Skip to content
Part 7 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Dariya Nafeesa tasa sosai tana kallon Mama kafin tace.

“Haba dai Mama yanzu dan kawai yamin wannan ƙaramar kyautar shikenan kuma sai kice ɗan satar mutane, kinga Mama wannan fa ƙaramar kyautace a wajen Haidar kinsan shi ɗin ɗan waye kuwa a wannan ƙasar, ina dai kinsan ambassador Ahmad Giwa?”

Kanta Mama ta ɗaga tare da cewa.

“Ƙwarai kuwa na sanshi bashi bane wanda yake kula da dukkan wasu lamuran Nigeria dake gudana a ƙasar American.”

“Shi dai Mama to Haidar ɗansa ne na cikinsa, kinga kuwa wannan ai ƙaramar kyauta ce.”

Dariya Mama tasa tana cewa.

“Ke kuwa Nafeesa a ina kika samu damar haɗuwa da ɗan manyan mutane haka, ina fatan dai Auren sa zakiyi.”

Nafeesa fuskarta ta haɗa jin Mama ta ambaci Aure.

“Aure kuma Mama, ni ba auren sa zanba, kawai kuɗin zan tatsa na rabu dashi.”
Mama gyara zamanta tayi tare da cewa.

“Da kuwa kin zamo cikakkiyar wawiya marar rabo, yanzu har ki samu wannan damar kiyi wasa dashi Nafeesa, kina tunanin zaki samu wanda ya fisa ne, Nafeesa dan Allah ki rufa mana asiri ki Aure wannan mutumin kije ki huta nima na huta, zamu shiga cikin daula muyi wasa da kuɗi yadda muke so, kiyi tunani Nafeesa.”

Tsuka Nafeesa tasa tare da cewa.

“Ni fa babu wani tunanin da zanyi Mama, bazan auresa ba na gama magana tun kafin shi ai dama asirinmu a rufe yake, kuma gaba ma zan samu wanda ya fisa.”

Tana gama Maganar bata tsaya ta saurari mai Mama zatace ba ta kwashi kayanta ta bar room ɗin, Mama da kallo ta bita tare da taɓe bakinta tana adana kuɗin ta.

Washegari da safe misalin sha ɗaya Amnat ta shigo cikin gidan su Nafeesa, Nazifa ta tarar a falon tana ganin Amnat ta kauda kanta gefe domin kuwa duk abinda Nafeesa keyi kusan rabi Amnat ce ta koya mata, da ƙyar ta amsawa Amnat sallamar ta, Amnat bata damu ba kasancewar ba yau Nazifa ta saba kawar mata da kai ba, bedroom ɗin Nafeesa ta nufa kai tsaye tana zaune ta saka waya a gaba sai famar chat take ɗagowa tayi ta kalli Amnat tace.

“Har kin iso kenan?”

“Umm na isa kiran me kike min haka kimbi kin uzura min.”

Murmushi Nafeesa ta saki tare da ijiye wayar tana jawo ledar da Haidar ya bata ta miƙa mata.

“Ki buɗe kiga abinda yake ciki.”

Babu musu ta amsa tare da buɗewa, a matuƙar firgice ta juyo tana kallon Nafeesa tace.

“Karki cemin Haidar shine ya miki wannan kyautar.”

“Ƙawata waye kuwa zaimin wannan kyautar alfarmar idan bashi ba, shegen fa ya shigo hanu Amnat.”

Gyara zamanta Amnat tayi tare da cewa.

“Ƙawata yanzu ace akwai samarin da suke irin wannan kyautar tun kafin Aure idan suka aureka kuma wani irin daɗi zaka samu, ƙawata karfa kiyi wasa da wannan damar domin kuwa muddun kika sake ta kufce miki mawuyacin abune ki kuma samun ta, gara kawai ki auresa yafi miki domin kuwa zaki samu jin daɗin rayuwa sama da wanda kike zato ma.”

“Hmmm!! Waya faɗa miki cewa irin waɗannan idan anshiga gidan su komai yankewa yake kyautar iya wajene kawai da zarar anyi ta ƙare, kinga ki daina bani wannan shawarar domin kuwa bazan ɗauka ba, na kiraki ne kawai na nuna miki.”

Amnat cewa tayi.

