Numfashi ya saki Haidar tare da harɗe hanunsa, Ummi fitowa tayi tare da mopper ahanunta ta goge wajen tas ta tsame ba tare da kowa ya lura ba, tollet ɗin ta ta mayar da mopper ɗin tare da wankesa ta tsame, ta kuma fitowa kusa da Al’ameen ta sunkuya, tana ɗan danna kafaɗartasa, ɗan ƙara ya saki na azaba, Haidar shima fitowa yayi tare da cewa.
“Kaji ciwo ne sosai a wajen.”?
Kansa Al’ameen ya ɗaga alamun ehh, Ummi miƙewa tayi tace.
“Kaga koma ciki ka cire wannan jallabiyar ka saka best bari nazo na farsa maka wajen da Ruwan ɗumi zai sake insha Allah.”
Tayi Maganar tana shigewa ROOM ɗinta, Al’ameen Haidar ya dafa ya tashi ROOM ɗin suka koma, bayan ya cire jallabiyar ne, Haidar ya fita da sauri abincinsa ya ɗauko masa ya dawo cikin ROOM ɗin, yana shigowa Ummi itama tana dawowa hanunta riƙe da plast da man zafi, da towel ƙarami, sai wani ƙaramar roba, ruwan zafin ta tsiyaya a cikin robar tare da zama gefen Al’ameen towel ɗin ta tsoma a cikin ruwan zafin, tare da tsamewa ta ɗan matse ta danna masa a kafaɗar tasa runtse idanunsa yayi cike da azaba haka Ummi ta dinga farsa masa wajen, sannan ta shafa masa man zafin, dubansa tayi tace.
“Sannu insha Allah zuwa anjuma duk zakaji ya saki, kaga karka kuskura ka sanar da kowa cikin gidan nan abinda ya faru saboda idan Inna Jumma taji bazata bar Maganar ba, ni kuma a gidan nasan babu wanda zaiyi wannan aikin saboda mugunta, may be a cikin kuskure ne ya zube.”
Haidar ne cike da mamakin Ummi yace.
“Kuskure Kuma Ummi? Wannan ba kuskure bane duk wanda yayi yana sane yay…………..”
Ummi tare numfashin Haidar tayi tare da cewa.
“Ya isa koma meyene nace abar maganar banason zargi ya fara shigowa cikin gidan nan.”
Tana Maganar ta tashi ta fice, Haidar duban Al’ameen yayi tare da cewa.
“Abin mamaki ta ya mutum zai nemi nakasa ka amma Ummi tace ayi shuru abar maganar.”
Ɗan murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.
“Tunda tace abar maganar, ya kamata mubarta Haidar, ni kaina bana zargin cewa akwai wanda zai cutar dani a wannan gidan, zai iya yiwuwa Maganar Ummin ne, maybe cikin kuskure ne ya zube dan Allah kabar samin waswasi azuciyata.”
Numfashi Haidar ya saki zuciyarsa cike fal da rashin yadda, sai dai kamar yadda Ummi tace ayi shuru da Maganar dole hakan za’ayi saboda babu abun zargi a cikin gidan.
Al’ameen abincin ya ɗiba yaci sama sama duk jikinsa baya masa daɗi, Ranar tare suka kwana da Haidar a room ɗinsa, koda gari ya waye Aunty Amarya bayan ta gama breakfast ne, ta hauro room ɗin Al’ameen da kanta a bakin ƙofar ta tsaya tana duba inda ta zuba karkashin cike da haushin rashin sa’ar da tayi yatsarta ta cije, tare da shigewa, yana kwance bacci sai Haidar dake zaune jikin dressing mirror yayi wanka yana shafa mai.
“Good morning Aunty Amarya.”
Yayi Maganar yana murmushi, itama Aunty Amarya murmushin tayi tace.
“Kar dai anan ka kwana.?”
“Ehh wallahi Aunty anan na kwana.”
