Skip to content
Part 6 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Kanta ke nauyi, idanuwanta na wani irin zugi tamkar wacce ta yi kwalli da tsidugu, a haka take ta juyi saman gadon da take jin tamkar ƙaya ne, a cikin yinin da bata taɓa sanin akwai yini mai nisan sa ba. Tana jin komai na fice mata arai, tana jin yadda tsantsanin haram ke gauraye gabadaya rayuwarta, hatta a tufafin jikinta.

A dukkan bugu na zuciyarta, yana fita ne da tarin ruɗaɗɗun kalmominsa, ta rasa gane manufarsu da yawansu, sai dai tana jin akwai waɗanda suka ci karo da addininta, akwai waɗanda har ƙasan zuciyarta take jin ba daidai ba ne, ya furta su ne dan kawai ta gane rashin muhimmancinta a rayuwarsa da dukkan abin da ta mallaka, duk da ita ɗin ba ta kasance mai addinin ba.

Ƙauna ce mai girma tsakaninta da kuɗi, idan akwai abin da tafi tsoro a gabaɗaya rayuwarta, to talauchi ne, me ya sa Haroun zai bi da ita ta inda ya san zai muzgunawa rayuwarta, ta sani har a cikin hankalinta, dukiyarta haram ce, sai dai ta ya ya za ta rabu da dukkan abin da ta mallaka saboda ta tuba, ta bar neman haram da abin da Allah Ya haramta? Da me za ta rayu? Me za ta ci? Tana buƙatar amsar nan, dole ta shirya ganin babban Malamin yankinsu, tana ma son sanin yadda ake tsarkake shi kanshi tuban. Akwai ƙuduri mai girma cikin ruhinta da ke ɗauke da tarin tsoron mahaliccinta, tabbas za ta ƙarbi dukkan abin da tambayarta ta amsa, za kuma ta yi tuba, sahihin tuba, tuban da ba za ta ƙara komawa aikinta ba, tuban da za ta dawwama tana neman tsarin hakan har ga iyalanta.

A hakan ta shigo inda take cikin sassarfa, kayan hannunta na zubewa, tana tuntube da tarin tarkacen da ke zube ƙasan, amma ba ta dakata ba, har sai da ta dangana da gadonta, ta tsaya tana fidda numfarfashi.

“Maa, ban yadda da Anty Bitil ba, yanzu na ganta a Higgah Restaurant ita da Alhaji Saleh Tumbi, akan ido na yake tura mata kuɗaɗan da bata cancanci mallakarsu ba…”

“Soupy!”

Ta kira ta a kausashe tana juya idanuwanta saman fuskarta.

“Menene dan ta tsaya da shi ba sana’arta ba ce? Yaushe kika fara shiga rayuwar da ba ta shafe ki ba? Har kinsan akwai kuɗin da ba su da ce da mutum ba? Kin sani na tsani munafurci ko?”

“Amma fa abin dubawa ne Maa, shekara nawa Anty Bitil ta yi ko tsuntsu bai neme ta ba? Da Alhaji Saleh fa na ganta, ke da kanki kika ce kar wanda ya sake harka da shi, kuɗaɗen da na ga ya aje gabanta ba na tunanin dan hajar tane. Akwai abin dubawa, ba ki san abin da ya faru jiya da yamma bayan fitar…”

“Get out!”

Ta furta a zafafe tana nuna mata ƙofa.

“Ki fita na ce, kin sani ba na son abin da zai shiga tsakanina da tunanina, me ya sa ba za ki gane bana son tashin hankali ko ya ya ne yanzu ba? Me ya sa ba za ki barni na ji da tarin wahalhalun da suke fuskanto rayuwata ba, kin fara koyan munanan dabi’u Soupy, fita…, kar ki ƙara shigowa sai na neme ki.”

A hankali ta juya, tana tafiya tamkar wacce kunkuru ya shigewa ƙafa. Tausayinta take ji mai girma a ƙasan ruhinta, tana jimamin abin da ke ƙoƙarin hargitsa rayuwar uwarɗakin tata, ba ta jin akwai alherin da zai haɗa Alhaji Saleh zama da Bitil, tana jin akwai gagarumin tashin hankalin da ke fuskan tosu, to, ta ya ya ma za ta yarda da Bitil? Matar da ta sha kamata tana zuba guba a cikin abincin Ashana? Sai dai ita ta faki ido ta canja, ta sha kama ta tana zuba garin Acid a cikin manshafawarta, sai dai ita ta ɗauka ta jefar a shara, Ashana ta zo ta yi ta faɗa ana mata ƙananun ɗauke-ɗauke, amma ba ta taɓa furta mata ba, duk da akwai sahihin zancen da ya tabbatar da babu annamimi, mai haɗa gulma, irin ɓarawo. Ta sani ita kam, ita dai Soupy, ta fita daban anan ɓangaren.

