Skip to content
Part 52 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Girgiza ta Maimu ta hau yi tana ambatar sunanta, ita kuwa tana jin tsabar jiri ne ya kayar da ita idanunta sun rufe koda maganar bazata iya yinta ba, Inna Jumma ce tace Maimu da Rufaida su kamata su kaita bedroom ɗin ta, ɗagota da zasuyi ta samu damar buɗe idanunta da suka sauya kala na baƙin ciki da tashin hankali kallon Al’ameen take cike da ƙunar rai, a hankali ta zame jikinta daga su Maimu ta nufi Al’ameen tana tan gaɗi, ta tsaya a gabansa idanunta ne suka zubo da hawaye cikin wata irin saiɓin murya mai cike da rauni ta fara magana.

“A duniya ina tsanar duk wanda ya aibata min mahaifiyata nayi takaici da danasanin saninka a duniya, cin mutuncin ka ya tsaya iya kaina banda Umma na domin kuwa ita ba mutumiyar banza bace duk da bansan ƙuruciyarta ba, a iya tashina da rayuwata da ita da mutumiyar banza ce bazan samu tarbiyya ba, kuma alhamdulillah! Ta bani tarbiyyar da masu uba suka gagara samu ta bani ilimin da masu uba basu samesa ba, ta kula da mu da iya ƙarfin ta da guminta ba tare da ta kauce hanya ba.

Maganar asali da kakeyi bazan kauce a nan ba har sai Umma tazo ta faɗa min asalina a gabanka wataƙil kaji kunya, kaico da rayuwa da wanda baisan darajar ɗan adam ba ko a cikin mafarki ban taɓa zaton cewa zaka aibatani da mahaifiyata ba, koda kuwa shegiyar ce ni, nayi yaƙi da mutuwa akanka Al’ameen kuma nayi nasara akan ƙaddarata, naje har bakin gaɓar mutuwa saboda kai amma ashe kaima dunduniyata kake ci kana burin kashe min rayuwata baka tsaya iya kashe min zuciyata da kayi ba har sai ka nemi kaini kabari, ka Sani bani nace ina sonka ba, kaine kace kana sona ka nace min ina gudunka saboda gudun irin wannan ranar amma haka ka dinga bina kana nuna min baka fi ƙarfina ba, har sai da ka saka na amince da soyayyarka ashe yaudararriyar soyayya ce kake min mena ci maka a rayuwa mena maka da zaka wulaƙanta ni Al’ameen ka sani idan ka cuceni Allah bazai barka ba, na sani akwai ranar da zaka yi nadama da danasani ranar da zaka nemeni ni kuma a lokacin na maka nisan da bazaka taɓa kamoni ba.”

Juyawa tayi ta kalli Inna Jumma tare da sunkuyawa a gabanta tace.

“Inna Jumma ina roƙon alfarma a gareki ina roƙonki da Allah da Manzonsa ki saka aje a ɗauko miki Umma dan Allah.”

Kanta Inna Jumma ta girgiza tare da cewa.

“Baza’ayi haka ba hakan zai zamo kamar titsiya ne Ablah ni na yarda da mahaifiyarki bana zarginta kibar maganar Ablah.”

“Bazan iya barin wannan maganar ba Inna Jumma ina haɗaki da girman Allah kisa a ɗauko Umma.”

Tayi Maganar tana sakin kuka mai cin rai, numfashi Inna Jumma ta saki tare da cewa.

“Shikenan Faruq tashi kaje.”

Tayi maganar cikin sanyin jiki da kunyar Ablah su Daddy da kallo suke binta yayin da ta rakuɓe gefen Inna Jumma tana rusar kuka.

Sun juma a zaune kusan minti 40 kafin Faruq ya shigo shida Umma da hankalinta ke tashe domin kuwa Faruq bai sanar da ita komai ba ya dai ce mata Inna Jumma tace ya taho da ita yanzu ita duk zatonta wani abunne ya sami Ablah tana saka ƙafarta cikin falon sukayi ido huɗu dashi saurin ja da baya Umma tayi tana mutstsika idanunta domin kuwa gani take idanunta kamar ƙarya suke mata, ƙara ware idanunta tayi tana kallonsa Tabbas ba mafarki take ba KABIRU take gani shima a matuƙar razane ya buɗe idanunsa yana kallonta a kuma tsorace ya miƙe tsaye yana nunata da yatsa.

