Skip to content
Part 14 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

A sulale ta je zata shige Ganin Shamaki a kofar Part din zaune yasa ta tsayawa tana sosa ƙeya cikin sauri ta tura wukar jikin sket dinta tana daura hannu ɗaya akai.

Durkusa mata ya yi yana fadin, “Ranki Ya Dade Gimbiya barka da fitowa.”

Gaaji ta bude baki tana sake hannun da ke kanta, “Ji mun wani sabon sana be kiran sallah da usur, wa ice ma ni sunana Gimbiya? Ahir dinka ina hwada ma kuma ni ba Ranki ya dade bane, kanka ka fadawa don ni daman mutuwa ba yanzu ba sai ka rigani ehee kana nan wani kato da kai da wani faffaɗan kirjinka kamar fukafukin baru, ni nan sunana Zainabu Gaaji, Gaajin Baffa Yar Gata Jiki duk Nonon Shanu.”

Shamaki kasan na ƙasa ba tare da ya dago ba yake sauraren duk wa inna suki burutsun Gaajin , cikin Nutsuwa ya ce, “Neman gafara nake Ranki Ya Dade.”

Tsaki tayi tana cuna baki, “Aradun Allah na ce ma ni ba Ranki ya dade bace Gaajin Baffa mai abun mamaki jiki duk Nonon shanu zakana cewa haka ake mun kirari a rugarmu kuma ni matsa mun shige ciki zan dauko abuna ne.”

Ta karasa maganar tana shigewa.

A hankali ta haura har saman, Prince Adeel kwance yana barci cikin Nutsuwa yanayin yadda ya kwanta kadai ya isa bayyanar da cewa ya jima bai samu barci kaman hakan ba, wani sanyi mai dadi na Ac na ratsa ilahirin jikinsa, kamar yadda ya saba daga shi sai gajeran wando babu ko singlet a jikinsa.

Gashin kirjinsa fal kwance yana shaki mai daukan ido, haka ma fuskarsa tamkar dukkanin su suna barci, duk da kasancewar barci yake amman kallo ɗaya za ayi masa a tabbatar da cewa cikakken namijine da ya amsa sunan maza mai dauke da izza gami da ilhama kwance.

Kallonsa tayi tana ƙasa-ƙasa da murya, “Alhmdu Lillah Allah na gode maka yana barci a hankali zanyi har in yanke ma in fice bai sani ba, da safe inya tashi bai gani ba kila ma ya aza mage ce ta cinye, ni kuma hikenan na huta da muguntar nan tasa, ysn kuma inna cire ma zuwa zanyi in jefa masa cikin bayinsa gun kashi shikenan in yaje kashi yaci karo da shi.”

Karasa maganar tayi tana ciro wukar da cikin sket dinta.

Ta washe baki tana, “Yanzu zan zare masa wannan nafkin din nasa kafin a shiga aiki, hooo ni Gaaji shugabar masu daukan fansa, hmm hmm mutum dani yake ai.”

Ta karasa maganar tana karasawa garesa, hannu tasa tana kokarin zame masa wandon da ke jikinsa, ja take amman tamkar gawa bai motsa ba kuma wandon bai ciru ba.

Ta gefe ya bude idanunsa a zuciyarsa yana fadin, “Zan ga gudun rawar haukar yarinyar nan yau dai.” Ya kara rufe idonsa tamkar yana barcin.

Ganin ta gagajara ja hakan yasata tayi tsalle ta dire masa a jiki tana fisgar wandon da hakoranta, “Yau dai kam kwanan wannan jelar ya kare, sai lahira kije can ko kya hadu da gamonki tunda ke mugunta ake da ke, kuma ma Allah baya son masu mugunta, Shiyasa ma kike muni tab.”

Ganin hakorinta ya gagara fisgo mata wandone kawai ta dauko wukar ta yanka.

“Heeeeee Ho ho ni Gaajin Baffa mai abun mamaki daukan fansa ba wasa, Ai daukan fansa ma wajibi ne ga wanda aka zalunta.”

Haka ta yanke masa wando, sake jikinsa yayi yana bi duk yadda tayi da shi, a tunaninta karfinta ke aiki ta tura shi gefe yadda zai juyo tana kallonsa.

Wata Dariyar ƙeta ta fara tana, ” shikenan kuma daga yau an rabu da wanga abu, Allah sarki har na fara jin tausayin ka aradun Allah.” Ta karasa maganar tana kara janye wandon.

Karasa yi masa tsirara tayi tas haihuwar uwa da uba.

Tana gama zamewa ta sa hannu tana rufe ido, “wai waii tab wayaga samudawa, wannan saidai idona rufe ma in yanketa don bazan iya ci gaba da gani ba.”

Rufe idonta tayi gam, tasa hannunta ta damko dayan hannun wukar ma ta daura kai.

Ji tayi dukka hannayen nata an rikesu gam.

