Skip to content
Part 5 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

A hankali take kwankwasa ƙofar har zuwa lokacin da ta ji takun tafiya an nufo ƙofar.

Gyara fuskarta ta ƙara gyarawa, tana ƙara rungume mazubin abincin da take ɗauke da shi.

Da murmushi kakkaurar kyakkyawar matar take dubanta.

“Oh, Rufaida ba ta gajiya, a daren nan ma sai ta turo ki Haajir ? Ƙara so to.”

Ta buɗa mata hanya zuwa cikin mayawalcin falon, ba tare da ta kula ba ta rufe ƙofar ba.

“Ga wannan ta ce na kawo miki, dambu ne da ta yi ɗazu.”

Ta faɗa bayan ta zauna saman lumtsuma-lumtsuman kujerun.

“Ta kuwa kyauta, ɗazun nan Alhaji ya gama tambayarsa…”

“Ɗaukan plate ki ga in zuba nawa, ƙamshinsa ya gama ta dan yunwa.”

Ta faɗa har yanzu da ƙayataccen murmushin saman fuskarta, akwai alamun tsakaninta da fara’a alaƙa ce dawwamammiya.

Kawo mata ta yi, ta buɗe ta zuba mata yadda ta san zai ishe ta, ta aje shi a gabanta, ta dawo mazauninta hannunta sakale da juna tana lankwasasu akai-akai.

“Ya karatun naku? Fatar dai ana mai da hankali?”

‘Matar nan ta fiye surutu’

Ta faɗa a ƙasan ranta, tana ɗora idanuwanta kan fuskarta, so take ta haɗiye abincin da ta kai bakinta kowa ma ya huta.

Ajiyar zuciya ta sauke ganin ta fara lumshe ido, cikin ƙasa da mintina biyu ta zube saman plate ɗin dambun da wani irin nauyayyan barci.

“You did it Rimo!…”

Ta tsinkayi muryar Reza

“Na ki kason daban yake da na kowa”

Ta faɗa tana bubbuga kafaɗarta.

Ƙayataccen murmushi ta sauke tana duban matar, shekara biyun da ta kwashe tana bibiyar gidan da daddaɗan Dambunta sun ƙare mata da sauƙin da bata taɓa zato ba.

A hankali ta miƙar da matar saman kujerar yadda barcin zai mata daɗi, ta sunkuya daidai saitin kuncinta ta aje mata sumba.

“Sleep well Mrs Nawazuddeen.”

Ta furta tana tahowa daidai saitin Fakriyya.

“Ke ce jagora ai daga nan Rimo, ina ne ɓangaren Alhajin?”

Maa yana sama part ɗinsa, sai dai kamar yadda na faɗa muku ban samu damar gane Codes ɗin buɗe ƙofar falon na sa ba, yanzu ko dosar ƙofar muka yi akwai na’urar da za ta fidda sauti, sautin kuma yana dangana da babban ofishin commissioner of police na ƙasar nan. Sai dai duk wani sirri da muke so yana cikin gurin. Menene abin yi…?”

“Amma kafin ku fara tunanin abin yi, akwai masu gadi guda biyu da ban gansu ba,

akwai mai wanki da mai bawa flowers ruwa. Akwai kuma CCTV jikin kowane labule da step na bene. Akwai mai kula da motsin na’urar, sai dai bansan in da yake ba cikin gidan, na fi dai tunanin yana nan.” ta faɗa tana warware taswirar ginin gidan dake hannunta.

” Idan zai yiwu, shi za a fara samu, yasan duk wani sirri da ke gidan.”

“Gashi nan a hannuna!”

Suka ji muryarta tana ratso falon, dauke da buhun algarara tana mirgino shi da ƙafarta yana ba da wata irin ƙara, ba muryarta kaɗai ke ba da tsoro ba, hatta zubin halittarta abin tsoro ne, basamudiya ce, irin baƙaƙen matan nan masu siffar doya.

Gabadaya ƙamewa suka yi suna mamakin yadda ta shigo team ɗin.

“Good job Fantasia!”

Muryar Reza ta ratsa kunnuwansa.

“Ke kika saka ta?”

Fakriyya ta furta da wani yanayi ɗauke saman fuskarta.