“HARI keeee! Idanu suke gani ko kuma gizon da suka saba min akanki ne yau ma suka min.?”

Juyawa Umma tayi da gudu zata bar falon idanunta na cikowa da hawayen baƙin ciki da danasanin saninsa a rayuwarta Inna Jumma ta dakatar dashi yayin da idanunta ke kan PAPA, har su Daddy kallonsu Suka mai da ga Papa.

“Ina zaki Na saka a kiraki?”

Cak Umma ta tsaya hawaye na gangarowa cikin idanunta ta furta.

“Inna bazan iya tsayuwa a nan ba idan na tsaya anan wajen ina kallon wannan azzalumin zuciyata zata fashe.”

Cikin sanyin jiki da damuwa Papa ya dubi Ablah tare da furta.

“Dama itace mahaifiyarki, dama kece Nusaiba! HARI ƙaddara da sharrin shaidan ya shiga tsakanina da ke, amma ban kyaleki saboda zalunci ko son zuciyata ba, ki fahimceni dan Allah na nemeki bayan rabuwata da ke amma kowa cemin yake baisan inda kika koma ba, ba irin nemanki da banyi ba Hari amma ban sameki ba dole tasa na hkr.”

“Ƙarya kakeyi Kabiru ƙarya kake, ka cuceni ka zalunci rayuwata ka ha’ince ni ka rabani da dangina kasa banga gawar mahaifina ba saboda kai, ya mutu da fushi na bansan wani hali mahaifiyata take ciki ba ta mutu ko tana raye ban sani ba, me zan cewa Ubangiji na mahaifina ya mutu da fushina Allah ya isa tsakanina da kai, ta ƙarisa Maganar cikin kuka tana kallon Ablah tace, ki tashi mu tafi kin gama zaman wannan gidan da nasan wannan gidan ahalin Kabiru ne da bazanyi kuskuren barinki ki shigo ba.”

Tayi maganar tana jawo hannun Ablah, Papa saurin saka hannu yayi shima ya riƙo Ablah tare da cewa.

“Ƙaddarar ubangiji ne ya jefota cikin ahalinta Nusaiba ƴata ce bazaki goge hakan ba tun ranar dana ganta jikina ya bani wani abu akanta ashe jini nane yake yawo a jikinta karki shiga tsakanin ta da ahalinta.”

Gabaki ɗaya da kallon mamaki da rashin fahimta suke binsu musamman Ablah da abun yafi bata mamaki muryar Umma taji tare da cewa.

“Na juma da share jininka daga jikinta, matuƙar ina numfashi Ablah bazata taɓa amsa sunan ƴarka ba, bazata kiraka da ubanta ba, saboda baka cancanci a kiraka da wannan sunan ba, kai ko kunya ma bakaji zaka wani ƙaddara ta jefota cikin ahalinta, na goge sunan Nusaiba daga gareta tun ranar da ka gudu ka barmu shima wannan sunan ya bar gareta dan haka ka fita daga rayuwata idan ba haka ba kotu ce zata rabani da kai na tsaneka Kabiru.”

Tayi maganar tana jan Ablah, fisge hannunta Ablah tayi tare da tsayawa gaban Inna Jumma tace.

“Inna wai me yake faruwa ki tambayeta me suka faɗa haka na kasa fahimta umma ina kika san Papa?”

Cikin gigitacciyar tsawar da ta firgita Ablah wanda tunda take da Ummu bata taɓa mata ba tace.

“Karki kuma kiransa da sunan Baba domin kuwa ba ubanki bane, idan kika sake kiransa da Baba Allah ya isa ban yafe ba, kuma sai na tsine miki albarka.”

Inna Jumma a razane ta taho gaban Umma ta tsaya tare da cewa.

“Wacce irin magana kike haka ne, ki dubi girmana da mutuncina ki zauna dan Allah, ki sanar damu meke faruwa ina kika san Kabiru ki sanar dani dan.”

Hawayenta Umma ta goge tare da zama cikin huci tace.

