Cikin zafin rai, Boka Rubbas ya fara yi wa kansa kirari, "Ni ne gawurtaccen bokan da babu kamarsa a faɗin duniya! Ni ne Tsumangiyar Kan Hanya, fyade yaro fyade babba! An haife ni cikin tsafi, na rayu cikin tsafi, na gaji tsafi! Ni ne ƙadangaren bakin tulu, na shiga na ƙi fita, a kar ni a kar tulun, a bar ni na ɓata ruwa. Ni ne Murucin Kan Dutse, Sarkin Hatsabiban Bokayen duniya..."
Bai ƙarasa kalamansa ba, sai ga Amrah ta bayyana tsulum a gabansa! Cikin wata irin siffa mai ban tsoro, gaba ɗaya jikinta ya koma na wata ƙatuwar. . .