“Lafiya kuwa ka kwana anan.?”
Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
“Lafiya ƙalau Aunty kawai na kwana ne kawai.”
Kanta ta kaɗa tana duban Al’ameen dake bacci idanunta ne ya sauƙa akan kafaɗarsa da tayi jajur har ya ɗan tashi murmushi ta saki domin kuwa ko basu faɗa ba tasan harin da ta kai masa ne.
“Ka tashe sa gacan breakfast yayi ready, domin idan ka biyewa baccin Al’ameen zaku makara baku fita aiki ba, ɗazu Rufaida ta shigo nemanka nace mata baka nan saboda bansan ka kwana anan ba.”
Okay yanzu zan shiga part ɗin namu ai kafin Al’ameen ya shirya.”
Kanta ta kaɗa tare da juyawa ta fice, Inna Jumma dake tsaye tsakiyar falon tana ta famar masifa, ita da Afnan tana cewa.
“Ayi yarinya da shegiyar kafirar zuciya, ke kullum cikin gidan nan babu da wanda ake kace nace sai ke, ki duba fa kiga irin shigar da kikayi shigar kafirai wai kuma a haka zaki tafi makaranta, to wallahi baki isa ba dan ubanki, bara Aminu ya fito ina nan ina tsaye.”
Tura bakinta Afnan tayi tana hararar Inna Jumma tare da cewa.
“Ni fa babu ruwanki dani, kunbi kun sanya min ido acikin gidan nan kamar ni kaɗai ce ƴarda aka haifa, to wallahi ko kasheni zaiyi idan ya fito bazan sanja kayana ba, kafin ma ya fito zan tafi breakfast ɗin ma na fasa, kinan kin tsufa amma baki daina sanya idanunki akan na mutane ba.”
Tayi Maganar cike da rashin kunya tana ɗaukar jakarta ta nufi hanyar fita da sauri, Inna Jumma kafaɗarta ta riƙe tana kallon ikon Allah kafin tace.
“Iyyye! Ehh lallai kin tabbata fitsararriya, to ko kin gayawa uwarki Amarya da kuma ubanki Amadu su kika faɗawa bani ba, kuma indai nice zaki dawo ki sameni wallahi sai na haɗa miki sharrin da bazaki iya suncesa ba a wajen Aminu ai dai kin san halinsa.”
Tayi Maganar cikin masifa, Maimu dake zaune a daining ne tasa dariya tana binsu da kallo ko ita tana jin takaicin shigar rashin ɗa’a da Afnan keyi, Afnan kuwa ko ta juyo ta cewa Inna Jumma.
“Idan kin faɗa masa ya kasheni.”
Tayi Maganar tana ficewa, Inna Jumma cike da mita ta nufi daining ɗin zama tayi tana ta famar masifa, Maimu ce tace.
“Inna Jumma, dan Allah kibar Maganar nan haka, kici abincin ki, ita kam badai ta tafi ba.”
Tayi Maganar dai-dai Haidar na sauƙowa Inna Jumma ya nufo tare da rungume ta, ta baya yana cewa.
“Wai waya taɓa min amarya ta ne tun daga sama nake jiyo hayaniyarki.”
“Waye kuwa zai taɓani a gidan nan idan ba wannan fitsararriyar ba Afnatu, shegiya marar ɗa’a ni nama taɓa ganin yarinya marar kunya irinta.”
Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
“Maimu wai meye Afnan ta yiwa Inna Jumma ne kam.”
Maimu cewa tayi.
“Yaya Haidar kaima fa kasan akan abinda ake samun matsala da Afnan, kaya tasa sun fitar mata da halittar jikinta, shine Inna Jumma tace ta koma tasa na mutunci, taƙi, shine ta mata rashin kunya.”
Carap Inna Jumma tace.
“Tamin rashin kunya ko ta zageni, Yarinyar da tace ko uwata ce ta dawo duniya bata isa ta sata ta sauya kayan jikinta ba bare kuma ni.”
