“Kira sunana da kyau dan ubanka, marar mutunci, ka kasheta sai ka huta tunda baka da imani.”
“Daddy marina fa kayi akan na hukunta Rufaida, menene laifina Saboda na kare mutuncin Aunty, bansan laifi bane a wajenka Daddy da na ɗaga kaina.”
Zama Daddy yayi yana kallon Ablah tare da cewa.
“Zo nan ƴata Ablah.”
A ɗan razane Ablah ta ɗago kai ta kalli Daddy tare da tahowa cikin sanyin jiki, Aunty Amarya da idanunta sukayi jan munafurci ne ƙirjinta kuma na dukan Uku Uku ta kai dubanta garesu, Daddy umarni ya bawa kowa ya zauna, bayan kowa ya zauna ne Daddy yace.
“Ablah kece zaki warware wannan ƙulla ƙullan na juma da fahimtar ki tun bayan rasuwar Ummin Al’ameen, ni ne na saka Abbas ya bibiyeki saboda ina zargin cewa da haɗin bakinki akeyin kisa a cikin gida na, lokacin da Abbas ya fara bibiyar ki daga lokacin zancen ya sauya salo sai na fahimci wacce take min ɗauki ɗai ɗai a gidana abun takaicin da ban haushin shine wai akan dukiya take hakan saboda kawai ta mallaki arzikina, ban nuna cewa na fahimci komai ba sai dai na sawa yarana tsaron sirri musamman Al’ameen, sai dai kash a haka ƙaddara ta faɗa min kan Ƴaƴana biyu Afnan da Ihsan bisa kuskuren Abbas na kare rayuwar Maimu domin kuwa ita akaso kashewa Allah bai ƙaddara ba, hmmm! Na danne zuciyata ina zaune da makashina waje guda Saboda Siyasata da kuma abun kunyar da bayyanar hakan zata jawo min, sai dai nayi alƙawarin cewa jinin Gaji da yarana bazan bari ya tafi a banza ba, kafin Al’ameen kamin tambayar da take cikin ranka bari na amsa maka, saboda nasan zaka tambayeni ya akayi nasa Abbas cikin sha’anina duk da bamu jituwa da ahalinsu, saɓanin fahimta ne a tsakanin mu kuma mun daidaita, sannan Abbas yaro ne mai basira da mungun wayo nasan zai iya shiyasa na sashi, da gaske yana son Ablah tun lokacin da ya haɗa idanu da ita, amma yasan ɗana yana sonta shiyasa ya sadaukar da soyayyarsa ya danni zuciyarsa, duk abinda ke faruwa tsakanin ka da tsohuwar budurwarka Nafeesa duk ina samun labari a wajen Abbas.”
Yayi Maganar cikin haɗa fuska, Inna Jumma a mungun zabure tace.
“Ni ba Yarinya bace da zan jira sai Ablah tayi Magana ko ba tace komai ba, na fahimci inda zancen ya dosa, hmm! Amarya kinji kunya kuma kinyi asara Tabbas zaki girbi abinda kika shuka kinzo duniya a banza zaki koma a wofi ban taɓa ganin asararren mutum irinki ba.”
Ihu Aunty Amarya ta saka tare da mikewa tsaye tana ihu tana cewa.
“Me kike nufi Inna kina nufin nine zan aikata wannan mummunan aikin, Daddyn Al’ameen ka sanar da ita cewa bani bace, nima fa harda ƴaƴana aka kashe zan kashe ƴaƴana da kaina ne, karki min ƙazafi Inna.”
“Baki kashesu da kanki ba, sai bisa kuskuren ki ne ya shafesu, sun mutu ne saboda zunubinki kuma alhakin jininsu yana kanki, tabbas itace makashiyar ta juma tana ɓarna a cikin wannan gidan kun gagara fahimta koda sau ɗaya musamman ma kai Al’ameen zafin zuciya kawai ka iya shine yake rufe maka idanu ya hanaka kallon gabanka, itace ta kashe Ummi ta sanya mata guba, abun takaicin ni ne ta bawa gubar na bata ba tare da na san guba bace a ciki, a idanuna Ummi ta cika saboda zaluncinki, Daddy akwai hujja tabbas a hanuna na kasa bayyanar hujjar ce bisa tsoron sharrinta kar aƙi yadda dani ko a juyo da laifin kaina ki gafarceni Rufaida na zaɓi ɓoye gaskiyar ne Saboda gudun faɗawa cikin masifa Aksat Ummi ihsan Afnan cirewar ƙafar Ashfat duk itace, tunda nake a rayuwata ban taɓa ganin mutum marar imani irin Aunty Amarya ba da Hajiya Mansura, ko kuɗin da aka ɗauka jiya na Daddy itace ta ɗauka, ka daki Rufaida ba bisa hakkinta ba, ka nemi afuwarta.”