“Soupy.”

Ta tsinkayi sautin muryarta yayin da take ƙoƙarin tura mata ƙofar.

Dawowa ta yi, ta tsaya tana kallon yanayinta.

“Zuwa yamma, ki tafi ki binciko min babban malamin da ya iya bada fatawa. Ta tsantsar gaskiya amma.”

Gyaɗa kai ta yi kawai, tana barin ɗakin.

Da ido ta bi bayanta, tana lura da sanyin jikinta, sai ta ji kamar bata kyauta mata ba, sai dai abin da ke rayuwarta ya fi ƙarfin ta tsaya kula Bitil, matar da ta san ta tsani ko da inuwarta ne, to, komai ma ya zo ƙarshe, abin da take yiwan ma ta kusa barinsa, ita sai ta ci gaba da ja, har zuwa inda rayuwa za ta kai ta.

***** *****

Sitting room ne babba da ke cike da tarin littattafan addini, daga tsakiyarsa kafet ne zubin ƙasar Masar, a samansa dadduma ce saƙar ƙasar Bahrain, a samanta kyakkyawan dattijon me cike da haiba ke zaune, gabansa ƙaton ƙur’ani ne bugun warshi yana karantawa.

A haka ya shigo, yana mai zubewa gabansa cike da girmamawa.

“Sheikh an samu baƙuwa tana son ganinka, sai dai…”

Ɗagowa ya yi, yana ƙare masa kallo ta cikin farin tabaron da ke idanunsa.

“Ya ka yi shiru? Ƙarasa mana, me ke tafe da ita?”

“Cewa ta yi tambayoyi gareta da kai kaɗai za ka iya amsa mata, sai dai kamar na ce ta tafi, na santa, babu wani alheri a ganinta, ina jin tsoron ko da wani mummunan abin ta zo, wannan shugabar karuwance Ashana, tsaye a ƙofar gidan nan.”

“Assha! Na hane ka da ƙin kyautatawa musulmi kyakkyawan zato Sabir, godiya za ka yi ga Allah da har ta iya zuwa ƙofar gidan nan, karka damu, je ka ce ta shigo, dukkan sharri yana bin mai shi ne, babu kuma wanda zai canja abin da Allah ya nufe shi, kabar dukkan zato ga Musulmi, ka kuma nemi gafararta.”

A suɓule ya miƙe zuwa ƙofar gidan.

A haka ta shigo, gabanta na dokawa a kowane takunta, a daidai ƙofar ta tsaya.

Kallonsa take, zuciyarta ta tsinke, girman ƙudirar Ubangiji na mamayeta.

Tun daga farcen ƙafarta take jin kunyar abin da ta taɓa aikatawa gare shi, shi ne dai, a zaune cikin falon.

Shi ne dai, Dattijon da ta yi ƙoƙarin ɗagawa hannu a wata rana, saboda kawai ya gogi jikin motarta, girman haibar da ta gani cikin idanuwansa ya hanata, ta dai ɓige da yarfa masa rashin mutunci tana zagin iyayensa. A yau gata tsaye gabansa, ta zo domin kawai ya gaya mata yadda za ta rabu da komai, ciki kuwa harda motar da bata taɓuwa.

Hawaye ke sauko mata, a hakan take gaggawar juyawa zuwa inda ta fito.

“A’a ƙaraso mana…”

Ta ji sautin muryarsa yana dakatarta, juyowa ta yi, ta zauna a gabansa, hannunta haɗe da na juna alamun roko.

“Ka yafe min domin Allah.”

Murmushi ya yi yana jinjina yanayinta.

“Fatar ba wannan ne ya kawo ki nan ba? Aike ɗiya ta ce, me zai sa na yi fushi da ‘yar cikina? Ba ɗabi ar musulmin kwarai ba ce zama da wani cikin ransa. Na daɗe da yafewa kowa. Na sani kuskure na ne ai, me ke tafe da ke?”