Daga sama sukaji muryar Al’ameen yana cewa.
“Ita Afnan ɗin ce ta faɗa miki haka.”?
Juyowa Inna Jumma tayi tare da sakin kuka tace.
“Haka ta faɗa min Aminu har tana nuna min yatsa ni dai yau a cikin gidan nan anci mutunci na, ban taɓa tsammanin akwai ranar da jinina zai zageni ba.”
Tayi Maganar tana mutstsike idanuwa Maimu idanu ta zaro tana yiwa Inna Jumma kallon tsoro, wai dama wannan tsohuwar haka ta iya sharri, shi kuwa Al’ameen hasala yayi cike da ɓacin rai ya dumfaro daining ɗin ya zauna tare da cewa.
“School ta tafi da waɗannan matsiyatan kayan ko.?”
Kanta Maimu ta ɗaga alamun eh.
“Yayi kyau.”
ya furta yana jawo plast ba tare daya kuma cewa komai ba, Haidar shima zama yayi suka fara breakfast, suna tsaka da breakfast ɗin Rufaida ta shigo hanunta riƙe da bag ɗin ta zasu shige school da Maimu, gefen Maimu ta tsaya tare da cewa Al’ameen.
“Barka da safiya ya Al’ameen.”
Ta gaishe sa tana tsaye ba tare daya amsa gaisuwar tata ba yace.
“Magani zaki bamu ne kika tsaya a kanmu kamar sa’o’inki nemi waje ki zauna ko kuma kibar kanmu.”
Murmushi Haidar yasa tare da ture cup ɗin tea ɗin yana miƙewa yaja hanun Rufaida yace.
“Kai dai ka cika takura a kanka ta tsaya ne, kinga zo muje ki bani labari.”
Bayansa Rufaida tabi Al’ameen ya bisu da harara, a kujerun falon suka zauna, Haidar a hankali ya raɗawa Rufaida a kunnenta.
“Ina labarin saurayin naki, kin sanar dashi kuwa?”
Rufaida haɗa ranta tayi tamau tamkar zatayi kuka bata amsa mishi tambayar tasa ba, Haidar murmushi ya kuma yace.
“Wai fushi kike ne akan abinda Haidar ya miki, to meye abun fushin, yayanki ne fa, har dukanki Yana da damar yayi bama faɗa ba.”
Ɗago idanunta tayi ta zubawa Haidar cike da Soyayya ji take tamkar ta rungumesa, cewa tayi.
“To me na masa da zai hauni da faɗa, kana gani fa ina zuwa wajen nan shina fara gaidawa ga Inna Jumma itace babba amma ban gaisheta ba sai shi, kuma shikenan sai ya hauni da faɗa.”
Hanunta Haidar ya kama wani irin zubawa tsikar jikin ta yayi a duk sanda ya kama hanunta sai taji jikinta ya zuba, a hankali ya ce.
“Kinga shifa Al’ameen haka yake babu mai iya sauya masa ɗabiar sa, hkr shine kawai zakuyi dole, ki amsa min tambayata kin sanar dashi jiyan.”
Kallon sa tayi tare da sunkuyar da kanta ta fara magana a hankali.
“A’a ban sanar dashi ba, saboda ina tsoro karna…”
Bata kai ƙarshe a maganar tata ba, wayarsa yayi ringin.
“Ɗan dakata ina zuwa.”
Ya faɗa mata yana ɗaga wayar cikin farin ciki yace.
“Farin cikin Haidar har kin tashi da wuri haka?”
Dam ƙirjin Rufaida ya buga da ƙarfi ita wannan a rayuwarta bata tashi kiransa sai ta dai-dai ci muna tare dashi, anya kuwa zan samu yaya Haidar a matsayin miji da alamu ta gama shigewa cikin zuciyarsa, duk cikin zuciyarta take wannan maganar cikin damuwa, Nafeesa kuwa daga can tace.
