Abbas nafi ƙarfin ayi maleji dani ka dubeni sama da ƙasa, meyasa kake son furtawa mutum maganar da kaga dama ne, idan har Rabuwar Nafeesa da yaya Haidar zai taimaka min wajen samun Masoyina, to kuwa kai kuma amincewa tsakanin Nafeesa da yaya Al’ameen zai jefaka…”

“Dakata da wannan maganar haka domin kuwa dukkan mu amincewa tsakanin Nafeesa da Al’ameen itace nasarar mu, nasan da hakan shiyasa na ƙyale maganar ina ma laifin kice ta wacce hanya zamubi domin kawo kusanci da yarda da kuma Soyayya ya shiga tsakanin Nafeesa da Haidar da sai nafi amince miki saboda shine abinda zamu samu nasara da kuma cikar burin mu, akasin ta kuma faɗuwarmu ne, amm kinyi magana kan cewa duk maganar da tazo bakina ina faɗawa Mutum ko, hmmm! Bana ƙwai na sai da zakara, duk abinda na furta shine gaskiyata, ke kanki kin sani Haidar baya sonki to ki faɗa min idan har ya rasa Nafeesa to fa zai aureki a dolene, kinga kuwa maleji zaiyi da ke MALAMA RUFAIDA AHMAD GIWA, sai kuma me kika kiran bayan wannan saboda zan gimtse wayata ne ina da aikin yi.”

Murmushin takaici Rufaida tayi sam ya kasa fahimtar ta numfashi ta sauƙe tace.
“Baka fahimceni ba har yanzu Abbas, ba Soyayyata bane damuwata a yanzu rayuwar ƴan uwana da kuma farin cikin Ahalina shi nake magana ko da zan faɗi a soyayyata Ahalina su sami kwanciyar hankali da nutsuwa, hmmm! Ni hakan shine nasarata, bana fifita burina fiye da farin cikin ahalina, so nake nasan meye shirin Nafeesa akan ƴan uwana, daga nan zansan yadda zanyi na kare su, ka taimakeni Abbas.”

Murmushi Abbas yayi yana kallon Momy da ta ɗago suka haɗa idanu miƙewa yayi zai bar wajen yaji muryar Momy na ce masa.

“Kuma ka zauna ka gama wayar a gabana ina son magana da kai.”

Komawa yayi ya zauna yana sosa kai ya cewa Rufaida.

“Bazan iya wannan aikin da zai rusa min rayuwata ba, ina son cikar muradina kuma ban taɓa son abu na rasa ba Rufaida bazan fara kada kaina akan buƙatar ki ba, nisanta Nafeesa da Al’ameen barazana ce ga soyayyata, dan haka ki barni na zauna a gefe naga abinda Allah zaiyi banyi yunƙuri ba domin kusanta Nafeesa da Al’ameen Saboda bana son shiga cikin lamarin da kuma naso shiga cikin sauƙi zan sauya lamarin sai banyi hakan ba Saboda bana zalunci a rayuwata, na tsaya ne kawai naga yadda Allah zaiyi kuma ina fatan yamin mai kyau.”

“Amma kuma Abbas ya kamata ka….

“Ya isa haka Rufaida tunda na ce miki bazanyi ba to bazanyi bane sai anjuma.”

Yayi Maganar yana katse kiran, bakinta Rufaida ta cije cike da takaici shi a rayuwarsa kansa kawai ya sani idan baiyi niya ba bazaiyi ba.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Wannan wacce irin masifa ce, mtsss ya zamo dole yau na koma gida.”

Tayi maganar tana ijiye wayar tare da fitowa wajen Hajja kaka.

Shi kuwa Abbas Momy ya kalla tare da cewa.
“Ina sauraranki Momy.”

“Abbas ya kamata kaje ka gaishe da Hajiya Suwaiba, na faɗa maka bata da lafiya har drip tasha, amma ban ji kace zakaje ka gaisheta ba meye nufinka, karka manta fa itama uwace a gareka tunda ƙanwata ce Uwa ɗaya uba ɗaya idan ka manta na tuna maka.”

“Momy zanje na dubata amma sai gobe Saboda yau ina da abunyi.”

“Au sai baka da abunyi shine zakaje ka gaisheta, kana gani ko kaina ne yayi ciwo haka ƴarta AKNAM take zuwa ta kwana a kaina, hmmm! Good yayi kyau.”

Abbas miƙewa yayi tare da cewa.
“Sorry Momy koda naje ai ba lafiya zan bata ba, ki bari kawai nayi uzurina goben naje.”
Yayi Maganar yana ficewa Momy girgiza kanta kawai tayi ta bisa da idanu.”

