Skip to content
Part 58 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Gefensa Inna Jumma ta zauna tana tofa masa addu’o’i falaƙi nasi ayatul kursiyu, da amanarrasulu, ta dinga tofa masa, wani irin gumi ne yake haɗawa duk ac dake cikin ɗakin sosai ya jiƙe da gumi, duk baccin da yake amma muƙurƙusu yakeyi, yafi awa uku yana wannan baccin mai wahalar gaske, Inna Jumma bata gusa daga kusa dashi ba, wayarta ta ɗaga ta kira Haidar yana zaune a garden yaga kiran Inna Jumma ɗagawa yayi.

“Kazo bedroom ɗin Al’ameen yanzu ka sameni.”

“Bedroom ɗin Al’ameen kuma?”

“Ehh kazo Yanzun nan.”

“Amma inna jum…”

“Karka cemin komai kazo kawai na ce maka.”

Tayi maganar tana katse kiran, tsuka Haidar yaja tare da tashi ya taho, tana zaune tayi tagumi.

“Lafiya Inna Jumma meyake faruwa.?”

Yayi maganar a gigice yana kallon yanda Al’ameen ke mutsuttsuku, ga gumi da ya wanke sa duk ƙarfin ac dake ɗakin 

“Ka zauna Ali.”

“Bazan iya zama ba har sai kin faɗa min meke faruwa da ɗan uwana?”

“Dama kana sonsa kake gaba dashi, meyasa zaka damu da halin da yake ciki.”?

“Ba lokacin amsa miki tambaya bane ki faɗa min meya samesa?”

“Ka zauna ka saurari wannan voice ɗin.”

Da sauri ya amshi wayar, a gigice ya danna record ɗin, Maganar Jamila da Abbas ne, inda take sanar dashi asirin da Nafeesa ta masa, cike da mungun mamaki da sanyin jiki ya zame ya zauna tare da dafa kafaɗar Inna Jumma yace.

“Itace ta sashi a cikin wannan halin, Inna meyasa Nafeesa zatayi haka, yaudarar mu tayi, me tayiwa ɗan uwana ki duba kiga halin da yake ciki, muje asibiti Inna karya shiga wani hali.”

“Asirin ke fita daga jikinsa babu buƙatar muje asibiti, ka jira ya dawo hankalinsa.”

A matuƙar gigice Haidar yake yiwa Al’ameen fifita tare da munguwar tsanar Nafeesa, gami da Allah wadarai da ita, a mungun firgice ya farka sai kuma ya hau wani irin baƙin amai, wanda ya tsorata Haidar riƙesa yayi, Inna Jumma na tofa masa addu’o’i sai da yayi aman sosai kafin ya fara furta.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Ablah! Ablah! Ablah.”

“Ablah bata nan Al’ameen.”

A hankali ya ɗago idanunsa da Sukayi jajur ya zubawa Haidar shigowar Nafeesa Office ɗinsa ranar da ta juya masa hankali ne ya fara dawo masa a ƙwaƙwalwar sa har zuwa abubuwan da suka faru, da ƙarfi cikin wani irin ƙunar rai yace.

“A’a! A’a impossible! Haidar me yake faruwa dani, me nayi wani irin kuskure na aikata, me Nafeesa ta watsa min a wancan Ranar.?”

Yayi maganar yana riƙe Haidar tare da cewa.

“Munyi faɗa da kai da gaske akan Nafeesa, ko dai mafarki nake, ku faɗa min ni ne na saurari Nafeesa, ina bani bane bazan taɓa son Wannan lalatacciyar yarinyar ba ƴar tasha, Haidar ina Ablah da gaske na wofintar da ita, itace rayuwata itace zuciyata.”

Shuru Haidar yayi tare da dafa kafaɗar sa yace.

“Ka nutsu ɗan na fahimci komai, na gane rayuwa da iya gudunta ga mai gaskiya da kuma marar gaskiya, ka sani ƙarya bata taɓa tsawo bata nisan zango duk abinda aka ginasa bisa turbar cutarwa dole wata rana zaizo ƙarshe, gaskiya itace bata da ƙarshe, na gane wacece Nafeesa, kuma zata girbi abinda ta shuka, ta maka asiri ɗan uwa Saboda kawai kuɗi, wai meyasa mutane muke da son Zuciya akan dukiya, hmmm! Ablah zata dawo gareka saboda kaine kafi kowa dacewa da Rayuwarta ka nutsu.”

Hawayene ya zubo daga idanunsu suka rungume juna.

“Bansan na aikata waɗannan munanan kuskuren ba a cikin rayuwata, ka yafe min Haidar.”