Murmushi ta yi tana zama kan kujerar, ta ɗora ƙafarta ɗaya kan ɗaya tana ƙare musu kallo.

“Ni na saka ta a tun ranar da Rimo ta faɗa mana tarin na’urorin da ke gidan, na sani, kuma kun sani su kaɗai ne babbar matsalar da za mu iya fuskanta. Dan haka na umarci Fantasia da ta kula da duk wani motsin namiji dake gidan, da hakane za a gano aikin da kowanensu ke yi.”

Gashi nan dai ya zo hannu, Hacker Ke Nan, yaron da kafin ya samu aiki cikin gidan nan ya taɓa fasa babban banking ƙasar Zimbabwe.

“Hoooooooo! Kuma Nawazuddeen ya ɗauke shi aiki”

Suka faɗa kusan a tare, fuskarsu ɗauke da ɗumbin mamakin Reza, ba su taɓa tunanin ta wuce dukkan tunaninsu ba.

Kafaɗarta ta ɗaga.

“Koma dai menene zamansa gidan ya mana rana. Ban san yadda za a bawa ƙasurgumin ɗan ta’adda amana ba.”

“A cewarsa dai, mai kama ɓarawo sai ɓarawo, shi ne hikimar zamansa cikin gidan nan”

Fantasia ta faɗa da murmushi saman nunanniyar fuskarta.

“Oh, haka ne fa, kwance shi muga abin da zai iya.”

Kwance buhun ta fara yi, ya fito da wata irin mummunar siffa, tundaga wuyansa aka sakalo ankwar zuwa tsakiyar cinyoyinsa, aka haɗe ta a bayansa, bayan an bankaro hannuwansa aka kulle da kwaɗo.

“God!”

Fakriyya ta furta ganin ɗaurin da aka masa.”

Motsi kawai yake yi da bakinsa yana nuna a cire masa salatif ɗin da aka sa aka liƙe.

Da ƙarfi ta sa hannu ta yage salatif ɗin.

“Madam na yi duk abin da kika sa ni, tun safe na cire duka na’urorin yadda ma ba za a samu kowane record ba, yanzu kuma menene na yi da za a kawo Ni haka?”

Ya faɗa da ƙarfin zuciyar da za a gane ba ƙaramin namiji ba ne da ya saba ganin gwagwarmayar rayuwa.

“Ba ka gama ba, maigidanka nake so ka ka kira min yanzu.”

“God! I can’t wallahi.”

Ba zan taɓa betraying ɗinsa ba irin haka, wannan ma da na yi dan na san ba zai gane ba tunda kun yi alƙawarin za ku jimin ciwon da zai gane har ni kuka taɓa.

“Oh, fatan za ka iya tuna wannan?”

Ta faɗa tana nuna masa hotan cikin wayarta.

Shiru ya yi gumi na sauko masa tundaga lokon hancinsa, ya za ai ya manta mutumin da ya fara saka shi prison a ƙasar Zimbabwe. Sauke kansa ya yi ƙasa yana nadamar abin da ya yi har cikin ruhinsa. A daren jiya sun yi forcing ɗinsa da yarinyarsa, yau kuma da mutumin da ya ƙi jini a dukkan rayuwarsa, wane irin mata ne waɗannan?

“Good! Na san dama ba za ka mantashi ba…”

“Yanzu zaɓi ya rage naka, na san ka gane komai, tunda ka ganshi a wayata ka gama sanin matsayinsa a rayuwata. Na san kuma kana da labarin irin nemanka da suke yi cikin duniyar nan har gobe, zan iya kiransa yanzu ma ku fara gaisawa idan kana tantama,” ta faɗa tana ƙoƙarin latsa lambobinsa.

No! Don’t call him please!”

“Zan yi koma menene, amma karki zama silar mai dani rayuwar dana ƙarar da dukkan dabarata wurin ganin ban koma ma ta ba. “

“Kwance shi!”

Nan da nan ta kwance shi, ya miƙe yana wata irin miƙa.

Kallon Lulu ta yi, take ta juya ta jawo yar jakar cike da maƙudan kuɗi, jefa masa ta yi ya cafe yana kallon Reza fuskarsa ɗauke da tarin tambayoyi.

“Idan ka sauko da Alhajin, kuɗin da ke cikin jakar sun ishe ka tafiya in da ba za a ƙara jin wanzuwarka ba.”

