Tunda ta dawo take sintiri baƙin ciki da ƙunar zuciyar rashin ƴaƴanta su suke cinta a zuciyarta kwatakwata bata jin daɗin rayuwar tunda ta rasa yaranta, wannan wanne irin rayuwace ashe haka zafin rasa ƴaƴa yake meyasa Mansura taci amanarta, mezata mata ta rama.
“Amarya lafiya kuwa?”
Taji muryar Inna Jumma, juyawa tayi tare da sakin kuka tace.
“Inna dama haka zafin rasa ƴaƴa yake, ciwo sosai nakeji a raina, na kasa jurewa”?
Kama hanunta Inna Jumma tayi suka zauna tare da dubanta cikin rarrashi tace.
“Amarya mutuwa huɗu suna da zafi wanda zafinsu bazai bar zuciyarka ba har kaima taka mutuwarka tazo ta sameka mutuwar iyaye mutuwar miji mutuwar ɗan uwa mutuwar Ɗanka daka haifa, wannan mutuwar suna da ciwo sosai a rayuwa, sai dai ya zamuyi dole mu hkr domin kuwa komai zamuyi bazasu dawo ba, kiyi haƙuri amarya ki dangana ki bisu da addu’a hakan shine kawai gatan da zaki musu.”
“Shikenan zanta musu addu’a.”
Tayi Maganar tana tashi tabar wajen.
Ko washegari da safe bayan sunyi breakfast Inna Jumma ta aika Faruq yaje ya ɗauko Ablah babu yadda ta iya haka dole ta dawo.
Suna zaune a falo da Inna Jumma Al’ameen ya sauƙo yana waya tare da zama gefe.
“Ina jinki Nafeesa, bana sanar dake cewa jibi su Daddy zasuzo tambaya sai ki sanar da Baba, sannan ki cewa Mama Garba zai kawo mata saƙon zuwa anjuma.”
Shuru yayi na ɗan wani lokaci kafin ya kuma cewa.
“Karki damu farin ciki na, kinsan dai babu abinda zan iya yi babu ke a rayuwata jigona ce ke dan haka ki kwantar da hankalin ki ni naki ne.”
Yayi Maganar yana katse kiran, Ablah runtse idanunta tayi cike da ƙunar rai ta tashi zata bar Wajen Inna Jumma tace ,
“Ina zakije Ablah dawo ki zauna ita ramin ƙarya ai ƙurarrece.”
“Inna bacci zanje na ɗanyi kaina ke ciwo.”
Fuskantar halin da ta shiga yasa Inna Jumma ɗaga mata kai barin wajen tayi Haidar kuma ya shigo ko inda Al’ameen yake bai kalla ba ya zauna gefen Inna Jumma.
“Kallon me kike min haka cinyeni zakiyi ne, na faɗa miki nafi ƙarfi nki sai sabuwar jini.”
Dariya Inna Jumma tayi tare da ranƙwashinsa tace.
“Ni yanzu ai Faruq shine nawa, kai da wancan hamagon bakwa lissafina, wannan farar takaddar kuma fa da take hanunka.”
“Au wannan takaddar, ungo riƙe.”
Inna Jumma hannu tasa ta amsa tare da cewa.
“Ta mecece.?”
“Zan buɗe Companyna ranar Monday, na gama komai sannan kayan da nake jira sun iso, A A M nig limited Company Aam dana sanya yana Nufin Aliyu Ablah Madina nayi amfani da sunan ƴan uwana na sanyawa Companyn suna, Companyn da za’a ke fita da Awudiga ne, da kuma ƙaro, na sanar da Daddy da Abi ranar monday za’ayi shagalin buɗe Companyn sannan na yanke cewa Ablah da Madina da kuma Maimu Rufaida duk zasu yi aiki a cikin Companyn wannan takaddar na ijiyewa Al’ameen aikinsa ne, ki basa.”
Tunda Haidar ya fara Maganar Al’ameen ke kallonsa har sai da yakai ƙarshe kafin Al’ameen yace.
“Kana ƙoƙarin aikata kuskure ne Haidar, kasan barinka ma’aikatata babbar matsala ce, matsalar dake tsakanina da kai bai shafi Companyn mu ba.”
“Hmmm! Babbar matsala to me zai shafeni da matsalar Companyn ka, ko dama kasa a ranka zan dawwama ne a ƙarƙashin ka ina maka bauta bazan tsaya da ƙafafuna ba, hmmm! Ka saɓa lamba domin kuwa na tashi na tsaya da ƙafafuna.”
