Skip to content
Part 9 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Wai meke damunka ne Al’ameen, wani irin magana ne ta cuceka, saboda bata hankali sai ta shigo titi dan kawai a bigeta,kaga malam dole zamu mai da wannan yarinyar hanun iyayenta da kan”

Haɗe fuska Al’ameen yayi tare da cewa

“Waya sani ko bata da hankalin, idan zaka maida ita ban hanaka ba, amma dai ba’a tawa motar ba, tunda ba motarka na hau ba.”

Murmushi Haidar yayi tare da miƙewa tsaye ya cewa Ablah,

“Ablah tashi muje kinji.”

Kanta ta girgiza cikin sanyin murya tace

“A’a ka bari kawai kuje zan koma da kaina akwai fahimtar juna tsakanina da iyayena zasu fahimce ni, bazan samu wata matsala ba, baya son ɗaukata karka takura masa.”

Tafi Al’ameen yasa yana sakin murmushin gefen baki yace

“Good sarkin iya tsara zance a fuska dai gaki kamar salaha amma Allah ne kaɗai yasan abinda yake cikin ki, to waye bashi da fahimtar juna da iyayensa, kinga tun sanda kika hau titi da gangan na Tabbata ke ƴar neman masifa ce, dan haka bazaki shiga motata ba, balle ki sake jawo min wata masifar.”

Haidar kansa ya dafe cike da takaici yaja hanun Al’ameen suka fito, a bakin room ɗin suka tsaya Haidar hanunsa ya haɗe duka biyu alamun roƙo yace

“Dan Allah badan niba kayi hkr mu maida Yarinyar nan gidan iyayenta, na roƙeka dan Allah badan niba.”

Bakinsa Al’ameen ya taɓe tare da cewa

“Baka tashi cuta ta, sai ka haɗani da ubangijina, nifa hankalina bai kwanta da wannan Yarinyar ba, kawai ku hau adaidaita kai ka maida ta.

Murmushi Haidar yayi tare da cewa

“Cool down Abokina kasan me, haɗuwarka da wannan Yarinyar iya na yaune fa kawai da zarar mun Kaita gidan su, ba zaka kuma ganinta ba, Please Abokina dan Allah ka sanyawa zuciyarka salama mu tafi kayi hkr.

Numfashi Al’ameen ya saki tare da ɗaga kafaɗarsa, Haidar ciki ya koma ya saka Ablah ta fito, baya ta shiga Haidar yaja motar, suka kama hanyar unguwar Durmi, ta mirror Al’ameen yake hango ta, ta sunkuyar da kanta idanunta sai zubar da hawaye yake, idanu ya zuba mata, cike da mamakin me kuma ya sata kuka, ko munafurci ne, bakin sa ya taɓe tare da kauda kansa daga mirrorn Haidar ne dake tuƙi yace

“Ablah ta ina gidan nakun yake.?

Saurin share hawayen ta tayi cikin sanyin murya tace

“Ɗan gaba kaɗan zamu ƙara.

Kansa Haidar ya ɗaga yace

“Ki dinga lura idan munzo sai kimin Magana ko.

Da to ta amsa, suna isowa ƙofar gidan nasu tace

“Mun iso “

Parking Haidar yayi tare da buɗe motar ya fito buɗe mata yayi itama ta fito, Al’ameen kamar bazai fito ba, sai kuma ya fito, duban gidan da yake gabansu Haidar yayi gida ne na langa langa babu gini ko ɗaya ƙofar gidan kuma an rufesa da bugu kana ganin gidan zaka tabbatar da gidan talakawa ne futuk, shima Al’ameen gidan yake bi da kallo a ransa yana furta cewa yanzu mutum ne ke zaune a cikin wannan gidan yake rayuwa, lallai rayuwa tana yiwa wasa wahala, numfashi ya saki sai kuma yaji tausayin Ablah ya kamasa, sam Yarinyar batayi kama da wacce zatayi rayuwa a cikin wannan gidan ba, Tabbas duk mai rayuwa a wannan gidan dole damuwa da tunani su kasance tare dashi, Haidar duban Ablah yayi yace

“Ablah nanne gidan naku.?”