Tayi Maganar tana ɗauko wayarta tare da miƙawa Haidar tace.
“Gashi yaya Haidar ka shiga AUDIO ka kunna kowa yaji wannan itace shaidar da Abbas ya samu, Rufaida tasan komai domin kuwa tayi aiki tare da Abbas saboda tono gaskiya, gode mata ya kamata kuyi ba ku mata sakamako da duka ba, bata cancanci wannan hukuncin ba.”
“Wannan Maganar ƙarya ce ta yaya zan aikata wannan mummunan laifin, bani bace karku min sharri mana, karku yadda da ita Al’ameen bani da hannu ban san komai ba, Daddyn Al’ameen ka…”
Katseta Inna Jumma tayi cikin tsawa, yayin da Al’ameen ya kasa koda motsi tsabar mamaki ji yake Tamkar mafarki yake zai tashi yaga ba haka bane, Haidar recording ɗin da Abbas yayi ya turo mata ya kunna duk maganganun Aunty Amarya da Hajiya Mansura ne yake reading, wani sarawa kan Al’ameen yayi, a matuƙar harzuƙe ya miƙe zaiyi kan Aunty Amarya ya shaƙota, Ablah tayi gaggawar tare Aunty Amarya tare da cewa.
“Karka kuskura ka taɓata, tamkar Ummi haka kake kallonta yanda zaka kare martabar Ummi haka zaka kare martabar ta, koda kuwa dukkan jikinka kunnene bazaka taɓa yadda da wannan ƙazafin da muka mata ba, ko ka manta uwace ta gari ita to meyasa kuma zaka aikata aikin tirrr kareta ya kamata kayi ba kokowa da ita ba.”
Tayi Maganar tana riƙe kunkumi, Haidar yafi kowa jin takaici da baƙin ciki shi gani yake magana ma ɓata lokaci ne, police ya kira ba tare da kowa dake wajen ya lura daya kira ba, Aunty Amarya kuwa sosai take cikin tashin hankali ji take tamkar tayi fitsari a wandonta bata taɓa tunanin wannan mummunar ranar zata zo mata ba, sosai take kuka cike da tashin hankali, Al’ameen cewa Ablah yayi.
“Ki kauce ki bani hanya na kasheta tamkar yadda ta kashe Ummina, nayi alƙawarin cewa sai na ɗau fansar Ummina, ki matsa daga gabana Ablah, na kareta saboda banyi zaton mungun iri bace, wallahi sai kin shiga Uku Amarya.”
Daddy ne ya miƙe zai jawo hannunsa sai ga police sun shigo zaro idanunta Aunty Amarya tayi tana riƙe Inna Jumma.
“Dan girman Allah Inna Jumma ku rufa min asiri kar asirina ya tonu dan Allah karki bari su tafi dani wallahi na tuba bazan sake ba.”
Bige hanunta dake jikin Inna Jumma tayi, cike da masifa ta turata gaban police ɗin tace.
“Dole asirinki ya tono duniya tasan ke wacece sannan tayi Allah wadarai dake domin kuwa ke tsinanniya ce amarya idan ba tsinanne babu mai aikata kisan kai ki sani har rai huɗu kika sheƙe kuma ran mutum ba ran cinnaka bane, ku tafi da ita.”
Tayi Maganar cikin tsawa, ankwa wasu police mata biyu suka sanya mata tare da saita kanta da bindiga suka fita da ita Al’ameen wani irin huci yake yana riƙe da kansa Faruq ne ya dafasa tare da cewa.
“Lallai rayuwa ta lalace ko acikin mafarki ban taɓa tunanin haka zata faru a cikin gidan nan ba, sai dai ka kwantar da hankalin ka, Aunty Amarya tana hanun hukuma kuma zata amshi hukunci dai-dai da laifin da ta aikata, ka daina ɗaga hankalinka.”
“Tayi kuskure, kuma wannan kuskuren itama shine ƙarshen rayuwarta.”
Haidar yayi Maganar a zuciye.
Cike da jimami gami da al’ajabi suka watse a falon.