Take Idonta ya yi zaro zaro, ana iya hango jijiyoyin da ke wuyanta tsabar tsoro, wani irin yawon razana ta hadiye nan take zufa ma ta keto mata, jiki na bari , murya na rawa ta ce, “Na higa tara na lalashe, mage na gani zata ci ma jelarka na zo yankawa.”

Adeel ya ce, “ke ce magen kenan ko? Yaushe zaki bar shiga gonata ne wai?”

Ya karasa maganar yana yin shiru tare da kare mata kallo mussaman yadda jijiyon jikinta ke yawo tsabar tsoro kafin ya ci gaba da magana

“Saboda har yanzu ban miki hukuncin da ya shiga jikinki mai kyau ba ko?”

Jiki na rawa ta ce, “Na tuba nikam ba ma zan kara zuwa nan ba ka yafe mun.”

ADEEL ya ce, “Oya bude idanunki.”

A tsorace ta bude ido, tana budewa idonta ya sauka kan jikinsa da sauri ta kawar da kai kamar wacce aka tsikarawa Allura.

“This is the first and the last warning, ka da in kara ganin wa innan kafafun naki masu kama da sauro a Part dinnan, in ba haka ba sai na babbalasu na jefar a bola.”

Ita dai gabadaya a tsorace take har lokacin jikinta rawa yake, bata san ma lokacin da ta sake wukar dake hannunta.

Cikin dagun murya ya ce, “Oya Get Out.” Kara firgita tayi tana gyara Tsayuwa kanta na kasa kafafunta suna kokarin kasa riketa batasan me yace ba.

A takaice ya kara fadin, “fice mun da gani.”

Tuni taja kafarta cikin sauri tana harhardewa zata fice kenan ya ce, “Dawo kizo nan.”

Ya tashi ya dauko wani gajaran wandon a Wadrope sannan ya zauna yana mika mata.

Karba tayi jiki na rawa.

Gaaji bata da burin da ya zarce ta bar wannan dakin a yanzu.

Sai da ya yi shiru tsawon dakiku kafin ya ce, “Bake kika cire wancen kika yaga ba?”

Ta girgiza kai alamar eh.

Ya ce , “Oya maidamun da abuna.”

Yana daga zaune ya daga kafafunsa Gaaji jiki na kara karkarwa ta zura kafafun. Sannan ya kwanta haka ta rufe ido ta ja masa wandon har kasa.

Tana gamawa tayi hanyar fita da sauri.

Ya kara katseta, “ke!.”

Ta tsaya sai ya yi shiru kafin ya ce, “kizo ki dau wukarki ki tafi da ita.”

Jiki a mace ta koma ta dauka, tana dauka ta fice kamar iska.

Shamaki na ganin ta ya ce, “Barkanki da fitowa Ranki Ya Dade.”

Ina Gaaji ko kallonsa batai ba, bare ta kulasa aguje ta koma Part Uwar Soro , tana shiga tayi dakinta ta shige cikin bargo.

Gaaji na tafiya ADEEL ya kasa samun sukuni tsananin yadda mararsa ke yi masa,ga shi ya yi alkawarin ba zai kara kokarin kusantar Gaaji ba, don ya tabbatar yana kara attempting hakan zata iya fada aji mussaman yadda bakinta ke zuba kamar jinin al’ada.

Kasa barci ya yi karfi da ya ji tun yana juyi har ya gaji ya hakura ya tashi yana nafiloli.

*****

Tunda ta shige cikin bargo tana rufe ido ba wanda idonta ke yi mata tozali da shi sai Adeel tsirara, wani zubin ma har firgita take, a karshe gajiya tayi ta fita a bargon tana jigina jikin Gadon,ba tare da ta ankare ba , wani barcin ya kara awun gaba da ita,wata irin kara da ta sake Saida Uwar soro ta fito daga bed room dinta cikin sauri tana, “Ya ya dai? Lafiya? Me ya faru?” Ta kara maganar tana shafa mata bayani.

Gaaji ta ce, “Yareema ne zai samun je…Sai kuma tayi shiru.

Uwar Soro ta ce, “Yareema ya miki me? Fada mun.”

Cikin sauri ta ce, “Mafarki nayi ya kara marina.”

Uwar Soro ta yi Murmushi tana, “Ke banda abunki ai mafarki ba gaskiya bane,ba na koya miki addu’ar da zaki dunga yi kafin ki kwanta ba?”

Gaaji ta girgiza kai.

“Yawwa Zainabuna to ita zaki dunga yi,ba Yareema ba,ko shedan ma bai isa ya kara marinki cikin barci ba kiyi ki kwanta Kinji.” Uwar Soro ta karasa maganar tana fita daga dakin.

Tana fita Gaaji ta rike baki tana, “Hmm Allah ya taimakeni da yanzu na fada mata yasamun jelarsa ranar da mugun cen ya kashe mun Baffana, kuma fa tsabar ya rainani wai ni yake cewa kafafuna masu kama da sauro ai gwamda ma ni banda abu me muni jikina kamar na shi, mugu mai kan gwanda kawai ni daga yau ma na daina shiga Gunsa ba zan kara ba.”