“Na juma da tashi ai Duniyata, yau kewar muryar ka nake sosai, kasan bana samun nutsuwa muddun banji daddaɗan muryar *DUNIYATA* ba, da fatan kana cikin farin ciki.”
Ɗan murmushi Haidar yayi yana lumshe idanunsa cike da tsantsar ƙaunar ta yace.
“A ko yaushe idan na tuna da cewa ina da ke, koda ina cikin damuwa sai naji ta yaye farin ciki sai ya zamo shine abokina a wannan ranar dalilin kenan ma dayasa na raɗa miki suna da *FARIN CIKI NA* muddun kika kasance a rayuwata bazan taɓa baƙin ciki ba, farin ciki shine zai zamo min dawamamme ina matuƙar ƙaunarki Nafeesa.”
Murmushi Nafeesa ta saki tana kannewa Amnat ido tace masa.
“Mai zai hana kuwa bazan kasance a rayuwarka ba, a duniya bani da wani farin ciki daya wuce kai, nakan godewa Ubangijin daya haɗamu domin kuwa ya aiko min da hasken rayuwata, idan harna tuna da cewa wata rana zan zamo mata gareka, sai naji Duniyar tamin daɗi, dole na ambaceka da *DUNIYATA* Domin kuwa kaine haske na kuma rufin asirina a cikinta, idan babu damuwa so nake kazo da daddare akwai.
Maganar da nake son muyi, sannan jiya naga katin waya na gode Allah ya ƙara arziki.”
Murmushi Haidar yayi maganganun ta na ƙara masa daɗi a kunnensa yace.
“Tabbas samun masoyiya ta gari ni’ima ce a rayuwa, ki tsumayi zuwana insha Allah zanzo, take care.”
Yayi Maganar yana katse kiran bakinsa ɗauke da murmushi ya dubi Rufaida da kanta ke ƙasa zuciyarta na ƙuna idanunta na zubda hawaye yace.
“Ina jinki Rufaida.”
Ɗago idanunta da suka kaɗa lokaci guda tayi hawaye na zuba daga idanunta Haidar idanunsa ya zaro ganin kuka take, kusa da ita ya matso tare da saka hanu ya ɗago fuskarta, hawayen yasa hanu ya share mata cike da tausayin ta yace.
“Rufaida! Soyayya kike yiwa kuka, shin wani mummunan amsa kika samu a garesa bayan kin sanar dashi.”
Kanta ta girgiza cikin rawar murya mai alamun kuka tace.
“Ban sanar dashi ba ya Haidar saboda na makara na riga da na faɗi a soyayyata, nayi rashin nasara yana da wacce yake so, a duk sanda nayi ƙoƙarin tunkararsa da maganata sai naga tazo wajen ta ɗauke hankalinsa daga gareni babu buƙatar na sanar dashi domin kuwa na faɗi warwas.”
Tayi Maganar hawaye na ƙara zubo mata, numfashi Ya Haidar ya saki tare da cewa.
“Faɗuwa ba ita bace take nuna rashin Nasara ka faɗi ka gagara tashi wannan shi ake kira da rashin Nasara amma muddun ka faɗi kuma ka tashi ina tabbatar miki da cewa, akwai Nasara a gabanki, baki faɗi domin kuwa zan miƙo miki hanu domin ki tashi zan tayaki yaƙi har sai kin amso Soyayyar ki, zan baki gudumowa a matsayina na yayanki, ki saurareni da kyau Rufaida ki fahimci abinda zan faɗa miki yanzu.”
Tunda ya fara Maganar ta zuba masa idanu tana ji a zuciyarta ko dai ta sanar dashi cewa shine wannan wanda take son, ina tsoro bazai barni ba, Haidar cigaba da Magana yayi.
