Skip to content
Part 55 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Ina matuƙar mamakin ka a wannan lokacin Abbas, domin kuwa banyi tsammanin akwai masoyi irinka ba har yanzu, kayi abinda ba kowa bane zai iya, ko ni bazan iya sadaukar da soyayyata Saboda wani ba, a wannan lokacin kake da damar yin amfani wajen mallakar Ablah, sai kuma bakayi haka ba duk da rashin jituwar dake tsakanin ka da Al’ameen tun bayan saɓanin Daddy da mahaifinka, Abbas naji daɗin yadda zaka taimaka mana amma shin anya kuwa Ablah zata so Al’ameen yanzu, saboda ya mata rashin mutuncin da ba lallai ta yafe masa ba, ya aibata asalinta sai ya zama ashe asalinsu ɗaya, Abbas Ablah da Haidar ubansu ɗaya.”

A matuƙar razane Abbas ya ce.

“Whattttttt! Faruq da gaske Ablah family ɗin ku ne, haba ai biri yayi kama da mutum, irin soyayyar da take gwadawa ahalinku dole akwai jininku a jikinta amma ya akayi kuka san family ɗin kuce?”

“Long story, zamuyi ta amma sai mun samu lokaci, gashi ina amsar gaisuwa kenan zamu bari ne sai an gama makoki muje wajen jamilar?”

“A’a zanje ko ni ɗaya ma karka damu, ban yiwa Al’ameen ta’aziyya b, saboda nasan zai iya bani kunya a cikin mutane , Faruq Rufaida tana matuƙar son Haidar ya kamata ya fuskanci mai ƙaunarsa, tana bani tausayi Yarinyar.”

“Abbas Haidar baya son Rufaida bazamu iya tilastashi ya sota dole ba dom…”

“Basai ka ƙarasa ba Faruq, lallai Haidar yaso mai sonsa kafin ta tsanesa domin kuwa Rufaida macen rufin asiri ce bata da son kanta, wanda yasan so shi yasan zafinta Faruq kuma shike Fuskantar ta bana son Haidar yayi biyu babu domin kuwa idan ya yadda ya rasa Rufaida bazai taɓa samun kamarta ba, sai dai ƙasa da ita, ana tilasta zuciya taso abu dole, kamar yadda na tilasta wa tawa zuciyar, sadaukar da Ablah, bawai saboda bana sonta bane a’a har yanzu ina sonta fiye da komai a rayuwata, na zabi farin cikin ta ne saboda bana son na auri gangar jikinta zuciyarta na ga wani, nasan idan Ablah matata ce dole alƙalamin ƙaddara zata sauya lamarin, ka fahimtar dashi da yaren da zai fahimta ni xan shige gida nasan Daddy nacan yana jirana.”

“Shikenan Abbas zanyi iya ƙoƙarina domin ganin na sauya lamarin nasu amma ba lallai na iya ba sai dai na gwada, na gode sai munyi waya.”

Yayi Maganar yana miƙawa Abbas hannu sukayi musabaha sannan Faruq ya fita shi kuma Abbas yaja motarsa yabar wajen, yana fita Nafeesa na shigowa ita da Jamila, Al’ameen dake zaune cikin mutane ya hango shigowar Nafeesa da sauri ya miƙe tare da ƙarisawa wajensu, murmushi ta saki tare da kashe masa idanu tace.

“My sai kuma naji labari marar daɗi, gashi har na yiwa Baba Maganar zaku turo kasan bana son Auren mu yayi dile mtsss wannan mutuwar bata mana adalci ba gaskiya.”

Har cikin ransa Al’ameen baiji dadin maganar Nafeesah ba, sai dai bazai iya mata musu ba, murmushi yayi tare da cewa.

“Karki damu da anyi sadakar Uku Daddy zasu nema min aurenki, mu shiga ki musu ta’azziya hubbina.”

Haidar da Faruq suna zaune daga inda suke kallo ɗaya Haidar ya mata ya kau da kansa gefe, Faruq kuwa girgiza kansa yayi tare da furta.

“Komai ya kusa zuwa ƙarshe gaskiya zatayi halinta.”

Idanunsa Haidar ya ɗago ya kalli Faruq ba tare da yayi magana ba yana kallon su suka shige cikin gidan, a falo kowa ge zaune Inna Jumma, momma Aunty, Aunty Amarya dama tana asibiti, a gaban Inna Jumma ta zauna cike da ladabin ƙarya tace.

“Sannu Inna ina wuni ya ƙarin haƙuri?”

