Shamaki yana tsaka da birgima, sai aka hango Malam Buba yana nufo fadar riƙe da hannun Amrah, matarsa Ladidi tana biye da su a baya. Da mutane suka hango su, sai suka fara zamewa ɗaya bayan ɗaya, suna barin fadar a guje. Kafin su Malam Buba su ƙaraso, gaba ɗaya jama’ar wajen sun tarwatse, sai Maigari da tsirarun fadawansa ne kawai suka rage.
Shi kuwa Shamaki, tun da ya ji ana cewa "Ga ta nan!" kuma ya ƙyallara ido ya hango su, sai ya rarrafa ya koma bayan kujerar Maigari, ya labe ya yi shiru, kamar ba shi ne. . .
