Skip to content
Part 62 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Zaune take a bedroom ɗinta ita da Hafsa da ta kawo mata ziyara tare da mata albishir ɗin dawowar Umma, murmushi Ablah ta saki tare da cewa Hafsa.

“Amm Hafsa akwai haɗin da nake son nayi da zaki bani dama kuma ki yadda ki amince.”

Gyara zamanta Hafsa tayi tare da cewa.

“Ban gane ba, wani irin haɗi kenan, faɗa min naji.”

“Hmmm! Abbas so nake na haɗa alaƙar Soyayya tsakanin ki da Abbas mutumin kirki ne bana son muyi asarar sa Hafsa, nasan Abbas bazai ƙi ki ba, saboda baki da aibun da namiji zai ƙi ki, Please karki cemin a’a tunda ba saurayi kike dashi tsayayye ba.”

Duban Ablah Hafsa tayi tare da miƙewa tana ɗaukar hijab ɗinta tace.

“Tashi muje ki rakani na koma gida.”

“Ha’a ya kuma zaki tashi muna magana, ko iskancin zaki min.”

“Kinga ni babu wani iskancin da zan miki, saboda Abbas yafi ƙarfin ajina dan Allah kibarni a inda Allah ya ijiyeni.”

Murmushi Ablah tayi ganin muddun Abbas ya amince Hafsa zata soshi ya sa Ablah tashi tace.

“Shikenan muje drever ya sauƙe mu, nima zanje wajen Umma na mata sannu da hanya.”

Tare suka fita ta yiwa Inna Jumma Sallama suka shige.

Yana zaune cikin Office ɗinsa shi da Accounter suna lissafin abinda ya fita a wannan watan, yaji shigowar text message cikin wayarsa dubansa ya kai ga wayar yaga saƙon Ablah ne, murmushi yayi ba tare da ya duba saƙon ba sanda suka gama lissafi aka watse kafin ya ɗaga wayar tare da buɗe saƙom.

_Ba kowa bane ake faɗa wa sirrin zuciya sai mai cikar matsayi da cancanta kuma wanda ya dace, Babu komai a cikin tawa zuciyar sai kai da tunaninka Fatana a ko da yaushe na kasance a kusa da kai, na kasance cikin fara’a domin ka, ko da tafiya nake ya kasance kana kusa da ni, ko da magana zan yi ya kasance kai ne mai amsa tambayata, Da za a raba kaina gida biyu a taradda kwakwalwata na san babu abin da za a tarar a ciki sai tarin tunaninka, Da za a buɗe kirjina a taradda zuciyata na san babu komai a ciki sai ajiyarka. Da za a tsaga fatar jikina jini ya fita na san tabbas sai an ga naka, Mun zama ɗaya, kuma ina fatan mu kasance a wuri ɗaya na har abada, ina sonka fiye da komai nawa, kafi komai mahimmanci a rayuwata Yayana kuma Mijina ina sonka ina sonka bansan wani irin so nake maka ba domin kuwa bashi da iyaka._

Murmushi mai alamun sautin dariyar Al’ameen yayi yana lumshe idanunsa cike da jin daɗin kalaman, ya karanta saƙon yafi sau goma yana murmushi Haidar daya shigo yake ta sallama ko kaɗan bai jisa ba, hankalinsa yana kan text ɗin Ablah yana shan murmushi, warce wayar Haidar yayi tare da zama yana duba saƙon, dariya Haidar yayi tare da ijiye wayar a gefe yace.

“Oh su Juliet da Romio, umm ka tasa saƙo a gaba kanata dariya tamkar zararre ko Magana bakaji.”

Murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.

“Ina zan jika tunanina da lissafina sun kunce, umm kasan fa duk sanda naga wani abinda ya danganci Ablah kasa control ɗin kaina nake, ina sonta fiye da komai a rayuwata fa.”

Sosai Haidar ke dariya yace.

“To ai kai yanzu Yaya Haidar ya kamata ka fara kirana yaro, ka kuma daina rainani Saboda ni surikinka ne, daga yau yaya Haidar.”

Dariya sosai Al’ameen yayi har haƙwaransa suka bayyana yace.