“Na manta da komai Al’ameen daga yanzu komai bai faru ba, amma dole Nafeesa ta gane kurenta.”

Yayi maganar tare da sakin Al’ameen wayarsa ya ɗaga tare da kiran Helina wacce rabonsa da ita ya juma sosai, tayi mamakin kiran nasa itama sosai, sanar da ita yayi cewa ta gayyato masa ƴan jarida da gidajen rediyo dana tv suzo Ambassador Ahmad Giwa Estate, yayi .aganar yana katse kiran, Inna Jumma ce tace.

“Me zaka yiwa ƴan jarida Ali.?”

“Idan sunzo zaki gani, mun gode sosai Inna Jumma kinyi namijin ƙoƙari wajen ceto rayuwar mu.”

“Bani nayi ƙoƙarin ba, Abbas da ɗan uwanku Faruq su zaku godewa domin kuwa Abbas shine jigon tonawa Nafeesa asiri, ya taimaki rayuwar ka Al’ameen ka gode masa mutumin kirki ne.”

Al’ameen duban Inna Jumma yayi cikin mamaki ya furta.

“Abbas, Abbas kuma Inna Jumma shine kike kira mutumin kirki wannan marar mutuncin.”

Daga bakin ƙofa yace.

“Abbas ba marar mutunci bane Al’ameen Mutumin ƙwarai ne Saboda ya sadaukar maka da rayuwarsa a lokacin da yake da damar mallakar muradinka Ablah, amma sai son Zuciya baisa ya yadda ya biye mata ba yayi ƙoƙarin ƙwaco rayuwarka daga JALALAR Nafeesa gode masa ya kamata kayi ba aibatasa ba, domin kuwa da yaso da yanzu zancen aurensa ake da Ablah.”

“Abunne ya bani mamaki ƙwarai Faruq ace wai Abbas shine yayi wannan abun kirkin nasan halinsa sarai fiye da yadda kuka sansa.”

“Hmmm! Koma yaka sansa zai iya yiwuwa yanzu ya sauya, kai dai ka masa godiya kawai kuma nima zan masa.”

Cewar Haidar.

Shikenan zan gode masa yayi maganar yana tashi ya fita da sauri da kallo suka bisa Inna Jumma tace.

“Ina kuma zaije kamar an zaburesa.”

Dariya Haidar yayi tare da cewa.

“Baki gane ba kee! Hmmm to wajen Ablah zaije.”

Dariya Inna Jumma tasa.

Bedroom ɗin ya tura tana kwance tayi shuru da alamu tunani take.

“Ablah!”

Ya kira sunanta a sanyaye, kamar a cikin mafarki taji muryar Al’ameen, a hankali ta ɗago idanunta ta dubi inda taji kiran, shi ta gani kuwa tsaye, kanta ta kawar gefe tare da jan tsuka.

“Ablah tsuka kika min bakya son ganina ne, Ablah! Nayi kuskure ki yafe min, ina sonki fiye da ko wacce mac…”

“Ka dakata dalla malam! Soyayyar banza Soyayyar wofi, Oh ita Amaryar taka fa, ina ka barta kaga bana son rainin hankali, na tsaneka ni kuma bana ƙaunarka I Hate you.”

Tayi maganar cikin zafin zuciya, Al’ameen ya buɗe baki zaiyi Magana, Ablah ta miƙe a fusace ta faɗa toilet ta rufe.

Idanunsa ya runtse ya zaiyi Ablah ta fahimci bashi da laifi akan komai daya faru, bakin toilet ɗin yaje ya tsaya tare da cewa.

“Dan Allah ki buɗe ki fito ki saurareni Ablah Nafeesa cuta ta tayi bansan na ce ina sonta ba, Ablah kin sani kece kaɗai muradin Al’ameen bani da wani burin da ya wuce na mallakeki a rayuwata.”

Yayi maganar hawaye na zubo masa Ablah kunnuwanta ta toshe duk abinda yake faɗa babu wani abu guda ɗaya wanda ta saurara ya juma sosai zaune a wajen Ablah taƙi buɗewa dole tasa ya fita badan yaso ba.

Cikin sanyin jiki ya fito, yana fitowa ƴan jarida sukayo kansa, cikin mamaki yake dubansu wani ɗan jarida ne yaji yana tambayarsa cewa.

“Al’ameen Ahmad Giwa yanzu aka mana kiran gaggawa game da zancen auren ka, da Nafeesa Bulama kyari, an saka ranar Auren ne.?”

Daga baya sukaji muryar Haidar ya ce.

