Skip to content
Part 13 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Ta yi saurin hankade sa kafin kafar ta sauka sai da ya yi tuntube saura kiris ya fadi.

Cikin Zafin rai ya dago yana, “Hee U Kina cikin hankalinki kuwa?” Ya ƙarasa maganar yana falla mata mari.

Tsayawa tayi kawai tana binsa da kallo na yan seconds kafin ta fadi kasa daidai inda Carpet din yake tana wani irin kurari.

Tsaki ya yi ya ,ya tsallaketa ya wuce, Uwar Soro ta karasa gareta da sauri tana, “Ka san dai yarinyar nan ba isasshen lafiya gareta ba amman shi ne zaka daketa? Allah ya kyauta.”

Ta karasa maganar tana kokarin janye Gaaji agun.

Wani irin nauyi ta mata tamkar dutse ko alamar motsi ba ta yi wani irin gigitaccen barci ya dauketa.

Zama ya yi cikin jeran kumbon dake farfajiyar wajen yana danna wayarsa hankali kwance bai ma san meke wakana ba.

Sai da Gaaji ta dauki kusan minti goma kafin ta farfado bayan Uwar Soro ta tofa mata addu’o’i,

Tana tashi ta kalli Uwar Soro murya a sanyaye ta ce, “Baba Kinga muguncen ya mareni a mafarki na ko? Sai na kuma ramawa kuma tunda shi ba zai daina Mugunta ba har cikin barci ms bina yake.”

Uwar Soro na dagata ta ce, “Na ji dai Yanzu kizo mu koma daki,ki sha magani ki ci abinci ki huta.”

Gaaji ta ce, “Tom amman Aradun Allah sai na rama tunda shi baya jin magana.”

Duk da cewa Jikinta ba kwari amman hakan bai hanata soki burutsun magana ba.

Suna shigewa kuwa sai ga Jakadiya na leken kofar Part din Adeel ta gefe, Khalesa da Hajiya Rabi ma sun fito domin tabbatar da aikinsu, haka ma Fulani, dukkaninsu ba wanda ya ga kowa amman sun yi matukar mamakin ganin sa da suka yi zaune a gun.

Khalesa ta ce, “Mom ki kalla , a yanzu ya kamata ace duk inda yake ya nemine yazo inda nake tare da neman alfarmar soyayyata.”

Hajiya Rabi ta ce, ” Tabbas ayi wadda za ayi ramamme ya zagi maye amman kin san miye ai sai an gwada akan san Na kwarai kinsan wannan isa da gadarar tasa ta jinin sarauta zata iya sawa ya danne ko da kuwa zuciyarsa na ƙuna, yanzu ki je gun sa mu ga reaction din da zai bada kada muyi saurin yanke hukunci.”

Khalesa ta ce, “tabbas kuwa haka za ayi.”

Fulani Kilishi na gefe tana saƙawa a zuciyarta, “lallai anyi ba ayi ba rufe kofa da barawo, ba zai saɓu ba, hakan ba ma zai taɓa sabuwa ba, ramin zaki ai ba wajen wasan yara bane.”

Ta karasa maganar tana kwafa.

Jakadaya kuwa rike haɓa ta yi tana, “ayi ma gani koda yake abun da kamar wuya gurguwa da auren nesa, yanzu za a fara wasan.”

Fitowar Khalesa tana wata irin tafiya cikin rangwadane dukkanin su ya dawo masu da hankalinsu kansu.

Karasawa tayi kusa da shi tana fadin, “zan iya zama nima?”

Girgiza mata kai ya yi a hankali ba tare da ya dago bare ya kalleta ba.

Ta zauna shiru bai ce mata komai ba ya ci gaba da danna wayarsa.

Ganin shirun bana kare bane ta ce, “Wai ba za ka kalleni bane? Ka ajiye wayar nan muyi hira mana Please.” Ta karasa maganar cikin wata irin Muryar kissa.

Adeel bai ce mata komai ba.

Ta kara fadin, “kwalliya fa nayi ma, ba za ka kalla ka ce mun nayi kyau ba? Don kai kadai nayi.” tana kara karyar da muryarta yadda zata iya canja tunanin kowanni irin Ɗa namiji.

Adeel ya dago ya kalleta nan take kuma ya kau da kai yana matsar da jikinsa ga inda take ya ce, “Khaleesa Please.