“Zanfi kowa farin cikin ka tsaya da ƙafafunka sannan zanyi farin cikin ka buɗe Companyn ka na kanka amma ka sani ban ɗauki Companyn da nake aiki a matsayin nawa ba, a matsayin namu mu uku yake kuma saɓanins dakai bazai sa na sauya hakan ba Haidar koda mutuwa nayi ko kayi ko Faruq yayi wannan Companyn dole ya zamana na gode saboda sunayen mune a takaddun, kuma akwai sa hanun kowannen mu a ciki, kaine jigon Companyn karka bari ya rushe zaka iya zuba ma’aikata ka bawa Rufaida shugabanci da jagorancin Companyn da ka buɗe kai kuma ka cigaba da aiki a Companyn mu shawara na baka gudun kuskure.”
Yana yin maganar ya kwashi wayoyinsa ya haura sama, Haidar shima miƙewa yayi yana duban Inna Jumma tare da ƙwalawa Ablah kira, cewa Inna Jumma yayi.
“Nasan yanzu kin daina sanya baki a cikin lamarin mu saboda kina jin zafin mu, sai dai zan roƙeki alfarmar ki basa takaddarsa, muddun barin Companyn sa kuskure na, to kuwa na amshi wannan kuskuren saboda kuskurene da zai zamo min alkairi a gaba, bana kallon Al’ameen a matsayin ɗan…”
“A’a yaya Haidar karka ƙarisa ruwa bazai wanke ba haka wuƙa bazai kankare ba, dole za’a kirasa ɗan uwanka.”
“Ki barsu Ablah su faɗi abinda sukaga dama, lokaci ne nan gaba zasu fahimci kuskuren su, basa ɗaukar zancen mu da mahimmanci dan haka babu amfanin dakatar dasu, ina zakije kika ɗauko jaka da hijab.?”
“Zamu fita ne, shopping da yaya Haidar.”
“A dawo lafiya.”
Inna Jumma ta furta tana tashi a wajen tare da ɗaukar takaddar, Ablah tare suka fita da Haidar Sahad store suka nufa, sosai ya mata siyayya sun fito zasu shiga mota, Haidar yaji an kira sa juyawa yayi yaga Nabil tsaye ya harɗe hanunsa, murmushi Haidar yayi tare da ƙarisawa wajensa yana basa hanu.
“Kaga mutanen Barno, yaushe ka sauƙa ɗan sanda Abokin kowa.”
“Kana da abun dariya Aliyu, jiya na sauƙa, amm waccar babyn fa da kuke tare.”
“Umm to Fa ina ka dosa ka taya ne.?”
Dariya Nabil yasa yana cewa.
“Idan nace na taya zakayi mamaki ne?”
“Ƙwarai kuwa saboda ban taɓa jin kayi budurwa ba.”
“To yau mata nayi ba budurwa ba, na taya nawa ka sayar min.”
“Farashin ta da tsada bazaka iya biya ba.”
Murmushi Nabil yayi tare da dukan kafaɗar Haidar ya ƙarisa gaban Ablah.
“Keee! Ɓarauniya, bani abinda kika sace mini.”
A matuƙar razane Ablah ta ɗago ta kallesa.
“Sata kuma ni Malam.?”
“Ba malam ba, Ɗan sanda ne mai ritsa ɓarayi da marassa gaskiya bani abinda kika satar min.”
“Ban fahimce ka ba Malam me zan satar maka ni ba ɓarauniya bace, yaya Haidar kazo mubar nan dan Allah.”
“To ni ɓarauniya na ɗaukeki saboda kin min satar zuciyata, I love You.”
“I love You! Mtsss, Malam kaga na maka kama da laila majnun ne.?”
“Ƙwarai kuwa kama ta haƙiƙa kuwa, ina son na zamo makullin zuciyarki fatan zan samu karɓuwa?”
“Bazaka samu ba.”
Tayi maganar tana buɗe mota ta shiga tare da rufewa, murmushi Haidar yayi tare da ƙarisowa yace.
“Na faɗa maka farashinta tsada garesa.”
“Na yadda, to a bani alakoron numbern waya.”
Dariya sukayi dukkan su Haidar ya basa numbern Ablah sannan Sukayi Sallama Nabil ya shiga sahat shi kuma Haidar ya shiga yaja motar sunyi nisa da tafiya Haidar yace.
“Sunansa Nabil mutumin kirki ne, zanso ki amshesa, Tunda kin rasa Al’ameen nasan zai baki farin ciki fiye da Al’ameen, Nabil baya ƙarya baya yaudara, sannan baya Neman matan banza, ya dace daya zamo surikin mu.”
“Yaya Haidar bana buƙatar wata Soyayya yanzu kawai mu rufe wannan babin.”