Ko da yamma tare da Haidar akaje gidan Hajiya Mansura arresting ɗinta, sai babu ita babu alamunta, wuni guda ana bincike a kanta sai dai ina tayi ɓatan dabo babu ita babu alamunta,a dole suka dawo gida tare da alƙawarin cewa police ɗin zasu binciko ta, abinda basu sani ba shine tabar ƙasar gabaki ɗaya.
*****
Sati ɗaya da kama Aunty Amarya yayin da aka wurgata prison na Wanda sai tayi sati biyu a ɗakin duhu ɗakin da ko tafin hannunka bazaka gani ba, kafin a miƙata ga sharia.
Nafeesa tana asibitin har yanzu ana mata jinyar fuskar yayin da idanunta guda ɗaya ya lalace ma’ana bazata gani da wannan idon ba, Mama itace a wajenta da ƙanwarta Nazifa.
Tare suka shigo asibitin Haidar da Al’ameen, suka nemi ɗakin da Nafeesa ke ciki, Mama suka samu zaune gefenta Nazifa ta fita tana bata abinci, Sallama Sukayi, Mama ta amsa idanunta na cikowa da hawaye.
“Haka kuma rayuwa tayi daku, umm ikon Allah Nafeesa haka kika zamo miskiniya.?”
Taji sauƙar muryar Haidar a kunnenta runtse idanunta tayi tana danasanin wulaƙanta rayuwarta da tayi.
“Daɗina da gobe saurin zuwa, gaskiya naji daɗin wannan abunda ya faru dake Nafeesa, wannan izna ce ga masu hankali irin naki, ko yanzu kinga sakamakon zalunci da cin amana, Hmmm! Jamila ta iya hukuncin da ya dace.”
Al’ameen yayi Maganar yana sakin murmushi daga bakin ƙofa Amnat da hawaye ke gudu a saman fuskarta na tausayin Aminiyarta tace.
“Nafeesa dama na faɗa miki halin Jamila kika ƙi yarda dani, nasan dole dama sai ta bar miki mungun tabo, da ace kin amshi abinda Allah ya baki baki bijire masa ba da duk haka bata faru da ke ba, kinyi biyu babu Nafeesa babu Al’ameen ba Haidar, ga lalacewar fuska abun takaicin ma harda asarar ido ɗaya, tabbas rayuwar bariki babu riba na fahimci hakan a tsakanin kwana biyu, lallai na tuba na koma ga ubangijina zan koma gida gaban iyayena nayi istibira’i nayi aure ne, bazan yadda ayar da ta sauƙa a kanki ta sauƙa a kaina ba, nazo na miki sallama zan koma garin mu yau, Allah ya baki lafiya ni kuma ina miki fatan shirya.”
Tayi Maganar daga bakin ƙofa tana juyawa tabar wajen wani irin kuka Nafeesa ta fashe dashi na baƙin ciki da danasani, Mama ganin ta fashe da kuka ya sata saurin dafa ta tana cewa.
“Ki daina kukan nan kin san ciwon ki zai samu matsala.”
“Kece ai kika sata a cikin matsalar tun farko da kin bata tarbiyya ta gari, bazata lalace haka ba, tana karuwanci tana kawo miki kuɗi kina amsa, har kina rakata gidan boka ke wacce irin uwace, duk abinda ya sameta a rayuwa kece kuma Allah sai ya muku hisabi, ki sani idan ɗa ya zamo na gari uwa ce, haka idan ɗa ya lalace daga uwa ce, kece kika cuci ƴarki da kanki, to dai yanzu gashi yadda rayuwa ta juya muku,sai kuje kuta fama da wahala.”
Yayi Maganar yana jan hannun Haidar suka fice daga asibitin.
Sanye take da doguwar riga baƙa wacce tasha stone mai ratsin blue ta yane kanta blue ɗin mayafi hannunta ɗauke da jaka ta fito da niyyar zuwa wajen Ummanta, Inna Jumma dake zaune ita da Al’ameen ne tace.
“Ablah ina zaki haka, kikaci ado kamar zaki wajen saurayi, bayan ga mijin naki a gefe na.”
Kallonta ta kai ga Al’ameen daya zuba mata idanu tare da kawar da kanta gefe ta amsawa Inna Jumma da cewa.
“Wajen Umma zani, sannan ni bani da saurayi bare kuma miji.”
Tayi Maganar a daƙile, murmushi Al’ameen yayi tare da cije leɓensa ya furta.