“Shikenan na daina, amma dai yanzu kam tunda kin samu mai baki ko babu jikinki ai dai zaki haƙura da bariki ko?”

Ɗan dariya Nafeesa tayi tare da cewa.

“Sanin kanki ne bazan taɓa iya daina bariki ba, suma kuɗin barikin ina buƙatar su, ai dai kogi baiƙi daɗi ba ko?”

Amnat shuru tayi ganin yau akwai ƴan iska akan Nafeesa, Amnat bata wani juma ba ta tafi.

*****

Tunda ya shiga Office ɗinsa aiki yake domin kuwa ya kwana biyu bai zo Office ɗin ba sanadin rasuwar da aka musu, yana nan zaune Haidar ya shigo, Al’ameen ɗago kai yayi ya kallesa tare da maida kansa kan aikin nasa ba tare da ya yiwa Haidar magana ba Murmushi Haidar yayi ganin har yanzu Al’ameen wai fushi yake dashi Magana ya masa yace.

“Wai har yanzu fushi kake dani ne, Maganar Kayan da aka fita dashi Egypt ne, sun turo kuɗin 3.2m wannan karon an samu matsala fa.”

Al’ameen ɗago Kai yayi ya kalli Haidar tare da cewa.

“3.2m ban gane mai kake nufi ba, taya zamu aika musu kayan 5.2 su aiko da 3.2, not possible, taya hakan ta faru?”

“Ni kaina tunani nake akan hakan, Joseph yace min su iya kayan da suka isa garesu kenan amma nafi tsamanin ko Ibrahim ne ya ɗebi Kayan idan ba haka ba taya hakan zata faru.”

Numfashi Al’ameen ya sauƙe tare da cewa.

“Haidar kaje kayi bincike da kyau duk wanda aka samu da hanu cikin sata a wannan Companyn na baka izinin a kamasa sannan a sallamesa a aiki, kuma kaya dole su dawo bazamu ɗauki asara ba, sannan akwai takaddun dana aika maka ɗazu ka saka hanu a miƙawa clener’s committee suna da sabon ma’aikaci da zai fara aiki dasu next week.”

Cike da mamaki Haidar yace.

“Ban gane sabon ma’aikaci ba, dama ana ɗaukar sabon ma’aikaci ne batare da mun zauna munyi Magana da juna ba.”

Murmushi Al’ameen ya saki tare ɗago kansa yace.

“Abinda nayi shine dai-dai domin ko mun zauna banbancin ra’ayi zamu samu, shiyasa na yanke hukunci ka saka hanu kawai.”

“bazan saka hanu ba, haka kuma babu wani ma’aikaci da za’a ɗauka ba tare da an cike ƙa’ida ba.”

Yayi Maganar yana kawar da kansa gefe, murmushi Al’ameen yayi tare da miƙewa tsaye ya zago kusa da Haidar hanu ya saka a kafaɗarsa tare da ɗan dukar ƙeyarsa yana murmushi yace.

“Wai yaushe muka dawo abokan faɗa ne, kaga Malam Haidar Ahmad Giwa, juyo ka kalleni kace bazaka saka ba idan ka isa.”

Yayi Maganar cike da zolaya, murmushi Haidar yayi tare da tashi ya rungume Al’ameen yace.

“Har abada bazamu taɓa samun saɓani ba Abokina, Amma dai na isan shiyasa na faɗa, wai ma tukunna waye zaka ɗauka aiki ne haka.”

Komawa Al’ameen yayi ya zauna tare da cewa.

“Idi drever, shine zamu ɗauka Saboda ya kamata yabar tuƙi girma ya Kamasa.”

Idanu Haidar ya zubawa Al’ameen cike da mamaki yace.

“Ban gane abinda kake nufi ba, yaushe ka saka aka saki Idi drever.?”

“Shiyasa nace maka bana buƙatar tattaunawa dakai akan wannan lamarin saboda bazaka fahimce ni ba, bani na saka aka sakesa ba Daddy ne.”

Murmushi Haidar yayi tare da cewa.

“Cewa zakayi kaine kasa Daddy ya sakesa saboda duk abinda ka cewa Daddy DASHI yake amfani dama na sani tunda ka furta sai ka aikata, fine ya maka kyau sai ka cigaba dayin abinda kaga dama zanje na saka maka hanu saboda koda bansa ba, ni ɗin ma zaka haɗani da Daddyn yasani na saka dole.”

