“Hmmm! Kana bani mamaki Faruq meyasa kake son shiga abinda babu ruwanka a ciki, kaga wannan fa rayuwata ce ba taka ba dan Allah ka barni nayi abinda naga ya dace da rayuwata, koda HIV ne a jikin Nafeesa bazai hana na aureta ba, ya kamata ka gane cewa babu wanda ya isa ya dakatar dani da aurenta dan haka ka daina bawa kanka wahala.
“Oh haba ashe rayuwarka ce, aini ban sani ba sai yanzu da kake faɗa min nayi zaton ai rayuwarka tawace ashe ka sauya lamarin, to bari kaji muddun dai ina doron ƙasa bazan taɓa barinka ka auri wannan yarinyar ba.
A mungun hasale Al’ameen ya buɗe bakinsa da niyyar magana Faruq ya dakatar dashi da cewa,
“Daina ɓata bakinka saboda maganarka bazai min amfani ba yanzu kaga fitata idan ka gama ka yi gaba
Yayi maganar yana saka kai ya fice daga ROOM ɗin Al’ameen yatsarsa ya cije cike da takaici shima ya sa kai ya fice.
Washe gari Hafsa da yamma tazo Ahmad Giwa Estate, ta samu Ablah duk ta jeme a cikin kwana ɗaya fuskarta ta tuje ga idanunta da suka faɗa ta zauna tayi shuru sai hawaye dake bin idanunta, zama Hafsa tayi tare da cewa,
“Ablah wai meke faruwa ne tun jiya nake cikin zullumi, tsoro da fargaba duk sun cika min ciki, gashi kuma nazo na sameki a cikin wani irin yanayi, amarya ce ta miki wani abun.
Maimakon Ablah tayi magana sai ta fashe da kuka mai cin rai, idanunta Hafsa ta runtse tare da cewa,
“Kina ɗaga min hankali Ablah zuciyata sai bugawa take dan Allah karki kasheni da zullumi ki faɗa min meke faruwa?”
“Hafsa rayuwata tana cikin garari Hafsa zuciyata zata fashe, bazan iya rayuwa babu shi ba shine farin ciki na Hafsa.
Shuru Hafsa tayi na wani lokaci kafin tace,
“Idan na fahimceki matsala kika samu da Al’ameen kenan.”
Kanta ta ɗaga tana shashsheƙar kuka tace
“Yace baya sona baya son ganina ya tsaneni bansan wani laifi na masa ba haka kawai ya gujeni dan Allah Hafsa kije ki basa hkr ya dawo gareni bazan moru ba idan babu shi.
A matukar razane Hafsa ta kalli Ablah tare da cewa,
“Whattttttt! Shi Al’ameen ɗin ne ya faɗa miki haka wani irin laifi kika masa haka innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Kai kai kai Rayuwa ina zaki damu cin amana yayi yawa a wannan Duniyar babu wani mutum ɗaya mai gaskiya.
Kafin Ablah tayi Magana sukaji tafin Aunty Amarya tana sakin dariya tace,
“Da kyau wannan abu yamin daɗi, to fa kinga wanda kike karewa yau ya kware miki baya, a hakan zaki kare rayuwarsa yana tozartaki, hmmm! Ablah kinyi kuskuren amincewa da Al’ameen domin kuwa kema kin san ruwa ba sa’an kwando bane ta yaya kina ƴar matsiyata kice zakiyi rayuwa da ɗan masu arziki wanda ya gaji arziki gaba da baya, mtsss! Bar wannan ma kinsan gajeren rayuwa zaiyi to meye zaki damu dan ya gujeki, biyoni kawai ki mara min baya mu kashesu kici arziki ko banza zaki fita acikin talauci.
Hafsa miƙewa tayi tsaye tana jefawa Aunty Amarya mungun kallo tace,
“Waya faɗa miki saboda tana sonsa take kare rayuwarsu, tun kafin ya furta mata kalmar Soyayya take ƙoƙarin karesu daga sharrinku, kuma bazata sauya ba akan wannan tsarin dan Allah takeyi badan Soyayya ba, ki sani Ablah bazata taɓa mara miki baya ba, saboda halayenki abun kyama ne ga al’umma, ki sani idan Al’ameen bai Auri Ablah ba bazata mutu ba zatayi rayuwa kamar na kowa ki sani.
Dariya Aunty Amarya ta saka tare da cewa
“Good yayi kyau bari mu gani ko zata iya dakatar dani.
Tayi Maganar tana fita, Ablah kuwa tsabar damuwar dake damunta ko kanta bata daga ta kalli Aunty Amarya ba.
“Ablah ki faɗa min me kika yiwa Al’ameen.?
“Hafsa me zan masa kinsan halina kinsan abinda zan iya aikatawa da wanda bazan iya aikatawa ba, babu abinda na masa haka kawai ya gujeni baya sona, na shiga uku.
