Tsaye suke a filin jirgin sun rako Faruq Da Daddy da Maimu zasu shige American dama abinda ya hana Daddy komawa matsalolin daya dawo ya tarar ne to amma yanzu tunda komai ya daidaita iyalansa suna cikin kwanciyar hankali babu wata matsala ko fargabar da suke fuskanta, Shi yasa zasu koma kan aiki shi da Faruq suna tsaye har jirgin nasu ya ɗaga zuwa American.
Kafin suka dawo gida, Ablah part ɗin Momma ta shige wajen Umma, ta samu Umman suna falo ita da Momma suna tsinkar ganyen zogale, kusa dasu ta zauna ta tayasu tsinkar suna hira jefe jefe, bayan sun gama Momma ta haura sama ta barsu a falon Umma duban Ablah tayi da cikinta ya turo gaba domin kuwa a yanzu cikin nasu yana da wata 7 bakwai Rufaida kamma tana cikin na 8 tace.
“Kina amfani da maganin zaƙin nan dai ko.?”
“Ehh Umma ina amfani dashi yama kusa ƙarewa.”
“Yauwa ya karkiyi wasa dashi domin yana taimakawa sosai wajen samun sauƙin naƙuda.”
Tayi Maganar dai-dai wayar Ablah na ringin hannu tasa ta ɗaga wayar taga Dear, ɗaga wayar tayi tare da cewa gata nan zuwa, miƙewa tayi ta cewa Umma.
“Umma bara naje Yaya Al’ameen na kira na.”
“Okay to shikenan.”
A falo ta samesa yana zaune shi ɗaya zama tayi tana wash.
Al’ameen hannunsa yasa a kan cikin nata yana murmushi yace.
“Baby na yau tun safe fa bamu gaisa ba, shine ke kuma zaki tafi ki barni ni kaɗai kinsan bana son ki dinga nisa da rayuwata.”
“Hmmm! Dear wajen Umma naje, kasan babu wanda ya kaini son kasancewa da kai, gobe ne fa zan koma awu.”
“Ina sane kinsan bana wasa da abinda zai shafi babyna, Ablah ina matuƙar ƙaunarki ina jin farin ciki a duk lokacin dana tuna cewa kece uwar ƴaƴana, ko iya haka na gode ubangijina domin kuwa yamin ni’imar da ba kowa ya yiwa ba.”
Murmushi Ablah tayi tare da kwantar da kanta a kafaɗarsa tace.
“Ina sonka nima mijina.”
Tayi Maganar tana sakin dariya cikin farin ciki.
*****
Ranar da Rufaida ta cika wata tara da kwana goma a ranar cikin dare ta tashi da naƙuda, ƙarfe Uku aka kaita asibiti inda tasha wahala sosai kafin ta samu kanta ana kiran sallar asuba, ko kafin gari ya waye haihuwar ta karaɗe dangi, ta samu ƴarta macet kyakkyawa, Haidar sosai yayi farin ciki, ai kuwa gari na wayewa asibitin ya cika da ƴan uwa, Ablah dake zaune da nata cikin ne a gaba ta ɗauki jaririyar a hanunta tana kallonta gwanin ban sha’awa Inna Jumma ce tace.
“Saura kuma ke Ablah Allah ya sauƙe ki lafiya kema, ganan yarinya kam kyakkyawa da ita, Hari ina A’isha ta kawo ruwan zafin ne.”
Umma ne ta amsa da.
“Ta tafi kawowa, amma naji Kamar Aliyu yana cewa yanzu ma za’a basu sallama.”
Bata rufe bakinta ba Haidar ya shigo tare da cewa an basu Sallama, Inna Jumma ce tace ya kira Aunty ya sanar da ita an sallame su karta kawo ruwan zafin, tayi Maganar tana tashi, ta hau haɗa kayan su, suka fito zuwa mota a hanya Haidar ke cewa Ablah.
“Saura ke, kema kina watanki Allah ya baki da sauƙi.”
Da ameen Ablah ta amsa har suka ƙarisa cikin gida, part ɗin Rufaida, Umma itace ta yiwa jaririyar wanka, Ablah part ɗin ta ta shige tana cire hijabin ta ta shige kitchen ta ɗaurawa Al’ameen girki, itace bata samu ta zauna ba sai shida nan ma wanka tayi ta shirya cikin riga da skert na less sosai tayi kyau abinta, ɗakinta ma ta gyara shi tass ta turaresa da turaren wuta, bayan sallar magaruba ya shigo, da murmushi ɗauke saman fuskarsa oyoyo Ablah ta masa tana rungumesa.