Inna Jumma kallonta take tana yatsina fuska cike da ƙyamar ta domin kuwa ta gane Yarinyar buɗar bakin Inna Jumma cewa tayi.

“Ina wunin gidan uwarki, da ban wuni ba zaki gani hatsabibiya shafaffiya da mai, ko kunya bakya ji kin ɗebo ƙafa kamar samarin lawashi wai ke kinzo gaisuwa gidan surikai to baki da surukai a gidan nan domin kuwa ni uwar masu gida muddun ina numfashi kuma na isa da ƴaƴana wallahi Aminu bazai auri ƴar marar sa tarbiyya irinki ba, fice mana daga gida bama buƙatar gaisuwarki shasha marar tarbiyya.”

Cike da mungun mamaki Nafeesa take kallon Inna Jumma domin kuwa ko a cikin mafarki bata taɓa zaton akwai wanda zai wulaƙanta ta a Familyn Ahmad Giwa ba saboda gaba ɗaya boka ya gama dasu har ita wannan tsohuwar, ashe dama asirin bai kamata ba, lallai kuwa akwai sake, wani irin kunya taji, shi kuwa Al’ameen cike da jin haushin abinda Inna Jumma ta yiwa Nafeesa yace.

“Haba Inna meye haka gaisuwa fa tazo muku, Nafeesa ce fa matar da zan Aura kike..”

“Rufe min baki dan ubanka daga kai har ita, na koreta sai kazo ka hukunta ni, idan kai sun asirce ka sun gama dakai to ni nafi ƙarfin bokan su wallahi na tsumu kuma na riƙe ayar Allah, kije ki cewa uwarki asirin da tayi bai shiga jikina ba, sannan kice mata wanda kukayi masa shima sai na karyasa, shige ki tafi sai wani kallona kike kamar wata munafuka.”

Gabaki ɗaya waɗanda suke cikin falon da kallo suka bi Nafeesa masu dariya nayi masu ganin laifin Inna Jumma suma sunayi, Al’ameen cike da takaici yace,

“Haba haba Inna Jumma! Wani irin asiri kuma, ni babu wani asiri da aka min.”

“Dama ina zaka yadda sun maka asiri tunda sun gama barbaɗeka ai bazaka yadda ba, kaga kafin naci ubanka da kai da ita ka jata tabar min gida tunda ba gidan tsohon ta bane, munafuka kin watsa min zumuncin jikokina sannan kice zaki shigo min gida ai ƙarya kike dan uban ubanki, da uwar uwarki, shegiya annamimiya.”

Wasu hawaye ne masu ɗumi suka zubo daga idanun Nafeesa takaici tunda take a rayuwarta ba’a taɓa wulaƙanta ta ba irin yau, da gudu ta fice daga falon tana kuka, Al’ameen bayanta yabi yana kiranta ko sauraronsa batayi ba, kasa nutsuwa yayi yaji wani irin tashin hankali ganin ranta ya ɓaci, ko kafin ya isota tuni ta shige adaidaita sahu, Duban Jamila dake tsaye yayi tamkar zaisa kuka yace.

“Jamila tayi fushi da yawa, banji daɗin abinda inna Jumma ta mata ba, ki jirani mu tafi tare.”

Yayi Maganar yana juyawa cikin sauri ya ɗauki mota suka bi bayanta, kusan tare suka isa tana sauƙa a adaidaita suma suna isowa, saurin fitowa yayi daga motar ya tare gabanta.

“Ablah meyasa zakiyi fushin dani bayan bani ne wanda ya miki laifi ba Why?”

Wani irin tsinkewa zuciyar Nafeesa yayi idanunta ta zaro tana kallon Al’ameen tare da nuna kanta da yatsa tace.

“Al’ameen ni kake kira da sunan wannan shegiyar, ni ce na koma Ablah Oh wato itace a zuciyarka ma, bayan wannan tacacciyar tsohuwar kakar taka ta gama cimin mutunci bai isheka ba sai ka biyoni ka ƙara min da naka, to bari kaji wallahi muddun kana son na kuma sauraronka jibi idan kunyi sadakar Uku ka turo iyayenka gidan mu kuma a cikin sati ɗaya nake son ayi auren saboda na nunawa wannan tsohuwar najadun cewa na zarce rashin mutuncin ta, idan kuma ba haka ba karka sake zuwa inda nake kaje kayi rayuwarka nayi tawa.”