“Baki shiga uku ba Ablah babu abinda ya shigar dake Uku, ki bari ni zanje office ɗinsa gobe zamuyi magana, kiyi haƙuri ki daina kukan Ablah na sanki da hkr da juriya kefa me hkr ne akan komai ki daure ki cigaba da addu’a insha Allah komai zai wuce.
Kanta ta ɗaga tare da kwantar da kanta jikin Hafsa, Hafsa ta juma a gidan tana rarrashin Ablah, da ƙyar ta samu hawayenta ya tsaya, sai dai damuwarta taƙi raguwa, sai yamma lis ta koma.
Da daddare gabaki ɗaya family ɗin suka haɗa meeting a babban falon da Daddy yake ijiye baƙinsa harda yayan Inna Jumma, Baffa Sale, Abi shine ya buɗe taron da addu’a, Inna Jumma ce tayi gyaran murya tare da,
“Baffa Sale gaka ga Amadu da ƴan uwansa ga kunan zaune kuma nine na kiraku saboda wata matsala da take faruwa a cikin wannan family ɗin, Ga Aminu da ɗan uwansa Ali matsalar ta shiga tsakaninsu akan wata shegiya fitinanniyar yarinyar shi Ali yace Aminu ya ƙwace masa budurwa shi kuma Amadu ya musa hakan yace bai sani ba ƙarya Ali yake masa to dai har dambe sunyi kuma suna gaba babu mai kula ɗan uwansa to bazan lamunci wannan ba, Uwar Amadu bata raye ta mutu kuma nasan da Gaji tana raye wallahi bazata bari wannan matsalar ta girmama ba zata dakatar na mata wannan shedar amma ga maimuna uwar Ali tana raye da idanunta tana kallon abinda yake faruwa amma babu wanda take yiwa faɗa a cikin su babu matakin da tayi ƙoƙarin ta ɗauka saboda rashin hankali irin nata Ali zagina yaso yayi amma maimuna gaki nan baki zo kin sameni kin bani hkr akan abinda ɗanki ya min to ni wannan bai dameni ba, amma fa ki sani ga iyayensu maza su zasu yanke hukunci, Baffa Sale kaji abinda yake faruwa.”
Numfashi Baffa Sale ya saki tare da duban Haidar yace,
“Gadanga abinda Jummai ta faɗa hakane.”
“hakane Baffa Sale sai dai ni ban mata rashin kunya ba, kawai tana bin bayan Al’ameen ne ni kuwa ta wareni gaskiya da na faɗa mata shi take kallo a matsayin wai na zageta, sannan Baffa Sale Al’ameen yaci amanata ya ha’ince ni ban taɓa zaton cewa zai min wannan cin amanar ba.”
Ya ƙarisa maganar cikin karyewar zuciya gami da baƙin ciki, Baffa Sale duban Al’ameen yayi yace,
“Hakane abinda Gadanga ya faɗa Aminu?”
Al’ameen babu kunya bare shakka yace
“Ba haka bane Baffa Sale, ni ban ƙwace masa budurwarsa ba, saboda bata sonsa ni take so kuma nima ina sonta, Soyayya ce a tsakanin mu mai ƙarfi, dan haka ba ƙwace na masa ba, shine yake ɗaukar hakan a matsayin ƙwace, amma ba ƙwace bane Soyayya ce kuma ina son Daddy suje su tambayo min Auren ta gobe zan sanar da ita ta sanar da iyayenta.”
Gabaki ɗaya wadanda suke wajen da kallon mamaki da rashin Kunyar Al’ameen suke kallon sa Inna Jumma tafi kowa kaɗuwa cikin masifa ta miƙe tare da cewa,
“Aminu me kake cewa so kake kace min dama maganar Ali gaskiya ce, eh lallai ka cika tantirin munafiki Aminu, eyyee! Yau naga rashin kunya ni Jumma, ashe Ali kana da gaskiya, to ita kuma Ablah daka ɗanɗanawa bakinta zaƙin soyayyarka meye matsayinta a wajen ka.”
Babu shakka Al’ameen yace,
“Bata da wani matsayi a wajena bana sonta kuma bazan aureta asali ma na tsaneta.
Bakinta Inna Jumma ta buɗe tare da miƙewa tsaye tace,
“Ai kuwa karya kake baka isa ba domin kuwa baka da matar da ta shige Ablah itace matar ka, ba wannan shegiyar munafuka ba, Oh Ali ka yafe min ashe ka fini gaskiya.”
Bakinsa Haidar ya cije cike da ƙunar rai, Al’ameen kuwa miƙewa yace,
“Ni fa bazai yiwu ba babu wanda zai min auren dole abarni kawai da zaɓi na ehee babu wata Ablah da zan Aura.”