Idanuwanta na kafe kan kafet ɗin, a haka ta kora masa dukkan tambayoyinta.

Allahu Akbar ya ke ambato, kafin kuma ya fara magana.

“Ai wannan ba ma sai karuwa ba, duk wanda yake neman kuɗi ta hanyar haramun, shi ma ya shiga cikin hukuncin, zina ce, ko sata ko fashi, ko siyar da giya ko dai wani abu da ya yi kama da hakan. Idan mutum yana irin wannan yana samun kuɗi da shi, sai Allah (S.W.T) ya shirye shi, to ya sani cewa wannan dukiyar ba fa tasa ba ce.

Tuban da ya yi, idan dai ya tuba tsakani da Allah, Allah zai ƙarbi tubarsa, amma dukiyar nan dai ba ta sa ba ce…”

Dakatawa ya yi yana dubanta, ganin yadda dukkan jikinta ke rawa, a haka ya ɗora

“Sai dai idan ya kasance shi faƙiri ne futuk! Babu yadda za a yi, lalura ta saka sai ya yi amfani da wannan dukiya, to fa zai iya cire iya abin da zai buƙatar shi na wannan lokacin. Idan ya so sai ya yi sadaka da dukiyar, abin da ya fi inganci ke nan, ya rabar da ita, ya yi amfani da wadda za ta amfane shi a daidai lokacin, saboda zai iya fita ya nemi abin da kuma zai ci, Allah mai azurtawa ne, kuma zai ba shi. Abin da malamai suka yi bayani akai ke nan.

Suka ƙara da cewar, idan kuma misali so yake ya ɗanyi kasuwanci haka, dukiyar tana da yawa, to sai ya ɗan cire abin da zai yi kasuwancin wanda ba shi da yawa, sai ya rabar da mafi yawa ko kuma ya rabar da ragowar dukiyar. Shi ne abin da akafi raja’a akai. Amma fa asali dukiyar ba tasa ba ce, sai idan ya kasance lalura, zai ya fi ci kaɗan, daga mafi yawan. Wallahu a’alam.

Wannan shi ne, Allah ya sa kin gane, kuma za ki yi ƙoƙarin tsarkake tubanki, na ji daɗi, haka ake son dukkan musulmi ya kasance yana hangen gabansa, ki tafi kawai, Allah mai rahma ne da jinƙai, da sannu zai gafarta miki idan kin tsarkeke zuciyarki, da sannu za ki ga kyakkyawar rayuwar da za ki fuskanta a gabanki, ku zo, da kaina zan ɗaura miki auren, tunda kince ba ki da ahali.

Hawayen farin ciki take, a hakan take takawa zuwa unguwarsa, ji take kamar ma dukkan burinta na duniya ya gama cika.

A tare suka wanzu gurin, shi yana fitowa daga shagon, ita kuma tana isowa ƙofar shagon.

Ita tana masa kallon ya zama mallakinta, shi yana mata kallon da ta gaza gane ma’anarsa.

Kanta a ƙasa, tana juya zoben hannunta ta fara magana.

“Soyayyar da na ke yi maka tamkar tafiya ce mai nisa da na fara yinta wadda ba ta da lokacin yankewa har abada. Na san burina zai cika matsawar ina tare da kai, domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samunka a matsayin miji, uba ga ‘ya’yana…”

Ta numfasa, tana ɗago da idanuwanta a hankali zuwa fuskarsa, a tsaye ƙyar! Idanuwansa ke dubanta, sai dai ta gaza gane yanayin da yake ciki har yanzun.

“Ka yadda muje gaban mutumin da na san babban malamin ka ne, ya ce zai ɗaura mana aure…”

“Na rabu da komai kamar yarda ka nusar da Ni, na bar kawai abin da zan baka ka yi jarin da za mu iya rayuwa. Domin Allah me ya sa ka nuna min abin da na mallaka duka sai na barsu za ka iya rayuwa da ni?Me ya sa kake son rayuwar talauchi?”

A gabanta ya ƙara so, ya tsaya a kan tsayinsa da ya zarce nata, a tsakanin daya saura gare su, take jin zafin hucin numfashinsa a fuskarta.