“Mijina ne shi, kuma shine uban Ablah labarina dashi bashi da daɗin sauraro Kabiru ya cuceni a rayuwata dashi, ya rabani da dukkan wani farin ciki ya samin baƙin ciki da ciwo tun ina ƴar shekara goma sha tara ni ƴar asalin Niger ne uwa da ubana duk a nan suke ƙaddarata ta fara ne tun daga Ranar wata laraba wacce ta haɗani da Kabiru.”

*****

Bari mu waiwaya baya muji meke tsakanin Umma da Papa.

Waiwaye

 “HARI yau wannan nonon fa da yiwuwar bazai ƙare ba, kawai ki tashi mu koma gida.”

Cewar ƙawata Habi wacce muke tare ko yaushe bamu rabuwa duban Habi nayi tare da cewa.

“Hakane habi muje kawai dama kasuwa haka ta gada ba kullum ake samun kasuwar ba.”

Nayi maganar ina miƙewa dai-dai Kabiru yayi mana sallama idanuna na ɗaga na dubesa tare da amsa sallamar, nonon ya siye gabaki ɗaya har da na habi, sosai mukayi farin ciki, muka koma cikin ƙauyenmu.

Sai ya zamana kullum muka fito tallah sai Kabiru yazo ya saye nonon mu, duk ranar da bai zoba kuwa sai munta jajen sa, sabo ne sosai ya shiga tsakanin mu dashi, har ya zamana Soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninmu akwai wata ranar talata ina zaune ni da Habi Kabiru ya yazo ya zauna a gefen ƙwaryar nono na, murmushi nayi tare da ɗago idanuna na kallesa murmushi yamin yace.

“Hari ya kamata naje cikin ƙauyenku fa, kinga maganar auren mu ya kamata a fara.”

Murmushi nayi tare da ɗago kaina nace masa.

“To shikenan ba damuwa zan faɗawa Dada sai ta sanar da Baffa zakazo.”

“Au ke bazaki iya sanar da baffan da kanki ba, har sai Dada ta sanar dashi umhumm na gano wato kunya ce irin ta Fulani ko?”

Dariya kawai nayi tare da kawar da zancen muka tafi wani zancen, wunin ranar tare muka yisa da Kabiru kafin ya raka mu muka koma gida da daddare Dada na zaune tana saƙar faifayi na zauna kusa da ita tare da kiran sunanta tace.

“Dada”

Ɗago kanta Dada tayi ta kalleni tare da cewa.

“Na’am Hari, menene, kinyi tatsar nonon kin kwantar.”

“Eh Dada na kwantar, Dada dama wannan mutumin da nake faɗa miki yana sayen nonon mu to shine yace na sanar daku cewa zaizo ya gaishe daku kuma zaiyi magana da Baffa.”

Dada dubana tayi tare da cewa.

“Hari saurareni da kyau na fahimci cewa wannan yaron yana sonki kuma kema kina sonsa, to bari kiji Hari ki fita a harkar wannan yaron saboda bamu san waye shiba daga haɗuwa da Mutum sai kuma yace zaizo yayi Magana da baffanki mu a cikin wannan ƙauyen zamu aurar dake bazamu bari ki fita cikin gari ba ki rabu dashi.”

Bakina na tura tare da cewa.

“Dada ki dai bari yazo suyi maganar da Baffa dan Allah tunda baki san me zasu tattauna ba.”

“Shikenan Hari yazo ɗin na sanar da baffan naki anjuma idan ya shigo.”

Dariya nayi tare da ɗaukar faifayin na fara taya Dada, munanan zaune Baffa ya shigo ina jin Dada ta sanar dashi baiyi wani musu ba yace Allah ya kawosa lafiya.

Ko da na sanar da Kabiru Baffa yace yazo shi baiyi ƙasa a gwiwwa ba kuwa washegarin ranar da na sanar dashi yazo ƙauyenmu, har cikin gida yazo ya gaishe da Dada ya kuma mata alheri A bukkar Baffa suka zauna inda Kabiru ya cewa baffa.

“Baffa ni da Hari muna son junanmu munyi magana da ita cewa zan turo magabata na azo ayi Magana shine naga dacewar nazo ku fara ganina tukunna kafin manya su shiga lamarin mu, Allah yasa bakayiwa Hari miji ba.”

Baffa murmushi yayi tare da cewa.

“Ban yiwa Hari miji ba, amma kai baƙo ne a idanuna ina son nasan asalinka da kuma sana’arka.”

