Skip to content
Part 48 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Faruq dake zaune cikin Office ɗin Daddy yana aiki ne yaji ringin ɗin wayarsa dubansa ya kai ga wayar Maimuta murmushi ya saki tare da sanya hannu ya ɗaga kiran.

“Hello! Maimuta ya akayi?”

Daga can Maimu tayi gyaran murya cikin ɗan shashsheƙar kuka tayi magana.

“Yaya Faruq akwai matsala.”

“Matsala kuma Maimuta, wacce irin matsala ki nutsu kimin bayanin meke faruwa?”

Cikin shashsheƙar kuka Maimu ta sanar dashi dukkan abinda ke faruwa tsakanin Haidar da Al’ameen, kusan suman tsaye Faruq yayi domin kuwa koda a cikin mafarki bai taɓa zaton akwai abinda zai shiga tsakanin su ba, yanzu ma jin maganar Maimu yake tamkar zolayarsa take.

“Maimuta bana son irin wannan wasan idan wasa kike to ki bari, nasan Al’ameen da Haidar babu wanda zai iya shiga tsakanin su koda kuwa shine iblis ƙarshen sheɗanci.”

“Wallahi! Wallahi! Yaya Faruq ba wasa nake maka ba da gaske nake maka wannan maganar, dan Allah ka dawo gida ko zaka iya maganin wannan matsalar.”

A razane Faruq ya miƙe tsaye yana furta.
“Whatt! Kina nufin da gaske kike Haidar da Al’ameen ne suka haɗa jiki da sunan faɗa, to wai ita wannan Yarinyar Nafeesan wacece me take nufi dasu, a iya sanina Al’ameen Ablah itace muradin sa, kuma Tabbas nasan Al’ameen bazai taɓa yadda ya nemi Yarinyar da Haidar keso ba, koda kuwa Soyayyar wasa Haidar yake mata, kinga turo min numbern Ablah idan akwai waya a hanunta karki damu ki kwantar da hankalin ki zan shigo Nigeria gobe dole na.”

“Shikenan yaya Faruq, bani da numbern Ablah, amma tana da waya bari naje na amshi numbern sai na turo maka.”

Da to ya amsa yana katse kiran, Maimu duban Afnan tayi tare da cewa.

“Yace na turo masa numbern Ablah, kuma yace gobe zaizo.”

“Numbern Ablah kuma meyasata a case ɗin nan ita kuma, well kije ki karɓa ki tura masa bamu san nufinsa ba.”

Kanta Maimu ta kaɗa tare da miƙewa ta fita, har bedroom ɗin Ablah taje ta amshi numbern a wajen ta turawa Faruq, kafin ta fita, Ablah kuwa sam ranta baiyi daɗi ba akan abinda ya faru, tasan koma menene wannan makirar Nafeesa itace ta haddasa saboda son zuciyarta, Numfashi ta saki tare da furta.

“Matsala a cikin gidan nan bata ƙarewa kana ƙoƙarin danne wannan sai kuma wannan ya ɓullo. Tabbas abubuwa sun zafafa ga matsalar amarya shin taya zata iya maganin waɗannan matsalar lallai ita ɗaya bazata iya ba, Duk da tasan Abbas yana taimaka mata sai dai har yanzu bata gama amincewa dashi ba wanda har zata iya basa yardarta.”

Ƙarar wayarta ne ya sata katse maganar tana duban wayar.

“Wannan kuma wacce irin number ce kamar numbern ƙasar waje.”

Tayi maganar tana saka hannu ta ɗaga wayar tare da sallama daga can Faruq ya amsa tare da cewa.

“Allah yasa dai da Ablah nake magana.?”
“Ehh ni ce, sai dai ban gane mai maganar ba.”
“Lallai kuwa bakya ɗaukar muryar Faruq Ahmad Giwa ke Magana.”

Murmushi Ablah tayi tare da cewa.
“Sorry muryar kane ta ɓace min shiyasa, ya aiki?”