“Rufaida! a Rayuwa ana bukatar jajircewa akan abinda kake muradi, mafarki baya taɓa cika har sai ka samu jajircewa, ba’a son saurin sarewa akan muradi a ko yaushe akan fuskanci ko wani ƙalubale da wahala domin kaiwa ga nasara akan muradi, ina so ki kasance jajirtacciya wacce bazata taɓa sarewa saboda wani ba, ke macece kuma itama macece na Tabbata bazata fiki da komai ba, meyasa zaki bari tayi Nasara akanki, na Tabbata idan har kin saka hkr da addu’a a Rayuwarki kuma kika dage da nunawa muradinki kulawa na san zakiyi Nasara, bazan taɓa yadda ki faɗi ba, karki bani kunya ki jajirce ki amso Soyayyar ki ƙanwata.”
“Na yadda da maganarka Ya Haidar, sai dai ina tsoron na tura mota ta tashi ta barni da ƙura gara na haƙura kawai ni na yadda na faɗi kawai, bazan ƙara maganar sa ba.”
Kansa Haidar ya dafe tare da cewa.
“Idan kina kiran kin faɗi sai naji kamar na mareki, bazaki hkr ba, na miki alƙawarin cewa sai kinyi Nasara akan soyayyarki.”
Zaro idanunta Rufaida tayi tare da cewa.
“Kamin alƙawari fa kace, idan har kamin alƙawari na yadda zan adana soyayyata kuma zanci gaba da nemanta, amma fa ka sani idan na kuma faɗuwa kaine wanda zanyi kuka dashi.”
Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
“Bazaki taɓa kuka dani ba Rufaida zan tsaya miki a matsayina na yayanki, idan ta kama ma, da kaina zan nemi nayi magana dashi wanda kike so ɗin zakiyi nasara domin kuwa Nasara a jininmu take..”
Murmushi Rufaida tayi dai-dai Maimu na nufosu tace.
“Muje Rufaida.”
Miƙewa Rufaida tayi tana ɗaukar bag ɗinta tace.
“Ya Haidar na gode.”
Murmushi kawai ya mata suka shige Inna Jumma ne ta dubi Al’ameen dake cin abincin kamar bazai ciba, tace.
“Aminu wai ya naji kayi shuru ne akan abinda Afnan tamin ko dai-dai tayi ne.”
Abincin Al’ameen ya ture gefe tare da miƙewa tsaye yana ɗaukar wayarsa yace.
“Ki jira kiga idan na barta sai kiyi mitar.”
Yayi Maganar yana barin daining ɗin, bakinta Inna Jumma ta taɓe tare da cewa.
“Ni ne ma mai mitar ko, ka faɗawa Uwarka to.”
Murmushi kawai Al’ameen yayi bai kulata ba ya cewa Haidar, ka shiga part ɗin naku kafin nan bara naje wajen Ummi, yayi Maganar yana haurawa sama, shima Haidar part ɗinsu yayi, Al’ameen room ɗin Aunty Amarya ya shiga bata ciki sai ihsan dake bacci, fita yayi ya shiga na Ummi tare ya sameta da Aunty Amarya suna zaune, gwanin sha’awa suna hira gefen Aunty Amarya ya zauna tare da kwantar da kansa a kafaɗarta yace.
“Amarya! Yau bake kikayi girki ba, domin kuwa test ɗin baimin ba.”
Murmushi Aunty Amarya ta saki tana shafa kansa tace.
“Wato dai duk sanda kaci abincin da ba nawa ba sai ka gane, Ladiyo ce ƴar aiki ta girka, kar dai har zaku fita?”
“Ai naji sauyi zamu fita, Ummi Barka da safiya.”
Murmushi Ummi tayi tace.
“Sai yanzu ka ganni kenan, tun ɗazu ai amarya kake kira.”
Murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.
“Kai Ummi, na isa na manta dake , kunga ni fita zanyi nayi let.”
Duk murmushi sukayi tare da masa addu’a cike da farin ciki Al’ameen ya fito.
