Skip to content
Part 50 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Momma na kasa fahimtar meke faruwa ne a cikin gidan nan mtsss hmmm! Yaya Al’ameen a yanda na fuskance sa yau bazai amince da maganar kowa ba akan wannan Nafeesan.”

“Nima na fahimci hakan yanzu kuma mun janye ƙudirinmu Allah yasa hakan shi yafi alkairi.”

“Ameen Momma shine addu’a.”

Tayi Maganar tana tashi ta haura sama bedroom ɗin Haidar ta nufa tare da kwankwasawa sai dai bai amsa mata ba hannu tasa ta buɗe ƙofar sannan ta shige ciki yana zaune takure jikin bed ɗinsa sai kuka yake tamkar ƙaramin yaro, numfashi Rufaida ta saki cike da tausayin halin da yake ciki ta zauna a gefensa tare da cewa.

“Yaya Haidar kuka bai dace da kai ba kai namiji ne da hkr da juriya aka sanku, dan Allah ka sanyawa zuciyarka hkr ka barwa Allah lamarinsa shiyasan me yake nufi da kai wannan ƙaddara ce kayi ƙoƙari ka rungumi ƙaddararka.”

Idanunss ya ɗago da sukayi jajur ya sauƙe su akan Rufaida wani irin kallon tsana yake mata ƙofa ya nuna mata tare da cewa.

“Ki daina min daɗin baki domin kuwa bazaki taɓa shiga zuciyata ba, na tsaneku domin kuwa dukkan mata basu da Amana macuta ne ku mayaudara maciya amana bazan ƙara amincewa da wata mace ba a wannan rayuwar ansha ni baza’a kuma ba ki fitar min daga room bana son ganinki I hate you!.”

Yayi Maganar cikin ƙaraji tamkar zai shaƙota, runtse idanunta Rufaida tayi cikin sanyin murya tace.

“Karka yankewa dukkan mata hukuncin wata ba’a taro an zamo ɗaya ba, ko da ɗabiarsa ko k…

“Karki ƙarisa maganar da take bakinki ki fitar min daga room dan Allah ki barni da baƙin cikin da yake damuna shi kaɗai ma ya isheni bana ƙaunar ganinki Rufaida nasha faɗa miki da dan Allah ki fita daga rayuwata.”

Shuru Rufaida tayi tare da miƙewa tace.

“Allah ya huci zuciyarka.”

Tayi Maganar tana fita daga ROOM ɗin cikin sanyin jiki.

Tuƙi kawai yake amma hankalinsa baya jikinsa takaici da baƙin cikin sauyawar Abokansa sun damesa ya rasa hanyar da zaiyi maganin wannan matsalar da wannan tunanin ya shiga unguwar mai tama a ƙofar gidan su Nafeesa yayi parking ya juma tsaye kafin ya samu yaron da yaje ya kira masa ita, bata wani juma ba ta fito tana yauƙi da kallon tsana Faruq ke binta domin kuwa shi kyamarta ma yakeji tsayawa tayi tana ƙare masa kallo sama da ƙasa ta taɓa ganin pictures ɗinsa da labarin sa a wajen Haidar.

“Faruq ko?”

Tayi Maganar a gadarance bakinsa ya taɓe tare da cewa.

“Kisan wanene ni bashi bane ya kawo ni nan Nafeesa Magana nazo nayi da ke ta fahimta.”

“Ina sauraranka faɗi abinda ya kawoka.”

“Nafeesa kina sane da kin aikata mungun abu ko domin kuwa kin shiga tsakanin ƴan uwa biyu meyasa kikayi haka.?”

Murmushi Nafeesa tayi tare da harɗe hanunta a ƙirjinta tace.

“Faɗa kuma Faruq hmmm! To gaskiya ni babu wanda na haɗa faɗa amma akan waye kake min magana ne?”

“Ina miki magana ne akan Al’ameen da Haidar.”

