Skip to content
Part 53 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Ablah wani irin kuka take mai cin zuciya na tausayin mahaifiyarta wani irin tsana da ƙyama taji tana yiwa Papa wannan wani irin zalunci ne haka, lallai duk wanda baiji Maganar iyayensa ba ba lallai rayuwa ta masa kyau ta tabbata duk wannan wahalan da Umma tasha a rayuwata sanadin bijirewa iyayenta da tayi ne shi Kuma ubangiji ya nuna mata iyakarta, amma duk da haka Papa ya zalunceta ya ɗauki haƙƙinsu a matsayin su na ƴaƴan sa, muryar Inna Jumma taji tana furta.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Allahumma ajirni fil musibati! Kai rayuwa ina zaki damu yanzu Kai Kabiru kaine kayi wannan mummunan aikin kaine ka zalunci ƴar mutane ka ha’ince mu muma a matsayin mu na iyayenka kayi Aure ba tare da mun sani ba har ka haifi yara biyu, duk matarka uwar gidan ka bata sani ba, kasan abinda ka aikata kuwa Kabiru kana haukane jinka Allah zai barka da haƙƙin waɗannan mutanen da ka zalunta ashe Uba zai iya watsar da yaransa cikin wahala yazo ya zauna yana wasa da dariya yana ci yana sha yana kuma jin daɗi Tabbas kai ba uba bane na ƙwarai baka da imani wallahi wallahi wallahi ka shiga Uku idan waɗannan bayin Allan basu yafe maka ba.?”

“Umma tabbas kinyi kuskure a rayuwarki ke da kanki kike min faɗa kike cemin karna yadda na bijirewa umarninki a matsayin ki na mahaifiyata domin duk wanda ya bijirewa iyayensa ya juya musu baya mussaman a rayuwar Aure, Auren bazai taɓa lasting ba, ashe wannan wa’axin da kike min ya faru ne wa ke, kuskuren ki shine guduwa daga gida, da kinyi hkr kin zauna gaban iyayenki dole zaki auri Papa, saboda babu namijin da yake Auren matar wani Allah ya rubuta kece matar Papa ba ta Garba ba, Amma gaggawa da sharrin zuciya ya saki kika kusanci ƙaddara ta hanyar da bata dace ba, muna aikata kuskure bisa son zuciyarmu sai mu danganta da ƙaddara Tabbas na ɗauki darasi a cikin Rayuwarki Umma, bazan taɓa yadda nayi kuskuren da kikayi ba, Umma koda Dada zata tsine miki ya kamata zuwa yanzu ki koma gareta nasan zuwa tsawon wannan lokacin tana mararin ganinki koda sau ɗaya ne kafin ta koma ga ubangijinta, Ni zan jagoranceki zuwa gareta zan karɓi hukuncinta a matsayin fansarki, Inna Jumma ban taɓa tsanar rayuwa ba irin yau ashe dama haka duniya ta ke cike da maha’inta wannan rayuwar abar tsoro ce, ka yadda da wani ya zamo abun barazana, shi wannan papan da aka kira da sunan mahaifina, ni ba mahaifina ba ne, saboda na juma da kashe uba a rayuwata, da hakan na taso bansan daɗi mahaifi ba, kuma bana buƙatar samu muddun daga wannan mungun mutumin ne, mahaifiyata itace gatana kuma itace abar kwaikwayo na, Inna Jumma ko ɗan banyi farin ciki da samun mahaifina ba, sai baƙin ciki da takaici da nayi a rayuwata da jin dama ɓarina akayi kafin nazo duniya muddun ta jikinsa zan fito, dama Abbas ya sanar dani cewa dukkan family na Ahmad Giwa ba mutanen kirki bane da Farko na ƙaryata hakan amma yanzu na tabbatar na kuma yadda domin kuwa ni nasan me nake gani a cikin wannan gidan, hmmm tsoho zalunci shima yaro zalunci ta yaya rahama zata shigo wannan gidan ba dole kuta gamuwa da masifa iri iri ba, papa nayi tir nayi Allah wadarai da fitowa daga gudan jininka ba kuma zan taɓa yafe maka haƙƙina dake kanka ba.”