Washegari litinin.

Washe gari misalin 2:30pm jirgin American ya sauƙa a babban airport dake cikin garin Abuja, Haidar tsaye yake ya zuba hannayensa a cikin aljihu, yana jiran sauƙowarsa gefe can kuma Al’ameen shima yana tsaye jingine jikin motarsa, sai Afnan da Maimu dake gefensa.

Sanye yake da suit baƙi da white ɗin jeans fuskarsa ɗauke da murmushi yake saukowa daga cikin jirgin ya ƙara fari yayi kyau sosai, murmushi Haidar ya saki hango sa yana sauƙowa, kusan a tare shida Al’ameen suka nufesa tare da rungumesa suna sakin murmushi.

“Welcome my Bros.”

Suka faɗa kusan a tare suna sakinsa murmushi Faruq yayi cike da farin ciki ya amsa da.

“Thank my brothers, kunyi kyau fa abunku.”
Murmushi Al’ameen tare da juyawa yana tafiya yace.

“Muje gida ka samu ka huta, ga can waɗancan ƙannan naka suna jiran kaje su maka welcome.”

Murmushi yayi tare da nufarsa Haidar da Al’ameen babu wanda yayiwa wani magana kowa ya shige motarsa, Faruq da kallo ya bisu tare da dafa kafaɗar Al’ameen yace.
“Bari na shiga motar Haidar kai ku taho da su Maimu.”

Kansa Al’ameen alamun to kafin duk suka shige cikin motocinsu.

Ko da suka isa gida babu wanda baiyi murna da dawowar Faruq ba, Inna Jumma tafi kowa farin ciki sai dai taso ace da Daddyn Al’ameen suka taho to shi yace ayyuka sun masa yawa bazai samu damar shigowa Nigeria ba sai upper week nan ma idan ya samu time.

Faruq kusan sati guda da dawowarsa sai dai har yanzu babu wanda ya tunkara da maganar Saɓanin Haidar da Al’ameen ko su kansu bai musu magana akan matsalar ba, bai kuma nuna musu yasan maganar ba haka suma babu wanda ya sanar dashi, sai dai sun tattauna sosai da Ablah da kuma Maimu akan maganar, a yayin da ya sanya a saka masa idanu akan Nafeesa.

Nafeesa tunda Mama ta bata maganin wajen bokan nan ta rasa hanyar da zata fara idda nufinta akansa, yau sammakon zuwa Companyn su tayi kasancewar yau Monday tana tsaye gefe da Companyn taga shigewar motar Haidar, ba’a wani juma ba kuwa sai ga motar Al’ameen ma ta shige murmushi Nafeesa ta saki sanda Al’ameen yayi wajen 30 minute da shiga sannan tabi bayansa wannan karon an samu sauyin sakatariya domin kuwa ba wacce ta samu randa tazo bane wata ce kuma dabam, gaisawa sukayi Nafeesa ta mata ƙarya da cewa ita ƙanwar Al’ameen ne tana son ganinsa tambayarta sakatariya tayi waye za’a ce masa tace ace Afnan ce, shiga tayi cikin Office ɗin, tana shiga Nafeesa tayi saurin ɗauko kwallin ta sanya a idanunta, tare da riƙe turaren a hanunta bayan ta buɗe kwalbar, ba’a juma ba ta fito tace zata iya shiga, shiga Nafeesa tayi tare da cire niƙaf ɗin sanda ta tabbatar ta sanyawa ƙofar key sannan ta nufi Al’ameen, kansa na sunkuye yana rubutu yaji tsayuwar mutum a kansa kafin ya ɗago yaji an watso masa turare saurin ɗago idanunsa yayi ido huɗu sukayi da Nafeesa wani irin sarawa kan Al’ameen yayi, dafe kansa yayi wani jiri na ɗibarsa kansa yaji yana juya masa idanunsa ya runtse murmushi Nafeesa tayi tare da neman waje ta zauna ta harɗe ƙafafunta, Al’ameen yafi 20 minute baya cikin hayyacinsa sai can ya dawo hankalinsa Nafeesa ya gani zaune a gabansa fuskarta ɗauke da murmushi.

“Nafeesa kece?”

Murmushi ta sakar masa cike da kissa yace.
“Ehh ni ne, Allah yasa banyi laifi ba shigo maka office da nayi, nazo ne dama na baka hkr akan shiga rayuwarka da nayi Tabbas ina sonka Soyayya ta gaskiya sai dai kai na fahimci baka sona bani bace a gabanka kayi hkr insha Allah bazan sake shiga rayuwarka ba s…

“Dakata Nafeesa karki ƙarisa waye yace miki bana sonki, ina sonki nima fiye da yadda kike sona.”