“Meyasa zakice haka, aure dole a ka…”
“Dan Allah yaya Haidar mubar Wannan Maganar.”
“Shikenan tunda haka kike buƙata.”
Yayi maganar yana cigaba da driving ɗinsa, ko da suka iso gida a part ɗinsu Haidar yayi parking tare suka shiga cikin falon Momma na zaune Ablah ta zauna gefenta shi kuwa Haidar shigewa bedroom ɗinsa yayi turus ya tsaya ganin Rufaida ta fito daga toilet ɗin sa.
“Rufaida! Meya kawoki room ɗina da har zaki shige min tolmilet?”
“Yaya Haidar wani irin meya kawoni, meye laifi dan nasan lungu da saƙon room ɗin ka, Aure fa muke shirin yi.”
Murmushin takaici Haidar yayi tare da zaman saman stool yace.
“Hmmm! Rufaida bansan ke mahaukaciya bace sai yau ke tunani kike zanyi rayuwar Aure da ke, hmmm! Bazan kaucewa umarnin Momma ba, sai dai ki saka a ranki ba Aure zakiyi ba, rayuwar kurkuku zaki shigo domin kuwa gidan maƙabarta zai zamo miki, bazaki taɓa samun zuciyata ba har abada.”
“Mukan manta da masoyan mu mu so maƙiyan mu, idan har ɗan uwanka ya iya tozarta ka to tabbas bare kuma kasheka zaiyi, bansan meyasa ake yawan rashin Sa’a a soyayya ba, Rufaida baki da laifi dan kin soshi domin kuwa ita zuciya bata da shamaki, yaya Haidar ban taɓa zaton zaka tozarta wani bare ba ma balle kuma ƴar Uwar ka, baka kyauta ba, duk tsiya masoyi yafi maƙiyi, ka faɗa min ita wacce kake son meta tsinana maka idan banda damuwa da baƙin ciki, shine kaima kake son ka karya zuciyar wata, hmmm! Rufaida wai kije inji Momma.”
Ablah tayi maganar tana juyawa wanda gabaki ɗaya basu ga shigowarta ba sai Muryar ta da sukaji Rufaida bayan Ablah tabi suka barsa tsaye cikin sanyi jiki.
Tabbas maganganun Ablah gaskiya ne babu abinda Soyayya ta tsinana masa sai baƙin ciki.
Numfashi ya saki tare da tashi ya shige toilet.
*****
Mama kin sanar da Baba cewa gobe iyayen Al’ameen zasuzo, ina farin ciki sosai Mama saboda zan shiga cikin daula, Mama da rabon kema hajjin bana dake za’aje.?”
“Nafeesa ai bazanyi bori da sanyin jiki ba, tun yaushe na sanar dashi harya sanar da baffanu Garzali zaizo goben su amshe su, yauwa Nafeesa kuɗi nake so ya za’ayi zan turawa ladi ta Mana turaren wuta idan akwai dubu ɗari zaki bani.”
“Baza’a rasa ba, zaizo anjuma Al’ameen ɗin zan amsa kuɗin a wajensa yauwa Mama amm kince zaki koma wajen boka akan wannan tsohuwar da wannan ɗan iskan titin Faruq Saboda sune matsalar mu yanzu.”
Tayi maganar dai-dai Jamila na shigowa, zama tayi Mama tace.
“Ehh gobe Talata baya aiki insha Allah sai jibi zanje, ina son ma ya bamu harda na mallaka, sannan munyi Magana da Asabe ƴar Katsina kan maganin matan da zata haɗa mana itama dai tace dubu arba’in zamu kawo, to kinga ya kamata mu samu kuɗi a hanunsa wanda zai ishemu.”
Jamila ce tace.
“Mama iyayen Al’ameen ɗin sunzo su ne?”
“A’a Jamila basu zo ba yace dai gobe zasuzo dan harma an sanar da baffanta.”
“To Allah ya kaimu, amm bara na shiga tollet na fito.”
Tayi maganar tana tashi ta shige bedroom ɗin su Nafeesa toilet ta shiga ta rufe tare da dannawa Abbas kira Abbas dake zaune ne a Office ɗinsa ya ga kiran Jamila hannu yasa ya ɗaga kiran tare da cewa.
“Lafiya kuwa Jamila?”
“Ba lafiya ba Abbas ko kana da labarin gobe iyayen Al’ameen zasu aiko a saka rana da Nafeesa?”
Numfashi Abbas ya sauƙe tare da cewa.
“Bani da labari amma bari na bincika naji zan kiraki anjuma.”