Tayi Maganar cikin matsanancin kuka tana kamo hanun Umma Aunty Amarya kusan suman tsaye tayi jin Ablah ahalin AHMAD GIWA ne, Tabbas biri yayi kama da mutum, irin wannan Soyayyar da take gwada musu da kare rayuwarsu dole sai jininsu yana yawo a jikinta hakan zata faru lallai akwai babbar tashin hankali da matsala, Al’ameen kuwa wani irin kunya yaji tamkar ya nutse kasa haka yake ji Haidar da Momma sosai wannan labarin mai kama da almara ya kiɗima su, Momma Sosai taji zafin abinda Papa ya mata gani take cin amanar ta yayi, Daddy baiyi magana ba ya zuba idanu yana kallon su sai yanzu yayi gyaran murya tare da cewa Papa.

“Ɗan Uwa, tabbas mun san zuwanka Niger Project kayi zaman shekara biyu duk da kana zuwa ka dawo baka taɓa sanar damu kayi Aure ba, abinda nake son na sani meyasa ka ɓoye mana kayi Aure sannan meyasa ka gudu ka barta, shin dama kayi niyyar aurenta ne saboda ka tozarta rayuwarta, menene dalilinka na guduwa ka barta, da ciki da goyo?”

Shuru PAPA yayi jikinsa yayi mungun sanyi INNA Jumma ce ta daka masa tsawa tare da cewa.

“Bakaji ne ana tambayarka?”

“Bashi da amsar tambayar ku, saboda shi marar gaskiya ko a Ruwa yake gumi yakeyi, ban taɓa ganin malalacin uba irinka ba, duk wanda ya fito daga jikinka tabbas ya gamu da babbar asara sab…”

“Ya isheki haka Ablah! Ki daina ci masa mutunci domin kuwa shi Mutum ne mai daraja, kuma komai lalacewar sa dai mahaifinki ne, ki san me harshenki yake faɗa a kansa idan kuma ba haka ba zan gimtse miki harshe.”

Murmushin takaici Ablah tayi tare da cewa.

“Ka daina kiransa da sunan mahaifina domin kuwa bazai taɓa amsa wannan sunan ba a wajena, ka cika son kai da yawa duk abinda wannan Mutumin ya mana na rashin kyautawa baka gani ba Saboda kai da mahaifiyarka ya rikeku ba tare daya tozarta rayuwarku ba, kana iya gimtse min harshen muddun akan wannan azzalumin ne, domin kuwa bazan daina faɗar Magana marar daɗi akansa ba.”

Daddy ne ya daka musu tsawa tare da cewa.

“Ya isa haka shi nake tambaya ba kuba, karna sake jin bakin wani a cikin ku, Ɗan uwa da kai nake ka bani amsa.”

Papa cike da mungun sanyin jiki yace.

“Duk abinda zan faɗa bazai goge min zunubin dana ɗauka ba tabbas ban kyautawa rayuwata ba, nasan na zalunce su naci amanar su, amma wallahi Allah ɗaya yana kallona kuma shine shaidata na koma neman ku ban sameku ba, har ƙauyenku naje wajen Daddy ta koreni bata saurareni ba, bata kuma amsa min da cewa bakya gunta ba, hakan yasa nayi zaton ko kina can dukkan kuskurena na amsa su dan Allah ku rufa min asiri ku yafemin na amsa laifina Hari nasan ke macece mai haƙuri da juriya baki da riƙo dan Allah ki yafe min ina Abdu yake ina son ganinsa?”

Miƙewa Umma tayi tare da kama hanun Ablah tace.

“Mu tafi Ablah.”

Tashi tayi tabi bayan Umma Inna Jumma tsabar damuwa da sanyin jiki ta gagara dakatar dasu shi kansa Daddy kunyarsu yaji gara ya bari su tafi daga baya su je su nemi afuwarta, har sunje bakin ƙofa Ablah ta tsaya tare da juyowa ta cewa Al’ameen.

“Allah ba azzalumin bawa bane kuma baya bari ayi zalunci, na tabbata zai min sakayya nasan Tabbas akwai ranar da zakayi nadama da danasanin abinda ka min a wannan lokacin na maka nisan da bazan taɓa dawowa gareka ba, ayau kaji asalina kuma ka gani cewa mahaifiyata ba mutumiyar banza bace, baffanka ƙanin mahaifinka shine mutumin banza ba uwata ba, domin kuwa itama shiya cuceta ya sata cikin bala’i kaje na barka da Allah.”