Murmushi Nafeesa tayi cikin zuciyarta ji take tamkar ta tashi ta taka rawa aiki yayi kyau dubansa tayi cikin wani irin yanayi tace.

“Kaine ka faɗa min hakan da bakinka idan da gaske kana sona to yaya zakayi da ɗan uwanka Haidar da kuma masoyiyyarka Ablah?”

“Ki rabu dashi babu ruwana dashi ko kowa zai gujeni muddun ke zaki kasance dani bazan damu ba, ita Ablah da kike magana a kanta bana sonta ni ke kaɗai nake so kuma kin isheni rayuwa.”

Dariya Nafeesa ta saka cikin farin ciki ta samu cikar muradinta, sun juma sosai suna hira da Al’ameen shi da kansa ya rakato waje tare da sawa a kaita gida.

Yadda boka ya bada umarnin yadda za’a gudanar da aikin su Nafeesa sunyi basu sami wata tangarɗa ba sai Inna Jumma kawai da suka gagara aiwatar da nata aikin.

A cikin sati biyu Ablah taga wasu irin sauyawa daga wajen Al’ameen rashin kulawa da kuma banza da ita da yake idan taje school baya ɗaukota wanda shi ya sabar mata da hakan, tun abun baya damunta har yazo yana damunta, sai dai ta kasa sanar da kowa sai Hafsa ƙawarta da tayiwa zancen kuma ta kasa tambayarsa me ta masa, ita kanta Inna Jumma ranta ya ɓaci da rashin zuwan Daddy domin kuwa gaba tsakanin Haidar da Al’ameen ya isheta kwatsam ranar Litinin sai Daddy ya kirata yake shaida mata cewa shigo Nigeria gobe sannan ya sanar da ita cewa Abi ma mahaifin Faruq yana hanya a goben sosai taji daɗin hakan, domin kuwa dole a tara family meeting domin kawo ƙarshen wannan fitinar tasu Haidar.

A ɓangaren Faruq kuwa ya samu dukkanin infomation akan Nafeesa inda ya tabbatar da karuwa ce, hakan ya sashi fara fuskantar Al’ameen da maganar karon farko kenan .

“Ina sauraranka Faruq tun ɗazu muka shigo garden ɗin nan kasa cemin komai meke faruwa?”

“Al’ameen ni fa abinda ya dawo dani ƙasar nan Saboda matsalar dake tsakanin ka da Haidar ne, yau satina uku a cikin garin Abuja, ban muku maganar ba sai yau nake son mu tattauna da kai, shin Al’ameen da gaske kanason Nafeesa?”

Murmushi Al’ameen yayi yana kallon Faruq ya ɗaga kansa tare da cewa.

“Ƙwarai ina sonta Soyayya kuma ta zahiri, Munyi waya da Daddy ma na sanar dashi na samu matar Aure yazo aje a nema min aurenta, gobe ma zai shigo kuma yazo ne saboda aurena da Nafeesa.”

Idanunsa Faruq ya zaro cike da kiɗima ya miƙe tsaye tare da furta.

“Whattttttt! Al’ameen kasan me kake faɗa kuwa, Nafeesan kakeso karka manta budurwar AMININKA ne fa kuma ɗan uwanka, da na ɗauka ƙarya ne da akace kana son NAFEESA SABODA nasan bazaka so budurwar AMININKA ba, sai ga kuma akasin haka wannan abun kunya ne Al’ameen, ka sake tunani ka dawo hankalinka, idan ma har ka barwa Haidar ɗin shima bata dace dashi ba Saboda karuwa ce mai bin maza bata dace da Familyn ba.”

“Hmmm! Bari kaji FARUQ Nafeesa rayuwata ne a yanzu ina sonta kuma zan iya rabuwa da kowa a kanta, saboda ita karuwa ce bai dameni ba, saboda ana ɗauko karuwa a sabon layi tayi istibira’i kuma a aureta ko duka mazan garin nan Nafeesa take bi na yadda zan aureta, ka daina kiran Haidar da aminina domin kuwa babu wannan amanar mantawa dashi nake a rayuwata dan Allah ka daina tuna min dashi a cikin rayuwata Nafeesa ta amince dani zata aureni dan haka ban damu da Haidar ba yaje yayi duk wani abinda yaga zaiyi.”