“Hmmm! Kauce kauce bashi yake ɓoye abinda yake zuciya ba, Saboda fuska tana bayyanawa yarinya, ko ki so ko ki ƙi, Al’ameen dai shine tauraronki, muje na kaiki.”
“Hmmm! Sai kuma kayi, ba ce maka akayi ina buƙatar ka kaini ba, tunda ba makauniya bace ni.”
Murmushi Inna Jumma tayi domin wannan damar tasu abun dariya ce.
“Kinga Ablah zo ki zauna muyi magana.”
Cewar Inna Jumma, Ablah harara ta sakarwa Al’ameen tare da zama gefen Inna Jumma tace.
“Gani.”
“Idan kinje ki cewa Umman taki, gobe idan Allah ya kaimu zamu shige Niger ni da babanki da kuma ke,ƙauyensu, sannan Ablah na fahimci har yanzu kina riƙe da mahaifinki a ranki, Saboda baki zuwa ki gaishesa, ki kula da rayuwa Ablah ba’a wasa da iyaye, ɗan uwanki Abdu jiya baban naku ke sanar dani cewa yana zuwa har Office ya gaishesa.”
“Shikenan Inna Jumma kiyi haƙuri zan gyara insha Allah, bara naje.”
Tayi Maganar tana tashi, Al’ameen bayanta yabi sanda suka fito waje tace.
“Wai wa kake bine kam.”
“Waye kuwa zanbi bayan ke, unguwar zan kaiki.”
“Na faɗa maka bana buƙata, koka manta da cewa baka buƙatata a rayuwa Saboda bani da Quality ɗin daya dace na zamo uwar ƴaƴanka.”
Numfashi Al’ameen ya saki tare da cewa.
“Oh Ablah kina da tuna baya abinda ya wuce kamata yayi mu manta dashi, kinsan wannan maganar da nayi bisa kuskure ne da kuma rashin sani, kuma koda kece kike a matsayin da nake abinda nayi shi zakiyi.”
Tsayawa daga tafiyar da takeyi tayi tare da cewa.
“Naji amma ni gaskiya ba wajen Umma zani ba, Prison zanje wajen Amarya.”
Cike da mamaki Al’ameen yace.
“Ban fahimta ba, Prison, akan meye zakije wajenta.”
“Saboda ina da buƙatar nayi magana da ita.”
“Koma menene bazaki ganta ba koda kinje saboda tana ɗakin duhu, kuma idan aka shigar da Mutum wannan ɗakin to babu wanda ake bari ya gansa koda kuwa uwace ko mahaifi, idan shi zai kaiki sai ki koma ciki.”
Numfashi Ablah ta saki tare da cewa.
“Shikenan bara naje wajen Umman to.”
Tayi Maganar tana ƙarisawa parking space numbern Rufaida ta kira tare da cewa tazo parking space ta sameta yanzu.
Shi kuwa motarsa ya buɗe mata yace.
“Ki shiga muje.”
“Amma kana ji fa yanzu na kira Rufaida ta same mu a nan kuma kace na shige mu tafi.”
“Meya haɗa hanyar ki da ta Rufaida?”
“Babu amma so nake tazo ka bata hkr.”
“Na bata haƙuri kuma,akan me ni zan bawa Rufaida hkr.”
“Akan cin mutuncin da ka mata ba da haƙƙin ta ba, ka daketa shiyasa nake son ka bata hke muddun kana buƙatar mu daidaita ni da kai.”
“Amma Ablah k…”
Hannu ta ɗaga masa tare da cewa.
“Ya zamo dole ka bata hkr yaya Al’ameen Saboda Rufaida tayi namijin ƙoƙari wajen bayyanar gaskiya, na sani ƙanwarka ce, amma ai durƙusawa wada ba gajiyawa ba ce Please ka bata hkr.”
“Shikenan tunda haka kike buƙata.”
“hakan shine dai-dai ma, to meye kuma na haɗa ran ka ɗanyi murmushi mana kafi kyau idan kayi murmushi.”
Tayi Maganar tana sakin dariya, murmushi yayi tare da rausayar da kansa yace.
“To ya na iya zuciyata tana neman matsugunni, nayi laifi har biyu ai bazan yadda na kuma na Uku ba, kin san me kuwa Ablah?”
Kanta ta girgiza tare da cewa,
“A’a ban sani ba sai ka faɗa.”