“Haba Nafeesa kinsan bazan iya rayuwa babu keba, kiyi haƙuri yadda kike so haka za’ayi ina sonki fiye da komai a rayuwata, bazan yadda a rabani dake ba, Inna Jumma bata isa ba dole tana gani zata haƙura na aureki.”

“Ni dai na baka umarni mafita ta rage gareka.”

Tayi maganar tana shigewa cikin gida a fusace, Jamila bayansu tabi yayin da Al’ameen ya shige motarsa cikin tashin hankali, duk abinda ke faruwa Abbas na zaune cikin adaidaita sahu yana kallon su, shi a yau Al’ameen tausayi ma ya basa domin kuwa yaga ikon Allah.

Tabbas Al’ameen baya cikin hankalinsa shine yake bawa Mace hkr tana zaginsa cikin ƙasƙantar da kai, lallai Nafeesa ta cuci Al’ameen numfashi ya saki tare da cewa mai adaidaitan ya juya dashi.

Washegari

A matuƙar razane ta farka tare da danna ihu.

“Ƙarya ne basu mutu ba, babu wanda ya isa ya kashe min ƴaƴana, Mansura kin cuceni wayyo Allah na wayyo na shiga uku.”

Tayi maganar tana wani irin fisga likitar dake gefenta ne tayi saurin riƙeta ita da Maimu tana ƙwalawa wata nurse kira, taje ta kira DOCTOR da ƙyar aka samu ta daina fisgar sai dai bata daina sambatu ba, kuka take tsakaninta da Allah tamkar ranta zai fita har da majina har shiɗewa take, runtse idanunta Maimu tayi cike da tausayin Aunty Amarya itama hawaye na bin idanunta tabbas akwai ciwo ace yaranka biyu su kenan ubangiji ya baka lokaci ɗaya ka rasasu Tabbas akwai baƙin ciki, da ƙyar ta daina maganganun sai kuka kawai da takeyi, Daddy Maimu ta kira a waya tare da sanar dashi Aunty ta farka babu ɓata lokaci Daddy yazo asibitin ya samu Aunty Amarya sai zabgar ihu take gefenta ya zauna tare da jawota jikinsa cikin tausayi da rarrashinta yake riƙe da ita Maimu ficewa tayi tabar room ɗin.

“Daddyn Al’ameen shikenan na rasa yarana dukkan su sun mutu, Ka cemin ƙarya ne ba da gaske bane na shiga uku nima mutuwa zanyi.”

“Ba zaki mutu ba Amarya, ita rayuwa dama haka ta gada babu wanda zai wuce lokacin sa, kwanansu ya ƙare bamu isa mu hanasu mutuwa ba. Tabbas akwai ciwo sai dai ya zamuyi dole muyi haƙuri mu rungumi ƙaddara mu bisu da addu’a, karki manta da cewa ni abu huɗu na rasa a rayuwata, matata Gaji ƴaƴana Uku Aksat da Afnan ga ihsan, ni kuma nace me kenan, Amarya yanzu haka ciwon zuciya ke damuna saboda damuwa da kuma yanayin aikina suka jawo min ga girma ya fara shigar min dan Allah ki daina damuwa saboda damuwarki zata ƙara shigar dani wani hali bana son wannan ciwon yayi sanadiyar da zan tafi na barku, kin rasa yaranki da kika haifa a cikin ki, amma ki sani baki rasa rayuwarki duka ba, saboda kina da wasu ƴaƴan ƴaƴan Gaji naki ne amarya bazasu barki ki shiga wani hali ba, kin sani tamkar Gaji haka suka ɗaukeki Al’ameen bazai barki ki shiga mawuyacin hali ba, dan Allah kiyi haƙuri.”

Yayi Maganar cike da taushin murya yana share mata hawayenta, Aunty Amarya cikin shashsheƙar kuka tace.

“Daddyn Al’ameen, ka sani kashe min su akayi kuma wallahi bazan ƙyale ba, itama sai na kasheta na kashe ƴaƴanta.”

Zaro idanunsa Daddy yayi cikin rashin fahimta yace.

“Kashe su akayi, kuma bazaki ƙyale ba itama sai kin kasheta kin kashe mata ƴaƴanta, kin san wanda yayi kisan ne Amarya.?”

Saurin kallonsa tayi, cike da tashin hankali domin kuwa bata san tayi suɓutar baki ba, hawaye ne suka zubo daga idanunta tace.

“Ban sani ba amma kowa cewa yake kashesu akayi kuma ko wayene sai na nemosa na rama kisan ƴaƴana.”