“Aiki alhamdulillah! Amm nasan zakiyi mamakin kirana, ɗazu Maimu ta kirani take sanar dani wasu matsaloli dake faruwa a gidan nan, na kasa yarda shiyasa na kiraki naji gaskiyar magana.”

“Matsaloli! Wacce matsala ɗaya ta maka Magana a kai.?”

“Hmmm! Matsalolin suna da yawa ne daman?”

“Ba haka nake nufi ba, ina nufin meta sanar dakai?”

“Ga me da rikicin dake tsakanin Haidar da Al’ameen ta sanar dani cewa har kokuwa sukayi, hakane?”

Shuru Ablah tayi kafin taja numfashi tace.

“Ehh hakane, indai akan yaya Haidar da yaya Al’ameen ta maka magana gaskiya ne dukkan abinda ta faɗa maka babu ƙarya a ciki.”

Idanunsa Faruq ya runtse cike da takaici yace.
“Kina nufin da gaske akan mace suke faɗa, a iya sanina Al’ameen ke yake so, Kuma bana tunanin cewa zaiso abinda Haidar ke so, ki sanar dani gaskiya, Al’ameen ya juya alƙibilarsa a gareki ne ko ya miki wani sauyi ma’ana har yanzu soyayyarki tana garesa.”

Ɗan murmushin takaici Ablah tayi tare da cewa.
“Hmmm! Kaima kana da tantama akan yaya Al’ameen ne?”

“Ba tantama nake akansa ba, bakin zaren nake son na kamo.”
“Idan bakin zaren yana tukukuye fa,anya kuwa zaka iya kamasa?”

“Me kike nufi da wannan Hausar taki.?”
“Babu abinda nake nufi sai alkairi sai hausata yana ga kan yaya Haidar domin kuwa ya ɗauki zafi da yawa shawo kansa harya fahimta zaiyi wahala saboda zuciyarsa ta rinjayi tunaninsa shiyasa na ce maka idan bakin zaren yana tukukuye fa Haidar shine tukukuyayyen bakin zaren ya harɗasa.”

“Baki bani amsa tambayata ba har yanzu.”
“Amsar tambayar ka a bayyane take, har yanzu nine a zuciyar Al’ameen kuma nima haka wannan Yarinyar itace ke ƙoƙarin shiga rayuwar yaya Al’ameen, kuma ya kauce mata har gobe kuma akan kauce mata yake, bansan menene manufarta ba akan soyayya da take so Al’ameen ya bata, bayan tasan alaƙar dake tsakanin sa da Haidar, bansan ya zan fassara manufarta ba, amma dai kowa yayi duba da lamarin zai fahimci gaba take son haddasawa a tsakaninsu.”

Numfashi Faruq ya saki tare da sakin murmushi na takaici yace.
“Ba gaba take son ta haddasa a tsakanin su ba, saboda hakan bazai amfaneta da komai ba, Tabbas akwai dalili mai ƙarfi da yasa take son Al’ameen, lallai akwai dalili bawai saboda ta haɗasu gaba bane.”

“To amma wani dalili ne zaisa taso yaya Al’ameen bayan tasan ba abinda zai yiwu bane?”

“Bazance ga dalilin ba gaskiya amma cikin biyu dole ɗaya zai faru, inma sonsa take da gaske saboda zuciya bata da ƙashi ƙawa gareta, inma saboda wata manufa dabam wanda mu bamu sani ba, amma ba damuwa zan dawo gobe lallai zan bincika komai zan gano dalilin Yarinyar na gode sai anjuma.”

Yayi maganar yana katse kiran, numfashi Ablah ta sauƙe. Tana taɓe bakinta domin kuwa ta rasa da wacce irin kalma zata kira wannan masifar, tashi tayi ta shige toilet da niyyarta taje ta samu Al’ameen sai dai tasan koda taje ba lallai ya saurareta ba.