“Ehh to Baffa ni ba ɗan Niger bane Ni ɗan Nigeria ne, ina zaune ne a gaban kawo na akwai wani project da ya kawoni nan iyayena suna can Nigeria nan project nazo kuma a wajen kawuna nake da zama.”

“Yaro naji maganganun ka, menene kuma triject.”

Murmushi Kabiru yayi yace.

“Baffa project yana nufin wani aiki ne da ake bayarwa a makaranta wanda zakaje kayi ka maida musu, shine abinda ya kawo ni Niger.”

“Na gane sai dai bazan iya baka Auren ƴata Hari ba, saboda kai baƙo ne kuma a al’adar mu ta wannan ruga bama bawa baƙo Auren ƴarmu wanda bamu san Asalinsa ba, dan haka kayi hkr.”

“Amma Baffa ya k…”

“Ba sai kace komai ba yaro wannan al’adar mu ce zaka iya tafiya.”

Baffa yayi maganar yana nunawa Kabiru hanya, miƙewa Kabiru yayi jiki babu ƙwari ya fita ko sallama bai minba yayi tafiyarsa.

Ina zaune a gefen rumbum hatsinmu naji Baffa na kwaɗa min kira tashi nayi tare da amsawa na shiga cikin bukkar sa yana zaune shida Dada dukkan su sunyi shuru, gefe na duba ko zanga Kabiru babu shi babu alamunsa, Baffa ne yace.

“Hari wannan yaron ki rabu dashi ɗan baƙi ne, kin sani mu kuma al’adar wannan ƙauyen bama aurar da yaranmu ga baƙi yace shi ɗan Nigeria ne wai yazo wani aiki ne cikin garin nan da alamu kuma ba yaro bane yana da mata, ki rabu dashi bani son ki kuma kawo min zancen sa.”

A mungun razane nake kallon Baffa domin kuwa ji nake bazan iya rayuwa babu Kabiru ba cikin sanyin murya nace.

    “Baffa tunda yana da Asali kuma akwai kawunsa a nan mai zai hana kawai ka barni na auresa tunda ba haramun bane Auren baƙo ni shi nake so Baffa.”

Dada ce ta hau ni da faɗa da masifa.

“Bazaki auresa ba Hari, bazamu karya al’adar mu ba akanki yadda muka aurar da yayyanki bisa al’ada kema haka zamu aurar dake, ai dama na faɗa miki tun kafin Maganar taje ga baffanki ki tashi ki bamu waje mun gama wannan maganar.”

Cikin sanyin jiki na bar bukkar, ranar kwana nayi Cikin tashin hankali, bacci ma ban iya yinsa ba, washegari da azahar na ɗauki nono na fita, tunda naje cikin kasuwar nake saka ran zuwan Kabiru sai dai har na sai da nono na bai zoba ƙin tafiya gida nayi na tsaya wai ko zaizo sai dai har rana ta faɗi bai zoba sosai hankalina ya tashi Habi ce ta dinga bani baki tana rarrashina daƙyar ta jani muka tafi gida, da daddare tisa Dada nayi a gaba da kuka ni lallai sai sun barni na auri Kabiru sai dai ina Dada ko saurarata ba tayi ba sai ma masifa da ta dinga min, cikin ikon Allah washegari da na tafi na samu Kabiru yazo sosai nayi murna nake tambayarsa dalilin da yasa jiya baizo ba sai cemin yayi tunda Baffa ya sanar dashi bazasu basa Aureta ba ya kwana bashi da lafiya, baki na basa Sosai tare da tabbatar masa da cewa zamuyi Aure, tun daga wannan lokacin muke samun matsala da iyayena sun dage cewa bazan Auri Kabiru ba a yayin da na kafe kan cewa ni lallai sai shi, Dada tayi dukan tayi zagin tayi nasihar amma duk naƙi ji, ni gani nake meye aibun baƙo tunda komai tsiya ai yana da Ahali,a gefe guda kuwa Kabiru kullum yana cemin idan har iyayena bazasu barmu muyi Aure ba, gara kawai muje wani waje a ɗaura mana Aure a wannan lokacin Soyayya ta rufe min idanuna ƙawata Habi kullum cemin take na hkr tunda iyayena basa so amma dashi ke nayi nisa sai na ƙi jinta.