Da sauri ya hau ɗaga kai yana ƙara matse jakar a kirjinsa, a haka ya do shi benen.

“Rimo ke da Lulu kuje ku rufe duk wani part dake gidan nan ta baya, kuyi amfani da spire keys ɗin, ku kuma barsu jikin ƙofar yadda ko da sunsa wani mukullin ta ciki ba zai buɗe ba.”

“Okay Maa.”

Suka amsa a tare.

“Ke kuma Sumoli ɗau wannan sarkar ki ƙara haɗe ta jikin get ɗin, yadda duk jan da za a mata ba za ta buɗu ba.”

Ta faɗa tana mai da idanuwanta kan Fakriyya da Fantasia dake tsaye.

“KU Zo ku kuma mu hau saman, ban san yadda zuciyata za ta gasgata Hacker ba zai iya betraying ɗinmu ba.”

Da sauri suka gyaɗa mata kai suna sauke takunsu kan kowane takunta.

Nesa da ƙofar gilas ɗin suka tsaya, suna iya hango abin da ke faruwa cikin ɗakin.

“Ya Rabb! Bantaɓa ganin mutum mai kyawunsa a dukkan rayuwata ba.”

Fakriyya ta faɗa da wani irin yanayi.

Harara Reza ta mata, tana ganin yadda take ƙoƙarin rasa nutsuwarta.

” To Yar Bunsuru, ki nutsu mu yi abin da ya kawo mu.”

A daidai lokacin suka ga dosowar Alhajin jikin ƙofar, suna ganin zai fito suka ƙara lafewa jin yana magana.

“To muje dai na ga ɗakin naka, yau ciwan kai duk ya hanani sukuni, ina ga gobe dole In leƙa Russia a duba…”

Kalmomin suka watse cikin bakinsa ganin tsinin bindiga saman goshinsa.

Kallonta yake da matsiyatan kayan da ke jikinta, yana kuma kallon Hacker da rashin gaskiyarsa ya gama bayyana zahiri saman fuskarsa.

“Ka yafe min, ba da san raina na ci amanarka ba.”

Ya faɗa yana mai ɓacewa cikin idanuwansa.

“Ya tafi, ba sai kana bin shi da kallo ba, ba zai taɓa dawowa ba, muje ka ba mu abin da muke so, babu abin da za mu taɓa na lafiyarka sai idan ka mana taurin kai.”

Ta faɗa a tausashe tana ingiza keyarsa zuwa cikin ɗakin.

“Hasbunallahu wa na’imal wakeel! Me kuke so gare ni, ina… Ina Far…”

“Karka damu da ita, matarka tana can mun sata daddaɗan barcin da za ta kwana biyu tana yi.”

Zuwa yanzu gumi ya gama jiƙa gaban rigarsa, ba yau ya fara ganin tashin hankula a rayuwarsa ba, sai dai wannan ya fita daban da kowanne, mata ne a gabansa tsirara, tsirara mana tunda daga su sai pant da bra da wata doguwar Safa da ta rufe cinyoyinsu, sai baƙin kyallen da suka rufe fuskokinsu da shi.

“Karka tsaya dogon tunani, ka bamu kalmomin sirrin da ake buɗe babbar ma’ajiyarka da ke cikin kamfaninka na Samsung. Ka kuma ba mu takaddun hannun jarinka na KIA MOTORS. Shi ke nan, ba wani abun tashin hankali ba ne da za ka dinga jiƙewa da zufa.

“Waya turo ku? Wannan abu sirri na ne da babu wanda ya sani idan ka ɗauke yarona…”

“Da kuma wa?”

Ta faɗa tana buga masa karshen bindigarta saman goshinsa.

“Ya isa Ree.”

Ta furta tana ƙarasowa gabansa, hannunta ta ɗora saman haɓarsa tana ɗagota zuwa fuskarta.

“Ina girmama duk wani da ya haura shekarun ubana, idan ba ka so na nuna maka ainihin kalata, to ka fiddo da dukkan abin da muka umarceta, taurin kanka daidai yake da ganin kan waccar matar taka a gabanka…”

“Ree, shige ya gwada miki inda komai yake, Ni kuma bari na ƙarasa bincika gidan, ban yadda da yawansu ba.