Tayi Maganar tana saka kai ta fice.

Taron haka ya watse cikin sanyin jiki da damuwa mussaman Inna Jumma hankalinta yafi na kowa tashi.

Tunda suka koma gida Ablah ta shige cikin ɗaki ta zauna tayi shuru wani irin haushi da tsanar Papa takeji da takaicin wai shine ubanta, gefe guda kuma ga Soyayyar Al’ameen da ta addabeta da ƙunar zuciya Tabbas a wannan lokacin rayuwa ta mata tsanani, Umma ce ta shigo tare da zama gefenta tace.

“Ablah karki saka wannan damuwar a zuciyarki harta ɗaga miki hankali sannan karki kuma aibata mahaifinki komai lalacewarsa ubanki ne shine gatanki domin kuwa ba’a tambayar asalin Uwa asalin Uba ake dubawa, mahaifinki ya mana kuskure ina mai baki hkr da ki taushi zuciyarki komai mai wucewa a rayuwa.”

“Umma zuciyata ƙuna take min ina jin haushi gami da tsanar Papa a cikin zuciyata, duk matsi da halin rayuwar da muka shiga shine ya samu a ciki meyasa zaki dinga nema masa afuwa da sassauci a wajena?”

“Saboda ubanki ne, zaki iya shiga wuta Muddun kika bijire masa, bana son ki aikata kuskuren dana aikata a rayuwata, shiyasa nake nuna miki hanya, wannan itace hujjata.”

Umma tayi maganar tana tashi ta fice, wunin ranar Ablah haka tayisa cikin damuwa da takaici.

Washegarin ranar Juma’a bayan an saƙƙo daga sallar juma’a Faruq da Abbas sukazo wajen Ablah, kasancewar shi Faruq yasan tana gidan su, Abbas shine ya kirata yace ta fito yana waje, bata wani juma ba ta fito, kana ganinta zaka fahimci tana da damuwa, ba Faruq ya fita amsar katin waya a shago, zama tayi seat ɗin gaba tare da cewa.

“Sannu da zuwa Abbas.”

“Yauwa, sannu, ya Umma jiya na kira wayarki a kashe.”

“Umm bani da caji ne.”

Dubanta Abbas yayi tare da cewa.

“Ablah meke damunki?”

“Meka gani?”

“Fuskarki ce ta nuna min kina cikin damuwa, ba’a ɓoye damuwa a fuska domin kuwa duk mai ƙaunarka yana fahimtar damuwarka, meke damunki Please.”

“Abbas ba ko wacce damuwa ake faɗa ba, kowa yana da nasa damuwar idan ka faɗi naka mutane bazasu maka uzuri ba, haka idan ka zaƙe wajen faɗin damuwarka wasu sai su maka dariya, ba kuma kawo maka ƙarshen matsalarka zasuyi ba.”

Numfashi Abbas ya saki yana dubanta tare da cewa.

“Amma kinsan barin kashi a ciki baya maganin yunwa ko, Abokin kuka shi ake faɗawa mutuwa, Ablah.”

“Hakane Umma tayi gaskiya babu wanda zai tsallake ƙaddarar sa, ƙaddara bata canjawa bani da wani zaɓin kuma rayuwa tana juyawa da bawa yadda taso ba tare da shawararsa ba sai dai tawa rayuwar ƙwallo tayi dani maimakon ta juya dani sai ta zaɓi wahalar dani lallai wannan Rayuwar mai cike da ƙunci ce.”

“Hmmm na fahimci ban cancanci sanin damuwarki ba, domin kuwa da alamu Al’ameen shi kaɗai kike iya faɗawa matsalarki.”

Yayi Maganar dai-dai Faruq na buɗe motar ya shigo, kanta ta ɗaga ta kallesa tare da cewa.

“Ya Faruq kaine.?”

 “Ni ne Ablah, ya kk?”

“Lafiya nake dama tare kuke kenan?”