Kanta ta ɗaga alamun eh, numfashi ya sauƙe tare da cewa

“Ki shiga ki mana Magana da babanki.

Cikin sanyin murya tace

“Bani da Baba, Babana ya juma da rasuwa, nida mamana da ƙanina kawai muke rayuwa acikin gidan, ita take ɗawainiya da rayuwarmu, bara na duba muku ita ko ta dawo daga gidan da take aikatau.

“Aikatau kuma?”

Haidar ya furta

“Ehh aikatau, dashi take rufa mana asiri, komai dashi take mana.

Runtse idanunsa Al’ameen yayi a rayuwar sa ya tsani ganin mutum cikin ƙangin wahala, sai yanzu ya fara fahimtar lallai damuwa tasa wannan Yarinyar shigowa titi ba tare da kula ba, numfashi Haidar ya saki yace

“Shikenan ki shiga ki duba mana ita.

Da to ta amsa tare da shigewa kanta a sunkuye

Haidar duban Al’ameen yayi yace

“Rayuwarta abar tausayi, da gani suna cikin matsala jagorancin gida a wajen mace akwai wahala.

Ɗan cije leɓensa na ƙasa Al’ameen yayi tare da cewa

“Ƙwarai kuwa suna cikin matsala, kowa da yadda Allah ya tsara masa tasa rayuwar.

Yayi Maganar Ablah na fitowa daga cikin gidan, tace su shigo, bayanta sukabi, koda suka shiga cikin gidan, tsakar gidan share yake fes babu wata alamar ƙazanta, komai a shirye yake, wata dattijuwar mata suka samu zaune a baranda wacce zata kai kimanin shekaru 45 gefenta yaro ne ƙarami shima zai kai shekara 10 yana shan garin rogo, Sannu da zuwa matar ta musu fuskarta cike da fara’a tare da musu nuni da tabarmar dake shimfide, zama sukayi itama Ablah ta zauna gefen Umma, Umma cike da sakin fuska tace

“Sannunku da zuwa maraba da hanya.

Haidar ne yace

“Sannu Mama, mun sameki lafiya.

Da lafiya ta amsa shima Al’ameen ya gaisheta, daga nan bai kuma Magana ba, hankalinsa yana kan Abdu dake shan garin rogo sosai tausayin yaron ya kamasa miƙewa yayi, duk suka bisa da kallo gaban Abdu yaje ya sunkuya tare da ɗauke garin a gabansa yayi wurgi dashi, yaron da kallo ya bi Al’ameen kamar zaiyi kuka itama Ablah idanunta ta zaro cike da tsoron kar a gidan nasu ma ya musu rashin mutunci, Haidar ma zaro idanunsa yayi yana tsoron Al’ameen ya basa kunya Umma mamakin ta duk yafi nasu cikin zuciyarta tana ambaton wannan wani irin mutum ne, Hawaye ne ya zubo daga idanun Abdu yace

“Yaya ka zubar min da abinci na, yanzu Umma ta bani kuɗi na sayo shine ka watsar min kuma yunwa nake ji.

Murmushi Al’ameen yayi tare da saka hanu ya shafa kan Abdu yace

“Wannan ba abinci bane, bazai riƙeka ba, yunwa kake ji babu wani abincin ne dole sai wannan.

Abdu cewa yayi

“Mu bamu da wani abinci shi kaɗai muke ci da rana da daddare kuma Aunty Ablah ta mana tuwo.

Numfashi Al’ameen ya saki tare da cewa

“Kayi hkr na zubar maka da abinci ko?

Yayi Maganar yana ciro kuɗi daga aljihun sa Naira dubu daya ya bawa Abdu tare da cewa

“Maza kaje shago su baka madara da milo da bread kazo kasha kaji.

Dariya Abdu yasa cike da farin ciki kamar bazai mutu ba ya miƙe tare da ficewa a guje, Umma murmushi tayi domin kuwa ta juma bata ga farin cikin ɗanta haka ba, Al’ameen dawowa yayi ya zauna kansa na ƙasa ba tare da ya kalli Umma ba yace

“Kiyi hkr Mama na bawa ɗanki kuɗi ba tare da izinin ki ba, amm nine Wanda na bige ƴarki Mama bisa kuskure na ɗauketa munje asibiti da wani dattijo, so yace min zaizo gida ya sanar daku ya dawo, tunda dai ya tafi ban kuma ganinsa ba, kiyi hkr dan Allah na miki kuskure.