“Waye zan cewa yayan kai ɗin, lallai kuwa kaci Kai yaro, amm ni ya Maganar buɗe Companyn ka ne, ya kamata Monday a buɗe, sannan abinda nake tunani mai zai hana ka bawa Rufaida shugabancin Companyn, sannan Ablah da Maimu Da kuma Khalifa da zai dawo next month Tunda ya kammala karatunsa, su jagoranci Companyn, amma kafin a ɗauki ma’aikata ana da buƙatar tantancewar ƙwararru ka fahimta ko?”

“Na fahimta nima tunanin da nayi kenan, sai dai Monday bazai yiwu ba mu buɗe, Saboda bamuyi interview da ma’aikata ba, ya kamata ace muna buɗewa kawai Companyn ya fara Reading, dole mu bari sai next month.”

“To shikenan Allah ya kaimu, ya Akayi meya shigo da kai.”?

“Takardar nan zaka bani na Alhaji Sabo wanda za’a kaiwa waken suya, idan ka saka hannun motar zata tafi yau.”

“Okay nasa hannun ma gata.”

Amsa Haidar yayi tare da ficewa, yana fita Al’ameen ya ɗaga wayarsa tare da ƙara karanta saƙon amsa ya mayar mata da.

_Son da nake yi miki tamkar madubi ne a cikin zuciyata, Ko da a ce ya fashe, idan kika sanya idanuwanki a kansa za ki tarar da ke a cikinsa, Son ki ya zamo jini a jikina ya bi ta jijiyoyin jikina ya narke a cikin zuciyata, Ranar da za a ce ga ki a kusa da ni, a wannan ranar zan ji ni a matsayin cikakken mutum mai sa’ar da babu irin sa, a wannan rana zan yi takun kasaita tamkar na sarkin da ke da daular da babu irin ta a duniya, saboda na mallaki mai kyawun da babu kamar ta, wadda nake fatan mu rayu tare rayuwa ta har abada, Ina hango mana rayuwa mai tsawo cikin shekaru masu ɗauke da ranaku masu ban mamaki a nan gaba, tare da kyawawan ƴaƴa masu kama da ke ina sonki fiye da yadda nake son kaina kece farin cikin Al’ameen i love You_

Sanda Ablah taga saƙon sosai taji daɗi suna zaune da Umma ne, Umman ne tace.

“Yauwa Ablah jiya babanku yazo yake sanar dani cewa sun zauna akan magabarku da Al’ameen, yace sun sanya ranar auren ku watan gaba dashi da Abi da Daddy da kuma Inna Jumma, shine baki sanar dani ba Ablah har sai da babanki ya faɗa min.”

Cike da mamaki Ablah ta zaro idanunta tace.

“Ban gane ba Umma, ansa ranar Auren mu kuma, ni bani da labari Wallahi idan ba yanzu da naji daga bakinki ba, ni Umma bama wannan maganar ba, Maganar komawarki gidan mu, ya kamata ki dawo kusa damu.”

“Hmmm Ablah kenan yanzu kece kike cemin na koma gidan babanki, ki sani babu Aure a tsakanina dashi domin kuwa a ƙa’idar sharia Idan Mace tayi sama da shekara biyu wasu ma sukace ɗaya bata tare da miji kuma babu abinda ya shiga tsakanin su na auratayya to wannan Aure babu shi ya mutu, sai dai idan lalura mai ƙarfi ce wacce za’a maka uzuri akanta to shine Aure yake nan, dan haka babu Auren babanki a kaina kuma bazan maida aurensa ba, nafi jin daɗin zamana a haka babu mijin.”

“Amma Umma ya k…”

“Karki yadda kice min komai idan ba haka ba ranki zai ɓaci, ni yanzu haka ma so nake na tattara na koma Niger kusa da Dada, tana buƙatata a kusa da ita, dan haka karna kuma jin wannan maganar daga bakinki, shima Abdu Daddyn ku yace zai nema masa gurbin karatu a Paris so ni yanzu na sauƙe duk wani nauyi da Allah ya ɗaura min a kanku.”

“Shikenan Umma, ni zan koma la’asar tayi.”