“Saboda sai da hakan ne zan gane abin da kike ikirarin za ki yi domina, na ji dukkan tattaunawarku da Sheik Hariss Ajmi, na ji kuma irin ƙaryar da kika masa na cewar za ki tuba ne domin Allah, idan ma baki san ina cikin gidan ba lokacin da kika je, to, akan idona akai komai, na kuma jinjinawa girman soyayyar da kike min da za ki iya taka gidan mutumin da kika taɓa kuntatawa, saboda kawai taki ta kai ki…”

” Sai dai ki sani, babu wani abu da zai canja zance na, saboda ra’ayi na ne na gaya miki, ba wai na miki togaciya da Addini na dan kawai ina son ki gyara. Ni A karan kaina ba zan taɓa aurarki da wani abu na ki ba, ko da kuwa tufafin jikin ki ne.

Idan auran nawa kike so da gaske, to ki sadakar da komai, ki zo wannan cikin shagon nawa mu rayu da ɗan abin da nake iya samu, idan kuma ba ki iyawa, sai ki shafa min lafiya, dama ban kawo ki ba.

Ke Ni zuciyata ma ta gaza aminta da wannan tuban naki, faɗa mini, menene sharuɗan tuba?”

Girgiza kai kawai take yi, hawaye na sintiri har ƙasan haɓarta, tana jin dukkan farin cikinta na komawa inda suka fito.

“Karka min haka Haroun, kar ka shiga tsakanin aikin bawa da ubangijinsa, Allah kaɗai ya san abin da ke ƙunshe a zuciyar kowane bawa, wallahi domin samun rahmarsa na tuba, domin gujewa azabarsa na bar komai, ba zan ƙara komawa zina ba, ba na fatar ko wani cikin Ahlina ya yi irin rayuwar da na yi. Ka dube Ni domin Allah ka sassauta mini. “

Kallonta yake yana ganin yadda take kuka da dukkan ƙarfinta, ba wai tausayinta ne ba ya yi ba, sai dai akwai abin da yake tsoro, da bai ma san inda zai aje girmansa ba.

Matar da ke tsaye gabansa, ta yi shaharar da har a makwaftan ƙasarsa suna da labarinta, shi ina zai ɓoye hakan a lokacin da ta zama mallakinsa? Zuciyarsa ta gaza yadda ma ba za ta sake komawa zina ba, sai dai zai bi shawarar da Sheikh Hariss ya ba shi, da yaje masa da batunta, zai yi shahadar ƙuda ya aureta, zai kuma kyautata zatonsa akanta, bai san abin da Allah ya ɓoye cikin lamarunsu ba.

A haka ya sauke numfashi yana duban yadda ta toshe bakinta da Tarhar kanta tana hawaye, wani abu ya ji ya tsinka masa zuciya, bai taɓa ganin kukan mace irin haka ba.

“Dan Allah ki bar kukan, kinga hanya ce ta mutane, ki tafi gida, nan da wata uku bayan kin kammala Istibra’i sai mu je Sheikh ya ɗaura mana auren, kafin lokacin na san na koyawa zuciyata yadda za ta so ki.”

Baya kawai yaga tana yi, yana ganin yadda kyallin haƙoranta ke bayyana saman kumburarriyar fuskarta, da gudu kuma ta juya tana dariya, tana rufe fuskarta da dukkan hannuwanta alamun kunya, a haka ta ɓacewa idanunsa.

Girgiza kai yake yi yana murmushi, sai ya ga ta zame masa yarinya futuk, da ya ƙara tuna yanayinta sai ya kyalkyale da dariya, a haka ya juya zuwa shagonsa.

Hmm yanzu za a fara!

***** *****

Zafin ranar da ta ji na ratsa ilahirin jikinta ne, ya ankararta da daɗewar da ta yi cikin waiwayen lokutan da ba za su sake dawowa ba.

Tabbas koma menene ke faruwa a yanzu cikin rayuwarta, Fakriyya ita ce sila, da ace tun farko ba ta kawo musu Alhaji Auwal Sheerif ba, har suka ƙarbi aikinsa, da yanzu ba ta san wani Hamoudi ba, har ma akai ga hakan.

Akwai abubuwa da yawa da ta gaza gane in da farkon zarensu yake, wanda Fakriyya kaɗai ke da amsarsu, sai dai ta ya ya za ta gano bakin zaren a yanzu da Fakriyya ta mata nisan da ko ganinta za ta yi sai ta ci kwakwa? Ba za ta huta ba, ba za ta taɓa zama ba har sai ta gano yadda ma akai Hamoudi ya san Fakriyya alhalin kullum yana tare da ita? Tana son sanin yadda suka shirya komai, har zuwa yadda aurenta da shi ya juye, ya koma kan Fakriyya.