Haidar da ya shigo garden ɗin tun ɗazu yake sauraronsa ne idanunsa suka ciko da hawaye baƙin ciki da takaici yake ji tamkar zasu kashesa ina baizo duniyar nan ba, ina ma ace tun yana jariri ya mutu da baiga wannan baƙin cikin ba, ashe dama Nafeesa ba sonsa take yaudararsa take ashe dama zata iya auren wani ba shiba a zatonsa fushi tayi zata dawo garesa ashe abun ba haka yake, lallai duniya babu Amana Nafeesa ta yaudaresa haka amininsa ya ha’incesa lallai ya tsani Nafeesa tsana ta haƙiƙa cikin rawar murya yace.

“Banji mamaki ba dan ka aibata ni saboda kai ɗan akuya ne, daga kai har Nafeesa ina tabbatar muku da cewa sai amanar Allah ta ciku rayuwace kuje zaku gani na barku da Allah gashi dama wannan takaddar na ijiye aiki daga companyn ka zan baka abinda ya kawoni kenan.”

Yayi maganar yana ijiye masa takaddar jiri na ɗibarsa hawaye wani na tsere saman fuskarsa Rufaida dake laɓe tana jinsu itama Hawaye ta share na tausayin Haidar Tabbas yaya Al’ameen yaci amanarsa ashe da gaske ne zargin da Haidar ke masa a baya aka ƙaryatasa ake kallon laifinsa juyawa tayi da gudu tabar wajen.

“Yayi kyau hakanma yamin kaje ka nemi aiki a inda yafi company na, kaine kayi asara ba ni ba.”

Al’ameen ya masa maganar yana sakin murmushi, shi ko kaɗan bai ga rashin kyautawar abinda yayiwa Haidar ba, murmushi Haidar yayi na baƙin ciki ba tare da ya kuma cewa Al’ameen komai ba ya juya yabar wajen, Faruq kansa ya riƙe shi kansa yaji haushin Al’ameen.

“Al’ameen baka kan dai-dai kayi kuskure baka kyautawa Haidar ba dan Allah dan Allah na roƙeka ka rabu da naf…

Cikin wata irin tsawa Al’ameen ya dakatar da Faruq yana buga teburin gabansa yace.
“Karka kuskura ka ƙarisa Maganar da take bakinka ni da Nafeesa mutu ka raba kuma zan iya rabuwa da kowa a kanta.”

“Al’ameen baka cikin hankalinka duk yadda akayi ba kai bane domin kuwa Al’ameen ɗin da na sani bazai aikata wannan cin amanar ba, ka sake tunani domin kuwa Allah bazai zuba ido ya barku kuna zalunci ba.”

Yana gama maganar shima yabar wajen a fusace motar sa ya hau yaja da ƙarfi cikin ɓacin rai zaije ya samu Nafeesan ya zamo wajibi a gareta ta fita a tsakanin ƴan uwansa.

Ita kuwa Rufaida part ɗin su yaya Haidar ta shiga da gudu Momma ta samu zaune ta faɗa jikinta ta saki kuka mai sauti tare da cewa.

“Momma yaya Al’ameen yaci amanar yaya Haidar ashe da gaske ne abinda yaya Haidar ke faɗa akansa ya cutarsa Momma yaya Al’ameen ya karya zuciyar mutum biyu waɗanda suka fi kowa yarda dashi ya Ablah zataji a ranta idan taji wannan mummunar maganar wanda tasa ranta akansa ta basa dukkan yardar ta, soyayyarta duk ta basa ashe yaudararta yake ba ita yake so ba budurwar yaya Haidar yake son aura ba ita ba, ya cucesu momma ya karya musu zuciya.”

Tayi .aganar cikin kuka da tausayin ɓangare biyu Haidar da Ablah, Numfashi Momma ta sauƙe tare da ɗan buga bayan Rufaida alamun rarrashi tace.

“Rufaida ki daina saurin yanke hukunci, wannan maganar bana son na kuma jinta, meye a ciki dan Al’ameen yaso wacce Aliyu yake so domin shi Aliyu ba aurenta zaiyi ba, na riga da na masa mata kuma kece to meye abun tada jijiyoyin wuya, sannan ita wannan yarinyar da kuka magana a kai a yadda akace ba mutumiyar kirki bace to fa iyayenku maza bazasu yadda su aurawa Al’ameen ita ba shima dole hkr zaiyi Saboda *MADINA* zamu basa.”

Zaro idanunta Rufaida tayi cike da mungun mamaki ta furta.


“MADINA kuma Momma shi da yace sun gama magana da Daddy yana zuwa gobe shi da Abi saboda su nemo masa Auren Nafeesa, amma ke kuma yanzu kina cewa MADINA za’a basa na kasa fahimta Momma.”

“Daddyn Al’ameen ɗin ne zasuzo da Abi nemawa Al’ameen Auren wannan matsiyaciyar Yarinyar, cap lallai kam…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 51Aminaina Ko Ita 53 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×