Inna Jumma zatayi magana Baffa Sale ya ɗaga mata hannu komawa tayi ta zauna tana huci numfashi Baffa Sale ya sauƙe tare da duban Al’ameen yace,
“Duk naji maganganun ku, da farko gadanga kai zan fara bawa hkr, abinda ɗan uwanka ya maka a mahanga ta hankali sam bai kyautu ba, amma ka sani da yiwuwa Allah akwai abinda yake nufi da haɗa ita yarinyar da Ɗan uwanka wataƙil shine mijinta kayi hkr ka ɗauki ƙaddara insha Allah Allah zai baka wacce ta fita, ka barwa ɗan uwanka ita Nafeesan yayi maganar yana maida kallonsa ga Al’ameen ya cigaba da cewa, Aminu Allah yasa haka shi yafi alkairi ka nemi afuwar ɗan uwanka, sannan ku janye gaba a tsakanin ku, baza’a je nema maka Aure yanzu ba sai anyi bincike akan yarinyar tukunna, Amadu sai kuyi bincike akan yarinyar idan kun samu ta gari ce sai aje a nemo masa Auren Allah yasa haka shi yafi alkairi.
Inna Jumma a zabure ta miƙe zatayi magana, Baffa Sale ya ɗaga mata hannu tare da cewa,
“Karkice komai na yanke hukunci kuma ya yanku.
“Kayi hkr Baffa Sale bazai yiwu ba bazan taɓa yadda da wannan Auren ba, ta yaya ma hakan zata faru Ablah tana raye da ranta ba mutuwa tayi ba wannan ai tamkar cin mutuncin ta ne bazan yadda da wannan ba muddun ina numfashi Aminu Ablah zai aura bazai lasawa yarinya zuma a baki ba ya ƙwace ya kawo mata maɗaci bazai yiwu ba.
Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa
“Inna ya kamata ki fahimci cewa rayuwa ta sauya ba ko wani yaro bane za’a masa Auren dole ya yadda ba kowa bane ki fahimta ni a nawa tunanin kawai abar Zaki da zaɓinsa Allah yasa haka shi yafi alkairi ita Ablar Allah ya bata wani mijin.
“Ƙwarai haka ne Inna maganar ambassador abar Al’ameen da zaɓinsa.
Abi yayi maganar yayin da Papa ya mara masa baya da cewa
“A ganina babu wani Illa dan ya Auri wanda ɗan uwansa yaso, Allah ya ƙaddara mijinta ne mu musu fatan alheri kawai.
Aunty Amarya ma cewa tayi
“Ƙwarai kuwa nima ina bayanku kawai a barsa ya auri wacce yake so”
Faruq ne ya miƙe a fusace tare da cewa
“Bazai yiwu ba ta yaya zaku amince da wannan maganar marar daɗin sauraro duk kun amince da ya auri Nafeesa a cikin ku babu wanda yayi tunanin ya ɗabiar Yarinyar da tarbiyyar ta yake ba, to baza’a ɗauko karuwa a kawo mana Cikin Family ba tazo ta haifa mana gurɓatattun ƴaƴa irinta domin kuwa rubutaccen alamari ne duk wanda yayi zina da ɗan wani shima sai anyi da tasa, dan kuma sanar dashi cewa bazai aureta karuwar titi ce.
A matuƙar fusace Al’ameen ya miƙe tare da shaƙo wuyan Faruq yana cewa,
“Ya isheka haka aibatata na faɗa maka cewa koda HIV take dashi ko itace ƙasar banɗaki mai ganin tsiraicin kowa sai na aureta, rayuwata ne ba taka ba, ka fita a hanyata Faruq kaima daga yau na raba gari dakai babuni babu kai, kowa yaje yayi rayuwarsa akan Nafeesa zan iya rabuwa da kowa, da kake kiranta karuwa ba gara ita ba ma tana da Asali ansan dangin uwarta dana ubanta, ita Ablah fa wayasan dangin ubanta bare na uwarta wama ya sani kota ƙszantacciyar hanya aka sameta ka sani bazanyi rayuwa da marar Asali ba ƴar Mace wacce bata samu tallafin namiji ba bare kuma tarbiyyar sa.
Yayi Maganar yana sakinsa tare da turasa baya da ƙarfi Faruq hannu yasa ya dafe bango cike da ɓacin rai, wannan maganar dai-dai a kunnen Ablah da ta shigo zata ijiye musu ruwa daga tsaye ta sake katon ɗin faron wani bugawa ƙirjinta yayi ji take falon na juya mata Hajijiya na ɗaukarta wani irin duhu ta gani take ta yanki jiki ta faɗi a wajen, gabaki ɗaya kallonta sukayi Inna Jumma runtse idanunta tayi cike da baƙin ciki da takaicin Al’ameen, Maimu ce ta miƙe da sauri ita da Inna Jumma suka yi kanta.