Ta gyara kwanciya tana shigewa bargo.

zuwa Gaaji ya zam karshen Barcin Adeel koda ya yi sallolin kasa komawa barci ya yi, a karshe ma sai System dinsa ya dauka ya fara wani bincike.

Tafiyar Gaaji ke da wuya JAKADIYA ta fara safarar jele tsakanin Part din Uwar Soro da na Adeel.

Har aranta tana jin cewa akwai wani boyayyen abu da Yareema da Uwar goyonsa ke shiryawa a ɓoye ba tare da sanin kowa ba, dadin daɗawa ma ciwon da ke goshinsa domin wannan bana bigewa bane,dole akwai wani abu a ɓoye.

Zaryanta ta gama yi,bata ga komai ba kuma bata ga alamar komai ba, hakan yasa ta komawa bangarensu da kudirin koma mene ne sai ta bankado kowa ya sani a Masarautar.

Washegari.

Uwar Soro na dawowa daga cikin Fada ta nufi bangaren Adeel.

Zaune yake a parlour,bayan tayi sallama ta nemi waje ta zauna, “Na zo ne mu tattauna, shin kasan cewa da gaske batun Auren Khalesa da kai ya tashi kuwa? Yanzu haka da naje Fada an tattauna yadda hakan zai kasance ne,shin ka amince baka da matsala da hakan ne ko yaya?”

Shiru Adeel ya yi, ya ma rasa abun furtawa.

Uwar Soro ta gyara zama sannan ta ci gaba da fadin, “Kodayake ma aikin gama ya riga ya gama tunda jiya baka musanta hakan gaban Mai Martaba ba, Allah ya tabbatar da alkairi, ka fara shiri.”

Tana fada ta fice daga Dakin.

Fitarta keda wuya ta ci karo da Jakadiya , “Maddallah da Uwar Goyon Yareema har an fara shirye-shiryen bikin kenan? Daman yanzu gunki na nufa ai inji me da me ake da bukata mu tanadar.”

Uwar Soro ta ce, “Ehto a halin yanzu dai bama da buƙatar komai.”

Jakadiya ta ce, “Okay amman ba zaiyi ace bakwa bukatar komai ba, dole akwai bukatar mu tattauna ai inaga muje ciki dai tukun.”

Uwar Soro ta ce, “Oh to shikenan Bismillah.”

Jakadiya ta ce, “Amman dai yau ba aljanun a kusa ko?”

Murmushi Uwar Soro tayi,ta ce, “Aljanu? Ranar ma ke kadai kika gansu.”

Jakadiya na leƙe-leƙe da waige-waige ta bi Uwar Soro a hankali tamkar ankama wata barauniya.

Suna shiga ,Gaaji na fitowa daga dakinta kenan ta sha farar hoda da kwalli duk ta gama barbazawa a fuskarta ga gashi carko-carko, Kayan Fulaninta farare tasa, gabadayanta yadda tai yanayin shigar in ba wanda ya mata kyakkyawan sani ba, babu shakka mutum zai iya tsurewa, suna haɗa ido da Jakadiya sai tuni jiki ya fara rawa ta saki fitsari, kankame Uwar Soro tayi cikin sarƙaƙƙiyar murya tana nuna Gaaji ta cee “kin….g…gaanta..ko…gata nan…sune wallahi….na…na…shiga ukuna….”

Ita ko Gaaji an samu abun nema tuntsire wa da dariya tayi tana wani irin gil-gilma idanu, nan take Asalin Aljanunta suka bayyana cikin wata irin razananniyar murya ta ce, “Mu kike nunawa da hannu karamar munafuka? Na ce mu kike nunawa da hannu?”

Kan kace me Jakadiya taji wani irin gigitacciyar mari ya sauka a fuskarta dukka bangare biyu.

Kare ƙankame Uwar Soro tayi tana sakin wata irin tusa mai bala’in kara tsabar razana ga kafafunta na rawa.

Da Ido Uwar Soro ta fara yiwa Gaaji magana, ina basu san tana yi ba ko da ido sunki yarda su hada da ita.

Wata irin tsawa suka yiwa Jakadiya nan take ta kame kam tana, “na tuba Don Allah na tuba kumun rai, Wa innahu sulaimanu wa innahu Bismillahi ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba, na ku yi mun rai.”

Cikin dagun murya suka ce, “ki fice daga nan kuma daga yau kar mu kara ganin kin dauko wa’innan kafafun naki masu kama da falwaya.”

Kan kace miye JAKADIYA ta fice a guje, banda ruwa ba abun da ke fita a jikinta tana tafiya tana sakin gudawa.

Tana fita Gaaji ta fadi kasa warwas.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Auren Wata Bakwai 13Auren Wata Bakwai 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×