“My Heart yau mun samu new Baby ashe masha Allah, yau mun girma,bara kiga naje naga jaririyar na dawo dan gaskiya bazan iya cin abinci ba banje naga ƴata ba.”
Yayi Maganar yana miƙawa Ablah jakar system ɗinsa, tana amsa ya juya tare da cewa bara yaje ya dawo.
Ablah tura cikinta da yayi uban girma tayi ga ƙafarta dake kumbure, ta shige bedroom ɗin Al’ameen ta ijiye system ɗin fitowa tayi taji wayarta tayi ringin Abbas ta gani a rubuce murmushi tayi tare da ɗaga kiran tana cewa.
“Ai nayi fushi Abbas.”
“Fushi kuma Ablah laifin me nayi haka”?
“Kaima kasan laifinka.”
“To kwantar da hankali ni buɗe mana ƙofa.”
Murmushi Ablah tayi tare da katse kiran tana zuwa ta buɗe suna tsaye shida AKNAM murmushi tayi tare da cewa.
“Bismillah ku ƙariso.”
Shigowa sukayi suka zauna Zainab mai tayata aiki Ta kwaɗawa kira tace ta kawo musu ruwa, ruwan taje ta kawo musu, bayan sun gaisa ne Ablah tace.
“Oh Abbas kirkin ka yayi yawa idan nace ka kusa 7 month baka kirani ba, banyi ƙarya ba, amm, Sister Aknam Amarya jiya yaya Haidar yake sanar dani cewa ansa ranar Auren ku Satin sama ko?”
“Ehh an saka, shine ai nace masa ya kamata muzo mu sanar dake, kullum idan nace masa ya kawoni sai yaƙi, sai yau Allah yayi.”
Murmushi Ablah tayi tare da cewa.
“Bashi da kirki ai Abbas.”
“Au nine bani da kirkin.?
Yayi tambayar yana nuna kansa.
Dariya Ablah tayi, tare da tashi tayi kitchen abinci ta kawo ta ijiye musu dai-dai Al’ameen yana shigowa, dariya Al’ameen yayi ganin Abbas yace.
“A’a yau kazo wanke kanka kenan a wajen sarkin ƙorafi na.”
Bakinta Ablah ta ɗan tura tare da cewa.
“Oh sarkin ƙorafi kuma na dawo saboda na jajesa ko.”
Zama Al’ameen Yayi yana tanƙwashe ƙafa tare da sanya hannu a plat ɗin da aka sanyawa Abbas abinci suka fara ci tare yace.
“Allah ya baki hkr suɓutar baki ne, kar amin hukunci, amm Abbas mutumiyar ka fa ta haihu Rufaida, ta haifi mace.”
“Wow masha Allah Rufaida ta haihu, kai alhamdulillah! Ai kuwa bara na gama cin abincin nan na ƙarisa naga ƴarmu.”
Yayi Maganar cike da nuna farin ciki sun juma sosai a gidan suna hira, har aka kira sallar isha’i sukaje sukayi sallar sannan suka shiga part ɗin Rufaida ganin baby.
Ranar sunan Rufaida Yarinyar taci sunan Ummi wato Maryam sunan da yayi goshi sosai kayan suna kuwa kamar ka ture haka ake kawowa Rufaida masu tsadar gaske Al’ameen da Ablah suma akwati guda suka kawo nasu, cikin mutuntawa akayi sunan aka watse inda suka yiwa jaririyar inkiya da Ummi.
*****
Haka kwanakin suka dinga tafiya musu cikin farin ciki da ƙaunar junansu basu da wata damuwa, ranar wata Jumma’a da yamma lis Ablah ta tashi da wani mungun ciwon baya, da kunkumi, ga ƙasan mararta tamkar ana tsaga mata shi da reza, tun tana daurewa har ciwon ya kwantar da ida, sai famar mutsuttsuku take a tsakiyar bed tana cije bakinta cike da azaba sai dai tsabar zurfin ciki irin na Ablah ta kasa kiran wani ta sanar masa, halin da take ciki, jikinta duk yayi laushi, cikin ikon Allah sai ga Rufaida ta shigo la’asariyya rungume da Ummi a hannunta, shuru taga falon babu kowa, Zainab ƴar aikin Ablah ta kwaɗawa kira itama shuru babu alamunta, hakanne yasa Rufaida shigewa bedroom ɗin Ablah, tana kwance sai nishi take ta jiƙe sharƙaf da gumin azaba idanunta kuma na zubar da hawaye, da sauri Rufaida ta kwantar da Ummi a kujerar dake tsakiyar ɗakin ta ƙarisa da sauri, inda Ablah take, riƙo ta tayi tare da cewa.