“Aliyu Ahmad Giwa shine zai amsa wannan tambayar tare da Umar Ahmad Giwa.”

Kansu ƴan jaridar suka juyo murmushi Al’ameen yayi tare da ɗaga wayarsa ya dannawa Nafeesa kira ringin ɗaya ta ɗaga tare da cewa.

“Sweetheart ya akayi?”

“Ki kunna tv ki saurari babban labari game da Auren mu, sai ki tanada min gorin albishir ɗina.”

“Wanne gidan tv.?”

“Duk wanda kika buɗe zaki samu live ne duk Abuja da kewayenta sun ɗauka.”

Katse kiran tayi cike da farin ciki domin kuwa ita zato take labarin saka ranar aurenta, za’a sanar Mama ta kwaɗawa kira tare da Nazifa ta kunna tv.

“Muna sauraronku Haidar.?”

Murmushi Haidar ya saki tare da cewa.

“Magana ce akan Aure tsakanin Al’ameen da Nafeesa wanda Abuja da kewayenta ta ɗauka cewa Bulama kyari’s zasu haɗa zuri’a da Ambassador Ahmad Giwa, to ga wata kyakkyawar sanarwa cewa babu Aure tsakanin Al’ameen da Nafeesa, Saboda basu dace ba, amm nasan zaata tambaya meyasa basu dace ba, ga wannan ku duba itace amsar tambayar ku.”

Ya yi maganar Faruq Kuma na miƙa musu wayarsa gabaki ɗaya ƴan jaridan idanu suka zaro domin kuwa video ne wanda akayi ɗaukar inda Nafeesa ta fara zuwa Office ɗin Al’ameen da barazanar da ta masa akan ɗan uwansa Haidar na ƙoƙarin shiga tsakanin su muddun bai sota ba, suna gama kallon wannan Faruq ya sa musu video na gaba wanda Nafeesa ke watsawa Al’ameen asiri a jiki, sai kuma ya sanya musu muryar Jamila da take sanar da Abbas asiri Nafeesa ta yiwa Al’ameen.”

Tunda Nafeesa ta sanya idanunta ta ga Abinda ke faruwa a gidan tv inda duk Abuja ke kallo tayi wani irin mungun razane tana furta.

“Whattttttt! Mama kina kallon abinda ke faruwa kina kallon tozarcin da suke min, Mama mafarki nane fa yake ƙoƙarin rushewa, sanda aski yazo gaban goshi sann…”

Bata ƙarisa ba taji a gidan tv Faruq na cewa.

“Dama Hausawa sunce aski idan yazo gaban goshi yafi zafi, sannan dama ai ramin ƙarya ƙurarrace, nasha faɗa mata cewa nine zan kawo ƙarshen makircinta, sai ta raina tunanina, to yanzu ga abinda ya faru kun gani kuma duniya ma ta gani da idanunta hisabi ya rage gareku, a yanzu babu mai zargin Familyn Ahmad Giwa da yaudara, bissalam.”

Remote ta ɗauka ta kashe tv idanunta yayi jajur ƙara ta saki tare da cewa.

“Ta ci amanata Mama Jamila taci amanata itace ta bayyana musu sirrina na tasa na rasa komai mafarkina ya rushe, sunana ya ɓaci Mama yanzu wa zai yadda yazo ya nemi aurena kowa gudun aurena zaiyi Mama, sun cuceni.”

Tayi maganar tana sakin kuka mai cin rai tare da faɗawa jikin Mama, numfashi Mama ta saki cike da takaici da mungun tashin hankali ba Auren da aka fasa bane ya ɗaga mata hankali sai sunan da aka ɓatawa Nafeesa.

“A’isha ashe dama haka kika tozartani a rayuwa ke da ƴarki, ashe dama makira ce ke mai bin bokaye ki rasa dawa zaki haɗa kanki sai ahalin da suka fiki matsayi da daraja kin cuceni kin ɓata min suna jama’ar gari kowa zai ke min kallon mutumin banza wanda bai isa da gidan sa ba, dole ki amshi hukuncin wannan mummunan saɓon da kikayi dan haka ki ɗauki ƴarki ku barmin gidana, na sake ki saki ɗaya, na tsaneki A’isha bana ƙaunar sake ganin wannan mummunan fuskar taki.”

A matuƙar razane Mama ta miƙe tana kallon Baba tamkar sauƙar aradu taji Maganar tasa.

“Saki ka sakeni Alhaji?”