Murmushi Al’ameen yayi yace.

“Hmmm!! Shiyasa nace bazaka fahimce ni ba, kayi hkr idan ranka ya ɓaci, ka tashi kaje ka bincika mana waye yake da hanu wajen salwantar kayan mu.”

Yayi Maganar yana jawo system ɗinsa, Haidar baice komai ba ya fita, bayan sun tashi daga Office ne Al’ameen kasancewar zaije, unguwar Durmi, bai tsaya neman Haidar ba, ya shiga cikin motar sa yayi tafiyar sa, cike da nutsuwa yake tuƙinsa ya kunna ƙira’ar Sudais Suratul ƙasas yana sauraro cike da nutsuwa.

Tafe take hankalinta duk a tashe burinta kawai ta isa gida ta samu ta kai musu garin rogon da ta sayo tasan yanzu haka Abdu yana can yana yiwa Umma kukan yunwa, gashi tun safe babu abinda ya saka a cikin sa, a bakin titi ta tsaya tare da duba hanun damanta ganin babu wata mota da take zuwa yasa tasa kai kawai ba tare data duba hanun hagunta ba, ai kuwa babu zato ba tsammani taji an ɗebeta Al’ameen dake cikin motar ne yayi saurin ja da baya jin ya bige Mutum gudun karda ya takata, idanunsa ya runtse cike da ɓacin rai, gefe yayi da motar yayi parking tare da fitowa da sauri, ko kafin ya fito ma harma mutane sunyo kanta, kutsawa yayi cikin mutanen, tana kwance zube a ƙasa da alamu suma tayi,tafin ƙafarta da goshinta sai fitar da jini yake, wani mutumi ne ya shawo kwalar rigar Al’ameen cike da masifa yace.

“Baka gani ne Malam zaka bige ƴar mutane ka cuci iyayenta, kuna tafiya a kan hanya kamar titin iyayenku, to wallahi wani abu ya samu wannan baiwar Allah bazamu barka ba.”

Tunda ya cakwamesa Al’ameen yake binsa da idanu zuciyarsa kuma na tafasa Lallai wannan baisan waye shiba shiyasa idan banda rainin wayo ma Yarinyar da ta masa shigen tsaye bata duba hanya ba ta shigo, amma waishi ake faɗawa Maganar banza, tsuka yaja tare da bige hanun mutumin daga jikinsa, ya nuna sa da yatsa.

“Kayi kuskuren cin kwalata, wannan ya zamo shine na ƙarshe, idan baka san waye Mutum ba karka kuskure ka nemi ƙalubalantarsa” duban wani tsoho dake tsaye akan ta yayi yace.

“Baba a ɗauketa muje da wani a kaita asibiti tana zubar da jini da yawa.”

Tashi tsohon yayi yace,

“Yaro ko munje bazasu karɓe muba dole sai da ɗan sanda.”

Murmushi Al’ameen yayi yace.

“Karka damu Baba muje zanyi waya police ɗin zasu samemu asibitin.”

Da to tsohon ya amsa suka ɗauketa dashi da wani saurayi suka sata cikin motar Al’ameen, hanyar SJ hospital suka nufa da ita, ko kafin su isa Al’ameen ya kira dpo yace a aika masa police ɗaya asibitin sj, babu ɓata lokaci kuwa suka isa cikin asibitin, emargency aka shiga da ita, Dressing ɗin ciwon aka mata, tare da allurar bacci sannan aka dawo da ita word mai ɗaki ɗaɗɗaya, bayan an gama komai dattijon yace zaije ya sanar da iyayenta abinda ke faruwa, kansa Al’ameen ya ɗaga alamun to, dubu Biyar ya bawa tsohon yace ya shiga adaidaita sahu, shi kuma ya tsaya a wajen Yarinyar, sai tsuka yake shi da yake da uzuri gashi ta cucesa ta hanasa uzurin sa, wayarsa ce tayi ƙara ya ɗaga *NAJIB* Numfashi ya saki tare da ɗaga kiran yace.

“Ka jini shuru ko, wallahi accident na gamu dashi akan hanya wata makahuwar yarinya wacce bata gani hanya na bige, yanzu haka ina asibiti, amma dan Allah NAJIB ka taimaka kaje wajen mutumin nan ka turo min account number zan maka transfer sai ka basa.”