Ana cikin haka kwatsam sai Baffa ya bijiro min da maganar zai haɗani Aure da Garba ɗan mai gari, sosai hankalina ya tashi da naji wannan maganar, baƙin ciki da takaici tamkar zai kasheni na nuna musu bana so amma ina suka ƙi saurarata hakanne ya sani yanke hukuncin bin Kabiru mu gudu muyi Aure kawai idan yaso bayan an ɗaura Auren na dawo gida nasan dole zasu hkr muddun da Auren Kabiru a kaina, haka kuwa akayi na gudu nabi kabiru aka ɗaura mana Aure dashi, akwai wani wanda ya nuna min da sunan kawunsa kawu Salisu, shine wanda ya jagoranci ɗaurin auren mu dashi da wani abokinsa, ya kuma bamu gida muka zauna, watan mu 6 da Aure da Kabiru a lokacin ina da cikin wata wata Biyar a jikina, duk na damu da abinda na yiwa iyayena kullum cikin tunaninsu nake a zuciyata nake jin ban kyauta musu ba, na gudu a gida nayi Aure ba tare da sanin iyayena ba har nayi wata shida bansan wani hali iyayena suke ciki ba duk Soyayyar da suke gwada min wannan tunanin shike sani cikin tashin hankali kullum.

Wata ranar asabar muna zaune da Kabiru na dubesa.

“Kabiru ya kamata naje ƙauye wajen su Baffa na nemi yafiyarsu.”

“Hakane Hari ki shirya gobe sai muje bara na fita sai na biya kasuwa na musu siyayya.”

Murmushi nayi cike da farin ciki na ce masa.

“Na gode sosai, kace bayan auren mu zaka kaini Nigeria naga dangin ka yaushe zamuje.”

Dariya yamin tare da cewa.

“Gaggawar me kike hari ai tunda kin aureni dole zaki san gidan mu, ki bari tukunna sai kin haihu yaushe zaki kwashi hanya da ciki idan kika haihu lafiya sai muje.”

Ban kawo komai a raina ba Saboda na yadda dashi nace Allah ya nuna mana lokacin.

Washegari da safe ƙarfe biyu a cikin ƙauyenmu ta mana tunda na doshi gida zuciyata take tsinkewa, da Sallama muka shiga cikin gidan Dada tana tsugunne gidin murhu jin sallamata yasa ta ɗago idanunta tana ƙare min kallo hawayene ya cika mata idanu tana nuna ni da hannu ta furta.

“Hari dama maganar da ake ta raɗi raɗi a kanki gaskiya ne cewa kin bi Kabiru kunje kunyi Aure hari harda ciki kika zomin, kinzo ne ki kasheni nima kamar yadda baƙin cikin ki ya kashe mahaifinki.”

A matukar razane jin wai Baffa ya rasu na ce.

“Dada Baffa ya rasu?”

“Ya rasu kuma kece kika kashesa, ki juya ki koma inda kika fito babuni babuke har abada ko mutuwa nayi kikazo kan gawata Allah ya isa ban yafe ba kuma har ina cikin kabarina bazan fasa ja miki Allah ya isa ba, ki juya daga dangin mahaifinki har dangina idan kika saka ƙafarki kika taka kikaje wajensu Allah ya isa ban yafe ba kuma sai na tsine miki albakar wallahi ko bayan na mutu kika ziyarci wani cikin zuri’arki sai tsinuwar Allah ta biki, ki fita min daga gida.”

Wani irin kuka na saki na danasani da takaicin mutuwar mahaifina Baffa ya mutu da fushina, ina jin Kabiru na bawa Dada baki amma ina cewa Wallahi idan bamu fita mata daga gida ba sai ta tsine min haka muka fita ina kuka tamkar raina zai fita wannan barin ƙauyen da nayi shine barina dashi da ban sake komawa ba.