“Okay na fahimceka yanzu, to meye abun haɗa faɗa Haidar bai dace da rayuwata ba, kuma bana ra’ayinsa shiyasa na fita daga rayuwarsa, shi ko Al’ameen mutumin kirki ne wanda ya dace a sosa dani dashi zuciyoyin mu sun kamu da son juna to meye aibu a ciki dan munyi Soyayya, ba haramun muka aikata ba, ba kuma zina zamuyi ba aurene sunnar Manzon Rahama.”

A fusace Faruq yace mata.

“Zinar ma ai kin saba aikatata, Nafeesa ki fita daga cikin rayuwar ƴan uwana idan ba haka ba kuma na rantse da sarkin da yake busa min numfashi sai kinyi danasani a rayuwarki kuma na rantse miki da Allah bazan taɓa bari ki auri Al’ameen ba zan duƙushe ki na kuma tozarta ki.

Faruq baya faɗa amma muddun aka tsokanosa faɗansa baya taɓa ƙarewa kiyi gaggawar samawa kanki lafiya tun kafin kiyi danasani keda malalatan iyayenki waɗanda suka kasa baki tarbiyya banza akuya wacce ko wani bunsuru yake munfi ƙarfin haɗa zuri’a da karuwa.”

Yayi Maganar yana huci Nafeesa madadin ranta ya ɓaci sai sheƙewa da tayi da dariya tare da cewa.

“Oh wato so kake kaga ina ta yawo a tiiti ina bin mazan shine burinka, to gashi kuma dai ɗan uwanka zai auri karuwar ya rabata da rayuwar titi na yabawa yunƙurinka ka gwada cika bakinka ka bani waje domin kuwa ko uban da ya haifi Al’ameen bai isa dakatar da aurena dashi ba, balle kai banza a banza ƙaramin tsagera.”

Murmushi Faruq ya saki tare da cewa.

“Okay yayi za kuma ki ga yadda zan rusa wannan auren ayi mugani idan tusa tana hura wuta.”

Yayi maganar yana buɗe motar sa ya shige tare da buleta da ƙura, bakinta Nafeesa ta cije cike da takaicin abinda Faruq ya mata sai dai tasan babu abinda zai iya cika bakin banza yake tana garantin aurenta da Al’ameen tunda boka ya tsaya mata tasan babu abinda zai gagara.

Ablah tana zaune cikin falon Al’ameen ya shigo ganinta ya sashi kawar da kansa gefe yana haurawa sama, numfashi Ablah ta saki tare da miƙewa tabi bayansa, bedroom ɗinsa ta shiga yana zaune da waya a hannunsa zai kira Nafeesa yaga Ablah ta shigo ijiye wayar yayi tare da cewa.

“Meya kawoki bedroom ɗina Ablah?”

Baki sake Ablah ke kallonsa tare da cewa.

“Yaya Al’ameen meya kawo ni bedroom ɗinka kuma kake tambaya, wai me yake faruwa ne kam kwana biyu naga ka sauya min kana min wasu abubuwa waɗanda bana fahimta, kama daina bani kulawa abubuwa da yawa kana min su waɗanda suke ƙona min rai wai me yake faruwa ne?”

Kansa Al’ameen ya ɗago cikin halin ko inkula yace mata.

“Kinga bacci nake sonyi dan Allah kijeki karki ɓata min raina Please kije anjuma zan nemeki idan na tashi.”

“Karna ɓata maka rai, ka faɗa min meke faruwa hankalina bazai kwanta ba idan har ina ganin sauyi daga gareka, ina sonka fiye da komai a rayuwata bazan iya jurewa sauyawarka gareni ba.”

Miƙewa Al’ameen yayi yana ƙare mata kallo tare da sakin murmushin gefen baki ya furta.

“Kinga Ablah bari na sanar dake abinda kikeson kiji, ki cireni daga layin rayuwarki domin kuwa na cireki a zuciyata ma’ana dai bana sonki Ablah kiyi haƙuri bazan iya aurenki ba Saboda baki dace da rayuwata ba, kije ki samu dai-dai ke.”