Sun ɗan juma suna waya da NAJIB ɗin kafin ya katse kiran, yana zubawa Yarinyar idanu, cike da haushinta, fara ce ba can ba, tana ƙaramin baki da hanci dai-dai gwargwado, ba laifi tana da kyau, duk kana ganinta zaka fuskanci alamar tana cikin wahala, idanunsa ya kawar gefe ya cigaba da danna wayarsa, har akayi kiran sallar magaruba iyayenta basu zo ba, hakanne ya ƙara hasala Al’ameen alwala yayi ya shige massalaci.

A hankali take buɗe idanunta harta buɗe su tas, tuno da abinda ya faru ya sata miƙewa a firgice, ɗakin tabi da kallo, sai yanzu ta lura a asibiti take, ƙafarta ta kalla tana duban yanda aka naƙe mata shi ga kanta daya mata nauyi hanu tasa nan ma taji a naɗe, numfashi ta sauƙe tare da furta.

“Umma hankalinta zai tashi, na barsu da yunwa gashi garin ma ya zube.”

Raurau tayi da idanunta tamkar zatayi kuka tuno da duk laifin ta ne data shiga titi ba tare da ta duba ba, tana nan zaune cikin tashin hankali ya shigo kallonsa tayi, tare da sunkuyar da kanta ƙasa, zama yayi yana harararta ba tare daya kulata ba ya zauna cikin sanyin muryar ta mai kama da sarewa tace.

“Kayi hkr dan Allah duk laifi nane dana shiga titi ba tare dana duba ba, hankalina ne yake kaɗe ana…”

Hanu ya ɗaga mata cikin tsawa yace.

“Uban waye ya tambayeki, ba dai kin cuceni ba, to ai sai kimin shuru bana buƙatar hayaniyarki, kuma barin faɗa miki ni dai bazan kwana a wannan asibitin ba, tafiyata zanyi tunda kin farfaɗo”

Yayi Maganar yana miƙewa tsaye tare da saka kansa ya fita cike da tsoron sa sunkuyar da kanta harya fita, yana fita ta saka kuka mai sauti.

Office ɗin doctor ɗin ya nufa tare da cewa karsu yadda su barta ta tafi zai dawo da safe.

Koda ya koma gida ya samu Haidar a daining table ɗinsu yana cin abinci bedroom ɗinsa ya haura, kayan jikinsa ya cire ya saura daga shi sai gajeren wando tollet ya shiga, ya kunna shower tare da tsayiwa ruwan yana ratsa masa jiki, runtse idanunsa yayi yana tuno kwalarsa da wannan mutumin yaci, sosai abun yaci masa rai, kuma ba kowa ta ja masa ba sai wannan mai kama da aljanun, koma karya koma asibitin ne yabar mayya taci kanta, tsuka yaja kafin yayi wankan ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, A bakin bed ɗinsa ya samu Haidar zaune dubansa yayi tare da jawo towel ɗin dake jikin bed ɗin nasa ya ɗaura a kansa yana tsame ruwan dake jikinsa, Haidar ne yace.

“Ina kaje ne bayan mun tashi a Company ban ganka ba.”

“Kasan munyi Magana da Alhaji Sajo zan basa kuɗin gidan waɗannan mutanen da suka roƙi basu da wajen zama a taimaka musu, so ya sanar dani cewa an samu gida a unguwar Durmi, can na nufa na duba gidan bamma isa ba, na haɗu da accident, na bige wata Aljanar yarinya, makahuwa wacce bata ganin hanya.”

Murmushi Haidar yayi tare da cewa.

“Aljana kuma, Aljanar zaka bige kuma ka dawo lafiya common waka bige.?”

“To me kake so na faɗa maka Yarinyar kama take da aljanna sam bata da kyau, gata da suffar munafukai tana magana kai a sunkuye cikin sanyin murya kamar marar gaskiya, kai nifa kwatakwata ma ban yarda mutum bace, tana can Sj hospital, bazan ma koma ba tasan yadda Zatayi ta biya su kuɗin sallamar su.”

Dariya ce ta ƙwacewa Haidar har yana kwanciya, kallon sa Al’ameen yayi tare da cewa.
“Meye kuma na min dariya, mahaukaci ka maidani ne.”

