Ta yi saurin hankade sa kafin kafar ta sauka sai da ya yi tuntube saura kiris ya fadi.
Cikin Zafin rai ya dago yana, "Hee U Kina cikin hankalinki kuwa?" Ya ƙarasa maganar yana falla mata mari.
Tsayawa tayi kawai tana binsa da kallo na yan seconds kafin ta fadi kasa daidai inda Carpet din yake tana wani irin kurari.
Tsaki ya yi ya ,ya tsallaketa ya wuce, Uwar Soro ta karasa gareta da sauri tana, "Ka san dai yarinyar nan ba isasshen lafiya gareta ba amman shi ne zaka daketa? Allah ya kyauta."
Ta karasa maganar tana kokarin janye. . .