“Hmmm! Amarya kin ɗimauce da yawa, mtsss! Hmm! Ki kwanta ki huta bara na yiwa DOCTOR magana ya sallamemu ko?”

Kanta ta ɗaga, Daddy ya fita tashi tayi ta zauna tare da sakin kuka mai cin rai ta furta.

“Kin cuci rayuwata Mansura kin kashe min gobe na, kin tarwatsa min farin ciki na, wallahi wallahi! Kamar yadda kika sakani kuka kema sai kinyi kukan da yafi nawa sai na tarwatsa rayuwarki bazan ƙyaleki ba.”

Tayi Maganar tana huci cikin kuka tamkar mahaukaciya shigowar Maimu ya sa tayi shuru ba ta ci gaba da Maganar ba, zuwa can Daddy ya dawo tare da cewa su tashi su tafi gida.

Koda suka koma gida babu wanda bai tausayawa amarya ba, Inna Jumma nasiha da bata baki ta dinga yi yayin da Amarya kukanta yaƙi tsayuwa, shigowar Hajiya Mansura ɗakin ya sata ƙara sakin kukan mai cin rai Ganin bazata iya jure ganin Hajiya Mansura ba ya sata tashi ta shige toilet ta zauna tare da kuma sakin kuka, Hajiya Mansura lura da yanayin Amarya ya sata binta toilet ɗin tana zaune sai kuka take Hajiya Mansura ne tace.

“Amarya kukan me kike haka kiyi haƙuri, ke kikayi wannan kuskuren kece kika bada address ɗin motar da yaranki ke ciki, naji baƙin ciki da takaicin mutuwarsu.”

Miƙewa Aunty Amarya tayi tana saka hannu ta goge hawayenta cikin dashashshiyar muryar ta da ta ƙoshi da kuka tace.

“Ƙarya kikeyi da gangan kika shirya kashe min ƴaƴana, su wanda kika saka ɗin mahaukata ne da bazasu gane ƴaƴana ba, cewa zakiyi kin shiryawa min zagon ƙasa, kuma ki sani Wallahi bazan ƙyale ba.”

Hajiya Mansura cike da mamaki ta zaro idanunta tare da cewa.

“Amarya kina hankalinki kuwa kinsan me kike faɗa, nine nake miki zagon ƙasan, ki sani fa kece kika kirani kika bani adreshin motar amma kice da gangan nayi, ki dawo hankalinki amarya kisan me kike faɗa.”

“Bazan dawo hankalin nawa ba tunda ce miki akayi hauka nake ƴaƴa biyu ba wasa ba kuma jini ba ruwa bane wallahi mansura sai kin girbi abinda kika shuka min.”

“Hmmm! Amarya kenan kuɗi fa kike nema kuma dama dole bazaki samesu cikin sauƙi ba, rasa waɗannan yaran bazai saka ki rasa ƙudirinki ba dole burinki zai cika ak…”

“Dalla rufe min baki macuciya ce miki akayi kuɗi yafi ƴaƴa ne, tambayarki nake kuɗi yafi ƴaƴa ne, ba komai kuɗi yake maka ba amma ƴaƴa zasu maka komai a rayuwa, a yanzu bana Maganar kuɗin fansar ƴaƴana nake Magana akai kuma dole ki amshi hukunci.”

“Na amshi hukunci, ni zan amshi hukunci, ehh lallai da alamu wannan mutuwar ta fara juya miki ƙwaƙwalwa, to idan kin manta bara na tuna miki kece kika kashe yaranki da kanki ba wani ba.”

Tayi maganar tana ficewa daga toilet ɗin cikin ɓacin rai tare da ɗaukar mayafinta tabar gidan gabaki ɗaya domin kuwa taga alamar hauka akan amarya zata iya tona musu asiri muddun ta zauna gara kawai ta tafi.

*****

Umma tun ɗazu take bugawa da Ablah akan ta shirya taje su yiwa dangin mahaifinta ta’aziya ita da Hafsa amma sam Ablah taƙi, Hafsa dake zaune gefe ne wacce ta dawo daga tafiya jiya tace.

“Umma tunda taƙi kawai ki ƙyaleta.”

“Bazai yiwu na ƙyaleta ba Hafsa, dangin mahaifinta ne fa kuma sune gatanta, bazan yadda ta raina su ba, kin fara min taurin kai Ablah abinda da bakya min shi, bazan lamunci hakan ba, bana son raini kwatakwata, ko ranan da kika faɗawa mahaifinki maganganu son ranki banji daɗinsa ba, saboda ban baki tarbiyyar raina na sama dake ba, ki daina jayayya dani Ablah.”