“Subahanallah! Ablah, kar dai labour kike.”
Tayi Maganar a gigice tana ɗaukar wayarta ta kira Momma, bayan ta kira Momma ne ta kira Al’ameen take sanar dashi halin da Ablah ke ciki, ai kuwa a gigice Al’ameen ya taho babu shiri shida Haidar ko kafin su iso tuni Momma da Rufaida sunyi asibiti da ita, darect ɗakin haihuwa aka shige da ita a mungun gigice Al’ameen ya shigo cikin tashin hankali, su Momma ya samu zaune suna jira.
“Momma ina take ina Ablah, wani hali take ciki.”
Kanta Momma ɗago ta kallesa tare da masa nuni da labour room, idanunsa ya runtse tare da jinginuwa jikin bango ƙirjinsa na dukan Uku Uku.
Ita kuwa Ablah tun shigarta room ɗin naƙudar ke taso mata gaf gaf ba ƙaƙƙautawa kusan awa biyu haihuwa ta gagara ga kuma naƙuda babu sassautawa, tun da sauran ƙarfinta har ta fara galabaita ƙarfinta ya fara ƙarewa nishin ma da ƙyar take iya yinsa, wasa wasa haihuwa taki zuwa har akayi sallar isha’i, Al’ameen yafi kowa damuwa ya gagara zama sai famar kaiwa da komowa yake, ƙarfe goma na dare doctor ta fito daga ROOM ɗin tana sharce gumi, Al’ameen da sauri ya nufota yana cewa.
“Likita wani hali matata take ciki ta haihu kuwa.?”
“Sorry matarka bata haihu ba gaskiya har yanzu, amma muna saka ran dole sai mun mata cs saboda ƙarfinta ya ƙare bazata iya nishin da yaro zai fito daga jikinta ba, bata da kunkumi ma’ana bazata iya haihuwa da kanta ba dole sai cs, dan haka zamuje ka saka hannu zamu shiga da ita ɗakin tiyata.”
Wani irin sanyi jikin Al’ameen yayi cs kuma.
Ya furta a cikin zuciyarsa, Rufaida ce ta dubi Momma tare da cewa.
“Momma dama akwai wadda bata da kunkumi ne.?”
“Eh Rufaida akwai matan da basa iya haihuwa da kansu dole sai an musu cs saboda kunkumi bashi da ƙarfi, fatan Allah dai Allah ya bada ikon tiyatar lafiya.”
Da ameen Rufaida ta amsa cike da jimami, Haidar ne ya dafa kafaɗar Al’ameen yace.
“Kaga tana can tana ta famar shan wahala, kar jaririn ya samu matsala, ya kamata muje ka saka hannu a mata aikin.”
Kansa Al’ameen ya ɗaga tare da shigewa gaba Haidar yabi bayansa, ya sanya hannun likitan ya ce su nemi jini leda biyu su ijiye kafin su fito daga cs ɗin.
Cikin mintuna kaɗan aka shiga da Ablah ɗakin tiyata, yayin da Al’ameen ke tsaye cike da tashin hankali, Momma ganin yadda hankalin Al’ameen ke tashe yasa Momma basa baki tana kwantar masa da hankali, sun kai kusa awa Uku a ɗakin tiyatan kafin sukaji kukan jariri daga inda suke tsaye, likitan ne ya fito yana sharce gumi Al’ameen nufosa yayi tare da cewa.
“DOCTOR ya ake ciki?”
Murmushi doctor yayi tare da dafa kafaɗar Al’ameen yace.
“Congratulation! Mun cire Baby lafiya itama Uwar muna saka ran zata farfaɗo lafiya, yanzu za’a fito muku da babyn Ka samu Yaro namiji.”
Numfashi Al’ameen ya saki cike da farin ciki ya furta.
“Alhamdulillah!.”
