Kanta ke nauyi, idanuwanta na wani irin zugi tamkar wacce ta yi kwalli da tsidugu, a haka take ta juyi saman gadon da take jin tamkar ƙaya ne, a cikin yinin da bata taɓa sanin akwai yini mai nisan sa ba. Tana jin komai na fice mata arai, tana jin yadda tsantsanin haram ke gauraye gabadaya rayuwarta, hatta a tufafin jikinta.
A dukkan bugu na zuciyarta, yana fita ne da tarin ruɗaɗɗun kalmominsa, ta rasa gane manufarsu da yawansu, sai dai tana jin akwai waɗanda suka ci karo da addininta, akwai waɗanda har ƙasan zuciyarta. . .
The novel is verrrrry intresting