Sai kuma ya yi shiru.

Kara matsawa inda yake tayi, nan take yaji mararsa na shirin kullewa, da sauri ya tashi ya barta agun.

Dafa kai Khaleesa tayi tana fadin, “Kenan duk abun da muka yi ya zama banza? Ta ya ma hakan zai faru akwai matsala.”

Wata irin Dariyar mugunta Fulani ta yi ta na, “Maddallah yanzu wasan ya fara abubuwa zasu tafi yadda nake so, duk da dai basu tafi a yadda na tsara ba.” Ta ƙarasa maganar tana koma cikin bangarenta.

Jakadiya ta saki wani munafukin murmushi, “makunshin gishiri ya fi gishiri zaƙi.” Tana fada ta koma cikin masarauta.

Wani takaici ne ya turnike Hajiya Rabi Khaleesa na zuwa ta fisgeta suka wuce bangarensu.

Adeel kuwa yana zuwa part dinsa ya kwanta kan gado ban da mutsu-mutsu babu abun da yake yana rike mararsa, ya rasa dalilin da yasa babu dama wata mace ta raɓesa sai ya shiga cikin wani yanayi duk da cewa ba iya aiwatarwan yake ba amman yana matukar shan wuya kafin ya dawo daidai hayyacinsa.

Na kwana biyun nan kam ya masa tsanani fiye da yadda ya saba ji tunda ya kusanci Gaaji, Dafa kansa ya yi yadda yake jin mararsa da cikin sa na masa zillimi, duk kokarinsa ga ganin ya daure gagara ya yi a karshe ya sume kan gadon.

Shamaki ya shiga sanar da shi cewa an kammala masa abincinsa kenan ya tarar da shi kwance sumamme.

A kidimance ya fito yana sanar da Uwar Soro.

Ita ma tana jin hakan ta karasa part dinsa da hanzari.

Tana ganinsa kwance,tuni ta kira Adnan ta sanar da shi.

Mintuna kadan sai ga Adnan da Dr Jawad.

Dubasa ya shiga yi ya basa taimakon gaggawa cikin sa’a kuwa ya farfaɗo.

Adnan ya ce, “Me ya sameka ne? Baka da lafiya amman ba za ka sanar akira Doctor ko muje asibiti ba?”

Adeel ya ce, “Nothing, I’m Fine.”

Ya fada yana gyara zama.

Uwar Soro ta ce, “Sannu amman gaskiya ana lura shiyasa ban so shamaki yana nisa da kai amman ka ki ji.”

Dr Jawad ya yi gyaram murya yana fadin, “Ina so in danyi magana da shi Don Allah in ba matsala.”

Adnan ya ce, “Nop za ka iya bara mu ba ku waje.”

Dukansu suka fita, suna fita Dr Jawad ya zauna kusa Da Adeel ya ce, “ka fi kowa sanin maganin matsalarka ba sai na fada ba, kuma nasan kana da damar magance ta ta kowanni fanni amman meyasa kake son jawa kanka Matsala?”

Prince Adeel ya yi shiru sai can kuma ya ce, “Matsala? I think ba na da wani problem ai.” Ya fada a gajarce yana janyo system dinsa.

Dr Jawad ya yi Murmushi yana fadin, “Ka bar batawa kanka lokaci,a yanzu ba bu abun da kake da bukata da ya zarce mace a kusa da kai, wanda hakan kuma zai iya zame maka illa babba, kasancewata likita na musamman dake lura da lafiyarka in nace zanyi shiru ba makawa na ci amanar Mai Martaba,na san a tunaninka ba ka da buƙatar matsayin mata da cewa baka da lokacin yin hakan saɓanin abubuwan da ke gabanka na rayuwa, ka kai minzalin da zaka yi aure tuntuni koma wacece kuma yar wane ne indai ba zaka fito da mafitar wannan matsalar taka ba ina sheda maka cewa ina daf da sanar da Mai Martaba Sarkin BENONI.”

Sai a lokacin Adeel ya dago kai, “Bana da bukatar sanin kowa, kamar yadda ka fada na san matsalata kuma ni zan yi mata magana da kaina, ka da wannan maganar ta je ko bakin Adnan bare wasu, let it be secret.”

Dr Jawad ya ce, “Alright amman ka tabbatar da cewa ka nemawa kanka mafita cikin gaggawa rashin hakan zai iya sawa ka jiyo abun da baka tsammani.”