Tana zaune cikin falon Hajiya Mansura ta shigo ranta a mungun ɓace kallonta Aunty Amarya tayi tare da cewa.
“Lafiya na ganki haka fuska kamar an miki mutuwa?”

Ga ba tayi ba tare da ta tsaya ba tace.
“Ba gara ace mutuwar aka min ba da tashin hankalin dake tunkaromu.”

Tashi Aunty Amarya tayi har jikinta na rawa ta biyo bayan Hajiya Mansura har cikin bedroom ɗinta ƙofar ta sanyawa key suka shige can ƙuryar ɗaki.

“Hankalina ya tashi ganinki haka wai meke faruwa Allah yasa ba kwaɓarmu bace tayi ruwa, ina gubar da zaki taho min dashi.?”

“Ke dalla! Wayake maganar guba yanzu, Amarya dawa kika fara sirri bayan ni, domin kuwa duk yadda akayi maganar da mukayi dake a waya na kashe Ablah kin sanar da wani, waye kika sanarwa?”

“Ban gane me kike cewa ba, a zatonki ina da wanda nake faɗawa sirrina bayan ke, ko kusa ko alama babu wannan mutumin kece kaɗai kika san sirrina kaf faɗin wannan duniyar, ni banyi wannan maganar da kowa ba dake kawai mukayi ta, ki faɗa min meke faruwa wani ne yaji maganar?”

“Ƙwarai wani yaji amarya tunda gashi har an fara min barazanar za’a tona mana asiri ki duba wannan saƙon da yake cikin wayata ki gani, sai kiran layi ki nake kin kashe min waya meyasa.?”

Karɓar wayar Aunty Amarya tayi hannunta na karkarwa take karanta saƙon cike da tashin hankali har gumi na keto mata ta furta.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Mansura waye wannan, bayan ke ni banyi wata magana da wani ba, anya kuwa babu wanda yaji mu muna waya.”

Shuru tayi tana tuno maganar da Ablah ta mata ɗazu.
(Hmmm! Amarya kenan, to ai Ni ne wanda kike hari zaki kashe kuma na faɗa miki kinyi sake ɗan zaki ya girma mutuwata ba abu bane mai sauƙi.)
Bakinta ta cije tare da furta.

“Ablah!”

A zabure Hajiya Mansura tace.

“Ablah kuma kamar yaya me kike nufi.?”
“ƙwarai kuwa Ablah nake zargi domin kuwa na sanar da ita cewa zanyi kisa idan ta isa ta gane wa zan kashe ta kare rayuwarsa, sai take cemin ai ta san ita nake hari kuma na sani nayi sake ɗan zaki ya girma kuma na mutuwarta ba abu bane mai sauƙi, ina zargin tana min laɓe duk yadda akayi laɓen tamin taji maganar da mukayi akanta hakan ne yasa ta nemo numbern ki ta turo miki wannan saƙon saboda ta ruɗa mu kuma ta raba mana hankali mu fara tunanin akwai wanda yasan sirrin mu bayan ita, amma kin kira layin ne sanda aka turo miki saƙon?”

Shuru Aunty Amarya tayi ko kaɗan tunaninta bai kawo mata cewa Ablah zata haɗa wannan shirin ba sai yanzu ta fahimta murmushi Hajiya Mansura ta yi tare da sakin ijiyar zuciya.

“Ko yanzu ma kafin na fito na kira layin a kashe, ana turo saƙon maybe aka cire sim card ɗin, lallai tayi wasa da hankalina, amma zata yabawa aya zaƙinta, abinda zai faru yanzu ki dinga kula sosai da ita domin kuwa tana bibiyarki ne, ki kiyaye duk sanda zamuyi waya ki tabbatar kin shigo ƙuryar ɗaki ke idan ma ta kama ki shiga toilet, dole zata mutu bazamu fasa kasheta ba saboda taji wannan, salo kawai zamu sauya da kuma hanyar kasheta, mu bar kanta yanzu saboda zata nemi kare rayuwarta ko ta halin yaya, Maimu zamu kashe target ɗin mu zai bar kan Ablah ya koma kanta, ba zamuyi kisan ta hanyar guba ba, wata hanyar zamu nema zanyi tunani akan hanyar zan nemeki, ni yanzu tafiya zanyi saboda nabar Najib a gida yana jirana.”

