Su Malam Buba suna zaune, sai suka ji sallama a ƙofar gida. Yana fita, ya tarar da fadawan Maigari guda biyar a tsaye. Bayan sun gaisa, suka ce masa ya zo fada nan take Maigari yana son ganinsa da gaggawa, amma idan zai tafi, ya je shi kaɗai. Suna faɗa masa, suka juya da sauri suka bar ƙofar gidan. Malam Buba ya canza riga kawai, ya saka takalmansa, ya nufi gidan Maigari.
Yana isa, ya tarar da fadar ta cika da manyan garin. Sannan ga wani babban boka a zaune gaban Maigari. Babu komai a jikin bokan sai warki da. . .