“Ban taɓa ganin mace mai kyawunki ba, annurinki daban yake, ke ɗin ta musamman ce a rayuwata, ban san wani irin so nake miki ba, saboda bana iya sarrafa kaina a duk sanda idanuna sukayi tozali da ke, zuciyata bugawa take da numfashin ki, shiyasa a ko yaushe nake jawa Nafeesa Allah ya isa na shiga tsakanin mu da tayi, duk da Allah ya nuna mata babbar aya ta hanyar sauya mata hallita amma bazan fasa ja mata Allah ya isa ba.”
“Hmmm! Yaya Al’ameen Tabbas Soyayya itace ginshiƙin rayuwa, musamman idan kayi da ce da masoyi na gari, ina sonka fiye da yacce nake son rayuwata, na shiga matsanancin hali sanda ka juyawa alƙibilata baya, sai dai kullum hasashena zaka dawo gareni muyi rayuwa wata rana ashe da gaske mafarkina zai tabbata, Tabbas Nafeesa abun Allah wadarai ne, sai dai yana da kyau mu yafewa waɗanda suka mana laifi a lokacin da nadama tazo musu ko suka shiga cikin masifa, saboda idan bamu yafe musu ba, zasu iya faɗawa cikin masifar da tafi wacce suke ciki, yafiya abune mai kyau a duk sanda ka yafe wani laifin daya maka a lokacin da kake da damar ɗaukar fansa sai kaga sanadiyyar wannan yafiyar Allah ya maka wata kyauta, halin annabawa ne yafiya kaga ina son ka yafewa Nafeesa, domin ta samu sassaucin hukunci a wajen ubangijinta, babu ɗan adam ɗin da baya kuskure a rayuwa, ka yafe mata nata kuskuren babu ruwanka da sake shiga sabgarta ko zuwa ka mata ba’a ka barta da ciwon da yake ranta ya isheta.”
Sosai jikin Al’ameen yayi sanyi, da maganar Ablah Tabbas maganarta gaskiya ce Allah yana son mai haƙuri da yafiya, samun mace ta gari mai nunawa mijinta hanyar aljanna abune mai wahala lallai yayi dace yana kuma godewa Ubangijinsa da baisa yayi asarar samunta a rayuwarsa ba, murmushi ya saki tare da cewa.
“Na yafe mata nurul ƙalbi na, Saboda ke, daga yau na manta da Nafeesa a babin rayuwata.”
“Hakan shine halin mutumin ƙwarai.”
Tayi Maganar dai-dai Rufaida na ƙarisowa wajen.
“Ablah gani.”
“Bani ke kiranki ba yaya Al’ameen ne.”
Cikin sanyin jiki Rufaida tace.
“Gani yaya Al’ameen.”
Kallonta yayi tare da cewa.
“Rufaida kiyi haƙuri da abinda ya faru jiya, na dakeki bisa kuskure da rashin sani, ban san abun haka yake ba.”
Murmushi Rufaida tayi tare da cewa.
“Shikenan yaya Al’ameen ya wuce.”
Murmushi yayi sannan ta tafi suma suka hau mota suka tafi.
*****
Yau sassafe Papa da Inna Jumma da Ablah suka kama hanyar Niger, a jirgi Awa ɗaya ya isar dasu, yayin da suka doshi ƙauyen su Umma, Papa ne ya musu jagora har cikin ƙauyen kasancewar shine yasan Wajen tunda suka shiga ƙauyen Ablah ke kalle kalle tana mamakin anan Umma tayi rayuwa.
Har ƙofar gidan Dada mahaifiyar Umma sukayi parking Inna Jumma da Ablah sune suka shiga da Sallama, wata matashiyar budurwa suka samu zaune a tsakar gidan tana surfen masara, amsa musu sallamar tayi tare da musu maraba, kujera ƴar tsugunno ta kawo musu, suka zauna bayan sun gaisa ne Inna Jumma ke tambayarta Ko Dada tana nan.
“Ehh tana nan, tana can cikin sauro bata fitowa ciwon ƙafa ke damunta, ku shiga tana ciki.”
Tayi Maganar tana nuna musu ƙofar sauron, tashi sukayi suka shiga da Sallama, tana zaune ta tsufa tukuf zama Inna Jumma tayi cike da tausayin tsohuwar dubanta tayi tare da cewa.
“Sannu Dada.”
Cike da kallon tsantsar kama da Ablah take da Hari take kallon Ablah kama ce sosai ta haƙiƙa, amsawa tayi da cewa.