“Ƙwarai na sakeki Aisha dama na gaji da mummunan halinki, sai ki koma ƙauyen naku wataƙila zaman can zaifi miki nan daɗi, tare da ita zaku barmin gidana kafin na dawo karna sameku cikin gidan nan idan kuma na sameku wallahi sai na muku korar kare garama ku bar min gidana cikin mutunci.”

Nazifa cike da tashin hankali tace.

“Dan Allah Baba kayi hkr karka koresu kasan Mama bata da kowa a cikin gari ƴan uwanta duk suna ƙauye, bazata iya zaman ƙauye ba dan Allah ka rufa mata asiri Baba kayi hkr.”

“Kinsan Allah Nazifa babu rufin asiri tsakanina da A’isha da wannan Yarinyar, suje can su ƙarata duk take takensu da rashin godiyar Allah da suke min a cikin gidan nan ina sane saka musu ido kawai nayi baga ina ƙarshen zalama zata kaisu to yanzu ga inda ta kawoku sai ku tafi can ku ƙarata, Nazifa Allah ya miki albarka baki taɓa bijire min ba, ke ƴar albarka ce, Kuma albarka ta dinga binki kenan a rayuwarki.”

Ihu Mama ta saka tare da durƙusawa tana cewa.

“Dan girman Allah Alhaji ka rufa min asiri bani da kowa bani da gata sai kai Wallahi na tuba bazan sake ba, dan Allah ka mayar da Auren nan.”

Tsuka mai ƙarfi Baba yaja tare da ficewa yana musu kallon banza Nafeesa tamkar zatayi hauka takeji tsabar baƙin ciki, lallai Jamila ta cika baƙar kunama, mai harbin mutuwa, ita Jamila zataci Amana, juyawa tayi a fusace zata fita taji muryar Mama na ce mata.

“Ina zakije Nafeesa, kizo mu tafi ƙauye kar dare yayi ya dawo ya samemu kin san halinsa fa. “

“Nazo mu tafi ƙauye, Mama ni ne zanje ƙauye na zauna wallahi bazanje ba, ina nan cikin gari, ke dai da ya zamo miki dole ki tafi.”

Tayi Maganar tana ficewa a fusace, Nazifa ne cikin kuka tace.

“Mama kinga ranar da nake tsoron zuwanta ko, tun sanda kuka kama hanyar ɓata, nake ƙoƙarin ku gane ku gyara amma sai kike min kallon bani da wayo ina yiwa Aunty Nafeesa baƙin ciki, Mama ni ce zan cutu muddun kika bar gidan nan, gashi ita babu ruwanta ta fita abunda ko ta damu da halin da kike ciki, Hmmm! Ba komai akwai Allah zai zamo gatana.”

Tayi maganar tana juyawa da gudu cikin kuka ta shige ɗaki, mama hawaye mai zafi ne y zubo daga idanunta bata taɓa zaton wannan mummunar ranar zata zo mata ba, ta ina zata fara iya rayuwa a ƙauye yanzu

“Tabbas nayi kuskure Nazifa gashi na fara amsar sakamako.”

Tayi maganar cikin zafin rai tare da shigewa bedroom ɗinta ta fara haɗa kayanta.

“Haidar nayi mamaki da saɓani ya shiga tsakanina da kai abinda ban taɓa zaton zai faru ba, Tabbas Nafeesa ta cuceni munguwar cuta.”

“Hakane Al’ameen amma ka ɗauka cewa wannan ƙaddarar mu ce rubutacciya da dole sai ta faru damu, ka manta nima na manta.”

“Haidar na yadda da kai amma fa bazan bar Nafeesa da iya wannan hukunci ba, dole sai nasa taji tsanar rayuwarta ta gwammaci mutuwa da rayuwa, abun takaicin ta haɗani da Ablah kwatakwata bata ma saurarona ina cikin damuwa fa.”

Dariya Faruq dake gefe riƙe da system ɗinsa yayi tare da cewa.

“Wai kai zato kake Ablah zata fahimci ka, kayi kuskure ai domin kuwa, ka mata wulaƙanci mafi muni a rayuwa, da karuwa fa ka danganta mata uwa ka sheganta ta, ta yaya zata manta wannan harta yafe maka, gaskiya zaiyi wahala, sannan ita wannan shegiyar Nafeesa ka shareta kawai ka zamo mai Aji da idan ka wuce babi baka kuma waiwayarsa.”

“Bashi taci Faruq kuma dole ta biya, ina bayan Al’ameen akan ƙudirinsa dole Nafeesa ta fuskanci JALALA.”

Numfashi Al’ameen ya saki zaiyi Magana Aunty Amarya ta sauƙo ita da Daddy, Daddy dubansu yayi tare da neman waje ya zauna yace.