Numfashi Aunty Amarya ta saki tare da cewa.

“Shikenan muje na taka miki.”
Tayi maganar suna fitowa a falo sukaci karo da Ablah zata shiga kitchen murmushi ta saki tana kallon Hajiya Mansura tahowa tayi gabansu tare da cewa.

“Sannu da zuwa Hajiya Mansura, ashe kina cikin gidan, kwana biyu babu labarinki kullum ina cewa Aunty Amarya ta gaisheki hope tana gaya miki dai ko?”

Tayi Maganar tana murmushi, Hajiya Mansura murmushin itama ta saki tana jin tamkar ta shaƙe mata wuya ta kasheta tace.
“Meyasa zaki damu da shuru na ai idan kikaji shuru alkairi ne, saƙon da zan aiko miki ya wadata basai kin ganni ba, da alama kin gaji da wannan duniyar kina buƙatar tafiya hayatul mahayat domin ki huta karki damu zan aikaki nan ba da jumawa ba.”
Murmushi mai sauti Ablah ta saki tare da cewa.

“Hayatul mahayat ai wannan rayuwar kowa zaiyita meyasa sai ni kike so nayi gaba kafin ke, hmmm! Oh na tuna ashe fa na tsare muku hanyar cin duniyarku da tsinke ne, sai kuma gashi mutuwata bazata zo muku da sauƙi ba, dole dai saina takurawa rayuwarku naga bayan zaluncin ku kafin na tafi zuwa ga rayuwar da kuka buƙatar ku turani.”
Tayi Maganar bakinta ɗauke da dariya, Hajiya Mansura a hasale cike da jin zafin maganarta tace.
“Ke har kin i…………..”
“Na isa harna fi, basai kin ƙarasa ba, na hutar dake, maza tafi ki cigaba da ƙulla sharrri kiga yadda zai dawo kanki.”

Tayi Maganar tana barin wajen, Kallon Aunty Amarya Hajiya Mansura tayi cikin ɓacin rai ta fice a fusace.

*****

“Ga saƙon boka na karɓo kuma yace lallai kar a saɓa daga sharuɗan daya gindaya yace idan aka saɓo koda guda ɗaya ne to duka aikin ya rushe ya zamo dole ki kula domin gabatar da wannan aikin yana da matuƙar wahala, dole sai kin kula ki tuna da nasararki kiji tsoron faɗuwarki.”

“Mama bazan saɓa ba duk sharuɗan daya gindaya zanyi dai-dai ko guda ɗaya bazan saɓa ba.”
Murmushi Mama tayi tare da cewa.

“Na farko kwallin nan zaki saka ki tunkari sa dashi ki tabbatar kun haɗa idanu dashi, kar kuma ki yadda ki haɗa ido da wani ɗa namiji idan ba Al’ameen ba, sannan sai wannan ƙasar ki tabbatar kin watsa a ƙofar gidan su, inda duk wanda zai fito daga cikin gidan sai ya taka koda tayar motar su ne ta taka wannan ƙasar bakinsu ya rufu akanki babu mai aibataki ko kusheki, zasu amince dake babu jayayya ko dogon bincike aka aurenki sai na ukun wannan turaren shima ki tabbatar kin watsar inda shi kaɗai ne zai shaƙi ƙamshinsa a wannan lokacin, kar wani ya shaƙa sai shi ya fara shaƙa, sai na huɗu, wanda shine mai wahalar, shi dole sai kin samu wanda zai shiga cikin gidan domin kuwa boka yayi duba cewa akwai wata tsohuwar da zata kawo tangarɗa a cikin Maganar aurenki kuma kowa na jin maganarta a cikin Family ɗin, to shine yayi aiki akanta, wannan kwalbar za’a ijiye a ƙarƙashin gadonta shikenan an rufe mata baki wannan shine aikin da boka ya bayar shi na tsohuwar koda an kuskuresa babu matsala sai dai tangarɗar da za’a samu a wajen ta amma sauran ukun idan kika kuskure kin rusa aurenki da kanki ki kiyaye.”
Dariya Nafeesa tayi tare da cewa.