“To ai Maganar taka ce ta bani dariya,kai yanzu mai kama da aljanun ne zakace bashi da kyau to ai idan kyawun mutum yayi yawa ne ake haɗa shi da aljani, kai dai Malam koma meye tunda ka bige ƴar mutane dole kuma ka koma, ni har rakiya ma sai na maka.”

Tsuka Al’ameen yaja yana fesawa jikinsa turare tare da miƙewa ya jawo jallabiyarsa ya saka, wayarsa ƙarama ya ɗauka tare da nufar door yana cewa.

“Da alamu cikinka ya cika ne shiyasa kake wannan shirmen.”

Yayi Maganar yana fita yabar Haidar a room ɗin, Al’ameen ya sako ƙafarsa kenan waje yaji santsi ya kwashesa, cikin hanzari ya saka hanu ya riƙo ƙarfen dake wajen kafaɗarsa ta daki ƙarfen da ƙarfi runtse idanunsa yayi cike da azaba, ɗan ƙara ya saki, jin wannan ƙarar yasa Haidar fitowa da sauri zai sako ƙafarsa da ƙarfi Al’ameen yace.

“Dakata a wajen karka fito!”

Cak Haidar ya tsaya tare da cewa.

“Meyasa karna fito me kuma ya sameka.”?

Al’ameen zamewa yayi ya zauna tare da cije bakinsa yana jin kafaɗarsa tamkar ta tsage, a hankali ya kai yatsarsa inda santsin ya kwashesa, yauƙi ne sosai, zaro idanunsa yayi tare da ƙwalawa Ummi kira Ummi da suke zaune da Inna Jumma da Aunty Amarya ne ta amsa tana cewa.

“Na’am lafiya kuwa Al’ameen kake min wannan kiran.”

Yana cije bakinsa yace.

“Ummi ki hauro.”

Miƙewa Ummi tayi tare da haurawa, yana zaune idanunsa sun sauya kala zuwa ja tsabar azabar da kafaɗarsa ke masa, can kuma ta hango Haidar a tsaye cikin hanzari Ummi take ƙoƙarin nufosa yace.

“Ki kula Ummi yauƙi ne ya kwasheni a wajen nan, meya kawo yauƙi nan Ummi.?”
Cike da mamaki Ummi tace.

“Yauƙi kuma a gidan nan Al’ameen?”

Kansa ya ɗaga mata alamun eh tare da mata nuni da wajen, Ummi sunkuyawa tayi tare da saka hanunta ta lakata, Tabbas kuwa yauƙi ne,kuma yauƙin sosai to kuma waya zuba yauƙi anan, ga yauƙi ga tayals idan ya ɗebi mutum kuma ai sai karaya koko kai ya taɓu, kanta ta ɗago ta dubi ɗan nata tare da cewa.

“Ina fatan kana lafiya?”

Bakinsa ya cije tare da cewa.

“Kafaɗata ta bugu, Ummi waye ne yamin wannan aikin domin aikin ganganci ne, tunda cikin gidan nan dai ba’a amfani da yauƙi ba’a miyar yauƙi, da gangan aka saka saboda a lahanta ni?”

Shuru Ummi tayi cike da mamakin waye yayi wannan aikin, numfashi ta sauƙe tare da cewa.

“Al’ameen ina zansan waya saka amma dai Tabbas duk wanda ya saka da gangan yayi to amma a gidan nan waye zaiyi wannan, mtss bance akwai ba, kaga kabar zancen kawai, duk wanda yayi shida Allah, karma kayi Magana su Inna Jumma suji bara nayi mopping ɗin wajen cire takalmin naka ka bani tunda ka taka yauƙin dashi.”
Cike da tunanin wanda ya zuba masa Al’ameen ya cire takalmin Ummi ta ɗauka tayi ROOM ɗinta dashi, Haidar shuru yayi yana nazarin wannan abun, Tabbas akwai wata a ƙasa a cikin gidan nan idan ba haka ba to ya za’ayi a zuba karkashi a ƙofar room ɗin Al’ameen, lallai ana sane akayi.

Yayi Maganar a cikin ransa sai dai babu wanda zai iya zargi a cikin gidan domin kuwa baya tunanin akwai wanda zai iya cutar da wani…

Ummu Nasmah

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita? 6Aminaina Ko Ita? 8 >>

1 thought on “Aminaina Ko Ita? 7”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×