Tamkar sauƙar aradu haka taji maganarsa wani irin tsinkewa zuciyar Ablah tayi numfashin ta ne ya ɗauke na wasu sakonni, jijiyoyin jininta taji sun dakata da aiki tamkar gunku haka ta dawo, ta gagara ko da motsi, sanda Al’ameen ya daka mata tsawa sannan ta firgita ta dawo hankalinta nuna kanta tayi da yatsa bakinta na rawa ta furta.

“Al’ameen yau ni kake cewa ban dace da Rayuwarka sanda nake cewa bazan soka ba saboda ban dace da rayuwarka ba, me kace min ka tuna cemin kayi kai babu ruwanka da dacewa kana sona kuma zakayi rayuwa dani ashe duk ƙarya kake min yaudarata zakayi, hmmm idan wasa kake min ka daina zuciyata bazata ɗauki wannan wasan ba.”

Tayi maganar jikinta yana rawar tashin hankali zuciyarta kuma sai bugawa takeyi, Al’ameen murmushi ya saki yace.

“Kinyi kuskuren ɗaukar wannan maganar a wasa, domin kuwa maganar gaskiya nake miki I hate you, bana sonki da Nafeesa zanyi rayuwa itace ta dace da rayuwata ba keba fice min daga bedroom karki kuma koda kallona ne bare kiyi tunanin kimin magana.”

Wani kuka Ablah ta saki tana durƙusawa tare da riƙe ƙirjinta ta ce.

“Karka min haka yaya Al’ameen, wallahi rayuwa zata min wahala muddun babu kai a cikin ta, na saita rayuwata da kai na sabawa zuciyata da ta buga a ko wani minti da Soyayyarka, dan Allah kamin sutura karka gujeni.”

“Kinga ki fice min daga room kafin na saka a fitar min dake bani da lokacin sauraronki tunda bani zansha wahalarba sai kiji ki ta fama da wahalarki muddun soyayyata ce sutura a gareki to kuwa zakiyi yawo tsirara, ki tashi ki fice min da gani.”

Miƙewa tsaye Ablah tayi tana tangaɗi ta fito daga bedroom ɗinsa tayi nata tana kuka cike da tashin hankali a bedroom ɗin ta ta faɗa ta saki kuka mai sauti, sosai take kukan harda majina ta juma tana kukan har muryarta sai da ta dishe, tashi tayi ta zauna tare da kiran Abbas a waya, kusan 4miss call bai ɗaga ba Hafsa ta kira cikin Sa’a kuwa ta ɗauka cike da tashin hankali tace idan ta dawo daga jamji jibi tazo ta sameta kafin ta katse kiran tana ijiye wayar kukan ta kuma sawa tana cikin kukan kiran Abbas ya shigo hannu tasa ta ɗaga kiran tare da cewa.

“Hello Abbas kana ina?”

Abbas dake zaune shida abokinsa Usman ne cikin Gidan gonar Daddynsa ya ce.

“Ina gidan gonar Daddy lafiya kuwa Ablah naji muryar ki kamar kina cikin tashin hankali da alama kinyi kuka tell me meke damunki.?”

Cikin rawar murya mai cike da kuka tace.

“Kazo gida ka sameni, ina cikin matsala rayuwata tana cikin haɗari.”

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Ina zuwa yanzu.”

Yayi maganar yana katse kiran tare da miƙewa tsaye yacewa Usman.

“Usman ka jirani akwai matsala zanje na dawo.”

“Okay ba damuwa ina jiranka”

Motar sa Abbas ya shiga baifi 20 minute ba daga inda yake ya iso Ambassador Ahmad Giwa Estate parking yayi tare da kiranta ya sanar da ita yazo babu jumawa ta fito idanunta sunyi jajur tamkar zata faɗi motar tasa ta buɗe ta shiga ta jingina kanta jikin sitiyarin motar hawaye na biyo idanunta Abbas cike da tashin hankali ya Dubeta tare da cewa.