“Bazan kuskure ba Mama komai sai ya tafi dai-dai hatta ga na tsohuwar ma sai nasa an ijiye min karki damu Mama komai zai tafi dai-dai zamuyi Nasara burinmu zai cika ina alfahari da ke mama.”

“Bani da haufi akanki Nafi nasan zaki iya, sai dai ina buƙatar ki kulane domin kuwa ba’a raina kuskure, ki ɗebi maganin ki sanya acikin jakarki Allah ya bamu Nasara mu samu wannan damar.”

Murmushi Nafeesa tayi tare da cewa.
“To Mama bara na kwashe sai naje na samu Jamila mu nemi hanyar da tafi sauƙi.”
”to shikenan ki gaida ta.”
Da zataji ta amsa tare da ɗebe maganin tasa a cikin bag ɗin ta sannan ta fice.

Abbas Zaune yake cikin falon Momy ya sanya tv a gaba yana kallon aljazira, Momy ce ta fito tare da zama a ɗaya daga cikin kujerun da yake falon, wayarsa tayi ringin dubansa ya kai ga wayar Rufaid
Daga can Rufaida dake zaune gefen Hajja kaka ta gyara zamanta tana kallon Hajja kaka da ta sanya mata idanu tamkar zata cinyeta miƙewa tayi tabar wajen tare da shige bedroom.

“Abbas ina son sanin wani abu game da Nafeesa Yarinyar da yaya Haidar yake so wacce yanzu suke faɗa da yaya Al’ameen akanta, ina son nasan menene nufinta akansu, Saboda tana neman haddasa gaba a cikin Family ɗin mu, sannan itace wacce ta tokare min burina akan yaya Haidar ta hana yasoni, dan Allah ka taimaka min Abbas.”

Shuru Abbas yayi yana kallon Momy da hankalinta baya kansa cewa yayi .
“Rufaida wannan ba hurumi na bane ban cika sa kaina a cikin abinda bai shafeni ba, duk abinda kikaga na shiga to ya na neman tokare min hanyata ne, Hmmm! Ita Nafeesan da kuke magana akanta na santa farin sani sai dai bansan dalilin da yasa take gwara kan Haidar da Al’ameen ba, Karuwa ce mai bin mazan titi Saboda kuɗi mayyar kuɗi ce akan kuɗi babu abinda bazata iya aikatawa ba, abinda na sani kenan akanta amma zai iya yiwuwa tabar Haidar ne tabi Al’ameen saboda kuɗi.”

Shuru Rufaida tayi, kafin tace.

“Wannan ba dalili bane da zaisa ta guji yaya Haidar saboda shima yana da kuɗi bashi da banbanci da yaya Al’ameen ni ina tunanin akwai dai wani dalilin da yasa tayi haka, dan Allah ka dubi girman Allah ka bincika min ina son yaya Haidar bana son na rasa shi kuma bana son abinda zai cutar da shi.”

Murmushi Abbas yayi yace.

“Idan har bakya son ki rasashi to dole ki cire Nafeesa daga idanunki ki barta da Al’ameen hakan shine zai baki damar mallakar abinda kike so, karki yi bincike a kanta domin rabuwarta da Haidar shine zai baki damar aurensa, idan ya rasata dole zai dawo gareki ko maleji ne yayi dake tunda bake bace muradinsa.”

<< Aminaina Ko Ita 50Aminaina Ko Ita 52 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×