Kanta Ablah ta ɗago idanunta na cikowa da hawaye tace.

“Umma baki fahimceni bane, ni ban isa na miki taurin kai ba ko nayi jayayya dake umma bana ƙaunar zuwa gidan ne saboda ganin Papa yana ƙona min rai, meyasa kuka kasa fahimtata akansa kuke ganin rashin kunya nake masa, sam ko kaɗan ba haka bane babu ɗan fa zaiƙi ubansa muddun uban na kirki ne, umma sanin kanki ne mun rayu cikin azaba da wahala kuma duk shine wanda ya jefa mu a cikin sa, mun rayu cikin talauci da yunwa, amma shi yana can yana rayuwarsa cikin daula da ƙoshi ya manta damu a rayuwarsa ya zubar damu a bola, baya ko tunawa da mu a cikin rayuwarsa, shine yanzu lokaci guda zaizo yace mu ƴaƴan sa ne, Umma ina roƙon ki da Allah karki sanar da ABDUL cewa muna da uba idan ya dawo hutu dan Allah na roƙeki domin kuwa bazamu taɓa karɓarsa a matsayin uba ba, Wallahi Umma na tsani Papa mungu…”

Ba ta kai ga ƙarshen maganar ba Umma ta kifeta da mari cikin ɓacin rai da takaici tace.

“Ba laifinsa bane! Laifi nane ni ce mai laifi da naƙi bin maganar iyayena shine ubangiji ya jarabceni da wannan jarabawar, hukunci na ne ya faɗa akansa ubangiji ya min hukunci da zafin rasa jin daɗin Aure, Saboda butulcewa iyayena da nayi, hausa sunce duk wanda baiji bari ba zaiji hoho, kuma ni banji bari ba, shiyasa na amshi hoho daga garesa, ni zaki tsana ki hukunta ba shi ba, Karkije tunda kince bazaki ba, babu damuwa iyakata da matsayina kika nuna min sakamako ne Ablah na gode.”

Runtse idanunta Ablah tayi hawaye ba biyo idanunta tace.

“Wannan ba laifin ki bane ki daina ɗaurawa kanki wannan ƙaddarar da baki da alhaki a cikin sa, Umma meyasa kike ɗaurewa Papa gindi ko dai har yanzu kina buƙatar mijinki ne, domin kuwa karesa da kike ya fara yawa, Umma ni fa na faɗa miki bazan taɓa amsarsa a matsayin uba ba, kuma bazan sake zuwa wannan Family ɗin ba.”

“Ko da kuwa shi masoyinki ya aure ki, shi kina sonsa har yanzu na sani Ablah domin kuwa kaf wannan duniyar babu wanda zai fahimci halin da kike ciki sama dani, kina tambayata ina bukatar mijina ko, hmmm! Ablah a yau kin faɗa min Magana mafi muni wacce ban taɓa tunaninsa daga gareki ba wai meyasa kika sauya ne lokaci ɗaya kike abu tamkar ba ke ba, bana nason na tsawaita fushina akanki sannan ina baki umarnin cewa ki tashi ki shirya yanzu ku tafi gaisuwa keda Hafsa umarni na baki.”

“Shikenan Umma bazan tsallake umarnin ki ba Hafsa muje.”

Tayi maganar tana miƙewa tare da ɗaukar hijabinta suka tafi Umma zama tayi tayi shuru tana tunanin rayuwa sosai ta damu da irin ƙiyayyar da Ablah take gwadawa mahaifinta.

Can kuwa Ablah sanda suka shiga Estate ɗin da Faruq ta fara cin karo cikin raha da wasa suka gaisa ta masa ta’aziya, inda Haidar yake suka nufa har Faruq ɗin.

“Yaya ina wuni.”

Ɗago kansa yayi ya kalleta tare da cewa.

“Lafiya ya Umma?”

“Umma tana lafiya, ya mukaji da hakuri?”

“Mun gode Allah, dama ina son zuwa gidan ku sai kuma wannan rashin ya faru amma insha Allah idan an gama makoki zanzo, Papa yana garden shi da Daddy sai kuje ki musu gaisuwa.”

“A’a yaya Haidar ba shi nazo na gaisar ba Inna Jumma kawai na yiwa ta’aziyya.”

Tayi maganar tana saka kanta zata bar wajen taji muryar Haidar.