“Ablah ki dakatar da wannan kukan hakan yana ƙona min zuciyata, ki sanar dani me yake faruwa.”

“Abbas ina cikin tashin hankali rayuwata tana shirin dukushewa, yaya Al’ameen ya juya baya yace baya sona ya tsaneni na shiga Uku rayuwata ta nukushe.”

“Baki shiga uku ba, babu kuma abinda zai nukusar miki da rayuwa meyasa Al’ameen zaice ya tsaneki ashe Soyayya tana zama ƙiyayya ca nake duk Soyayyar da ta ginu bisa amincewar Mutum biyu kuma bisa gaskiya da amana babu abinda zai rusata ko kawo tasgaro a cikin ta rayuwa ta farin ciki da kuma ɗaurewa bisa jagorancin inuwar Aure shine zai tabbata a garesu, sam bai kamata mu dinga juyawa masoyanmu na gaskiya baya ba wannan karya zuciyace Ablah Soyayyar ɓari ɗaya sam bata riba kamata yayi wanda yace baya sonka ka rabu dashi ka rungumi ƙaddararka na tabbata zaka gamu da Soyayyar da tafi wacce ka rasa, meyasa Al’ameen ya tsaneki wani laifi kika masa.?”

Hawayen idanunta ne suka ƙaru hanu tasa ta goge hawayen tare da cewa.

“Ban san laifin da na masa ba, ban san meyasa ya tsaneni ba, hankalina yana tashe bance bazan rayu ba danna rasa Al’ameen sai dai nasan zanyi macacciyar rayuwace da babu zuciya a cikin ta, domin kuwa na juma da basa zuciyata rayuwa zata wahalar dani idan babu shi a cikin ta, sai dai kukana da ƙarin takaicina shine cin amanar Al’ameen ba iya kaina ta tsaya ba har kan Haidar domin kuwa ya faɗa min Nafeesa zai aura abun ya bani mamaki domin kuwa a baya ya tsaneta tsana ta haƙiƙa to meyasa yanzu yake sonta?

Sosai ta basa tausayi domin kuwa yasan yana sonta Soyayya ta gaskiya, wallahi da ace Al’ameen zai sauya alƙibilarsa zai sadaukar da soyayyarsa saboda farin cikin ta domin kuwa ya lura Al’ameen shine burinta.

“Ablah mafi akasarin lokuta abinda muke so shike wahalar damu, mukan zurfafawa Soyayya a ƙarshe ta dawo damuwa a garemu, hmmm! Al’ameen yayi kuskure a rayuwarsa domin kuwa sakin mace irinki Babbar asarace, amma meyasa kika zaɓi ki sanar dani damuwarki shin kina tunanin zan iya miki maganin matsalarki ne.?”

“Saboda na yadda da kai ina ɗaukar ka matsayin abokina hakan ta faru ne sakamakon ceto rayuwata da kake daga shiga cikin haɗari, nasan zaka taimakeni shiyasa na zaɓi na sanar da kai.”

Numfashi ya saki yana dafe kansa tare da ɗagowa yace.

“Ban isa na dawo da soyayyarki a zuciyar Al’ameen ba domin kuwa zuciyarsa ce kuma mallakinsa, shike da ikon sarrafa kayansa bansan yadda zanyi na miki maganin wannan matsalar ba, sai dai abinda nake tunani babu ta yadda za’ayi Al’ameen ya faɗawa Soyayya da Nafeesa lokaci ɗaya haka ba, lallai akwai wani ƙulli wanda bansan menene ba, amma na miki alƙawarin bincike akan tsakanin su idan har zargina ya tabbata to na miki alƙawarin sai na kunce wannan ƙullin, naji Faruq ya shigo gari, shi mutum ne mai fahimta wanda bashi da gaba zan nemesa muyi magana kiyi haƙuri ki share hawayen ki komai zai daidaita.”

“Wani ƙulli zata masa shi dai kawai gani yake ban dace da rayuwarsa ba Nafeesa ta fini asali shiyasa ni zai gujeni.”