Tayi Maganar tana tashi, tare da bawa Umma 10k tace.

“Gashi Umma.”

Karɓa tayi tare da saka mata albarka sannan ta tafi.

Washegari da yamma lis aka kira Daddy daga kotu cewa yau za’a rataye AUNTY Amarya idan zaizo ayi a idanunsa, Daddy cewa yayi shi bazaije ba, ko su Al’ameen babu wanda ya sanarwa a cikin su, sai da aka gama sannan aka sanar dashi cewa an ratayeta za’ayi jana’iza da misalin sha daya na safe, ko da gari ya waye kuwa su Al’ameen ƙin zuwa kan gawar Aunty Amarya sukayi sai Daddy kawai daya halatta.

Bayan kwana uku da rasuwar Aunty Amarya suna zaune da Daddy da Inna Jumma Al’ameen ya dubi Daddy tare da cewa.

“Daddy maganar mu da Ablah naji kayi shuru baka ce komai ba.”

Murmushi Daddy yayi tare da cewa.

“Oh my son sorry mun gama Magana da Papan ku, mun yanke hukunci za’a haɗa auren naku duka lokaci ɗaya ku ukun, na kira Faruq naji ta bakinsa yake sanarmin cewa Maimu yake so, to mun yanke za’ayi Auren watan gaba, a cikin Estate ɗin nan zaku zauna bakwa buƙatar gini sai dai kuje ku duba part ɗin da zaku ɗauka, idan kuna da buƙatar gyara sai kuyi, sai ku fara shirye shiryen ku.”

Murmushi Al’ameen yayi cike da jin dadi yace.

“Yess Daddy naji daɗin saka wannan Ranar kusa hakan yamin.”

Yayi Maganar yana tashi, zai bar wajen Inna Jumma tace.

“Oh yaran zamani ko kunya bakaji kake murnar saka ranar aurenka a gaban mu.”

Dariya yasa yace.

“Bana take tsohuwa yau ranar farin ciki nane.”

Yayi Maganar cikin dariya yana barin wajen.

*****

Tunda aka sanya ranar Auren nasu Suka dage da gyaran part ɗin da zasu zauna yayin da kowa ya ɗauki part ɗaya.

Gefe guda kuma Ablah ta dage wajen ƙoƙarin haɗa Hafsa da Abbas yayin da abinda bata sani ba shine Abbas ya amince da Auren ƴar Uwar sa Aknam sanda ya sanar da ita dole yasa ta haƙura ta masa fatan alheri.

Gefen Umma kuwa, da kanta tazo ta samu Inna Jumma ta sanar da ita zata ɗauki Ablah ta koma gidanta zata mata gyara na amare, babu jayayya Inna Jumma tace ta ɗauki ƴarta tare da basu kuɗi masu yawa tace a mata gyaran dashi, suka koma unguwar Durmi tare da Umma, tunda suka koma Umma take gyara Ablah kasancewarta buzuwa.

Yau da yamma lis ana saura sati biyu Auren Al’ameen yayi parking a ƙofar gidan Umma tare da kiran Ablah yace ta fito tazo ta samesa bai juma ba ta fito sanye da hijab har ƙasa, motar ta buɗe ta shiga tare da zama tana lumshe idanunta ta furta.

“Missing You My Heart.”

Daga bayanta taji muryar Haidar na cewa.”To rasa kunya muna bayanki.”

  Bakinta ta toshe tare da juyowa tana dariya Haidar ne da Rufaida.

“Au yaya Al’ameen ai cemin zakayi da wasu a baya, Rufaida kwana biyu ko waya babu.”?

“Wallahi kuwa ke dai bari abubuwan ne sai a hankali.”

Gyaran murya Haidar yayi yace.

“Sauri muke zamu shige Company abinda ya kawo mu shine maganar event me kuke so ku shirya.?”

Kallon Rufaida Ablah tayi tare da cewa.

“Ehh to gaskiya ni kam bana son wasu bidia walimah kawai ya isa sai dai bansan Rufaida ba, ko tana da wasu shirye shiryen ta.”

Kanta Rufaida ta girgiza tace.