Dariya Momma tayi suma cike da farin ciki, nurse ta fito da jaririn a hannunta ta miƙawa Momma amsa Momma tayi tare da Bismillah aka turo Ablah a gado zuwa ɗakin hutu, buɗe jaririn sukayi suna kallonsa kyakkyawan yaro fari tas gwanin sha’awa ƙaton yaro, murmushi Al’ameen yayi tare da amsar sa, Haidar ne ya sanya hannu a aljihun sa, ya ɗauko dibino tare da sakawa a bakinsa ya tauna ya lakatawa yaron a bakinsa tare da basa Zam zam amsarsa yayi tare da masa kiran sallah a kunnensa, sannan ya miƙawa Rufaida shi, Momma su Umma ta kira ta sanar dasu haihuwar, sanda Daddy yaji sosai yaji daɗin samun aboki da yayi.
Ai washegari da safe asibitin ya cika da mutane, yayin zuwa wannan lokacin Ablah ta farfaɗo, kowa yaga jaririn sai yaji sha’awarsa, Ablah sosai take jin ƙaunar yaron a ranta, Momma itace ta zauna a asibitin tare da Ablah.
Randa suka cika kwana uku a asibitin da safe Al’ameen yazo asibitin Momma ta fita waje sai Ablah da Baby kawai dake kwance, gefen Ablah ya zauna tare da manna mata kiss a goshinta, ya saka hannu ya ɗauki Jaririn murmushi Ablah ta saki tare da cewa.
“Ina kwana yaya Al’ameen.”
“Lafiya Maman Baby, kinsan yaron nan da ni yake kama.”
Dariya Ablah tayi tace.
“Dama kyan ɗa ai ya gaji ubansa, da wani suna ka masa huɗuba.?”
“Zakiji ranar suna, sun sallamemu Momma na shigowa zatazo mu tafi yanzu.”
“To shikenan”
Tayi Maganar dai-dai Momma na shigowa, kayansu ta haɗa musu suka dawo gida.
Umma kunyar ɗan fari ya sata bata cika shigowa wajen Ablah ba.
Tunda akayi haihuwar Al’ameen ke hidima da Ablah sosai yake biƙinta.
*****
Ranar suna yaron yaci sunan Papa, wato Khabeer inda suka masa inkiya da Naseem, sosai Papa yaji daɗin karar da Al’ameen ya masa, akwati Huɗu Al’ameen ya yiwa ɗansa, Haidar shima akwati ya cika nasa banda nasu da Daddy, suna dai alhamdulillah! Yayi goshi sosai, inda akayi taro lafiya aka watse lafiya, Momma ɗauke Ablah tayi ta maida ita part ɗin su.
Kullum da safe sai Al’ameen ya shiga ya duba matar sa, da ɗansa.
Cike da kulawa Ablah ke renon yaronta, Naseem yaron yayi fari tas yayi ɓul ɓul dashi, ko wacce wayewar gari ƙara wayo yake.
Inda akayi Auren Abbas Ablah na jego bata samu ta hallaci bikin ba, sai dai ta kirasa ta masa Allah ya sanya alkairi sannan ta aika masa gudumowa,
Kafin Ablah ta cika kwana arba’in Momma da kanta ta dinga gyara Ablah, da tayi arba’in ma har Niger sanda taje wajen Dada, da ta dawo kuma ta koma part ɗinta.
*****
“Wai Ablah meya samu Naseem ne nake jiyo kukansa.?”
Al’ameen yayi tambayar yana shigowa cikin bedroom ɗin Ablah da yake jiyo kukan Naseem tare da saka hannu ya ɗagosa.”
“Tun ɗazu yake kuka haka kawai bansan meke damunsa ba, na basa nono ma yaƙi amsa.”
“To ko zamuje asibiti ne.?”
“Asibiti kuma, ina ga fa rikici ne kawai babu abinda yake damunsa.”
“Umm umm Ablah bafa naso nayi wasa da lafiyar Naseem gara dai muje asibitin.”
Murmushi Ablah tayi tare da matsowa kusa dashi tana sanya hannun ta a jikin Naseem ɗin tace.
“Babu fa abinda ke damunsa, wai ma dakata Dear naga alamar fa yanzu Naseem ya ƙwacen fadar soyayyar tabar kaina ta koma kansa to bazan yadda ba.”
Tayi Maganar cike da zolaya, jawota jikinsa Al’ameen yayi yana dariya yace.
“Wa ya faɗa miki, har abada kina cikin zuciyata bazaki taɓa fita ba, ina ma miki albishir da cewa Naseem yana cika shekara zamu wuce umara ƙasa mai tsarki, daga nan zamu wuce American muje mu kaiwa su Daddy ziyara, ina sonki fiye komai a rayuwata Ablah ina faɗa kullum.”