 Nayi baƙin ciki nayi kuka harna hkr, damma ina jin daɗi a wajen Kabiru yana rarrashina da bani hkr yace duk laifinsa ne shine ya jawo min, wannan tabon na fita daga cikin dangina harna haifi Ablah bai goge min ba wani sa’in idan takaicin ya isheni sai na shiga ɗaki nasha kuka ba tare da Kabiru ya sani ba, sanda na haifi Ablah babu wanda yamin wankan jego saboda rashin gata kawun Kabiru Salisu tun randa akayi auren mu ya bamu gida ban sake ganinsa ba, ban san ya ake wankan jego ba, haka nayi da kaina sai dai cikin ikon Allah, Allah ya tsareni babu wata matsala dana samu inda yarinyar taci sunan Nusaiba, gata da kulawa a wannan lokacin babu wanda Kabiru bai nuna mana ba ni da ƴata Nusaiba na da shekara ɗaya sai ga wani cikin ya ɓullo wanda sam bama ankara akwai cikin ba.

Ranar da bazan taɓa mantawa da ita ba a rayuwata itace ranar da Kabiru yace min ya fita kasuwa Wacce itace ranar da Kabiru ya gudu ya barni da ƴarsa da kuma ciki, baiyi tunanin wani hali zan shiga ba, ganin har sha biyu na dare bai dawo ba ya sa na shiga cikin tashin hankali ranar ban iya bacci ba, washegari duk inda nasan kabiru yana zuwa sai da naje baya nan waje na ƙarshe da naje inda yafi zama suke sanar dani cewa yazo ya musu sallama ya koma garinsu ya gama abinda ya kawosa Niger, nayi kuka da danasani a rayuwata Na bijirewa iyayena da nayi a rayuwa a wannan lokacin na fahimci cewa duk wanda ya saɓawa umarnin iyayensa Tabbas bazai taɓa gani da kyau ba dole rayuwa sai ta tambayesa, a wannan lokacin na gane cewa da nabi Maganar mahaifana da yanzu ina cikin kwanciyar hankali, washe gari na fara neman kawu Salisu akace ai shima ba ɗan uwansa bane ba’a ma san inda ya nemosa ba, aka tabbatar min da cewa wannan gidan na Kabiru ne shine ya saya da kuɗin sa nayi mamakin inda ya samu kuɗi harya sayi wannan gidan nayi tunanin komawa ga iyayena sai dai maganganun Dada da tabbatuwar tsinuwar da zata bini yasa na hkr na yanke shawarar sayar da gidan da muke ciki nazo Nigeria na nemesa, Lado shine ya tabbatar min da cewa KABIRU ya taɓa sanar dashi iyayensa suna garin Abuja hakanne yasa da na sai da gidana na ɗauki kayan sawa na dana ƴata muka taho Abuja a mota na gamu da Mahaifiyar Hafsa Hajiya larai wacce itace tamin sutura ta bani wajen zama a gidan ta, ko nazo Abuja bamu zauna ba kullum cikin neman Kabiru muke amma babu wani labari na ɗau tsawon wata biyar ina neman sa ban samu ko da wanda yace ya sansa ba gashi bani da wani abu da zan nuna wanda za’a iya ganesa, a lokacin babu waya kuma bani da hotonsa, a ƙarshe hkr nayi na kuma ji duk duniya babu mutumin dana tsana sama da Kabiru, tsanarsa tasa na sauyawa Ablah suna daga Nusaiba zuwa Ablah kuɗin gidan da muka sayar na sayi ƙaramin gida wanda babu gini ɗaki biyu ne kawai da banɗaki sai katangar zana, sauran canji na na fara sarin kayan gwari dashi na cire Kabiru a babin rayuwata na cigaba da rainon ƴata da cikin da ke jikina, na manta da Kabiru a rayuwata, da wannan sana’ar ta gwari muke ci muke sha harna haifi ɗana namiji na sanya masa sunan Abdulrahman, muke kiransa da Abdu haka muke ta rayuwarmu har izuwa wannan lokacin ban kuma yi Aure ba duk ina da damar da zancen kotu ta bani takaddata amma banyi hakan ba.

Dawowa cikin labari.

*****

Duban Inna Jumma Umma tayi idanunta na zubar da hawaye tace.

“Wannan shine mummunan tarihin rayuwata wanda wannan baƙin mungun ya jefani a ciki bansan wani hali Dada ke ciki ba ta mutu ko tana raye ban sani ba.”

Gabaki ɗaya waɗanda ke wajen sai da jininsu yayi sanyi shi kansa Papa hawayene ke biyo fuskarsa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 54Aminaina Ko Ita 56 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.