“Nima gaskiya bawai son bidia nake ba, walimah kawai yayi, dan Allah yaya Haidar karku wani saka denear kawai a ɗaura Aure ayi walimah ya isa.”

Al’ameen ne yace.

“Hakan ma yayi dama kinsan nima ba son hayaniya nake ba, sai dai ita Maimu bamu san shirinta ba karmu shiga haƙkinta.”

“Hakane zanyi Magana da ita.”

Cewar Faruq, sun ɗan juma suna tattaunawa lamarin bikin nasu kafin sukayi Sallama tare da tafiya.

Rayuwa ta yiwa Nafeesa zafi ta samu sauki sai dai idanunta ɗaya ne yake gani yayin da gefen fuskarta yayi damage, kullum tana maƙale da baƙin glass mai tintak, ko waje bata son fita yayin da kullum take shan tsangwamma da zagi wajen babanta sam bata jin daɗin gidan muddun yana nan, a wajen Nazifa kawai take samun sauƙi ga Mama tana ƙauye Baba ya koreta , gajiya da zama yasa Nazifa cewa suje kasuwa suyi siyayya, fita sukayi tare suna tafe suna zance, sunzo dai-dai temple ɗin wasu samari dake cike sukaji wani na cewa.

“Usman waccar kamar Nafeesa baka ganeta ba.”

“Ai kuwa itace, Oh kaga shegiya yadda ta sauya kamanni.”

“To idan banda kai Usman ina ka taɓa ganin lalatacce ya gama lafiya ai masifa yanzu ma ta fara gani, yanzu tayi karuwancin mu gani.”

“Ai na faɗa maka ko a tire aka kasata babu ɗan barikin da zai ɗauketa kasan bariki yayi ne sai diri da kyau ake binka daga lokacin da ka zamo ranar yamma kuma an gama da babinka, an dai yi asarar rayuwa.”

“Hmmm lallai bariki tayi riba, dan kuwa ga tabo an samu Allah ya kiyashe mu taɓewa.”

Sukayi Maganar suna mata mungun kallo wani irin ƙuna da baƙin ciki ne ya daki zuciyar Nafeesa idanunta ta runtse hawaye ya gangaro daga idanunta, ta gwammace bata fito ba da wannan baƙar Maganar da taji, ashe dama haka ake Allah wadarai da ita ana zaginta, wannan wacce irin mummunar rayuwa tayi, Nazifa ce tace.

“Aunty Nafeesa, kiyi haƙuri dama dole zaki ji maganganu irin waɗannan saboda kinyi abubuwa marassa kyau a rayuwarki da dole su bibiyeki kiyi haƙuri.”

“Na sani Nazifa amma ban zaci haka duniya take Allah wadarai dani ba, ashe kowa madalla yake da wannan mummunar ƙaddarar da ta sameni Jamila ta cuceni.”

“Ba jamila bace ta cuceki kece kika cuci kanki Aunty Nafeesa da kin zama mutumiyar kirki bazaki haɗa hanya da Jamila ba, bare ta cuceki, ki daina tada jijiyoyin wuya kawai ki tuba ki koma ga ubangijin ki.”

Shuru Nafeesa tayi zuciyarta na ƙuna har sukaje sukayi sayayyar suka dawo gida.

Ranaku sai gudu suke yayin da lokuta ke tafiya, yayin da bikin su Al’ameen ke ta ƙaratowa, gyara iya gyara Ablah tana shansa wajen Umma, yayin da fatarta tayi santsi tamkar flower, sai hada hadar biki suke kullum Ablah tana tare da Hafsa ƙawarta, gefen su Rufaida suma suna ta shan gyara, biki saura sati ɗaya Umma taga gatan da tayi tsammanin cewa tayi bankwana dashi, wato danginta domin kuwa mota guda ne sukazo mata daga jamhuriyar Nijar, sosai Umma taji daɗin ganin su.

Suma angwaye gefensu hakan take, suna ta nasu shirin gabaki ɗaya gari ya ɗauka Auren ƴaƴan Ahmad Giwa, saura kwana biyu Aure, Safwan Nabil Da Ishaq suka diro Abuja bikin abokansu, yayin da sukace su ina dole sai anyi denear da kansu suka haɗa denear ɗin suka kama hole mai tsadan gaske sanda Ablah sukayi waya da Al’ameen yake sanar mata cewa Safwan ya haɗa musu denear bata so hakan ba sai dai babu yacce ta iya tunda ya riga daya kama hotel.

