Dariya Nafeesa tasa sosai tana kallon Mama kafin tace.
"Haba dai Mama yanzu dan kawai yamin wannan ƙaramar kyautar shikenan kuma sai kice ɗan satar mutane, kinga Mama wannan fa ƙaramar kyautace a wajen Haidar kinsan shi ɗin ɗan waye kuwa a wannan ƙasar, ina dai kinsan ambassador Ahmad Giwa?"
Kanta Mama ta ɗaga tare da cewa.
"Ƙwarai kuwa na sanshi bashi bane wanda yake kula da dukkan wasu lamuran Nigeria dake gudana a ƙasar American."
"Shi dai Mama to Haidar ɗansa ne na cikinsa, kinga kuwa wannan ai ƙaramar kyauta ce."
Dariya Mama tasa tana cewa.
"Ke kuwa Nafeesa. . .
Assalamu alaikum