Zaune take a bedroom ɗinta ita da Hafsa da ta kawo mata ziyara tare da mata albishir ɗin dawowar Umma, murmushi Ablah ta saki tare da cewa Hafsa.
"Amm Hafsa akwai haɗin da nake son nayi da zaki bani dama kuma ki yadda ki amince."
Gyara zamanta Hafsa tayi tare da cewa.
"Ban gane ba, wani irin haɗi kenan, faɗa min naji."
"Hmmm! Abbas so nake na haɗa alaƙar Soyayya tsakanin ki da Abbas mutumin kirki ne bana son muyi asarar sa Hafsa, nasan Abbas bazai ƙi ki ba, saboda baki da aibun da namiji. . .