Ranar Juma’a akayi walima a Ribaɗo hotel, walimar da ta tara manyan mutane, duk wanda yaje wajen sai ya bada labari yayinda amare sukayi kyau har suka gaji, anko ɗin less sukayi, mai kalar duhu da ratsin orange color, Sosai sukayi kyau bayan an gama walima, aka ɗauki dangin Umman Ablah da ita aka maida su gida.

Ranar deaner kuma da daddare, kowa ya shirya yayin da Ablah Aunty Saude ta shiryata cikin wani farin doguwar rigar net Wanda ya mata ɗas a jikinta sai goggoro da aka mata da ash color ɗin Flower saything Sosai tayi kyau, motoci abokan ango suka turo aka dinga ɗibar mutane ana tafiya dasu, yayin da ita kuma Ablah aka ce ta jira Al’ameen shi da kansa zaizo ya tafi da ita, gidan nasu shuru yayi kasancewar duk sun tafi Wajen deaner ɗin, har Hafsa, sai Ablah kawai dake jiran Al’ameen bai zoba sai ƙarfe, 9 a ƙofar gida yayi parking tare da kiran Aunty Saude a waya ya sanar mata cewa yana waje a turo masa Ablah, babu jumawa kuwa Aunty saude ta fito da ita tunda suka fito Al’ameen ya zuba mata idanu tamkar zai haɗiyeta sosai ta masa kyau kasancewar ƙofar gidan nasu, tarwal yake da haske, motar Aunty Saude ta buɗe mata ta shiga tare da cewa.

“Ku kula Dan Allah Al’ameen sannan ku tashi da wuri karku raba dare.”

“Shikenan Aunty insha Allah.”

Motar ta rufe musu, alamu Al’ameen ya yiwa drever daya ja su tafi kafin ya maida kallonsa ga Ablah tare da sakar mata murmushi.

“Kinyi kyau gimbiyata, anya kuwa kishi zai barni ki shiga wajen deaner ɗin nan a haka kuwa, tamkar zinariya haka nake kallonki sweetie na ina sonki fiye da komai a rayuwata.”

Murmushi Ablah tayi tare da cewa.

“Umm YANZU a hakan wai nayi kyau kenan, kasan fa ka fini kyau nesa ba kusa ba annuri na.”

Murmushi Al’ameen yayi yace.

“Oh zageni kawai malama, idan na fiki kyau kuma ai sai na fara girman kai.”

Dukkan su dariya sukayi, cike da so da ƙauna suke hira har suka iso cikin hole ɗin,tun daga bakin get ɗin hole ke haskawa da wani ado mai sauyin color, ƙofa aka buɗe masu suka fito hannun Al’ameen na maƙale dana Ablah suka shiga ciki, a cike hole ɗin yake yasha ado yayin da kiɗa ke tashi, su Faruq tuni sun juma a wajen program ɗin, Al’ameen shine yayi delay, a kujerarsu suka zauna yayin da Haidar ke yiwa Al’ameen raɗa a kunne bansan meya faɗa masa ba, sai Al’ameen ya yiwa Nabil alama da hannu yazo.

“Nabil bana son wannan taron ya juma Please a ƙarƙaresa a 1hours Please.”

Murmushi Nabil yayi tare da ɗaga masa kai alamun to.

Haka kuwa Akayi cikin tsari da burgewa sukayi deaner ɗin nasu yayin da Hafsa itace tayi gabatarwa akan Ablah itace Babbar Aminiyarta, Abbas shine ya wakilceta matsayin aboki.

Ƙarfe sha ɗaya aka tashi daga taron kamar yadda suka ɗauko kowa haka aka mayar da kowa inda aka ɗaukosa Al’ameen da

kansa ya sauƙe Ablah sun ɗan juma cikin motar suna hira kafin ta shiga cikin gida, cike da gajiya…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 64Aminaina Ko Ita 66 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×