Tare suka fita da Haidar a mota ɗaya, sunzo dai-dai Amina kitchen Haidar yayi parking dubansa Al’ameen yayi tare da cewa.
“Me kuma ka tsaya zakayi.?”
Haidar baice masa komai ba ya fita, Amina kitchen ɗin ya shiga, ya sayi abinci na 2k take away biyu, da lemo ya fito, gidan baya wurga ledar tare da jan motar suka nufi Sj hospital, a harabar asibitin sukayi parking tare suka fito Haidar ya ɗauki ledar, suka shiga, Al’ameen a bakin Office ɗin doctor ya tsaya tare da cewa Haidar.
“Room 10 zaka shiga anan take, ni bara na shiga na sallami doctor ina zuwa na sameka.”
Kansa Haidar ya ɗaga tare da shigewa shima Al’ameen ya shiga Office din doctor.
Haidar da Sallama ya shiga room ɗin tana zaune kanta a sunkuye, tayi shuru ga wani uban yunwa dake addabarta kanta ta dago tare da amsa sallamar, tana maida kanta ƙasa, Haidar zama yayi tare da cewa.
“Sannu ƴan mata ya jikin naki.”
“Da sauƙi.”
Ta amsa a hankali kanta na sunkuye, murmushi Haidar yayi ganin kamar tana cikin tsoro yace.
“Baki sanni ba ko.?”
Kanta ta ɗaga alamun eh, murmushi yayi yace.
“Sunana Haidar abokin Al’ameen wanda ya bigeki, kinci abinci ne jiya da dare?”
Kanta ta kaɗa alamun a’a, zaro idanunsa Haidar yayi yace.
“Yanzu fa kinyi breakfast.”
Nan ma Kanta ta ɗaga alamun a’a, Haidar cikin ransa ya furta, lallai Al’ameen bashi da imani, ashe haka yabar Yarinyar nan babu abinci sai kace ya ijiye dutse, numfashi ya sauƙe tare da miƙa mata ledar take away ɗin hanunsa yace.
“Ga abinci kici, meye sunan ki.”
“Sunana *ABLAH* “
Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
“Nice name, kici abinci Ablah.”
Kanta ta kaɗa tare da buɗe ledar, take away ɗaya ta ɗauka tare da fara cin abincin a hankali kamar bazata ciba kaɗan taci ta ijiye ruwa tasha a hankali ta furta.
“Na gode.”
Murmushi kawai Haidar yayi yace.
“Karki damu ya shiga wajen DOCTOR bara a sallameki sai mu kaiki gida ko.”
Kanta ta ɗaga alamun to, suna nan zaune Al’ameen ya shigo ko sallama baiyi ba ya tsaya a kanta tare da zaro dubu biyar ya ijiye mata a gefen gadon yace.
“An sallameki, ga wannan ki hau adaidaita ki koma gidan ku, Haidar tashi mu tafi.”
Hararar sa Haidar yayi tare da cewa.
“Naƙi na tashin yanzu kai sai ka barta ta koma gida ita kaɗai, ka bige ƴar mutane ka Kaita asibiti, ta kwana a matsayin ta na mace, kuma sai ta koma gida ita kaɗai ta cewa iyayenta meye, kaga Malam tare zamu tafi da ita a mota mu danƙata a hanun mahaifinta mu basu haƙuri tashi muje ABLAH mu sauƙeki a gida.”
Tsuka Al’ameen yaja yace.
“Ta tashi muje ina, bazata shiga min mota ba, ina ruwana dame zata faɗawa iyayenta, ni na bigeta da ganganne itace fa ta min shigar tsaye ta cuceni, bazan kaita gidan nasu ba, ka tashi mu tafi ta nemi adaidaita ta koma.”
Ablah ɗago idanunta tayi ta kalli Al’ameen, tana mamakin mungun halinsa, ayi mutum a rayuwarsa bashi da imani…