“Yauwa sannunku da zuwa, sai dai ban ganeku ba.”
Murmushi Inna Jumma tayi tare da cewa.
“Amm sunana Jummai, munzo ne daga Nigeria, wannan kuma jikarki ce Ablah ƴar gidan Hari.”
Dada raurau tayi da idanunta na cikowa da hawaye, tace.
“Allah sarki dama naga kama matso kusa dani yarinya kinji, ina Hari take ta min nisa ina son sake ganinta a rayuwata, nayi kuskuren koranta kullum addu’a nake Allah ya sa na ganta ko da sau ɗaya ne a rayuwata.”
A jikinta Ablah ta jingina itama idanunta na cikowa da hawaye tace.
“Itama kullum maganarki take, tana son zuwa tana tsoron kalaman da kika mata.”
“Ɓacin rai ne ya sani yin wannan maganar amma daga baya na yafe mata na saka a kira min ita akata nemanta babu labarinta, kinga ni bani da ƙafa yanzu bazan iya zuwa inda take ba, yanzu ku ce mata tazo ina son ganinta kafin na koma ga ubangijina.”
Numfashi Inna Jumma ta saki tare da bawa Dada labarin dukkan abinda ya faru da Umma bayan barinta Niger tare da ƙarisawa da cewa.
“Dashi mijin nata muke tafe yana waje, dan Allah ina neman Alfarma dan Allah idan Hari tazo ki bata damar komawa ɗakin mijinta.”
Sun ɗan juma suna tattaunawa inda Dada ta amince da buƙatar Inna Jumma, shima Papa an masa iso yazo har soron Dada suka nemi afuwar juna sosai Ablah taji daɗin yadda Dada ta amshesu, sosai suka mata tara ta arziki kafin suka dawo gida Nigeriya.
Ko da Umma taji labarin yadda Dada ke kewarta sosai taji daɗin hakan, washegari ta shirya itama ta tafi wajen Dada.
*****
Yau ta kama Monday itace ranar da aka kawo Aunty Amarya kotu yayin da kotun ya cika maƙil da jama’a ƴan jarida sun zagaye ko ina na kotun jin cewa shari’ar Gidan AHMAD GIWA za’ayi Al’ameen Faruq Haidar Abbas Papa Daddy Abi kowa dai dake cikin gidan ya hallara a kotun yayin da ake jiran a shigo da Amarya, zuwa can aka taho da ita hannunta ɗaure da ankwa ko ta ina police sun zagayeta da bindiga, da wani irin mungun tsana Al’ameen ke kallonta yayin da Daddy ko inda take bai kalli ba Saboda yadda yake jin zafi a cikin zuciyarsa.
Ko da aka fara Shari’a ba’a wani jata tayi tsawo ba, duba da ƙwararan hujjojin da suke hannu ita kuma bata wahalar da Shari’a ba, alƙali ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya duba da laifin da ta aikata na kisan rai har huɗu, Al’ameen sosai yaji daɗin hukuncin da akayiwa amarya ko banza jinin Ummin sa bai tafi a banza ba, Aunty Amarya kuwa sai ihu take ita da ƴan uwanta tamkar ranta zai fita, alƙali umarnin a maida ta gidan yari ya bayar zuwa gobe a mata hukuncin ta, koda aka zo fita da ita Ablah tayi saurin tare gabanta tare da dubanta tace.
“Kowa da kalar tasa ƙaddarar wani tashi mai kyau wani kuma marar kyau, ke taki ƙaddarar mummuna ce kuma kece kika ƙaddarawa kanki, dama na faɗa miki cewa muddun ina numfashi burinki bazai taɓa cika ba, to kin gani ga yadda ƙarshenki yazo ina miki fatan alheri Allah ya yafe miki zunubinki idan kinyi nadama wataƙil kabarinki ya samu sukuni.”
Tunda ta fara maganar Aunty Amarya ke kallonta tana kuka ta kasa koda furta kalma ɗaya har police ɗin suka turata a mota.
Al’ameen a yau dukkan baƙin ciki da ciwon da yakeji akan mutuwar ahalinsa, ya kau fes yake jin zuciyarsa Daddy Sanda yayi hawaye yayin da ƴan jarida suka ruhu a kansa suna masa tambayoyi ko ɗaya bai amsa masa ba, Al’ameen shine ya janye Daddy suka shiga mota, cike da alhini suka koma gida.