I zuwa yanzu ita kanta satar da suka je har ta haɗu da Hamoudin ba ta yarda da ita ba, akwai wani abu ɗaurarre da ya fi hangen dukkan hasashenta, amma kuma, shin yaushe ta yi girman da za ta aje makiya har haka? Wa ke da burin tarwatsa rayuwarta?

A haka ta miƙe akan ƙafafunta da sukai tsami, tana ɗaga su a hankali zuwa inda motarsu take.

Sumoli na ciki ta yi rashe-rashe a baya tana tiƙar barci, buɗe wa ta yi, ta figi motar da ƙarfi, wanda ya sa Sumoli farkawa a ruɗe, tana ambaton.

“Sorry Maa.

Ko da shigarsu gidan, Soupy ce ta taso hankali tashe tana kallonsu da tarin tambayoyi a fuskarta, sai dai kanta furta, Reza ta ɗaga mata hannu, tana ƙarasawa kusa da matar da ke zaune saman wheelchair.

A idanuwanta take gane magana take son yi mata, kasancewar ba ta umm ko uhmm ya sa kawai ta zura mata idanu, tana dubanta cike da gargaɗi, murmushi ta yi a hankali tana shafa fuskarta, “Karki damu, komai zai zama daidai,” ta furta a saitin kunnenta, tana miƙewa, ta ƙarasa zuwa ɗakinta.

“Ba na buƙatar kowa.”

Ta faɗa tana buga musu ƙofar.

Ajiyar zuciya Soupy ta sauke, tana duban Sumoli, sai yanzu hankalinta ya kwanta da taga dawowarsu lafiya.

“Ina kuka kwana ne?” Ta furta har yanzu idanuwanta kan Sumoli

“A bakin kogin da suke zama da Hamoud ta kwana, Ni kuma a mota.”

“Oh ni Soupy?”

“Yanzu duk wannan uban sanyin asubar can yarinyar nan ta kwana? Kina uban mene da baki kirani ba? Ya ya ma suka yi da Fakriyyar?”

“Ina zan sani? Ba abin da ta faɗa mini, na ga dai ta fito da ninkin tashin hankalin da ta tafi da shi, sannan ko na kira ki me za ki yi? Na ga a gabana ta manta dukkan abin da ke tsakaninku ta…”

“Sumoli!”

Ta kira ta a kausashe tana nuna mata ƙofa.

Juyawa ta yi da fushi tana barin falon, ita fa, ba ta ga ma abin da zai sata son wani banza ba, wai kuma da aure, menene cikin aurenma? Menene babu a jikin mazan da take kulawa da har sai anyi aure ne za ta samu? Sosai take jin ɓacin ran abin da ke samun uwar ɗakin nata Reza.

A sannu ta watsa ruwa ta fito, cikin rigunan da Hamoudi ya ba ta, ta zura guda ɗaya, saman gadonta ta zauna idanuwanta na sauka kan kwalin, a hankali ta ɗauka tana jujjuya shi, kafin kuma ta buɗe ta zaro dalleliyar wayar.

Ta sani Soupy CE ta ajiye mata, zuciyarta taji ta tsinke da wani irin nauyi, sai yanzu abubuwan da ta yiwa Soupy ke dawowa gareta. Bata taɓa mata rashin kunya me girman ta jiya ba, dole ta bata haƙurin jifanta da iron da ta yi. Numfashi ta sauke tana ƙoƙarin saka layinta da ta gani a gefe.

Da gama haɗa wayar message ya shigo cikinta, a kwance take sai gata ta tashi zaune, ƙarshe ma ta miƙe gabaɗaya a saman gadon, ganin sunan Hamoudi ne kwance saman risalar.

My everything!

Na sani kina cikin kewata a halin yanzu, Ni kaina na kasa runtsawa a dalilinki Hajjatee, na kira ki sau ba adadi ban sameki ba. 

Please ki daure mu haɗu a yau, a inda muka saba haɗuwa. 4:30, Cindrella Park, akwai abubuwa da yawa da nake son faɗa miki. Zan fara roƙanki da ki yafe mini tun a yanzu. 

Homoud

*****

Please ku dinga kankaro mutunci ta hanyar yin comment da liking.

<< Asabe Reza 5Asabe Reza 7 >>

1 thought on “Asabe Reza 6”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×