Murmushi Umma tayi idanunta na cikowa da hawaye tace

“Yaro hankalina ya tashi sosai da banga Ablah ba, nayi ta yawon nemanta amma babu labari, duk inda nasan Ablah na zuwa naje bata nan, shi wannan dattijo Tabbas yazo sawunsa Uku muna saɓani, na tafi neman Ablah, sai sha ɗaya ya kuma zuwa yake sanar dani abinda ke faruwa, naso ma naje asibitin a wannan lokacin, amma ya hanani yace dare yayi nayi hkr har zuwa Safiya ya tabbatar min da ABLAH tana hanun mutumin kirki, yadda da Baba yasa dole na hkr amma har ga Allah banyi bacci ba, yanzu haka shina tsaya jira yazo muje sai kuma gata tayi sallama, karka damu ba komai ƙaddarace ai.

Murmushi Haidar yayi cike da jin daɗin karancin matar yace

“To mun gode mama Allah ya ƙara sauƙi mu zamu koma

yayi Maganar suna miƙewa kusan a tare ko wannensu ya ajiyewa umma kuɗi tare da cewa ta sayi abinci, da farko Umma taƙi amsa, dole tasa ta amsa ganin sun fita sun barta da kuɗin, sanda suka fita Umma ta dubi kuɗin tace

“Sannu Ablah, ya kike jin jikin.”

Murmushi Ablah tayi tace

“Bana jin komai yanzu Umma,  dama nayi tunanin hankalinki zai tashi.

“Ba dole hankalina ya tashi ba, alhamdulillah tunda Allah yasa kina hanun na gari

Kuɗin Umma ta kalla ɗagawa tayi taga wanda Al’ameen ya ijiye mata 200k shi kuma Haidar 50k numfashi Umma ta saki ta cigaba da cewa

“Alhamdulillah! Mun sami kuɗin registration ɗinki Ablah idan kace ya zakayi ka manta da Allah, gobe da sassafe zanyi sammako naje na biya kuɗin nan dubu hamsin kuma sai mu sayi kayan abinci.

Tayi Maganar cike da farin ciki, a da harta fitar da ran cewa ƴarta zata yi karatun likita, saboda bata da kuɗaɗen registration dana littatafai, sai gashi yau Allah ya mata, itama Ablah murmushi ta saki tace

“Umma bara naje na kwanta.

Da to ta amsa Ablah ta shige ƙaramin ɗakin nasu, bata juma da shiga ba Abdu ya shigo da gudu hanunsa riƙe da leda ya sayo kayan shayi a gaban Umma ya zauna yana dariya da kanta Umma ta haɗa masa tea ɗin kafin ta tashi ta ɗauki hijabin ta tare da leƙawa ta cewa Ablah ta shige gidan aikinta

Da adawo lafiya Ablah ta amsa mata tare da maida kanta ta kwanta gidan su ƙawarta Hafsa take son shiga sai dai bazata iya sakamakon ƙafarta dake ɗaure

Tunda ya zauna a Office ɗinsa jikinsa duk yayi sanyi, bai taɓa zaton cewa akwai waɗanda suke cikin ƙuncin rayuwa ba haka, ace abincin da zakaci ya gagareka, wai garin rogo shine abi

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!!!

Ya furta yana tuno kukan da yaga Yarinyar tanayi a cikin mota, gata kyakkyawa amma sam ba jin daɗin rayuwa, ga rashin mahaifi, Tabbas suna buƙatar taimako, amma duk da haka sai yake ganin Yarinyar kamar munafuka ce

Yayi Maganar cikin ransa, ya juma yana jinjinawa lamarin wunin ranar dai haka yayi aikin cike da tunani

Koda suka tashi a aiki tare suka dawo gida da Haidar sai dai basu kuma Magana akan gidan su ABLAH ba har suka shigo gida, Haidar part ɗinsu ya shige shima Al’ameen ya shige nasu, Ummi ya samu ita da Inna Jumma suna zaune a falon sun zubawa tv idanu da Sallama ya shiga jikinsa duk a sanyaye ya zauna kusa da Ummi tare da kwantar da kansa a cinyarta idanunsa ya lumshe yana sakin ajiyar zuciya aduk sanda ya kwanta jikin mahaifiyar sa sai yaji nutsuwa da sanyi na ratsa jikinsa damuwar dake damunsa sai ta kau, Inna Jumma ce tac

“Yau naga wani sabon salo, dan Allah dubeka goɗai goɗai dakai ka kwanta mata a cinya kalan ka karyata, ke kuwa Gaji kin zuba masa idanu tsabar jarabar son ƴaƴa, dallah ɗagata Malam.