Dr Jawad na gama magana ya fice daga dakin.

Adnan da Uwar Soro suna shiga Gaaji na kwance ta ce, “Kambun bala’i, za ayi zarfan masifa da bala’i wane ne ya ji maka ciwo a goshi?”

Uwar Soro ta ce, “Oh Gaaji rigima ba lafiyan ma jiki ba zai mutu ba ko?”

Adnan ya karasa ya zauna gefen inda take ya ce, “tana dai cin abinci kuwa?”

Uwar Soro ta ce, “a a fa dai kam ba sosai ba acin abincinta ko kwatansa batayi ba da kyar ta sha tea kadan dazu ko rabin kofi bai kai ba sauran su Bread da abincin ma kuwa ko dandanasu batai ba.”

Adnan ya dauki ba na na yana barewa ya ce, “Oyaa to aiko yanzu dole ki ci wannan ko in miki dure.”

Gaaji ta taɓune ba ki, “wato ba za ka fada mun wane ne ya fasa ma koshi ya yi kullu ba ko? An wani sa farin abu an lullube, na ma gane Aradun Allah yau sai na rama maka.” Ta karasa maganar tana tashi ta za ta fita.

Adnan ya ce, “ina za ki? Dawo nan karki fita fa.”

Fuu Gaaji ta ja kafa tana, “daukan fansa, daukan fansa zanje yi tunda aka tabamun kai, daman dazu ya mareni a mafarki na barsa Yanzu kam sai na dau mana fansa.”

Fita tayi tana hamamin masifarta tana zuwa ta tura kofar da sauri ta shige dakin, Adeel ya juya baya kafafunsa tankwashe ji ya yi kawai an duma masa dundu.

Juyowam da zaiyi ya ga Gaaji tsaye ta riƙe kwankwaso tana murgada baki,su kansu idanunta juyawa suke ta ce, “Waya ce ka taɓamun abokina waya ce ka ji masa ciwo? Don ka ga dazu ka mareni a mafarki na barka ko? To aradun Allah ramarka ta kiyayi ta shuri zan faffasa maka kai,kuma daga yau kar ka kara taɓa mun shi , sonsa nake aurenmu zamuyi mu haihu abun mu kana ji ko?”

Tana cikin sambatu ta rufe ido tsabar bala’i ji tayi kawai ya cafketa yana kokarin kaita gado.

Sai a lokacin Gaaji ta tuna da abun da ya mata waccen ranar.

Ihu ta fara kwallarawa tana, “Na shiga ukuna na mutu na lalace wallahi wasa nake ba daukan fansa nazo yi ba, don Allah karka ce zaka kara samun wannan abun.”

Ta fara hulli da kafafu har sai da ta tusa masa kafa baki.

“Ka bar ni in tafi nace ma ka barni in tafi mugu, ni ba abunda nazo ma kawai gaishe ka Babata tace inzo inyi ka mun rai kar ka kasheni.” Tuni ta fara wani irin kuka mai tsuma zuciya fuskata duk ta caɓe cikin lokaci kadan.

Saketa ya yi, da gudu ta sauka ta yi hanyar fita, tana fita ta samo wani mummulan dutse,ta kara komawa dakin cikin sanɗa sai da ta tabbatar suna da tazara mai yawa kafin ta ce, “kai mugu mai jelar saniya ,idanun mage da duwawu kamar na bunsuru.”

Juyowan da Adeel zaiyi kawai sai dutse Bam a goshinsa, tana buga masa kafa mai na ci ban baki ba, adari ta zura a guje ta shige Bayan Adnan tana haki.

Uwar Soro ta kalleta cike da mamaki fuska duk caɓe da majina da hawaye ta ce, “ke kam lafiyanki kuwa? Ince dai ba bari kika yi aka ganki ba.”

Tana numfarfashi ta ce, “Fansa na daukan… Mana…ni da…ni da… Abo…

Kafin ta karasa sai ga Adeel ya shigo goshi jini na kwarara kamar ruwa, hannunsa dauke da belt,yanayin yadda fuskarsa ke a fusace Uwar soro da Adnan su kansu sai da suka razana.

Gaaji kankame Adnan tana, “don Allah karka bari ya taba ni, dukana zaiyi ya mun mugun…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Auren Wata Bakwai 12Auren Wata Bakwai 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×