Yayi Maganar yana katse kiran, wayar Jamila ta kashe tare da juyowa sukaci karo da Nazifa dake tsaye tana sauraronta wani irin tsorata Jamila tayi, murmushi Nazifa tayi tare da cewa.
“Kiyi haƙuri bansan kin shigo ba, na sa kaina.”
Tayi Maganar tana juyawa, Jamila cewa tayi, karkiga laifina Nazifa ba cutar Nafeesa nake ba.”
“Meyasa zanga laifinki bayan nasan akan dai-dai kike zanfi kowa farin ciki idan aka rusa wannan Auren Saboda ba Aure bane da za’ayisa dan Allah, nafi son Nafeesa ta shiryu tayi komai dan Allah, karki damu ni bazan tona miki asiri ba.”
“Na gode sosai Nazifa.”
Tayi Maganar tana ficewa falo ta koma ta samu mama da Nafeesa inda ta barsu Nafeesa ce tace.
“Jamila jibi Mama zata koma wajen boka, akan wannan tsohuwar da Faruq meyasa bazaki bita ba, ki kai sunan Alhaji Badamasi dan naga yanzu yana baki matsala.”
“Karki damu Nafeesa zan bita goben.”
Sun juma sosai suna taɗi kafin daga baya Nafeesa suka fita da Jamila.
*****
“Inna Jumma ga abinda Malam ya bani wannan rubutu ne yasa a dinga saka mata a cikin ruwan da zaisha, sannan wannan ƙullin maganin kuma yace hayaƙi ne za’a turara masa, sannan suna sauƙar alƙura’ani zasuyi sadaka gobe yauwa yace wai a tsakiyar first get ɗin gidan nan anyi wani ƙulli a wajen yace a watsa ruwan rubutun a Wajen.”
Numfashi Inna Jumma ta saki tare da furta.
“Yauwa to alhamdulillah! Bani ka gani ni da kaina zanyi wannan aikin.”
Tayi maganar tana amsar maganin, wayar Faruq ne tayi ringin ya ɗaga yaga Abbas.
“Faruq wai da gaske ne gobe za’aje a sawa Al’ameen rana da Nafeesa.”
“Ehh Abbas amma insha Allah hakan bazata faru ba, yanzu ma daga wajen mai sangaya nake.”
“To shikenan sai na fito daga Office zan biyo.”
Sallama sukayi tare da katse wayar miƙewa Faruq yayi yace.
“Bara naje Company.”
“Allah ya tsare a dawo lafiya.”
Inna Jumma itama tashi tayi ta buɗe fridge ta tsiyayi coca cola mai duhun baƙi ta zuba rubutun a cikin sa bedroom ɗin Al’ameen ta nufa yana waya Inna Jumma ta zauna a bakin gadonsa.
“Ta yaya za’ace babu abinda kuka gane game da wannan haɗarin so kuke ku ce shima wannan mutuwar zai wuce a banza kenan bazai yiwu ba dole ne kuyi kokari ku gano wake da saka hannu cikin wannan accident ɗin.”
Yayi .aganar yana huci tare da katse kiran, duban Inna Jumma yayi yace.
“Yanzu Inna kina kallo zaki zuba idanu Haidar ya wofintar da Companyn da muka juma muna rayasa, kinsan wannan Companyn zai iya rushewa muddun babu Haidar a cikin sa.”
“Na sani Aminu, Haidar bazan barsa yabar aiki a cikin wannan Companyn ba, hmmm! Gashi shanye ka bani cup ɗin.”
Kallon cup ɗin Al’ameen yayi tare da cewa.
“Coca Inna kinsan bai dameni ba.”
“Kasha Aminu tunda na baka.”
Hannu yasa ya amsa babu musu idanunsa ya runtse ya shanye tas sannan ya bata cup ɗin amsa tayi tare da tashi tace.
“Ka jirani ina zuwa.”
Bedroom ɗinsa ta rufe tare da dawowa ta jona kaskon turaren wuta a socket shi dai Al’ameen da idanu ya bita yana kallon ikon Allah, wannan garin maganin ta zuba a ciki, a hankali hayaƙi ya fara tashi yayin da Inna Jumma ta rufe ko ina, tunda hayaƙin ya turniƙe ɗakin, Al’ameen yace.
“Inna meye haka wannan ai sai y…”
Bai ƙarisa ba kansa ya fara wani irin juyawa ji yake tamkar ana tsinka masa jijiyoyin kansa dafe kansa yayi tare da runtse idanunsa yana cije bakinsa, cike da azaba zuwa can ya kwanta tare da rufe idanunsa bacci ne mai nauyin gaske ya ɗaukesa…