Murmushi Al’ameen yayi idanunsa na rufe a hankali tamkar baya son Maganar yace

“Ai ke matsalarki kenan shishshigi da saka idanu meye matsalarki dan ɗa ya kwanta a jikin Maman sa, Please karki dameni nutsuwa nake nema.

Tsulum Inna Jumma ta miƙe Ummi na dariya ba tare da tace komai ba, zuwa tayi ta ɗakawa Al’ameen duka tare da cewa

“Allah sai ka tashi, baka isa ka nakasa min ƴa ba.

Dariya Al’ameen yasa tare da miƙewa ya cewa Inna Jumma

“Oh Wannan tsohuwa kin isheni, yauwa Inna Afnan ta dawo ne.?

Murmushi Inna Jumma tayi cike da salon mugunta tace

“Ɗan albarka ta dawo tana can Uwar ɗaka yanzu ta gama min dariya kamar taga mahaukaciya.

Miƙewa Al’ameen yayi ba tare da yace komai ba ya haura, Ummi da kallo ta bisa domin kuwa ita bata san neman me Al’ameen yake yiwa Afnan ba, bedroom ɗinsa ya shiga tare da ijiye jakar sa, belt ya ɗauka ya fito ROOM ɗin su Afnan ɗin ya shiga tana zaune ta ƙure digin daga ita sai best da legis, kallonta yayi gaba ɗaya hankalinta naga waƙar bata ma lura dashi ba, hanu yasa ya dannawa ROOM ɗin key ya tako har gabanta sai da yazo gabanta Afnan ta kula dashi cike da tsoro taja baya tana zaro idanunta ganinsa da belt, hanu yasa ya kashe waƙar yana dubanta tace

“Me kika cewa Inna Jumma da safe, wato a gidan nan kin zamo fitsararriya ko, kina ganin kin isa kinfi ƙarfin kowa, to ko Daddy bazai zageta ba bare kuma ke, ban hanaki kiyi wannan shigar banzan ki fita dashi ba.?

Cikin in.ina Afnan tace

“Ni..ni.. fa ban zageta ba walla…….

Tsawa ya daka mata tare da cewa

“Rufe min baki dan ubanki sharri zata miki.

Yayi Maganar yana zuga mata belt ɗin wani irin ƙara tasa na azaba, shi kuwa sai zuba mata yake tana ihu Ummi dake zaune ne ta jiyo kamar sautin kukan Afnan ne ta tashi da sauri ta haura wato neman da yake mata kenan room ɗin ta nufa tare da turawa rufe gam taji sa, ga kuma Afnan na zunduma ihu, Ummi ƙofar ta buga tana cewa

“Al’ameen ka buɗe min ƙofar nace!

Yana jinta yaƙi amsawa bai kuma fasa dukanta ba, muryar Ummi da yaji cikin tsawa ya sashi dakatawa

“Ina maka gana dan ubanka bazaka buɗe ba! Idan ka kuma saka hanu jikinta wallahi sai na saɓa maka.

Runtse idanunsa yayi domin kuwa a duk sanda zai hukunta Afnan Ummi ke dakatar da shi, belt ɗin ya sake tare fitowa a fusace ya buɗe ƙofar bai kula Ummi dake tsaye bakin room ɗin ba, ya shige ROOM ɗinsa cikin ɓacin rai, Ummi shiga tayi tana kamo Afnan jikinta duk ya tashi yayi ja abinka da farin mutum, sosai Ummi ke faɗa, shi kuwa tollet ya shige yaje ya sakarwa kansa ruwa ya juma sosai cikin tollet ɗin kafin ya fito, wayarsa ce tayi ringin tare da dubawa *BROTHER KHALIFA* ɗan murmushi ya saki tare da ɗaga kiran yana cewa

“Ya akayi ne mutanen Egypt.