“Tare muke, Ablah Maganar Al’ameen ce ta Kawo mu Abbas ya sameni munyi magana dashi sann…”

Hannu Ablah ta ɗaga masa tare da cewa.

“Ya Faruq kubar wannan maganar dan Allah, na haƙura da Al’ameen da arayuwa ba komai kake so ya zamo ka samu ba, ba lallai abinda muke so ya zamo mana alkairi ba, ni Umma na jirana zamu je unguwa sai anjuma.

Tayi Maganar tana buɗe motar da sauri ta fice da kallo Abbas ya bita tare da cewa Faruq.

“Jikina yana bani akwai rashin ɗa’ar da Al’ameen ya yiwa Ablah saboda ta ɗauki zafi da yawa, amma koma meyene ya dai kamata mu dakatar da Nafeesa, zanje na saurara bincike akanta kuma insha Allah zan samo hanyar da zamu dakatar da wannan Auren, zamu fitar da hujjar da zata saka kowa ya tsaneta.”

Numfashi Faruq ya saki tare da cewa.

“Nima ta gefena zanyi ƙoƙari domin kuwa nayi rantsuwa cewa wannan auren baza’a yisa ba, muje ka sauƙe ni a gida.”

Kansa ABBAS ya jinjina tare da jan motar.

AUNTY Amarya sosai hankalinta ya tashi jin wai Ablah jinin Ahmad Giwa ne, sai kaiwa da komowa take, tana wannan sintirin Maimu ta fito hannun ta riƙe da jaka.

“Aunty zan shige gidan Aunty Zainab.”

“A dawo lafiya.”

Tayi Maganar a taƙaice har Maimu zata fita tace.

“Da wacce mota zaki fita.”?

“Da venz zan fita.”

“Okay”

Fita Maimu tayi, parking space tayi har zata shiga cikin motar Afnan ta fito da sauri tana kiranta tana riƙe da Ihsan a hannunta, ɗago kai Maimu tayi ta kalleta tare da tsayuwa isowa Afnan tayi tare da cewa.

“Sorry Maimu dan Allah ki bar min motar nan, zan fita dashi Please.”

Murmushi Maimu tayi tare da cewa.

“Ba komai bani key ɗin hannunki na hau waccar.”

Tayi maganar tana amsar key ɗin taje ta hau waccar motar ita kuma Afnan da Ihsan suka hau venz ɗin.

Aunty Amarya Hajiya Mansura ta kira a waya tana ɗagawa tace.

“An samu matsala, Ablah asalinta ya fito amma yanzu ba shi bane a gabanmu saboda bata gidan nan yanzu sannan Maimu ta fita yanzu a venz zan turo miki lambar motar a gama da ita kawai.”

Dariya Hajiya Mansura ta saka tare da cewa.

“Dama mai kyau, ai kuwa tunda muka samu wannan damar zamu dama, kisa a ranki gawar Maimu za’a dawo miki da ita, bara na kira Ajabo.”

Tayi Maganar tana katse kiran.”

Aunty Amarya zama tayi ta zabga tagumi ita fa wannan tashin hankalin Ablah take ji dama take da ƙwarin gwiwwar tare mata hanya bare kuma yanzu da ta haɗa jini dasu, numfashi ta sauƙe tare da jingina kanta jikin kujera.

Afnan sunyi nisa da tafiya kamar daga sama sukaji Babbar mota tayi sama da motar su, runtse idanunta tayi tana ambaton ubangiji, ihsan kuwa ihu tasa, dawowa ƙasa motar tayi cike da mugunta drivern doguwar motar yabi ta kan motar, jama’a an taru sai Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un ake yi,koda ya taka su jan motar yayi ya bar wajen da mungun gudu jama’a suna ya tsaya amma ina tuni ya figi iska kan motar su Afnan Akayi, tayi kwatsakwatsa daƙyar aka buɗe motar aka fito dasu, innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Afnan tayi wani irin buguwa ko ta ina jini ke fita a jikinta bakinta kunnenta hancinta duk jini yake fitar wa, koda aka ciro su tuni rai yayi halinsa…

<< Aminaina Ko Ita 55Aminaina Ko Ita 57 >>

1 thought on “Aminaina Ko Ita 56”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.