Ta faɗa tana wucewa wani part da take hange can gefe.

Murmushi ta saki tana kallon cikin idanuwansa, a saitin kunnensa ta duƙa yadda yake hango komai da ke cikin bra ɗin ta.

“Muje ka fara sauke min haƙƙin matarka na yau. Na sani kana takaicin kwanan da za ka yi yau ba tare da ɗuminta ba, karka damu, ina da duk abin da kake buƙata da zai gamsar da kai, ka manta ma ka taɓa sanin wata mace bayan Ni.”

Ya ji kalmomin sun ruga cikin kunnuwansa, suna zarcewa can cikin zuciyarsa da ke yanke ƙauna da dukkan rayuwar ta duniya.

kallonta yake yana neman tsari da sharrinta, ko da yake matashi bai taɓa sha’awar zina ba, balle yanzu da yake dattijo. Hawaye ya ji suna sauko masa saman gemunsa da furfura ta fara ratsawa.

Tunda yake, ba a taɓa cin mutuncinsa irin wannan ranar ba, bai taɓa nadamar kasancewarsa mai arziƙi irin daren nan ba, da yarinya ƙarama, yar cikinsa ke neman haiƙe masa.

“Zan ba ki ko menene, amma karki sani aikata zina dan girman Allah, dattijo ne Ni mai tarin iyali. Ki ji tsoron Allah.”

Murmushi ke bayyana saman laɓɓanta, wani irin yanayi take ji a dukkan buɗe bakinsa da zai yi. Ba ta jin za ta iya barin wannan romon da take hange, ba ma wannan ba, akwai wani zaunannen abu cikin zuciyarta da take burin aiwatar shi. Kaɗa masa kai kawai ta yi tana ingiza keyarsa.

Da baki yake nuna mata inda komai yake tana ɗaukowa kasancewar sun ɗaure hannuwansa.

Kallonsa take bayan sun ƙare.

A hankali kuma ta hankaɗashi saman faffaɗan gadon nasa, saman gadon ta bi shi, hannayenta saman fuskarsa tana zagayawa, hawayen da yake yi ta dangwalo ta lashe a bakinta, idanunta a lumshe cikin bakin ƙyallen, a haka ta fara zare dukkan suturar jikinsa, tana mai haiƙe masa.

Can ɓangaren Reza zuciyarta ke ingizata akwai wani abu cikin part ɗin da take hange, a hankali ta ƙarasa tana mai murɗa ƙofar, ga mamakinta a buɗe take da wani irin ƙamshi da ke tashi, shiga ta yi tana jinjina kyawun gurin, cusa kai take sake yi ƙamshin turaren da take ji na kai zuciyarta wani nisantaccen yanayi.

A haka ta ƙarasa jikin ƙofar banɗakin da ƙamshin ya fi yawa, ƙofar ta buɗe da wata irin sassanyar iskar da ta ɗage abin da ta rufe fuskarta, ta yi tozali da mutumin da ya dakatar da bugun zuciyarta na wasu daƙiƙai, shi ma kallonta yake, yana jin Hello ɗin da ake ta ambata ta cikin wayar da ke kunnensa, amma ya gaza magana, wani abu ke dukan zuciyarsa da ƙarfin da bai san ya zai kwatanta ba, wani abu ke ta da masa abin da ya kwashe shekaru yana jinyarsa, abin da ya kwashe shekaru yana mafarkin zai ƙara wanzuwa gare shi. Abin da ya kwashe shekaru masu tarin yawa yana nema, Yau gashi gabansa a inda bai taɓa za ta ba, a siffar da ba zai taɓa zama gare shi ba ko da cikin mafarkinsa.

“Reza! Please taho mu tafi, bantaɓa ganin Yar Akuya irin Ree ba, sai da ta haiƙewa Dattijon nan, yana can baƙin ciki ya sumar da shi…”

A haka Fantasia ta zo tana jan hannuwanta, tana kallonsa sa’adda da yake ɓacewa cikin idanuwanta.

Nutsuwarta da dukkan tunaninta sunyi nisan da ba ta jin abin da Fantasia ke faɗi.

*****

Comment da liking dinku shi ne sakayyar alherinku gare ni.

<< Asabe Reza 4Asabe Reza 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.