Daga can Khalifa yayi dariya tare da cewa

“Kaga sauri nake jirgin mu yanzu zai tashi, nan da 8 kazo ka ɗauke mu a airport.

Murmushi Al’ameen yayi tare da cewa

“Au wato ma bazata ka mana, har kun gana exam ɗin kenan, to Allah ya kawo ku lafiya.

Da ameen Khalifa ya amsa suka katse kiran, Al’ameen Aunty Amarya ya kira, duk yasan ta fita unguwa amma dai yasan itace kawai zatayi wa su Khalifa abinci mai kyau, tana zaune gaban Hajiya Mansura ya kirata bayan ta daga ne ya sanar da ita cewa su Khalifa suna hanya ta dawo ta haɗa musu abinci, murmushi ta saki ta amsa da to tare da kashe wayar

Dariya Aunty Amarya ta saki tare da cewa Hajiya Mansu

“Albishir!

Murmushi Mansura tayi ta amsa d

“Goro!

“Ƙaramin marar kunyan yana hanya shida Ashfat, zasu iso nan da 8.”.

Guɗa Hajiya Mansura ta saki tare da cewa

“Ta faɗi ƙasa gasassa,dama ta samu, Amarya zamuyi amfani da wannan damar mu aikasu lahira kafin ma su iso gidan, kuma cikin hanya mai sauƙi zamu haɗamu musu accident Wanda babu wanda za’a zarga a cikin mutuwar sai a ɗauketa a hatsari.

Dariya amarya tasa suka tafa tace

“Bani da ja acikin zancen ki, bara ma kiga na tashi naje, ki tsara komai kimin text zan miki transfer ɗin kuɗi sannan zan sanar dake da zarar an tafi ɗaukosu sai kubi bayan su.

“Ki tabbatar fa kin sanar damu akan lokaci yanzu zan nemi Isah Alolo.

Murmushi amarya tayi tare da cewa

“Baki da matsala dani ƙawata.

Tayi Maganar tana dariya cike da farin ciki suka rabu.

*****

Kallon Amnat tayi tare da sakin dariya ta

“Ko tsarin nawa bai miki bane, idan akwai shawara gara ki bani time na ƙurewa, gida nake son na samu yau a wajen sa koda ƙarami ne.

“Nafeesa sai naga kamar kina nuna haɗamarki da wuri yaushe ma kuka haɗu dashi da har zakiyi plan ɗin samun gida, mtss! Karki kuskura ki bari ya fahimceki da wuri domin kuwa duk son da yake miki wallahi zai watsar dake, yanzu abinda zakiyi maimakon kiyi ƙaryar cewa sister ɗinki tana cikin matsala an koreta a gidan haya ya taimaka musu ya basu inda zasu zauna, to gara ki sauya da cewa ya taimaka musu da kuɗin haya,  idan kika bi a hankali gidan ma zai saya miki wata rana, amma ni ga wani shawara mai zai hana ki kai sunan Haidar wajen Malam ya miki aiki akansa duk abinda kika tambaya ya baki babu musu bare bincike ni ina ga zaki samu idan kin kaisa wajen Malam………………….”ce.✨✨✨.”.””.”. “a”ra..”.”.”.”.”.”.”.”.”.”.”.”.”e…”nci…”.”.””.?.”.”.”.”.”.”.”.”.”.”.”.”..”.”..”.”…..”.”.”.”.”.”.”.”.” “.mu.”.”ce.✨✨✨.”.””.”. “a”ra..”.”.”.”.”.”.”.”.”.”.”.”.”e…”nci…”.”.””.?.”.”.”.”.”.”.”.”.”.”.”.”..”.”..”.”…..”.”.”.”.”.”.”.”.” “.mu.”nsa duk abinda kika tambaya ya baki babu musu bare bincike ni ina ga zaki samu idan kin kaisa wajen Malam…………………..”

<< Aminaina Ko Ita? 8Aminaina Ko Ita? 10 >>

1 thought on “Aminaina Ko Ita? 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×