Dariya Ablah tayi cike da farin ciki ta ce.
“Hmmm! Kullum idan na tuna cewa kaine mijina kuma gatana inuwata sai naji nafi kowa farin ciki a cikin rayuwata, Tabbas haƙuri shine gishirin rayuwa, ba’a taba samun Nasara da ɗaukaka har sai ansha wahala kuma anyi hkr, yau na tsinci ribar haƙuri, ina sonka Mijina.”
Tayi Maganar tana rungumesa cike da farin ciki.
*****
A gurguje.
Bayan shekara Biyu A cikin wannan shekara biyun Ablah suka ziyarci ƙasa mai tsarki yayin da suka kaiwa su Daddy ziyara can American, ta ɓangaren Haidar shima yana rayuwarsa cike da jin daɗi yayin da ya buɗe Companyn sa da farko sunso sanya su Ablah su wakilci Companyn sai suka fasa domin kuwa gani suke gara kawai matan nasu su zauna a gida su yi tarbiyyar yaransu, inda Khalifa da Abdu ƙanin Ablah sune suke jan ragamar Companyn, Daddy da kansa ya biyawa Umma da Aunty Saude kujerar hajji sukaje suka sauƙe farali, rayuwa ta musu daɗi basu da wata matsala, yayin da Ummi ƴar Rufaida da Naseem yaran suna gudu har da gwarin magana ko ina gwanin sha’awa musamman Ummi da take mace domin kuwa kyakkyawa ce Yarinyar Ajin farko, inda a cikin wannan shekarar akayi Auren Madina da su Samira, Maimu ta haifi ɗanta namiji mai sunan Abi wanda suke kiransa da Aryan, rayuwa ce suke ta farin ciki.
Tafe suke sun fito daga sahad store, Ablah tana riƙe da hannun Ummi da Naseem, ta hango mabarata zaune gefe, duban Al’ameen tayi tace.
“Abban Naseem, muje na bawa mabaratan nan sadaka.”
Bai musa mata ba, yabi bayanta suka ƙarisa wajen, sadaka ta basu tare da miƙowa wata mata da kanta ke sunkuye fuskarta duk ta jeme sadaka, ɗagowa tayi zata amsa sukayi ido huɗu da Ablah da Al’ameen, cike da mamaki Ablah ta zaro idanunta tare da furta.
“Hajiya Mansura kece cikin mabarata.?”
A mungun tsorace ta zabura da ƙyar cike da tsoron kar Al’ameen yasa a kamata ta hau titi da sauri ba tare da ta duba ba, ji kake ƙiiii! Ƙiiii! Mota ta kwasheta, runtse idanunta Ablah tayi jin ƙararta, domin kuwa doguwar mota ce tabi ta kan ƙafafuwan ta, ta niƙe su, Ummi ce ta danna ƙara na tsorata, da sauri Al’ameen ya saka hannu ya ɗaga ta.
Mutane ne suka taru akan Hajiya Mansura dake ihun azaba, Ablah zata ƙarisa Wajen Al’ameen ya sanya hannu ya jawo Ablah tare da girgiza mata kai alamun karta je cikin tausayawa Ablah tace.
“Meyasa zamu tafi mu barta, bayan….”
Hannu ya ɗaga mata tare da cewa.
“Ta girbi abinda ta shuka duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa zai doka, Ablah ki sani duk wanda ya sayi rariya yasan zata zubda ruwa, idan ba so kike raina ya ɓaci ba ki shige mu tafi.”
Kanta Ablah ta girgiza tare da shigewa suka bar Hajiya Mansura yashe a tsakiyar titi tana danna ihu cike da munguwar azaba ga kuma asarar ƙafa biyu.
Alhamdulillah! Tamat bilhamdulillah! Duka duka anan na kawo ƙarshen wannan labarin ina fatan ladan dake ciki Allah ya bani zunubin dake ciki kuma Allah ya yafe min ina roƙo gareku masoya da muka kasance daku a cikin wannan labarin idan akwai abinda na muku na rashin kyautawa kuyi haƙuri ku yafe min, ina ƙaunar ku tamkar yadda kuke ƙaunata.
Sannan ina muku albishir da NEW novel ɗina da zaizo muku mai taken DOCTOR HASSAN ina muku fatan alheri.