Girgiza ta Maimu ta hau yi tana ambatar sunanta, ita kuwa tana jin tsabar jiri ne ya kayar da ita idanunta sun rufe koda maganar bazata iya yinta ba, Inna Jumma ce tace Maimu da Rufaida su kamata su kaita bedroom ɗin ta, ɗagota da zasuyi ta samu damar buɗe idanunta da suka sauya kala na baƙin ciki da tashin hankali kallon Al'ameen take cike da ƙunar rai, a hankali ta zame jikinta daga su Maimu ta nufi Al'ameen tana tan gaɗi, ta tsaya a gabansa idanunta ne suka zubo da hawaye cikin wata irin. . .