Numfashi Abbas ya sauƙe tare da cewa.

“Ablah ya kamata ki binciki asalinki a wajen mahaifiyarki sanin dangin mahaifinki shine gatanki, ya kamata ki sansu suma su sanki bawai mahaifiyarki ta dinga baki labarinsu a baki ba, ni zanje sai kin jini.”

“Shikenan na gode sosai Abbas ya maganar su Aunty Amarya akwai wani shiri da suke yi ne.?” Murmushi Abbas yayi yace.

“A wannan halin da kike ciki bai kamata ki saka damuwar su amarya ba sai damuwar ta miki yawa har yanzu shuru banji sunyi wani yunƙuri ba, idan ma kuma sunyin ki barni dasu.”

Kanta ta ɗaga tare da buɗe motar ta fita, motar yaja ya kwashi hanya, yana son Ablah fiye da komai a rayuwarsa, gefe guda kuma ga Ablah ta basa dukkan yardar ta gani take zai iya mata maganin matsalarta, ya zamo wajibi a garesa ya sadaukar da soyayyarsa muddun yana son farin cikin Ablah, rayuwa da mutumin da baya sonka sam babu armashi.

Har koma cikin gidan gonar nazarin da yakeyi kenan.

Misalin ƙarfe Huɗu na yammacin ranar juma’a Daddy ya sauƙa daga jirgi Al’ameen shi da Faruq suka ɗaukosa, cike da farin ciki Al’ameen ya rungume mahaifinsa mota ɗaya suka hau suka dawo ambassador Ahmad Giwa Estate, falon cike yake da hali kowa yana murna da dawowar Daddy yayin da ƴan aikin gidan suke ta hidimar jera abinci a daining Daddy bai juma da shigowa ba shima Abi ya jirgin su ya sauƙa shida Auntyn Faruq, su Haidar da Rufaida ne suka ɗaukosu Abi sanda yaga Haidar sosai ransa ya ɓaci domin kuwa yayi baƙi ya rame sosai ya yi baƙi, part ɗin su suma suka sauƙa, sanda sukayi wanka sukaci abinci sannan kowa ya shiga room ɗinsa ya huta.

Al’ameen yana kwance yaji ringin ɗin wayarsa ɗagawa yayi yaga Nafeesa ce murmushi ya sanya tare da ɗagawa.

“My love nayi kewarki.”

Daga can murmushi Nafeesa tayi tana kallon Jamila ta sanya kukan munafurci tare da cewa.

“My dear kaine ka turo Faruq yazo yaci mutuncina?”

Miƙewa zaune Al’ameen yayi tare da furta.

“Whattttttt! Me kike nufi shi Faruq ɗin ne ya ci miki mutunci?”

“Ƙwarai kuwa har da marina , wai na shiga tsakaninka da Haidar sannan yamin alƙawarin sai ya Dakatar da aurena da kai ba irin cin mutuncin da bai min ba.”

Cike da ɓacin rai Al’ameen yace.

“Bari naje na samu Faruq ɗin ina zuwa zan kiraki.”

Yayi maganar yana katse kiran tare da tashi ya nufi part ɗin su Faruq darect bedroom ɗin FARUQ ya shiga yana zaune ya saka system ɗinsa a gaba yaji an bugo masa ƙofar ɗaki da ƙarfi ɗagowa yayi ya kalli Al’ameen tare da cewa.

“Lafiya zaka shigo min bedroom a fusace?”

Hannu Al’ameen ya saka ya watsar da turaren dake mirror ɗin Faruq yace.

“Uban waye yace kaje gidan su Nafeesa ka ci mata mutunci?”

Murmushi Faruq yayi tare da gyara zamansa yace.

“Oh dama akan wannan ne ka shigo min a fusace, naci mutuncinta sai ka hukuntani ubana, Al’ameen kasan Allah indai wannan karuwar titin ne yanzu na fara cin ubanta idan tayi wasa ma wata rana sai since mata zani a kasuwa…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 52Aminaina Ko Ita 54 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×