“Wani irin shashanci da rashin kai kukayi yau wa yace ku gayyato min ƴan jarida gidan nan?”

Haidar ne yace.

“Daddy ita wannan yariny…”

Hannu Daddy ya ɗaga masa tare da cewa.

“Ba sai kace komai ba na saurari komai duk da haka abinda kuka aikata mata bai kyautu ba.

Wulaƙanta ɗan Adam ba abu bane mai kyau nan gaba karku kuma wannan kuskuren, yanzu ya maganar zuwan mu gidan su yarinyar.”

Saurin ɗago kansa Al’ameen yayi tare da furta.

“Waye ni cap hmmm! Allah ya tsari gatari noma, me zanyi da wannan jakar Daddy, Yarinyar da ta nemi tarwatsa min rayuwata, Daddy ni fa Ablah nake so.”

Murmushi Daddy ya yi tare da miƙewa yana cewa.

“Bazan baka ƴata ba, kaje ka nemo wata da ai cewa kayi baka sonta ko ka manta ne.”

Duban Daddy Al’ameen yayi tare da cewa.

“Za kuma ka rasa ɗanka.”

Shima Daddy murmushi kawai yayi tare da ficewa, Aunty Amarya sama ta haura ba tare da tace komai ba domin kuwa ita damuwarta kawai ke damunta ta yaya zata karɓi kadararta a wajen Mansura.

A fusace ta shigo cikin gidan babu Sallama ta faɗa bedroom ɗin Jamila tana kwance tare da wani gaye suna bacci Nafeesa ta buɗe fridge ɗinta ta ɗauko goran ruwan sanyi ta watsa musu a firgice suka farka Jamila tana ɗaga idanunta Nafeesa ta gani tsaye, numfashi ta saki dama tunda taga hirar da akayi da ƴan jarida a gidan tv tasan dole Nafeesa zatazo ta.

“Baƙar munafuka annamimiya tsinanniya, wallahi Jamila kinyi asara kinji kunya, wai Jamila ni zaki ci amanata, nawa aka biyaki kikayi wannan aikin?”

Dariya Jamila tasa sosai tare da kallon wannan saurayin dake gefenta tace.

“Masi let go, zuwa anjuma zan kiraka.”

Sanda saurayin ya fita sannan Jamila ta Dubeta tana taɓe bakinta tace.

“Dama bariki akwai amana ce, gani nayi neman kuɗi na fito, sannan ba harkar mutunci bane ta haɗamu bare kiyi tunanin za’a samu Amana, ke kan idan kina da kunya bazaki tunkareni kice naci amanarki ba, ke ba amanar kikaci ba, ko Al’ameen ɗin shine yace yana sonki, amanar ɗan uwansa kikaci, kinga kuwa idan naci amanarki ai banyi laifi ba daga gareki na koya, gashi dai yanzu kinyi biyu babu ba Al’ameen ba Haidar sai a kama wani sarkin.”

Hannu Nafeesa ta ɗaga a zuciye zata wanke Jamila da mari ta riƙe hannunta tana cewa,

“Idan kikayi kuskuren saka hannu a fuskata wallahi bazaki bar gidan nan ba sai na watsa miki acid a fuskarki dan…”

Bata kai ƙarshe ba ta ɗauketa da mari ta kuma ɗauketa da wani dafe fuskarta, Jamila tayi tana kallon Nafeesa cikin huci ta juya da gudu tayi falo, Nafeesa ganin Jamila ta fita ya sata tunanin ko guduwa zatayi ta fito da sauri, bata ankara ba taji sauƙar ruwan acid a gefen fuskarta, wani irin gigitacciyar ƙara Nafeesa tasa, ganin haka yasa Jamila ɗaukar akwatinta tare da cewa Nafeesa dake ihu.

“Ba’a taɓa taka Jamila a zauna lafiya, dama haushinki nakeji, Saboda kin fini farin jini, komai ke kike samu, burinki mu biki, yanzu sai naga da wani kyawun mazan zasu soki, zan bar garin nan yanzu bazaki sake ganina ba har abada, ko yanzu kasuwa ta watse ɗan koli yaci riba.”

Tayi Maganar tana ficewa da sauri Nafeesa tsabar azaba da baƙin ciki Magana ma ta gagareta, waje ta fito da ƙyar tana faɗuwa bata kallon gabanta, mutane ne sukayo kanta babu wanda ya ganeta saboda toyewa da gefen fuskarta yay…

<< Aminaina Ko Ita 60Aminaina Ko Ita 62 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×