“Uba ubane komai lalacewar sa, kina da tarbiyya da ilimi karki ɓata wayonki da aikin jahilai, Papa yayi kuskure kuma ya amshi laifinsa sannan komai zamu gyarasa meyasa bazai ci arzikin mu ba ki yafe masa.”

Idanunta Ablah ta runtse tare da shigewa ba tare da ta amsawa Haidar ba.

A bakin falon su Al’ameen taci karo dashi zai fito gefe ta matsa ya shige ko idanunsa bai ɗaga ya kalleta ba, hawaye ne suka biyo idanunta ta bisa da kallon so domin kuwa ta kasa ciresa a zuciyarta, cikin sanyin murya ta furta.

“Bansan mena aikata masa ba ya yasar dani, na kasa ciresa a raina ina sonsa Hafsa.”

“Ablah ki daina saka damuwar wanda bai damu dake ba a zuciyarki, kiyi haƙuri ki roƙi Allah ya cire miki sonsa a zuciyarki, ki share hawayen ki mu shiga.”

Hawayenta ta share tare da shigewa ciki room ɗin Aunty Amarya suka fara shiga, tana zaune gefen bed ɗin ta idanunta sun kunbura Sosai tsabar kuka, har cikin ranta Aunty Amarya ta bata tausayi, gaisawa sukayi da Aunty Mami addan aunty Amarya, kafin Ablah ta dubi Aunty Amarya tace.

“Ya hkrn rashi?”

Idanunta ta ɗago tare da kallon Ablah cikin muryar kuka tace.

“Kinzo ne kimin dariya ki mayar min da martani?”

“Hmmm! Cuta da mutuwa ba’a musu dariya domin kuwa basu tsallake kan kowa ba, ita Afnan meye laifinta da zan yiwa mutuwarta dariya, ina tsammana mata rahama kuma naji zafin mutuwarta Allah ya jiƙanta da rahama.”

Tayi maganar tana tashi ta tafi tabar ɗakin Aunty Amarya gagara magana tayi sai hawayenta dake cigaba da zuba.

Ko da suka shiga bedroom Inna Jumma cike yake da mutane, sosai Inna Jumma taji daɗin zuwa ta domin kuwa batayi tunanin zata zo ba.

“Ablah kece tafe?”

“Ehh Inna Jumma nice ya hkr?”

“Mun godewa Allah Ablah naji daɗin zuwanki ina Umman taki ba tare kuke bane?”

“Umma tana gida, bana tunanin zatazo.”

Kanta Inna Jumma ta girgiza, jira take a watse daga makoki zasuje domin neman afuwarta.

Sun juma sosai a bedroom ɗin Inna Jumma kafin suka koma gida.

*****

Washegari da misalin sha biyun rana, Abbas yaje gidan Jamila domin ya haɗu da ita, cikin Sa’a kuwa ya sameta ita kaɗai, har cikin falonta ta shigar dashi.

“Nayi mamakin ganinka domin kuwa ban taɓa tsammanin zaka za ziyarce ni ba.”

Murmushi ABBAS yayi tare da ɗaukar jagar daya shigo da ita ya ijiyewa Jamila a gabanta yace.

“Ki buɗe wannan jakar kafin mu fara Magana.”

Hannu Jamila tasa ta ja zif ɗin zaro idanunta tayi ganin wasu mahaukatan kuɗaɗe.

“Waɗannan kuɗaɗen fa Abbas na meye.”?

“Na ki idan har kin amince da contract ɗin dana zo miki dashi, wannan ma kaɗan zan ƙara miki biyun wannan.”

“Contract, Abbas faɗa min ko menene komai wuyarsa da azabarsa, zan iya muddun zan samu irin wannan kuɗaɗen.”

Murmushi ABBAS dama yasan za’a rina.

“Jamila aikin cin amana ne, anya kuwa zaki iya.?”

“Hmmm! Abbas ko amanar waye ne zan iya cinta muddun zan samu kuɗi domin kuwa duk yawon bariki na ban taɓa haɗa ido da irin waɗannan kuɗaɗen ba, bazan barsu su shigeni ba.”

“Well tunda zaki iya, Ƙawarki Nafeesa nake son ki sanar dani ta yaya akayi har Al’ameen ya amince zai aureta kuma take juyasa YADDA take so, bama nason ki ɓoye min komai idan kika min ƙarya ko kika yaudareni kin san halina wannan masifa zai zamo miki muddun kika yaudareni.”

Shuru Jamila tayi…

<< Aminaina Ko Ita 57Aminaina Ko Ita 59 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×