Skip to content
Part 12 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Prince Adeel ya yi gefe yana fadin, “Munah kina cikin hankalin ki kuwa? Na fada miki duk bukata ta ba zan iya biyanta da ke ba, i can’t, ki fita kawai kafin in kira miki securities.”

Kuka ta fara ta ce, “Me yasa zaka mun haka? Me yasa sai da ka gama tada mun da sha’awata zaka ce aa? Shin kasan yadda nake ji kuwa? Wannan ai Mugunta ne, this is not fear, kana so ka ja mun illa, kasan shekaru nawa nayi ina jiran wannan ranar kuwa? Shin ka ma san irin shirin da nayiwa wannan ranar kuwa? Kar ka mun haka, Don Allah ka taimaka mun, ina taraiya da maza daban-daban kasashe daban-daban amman babu wanda zuciyata ke da muradi sama da kai, kai nake da bukata kai nake so wallahi Allah ni in zaka aureni ma ka maidani Nigeria na aminci zan daina dukkanin abun da nake inma kyamata kake Don Allah ka ceci rayuwata ka amince dani.” Ta kara sa maganar cikin raunanniyar murya tana durkusawa gabansa ban da hawaye ba abunda ke fita daga idanunta.

Prince Adeel dagowa ya yi da jajayen idanunsa da suka kara fitowa fili ya ce, “Munah Am so Sorry, ban san hakan zai kasance ba, a tunina zan iya aikata koma mene ne ganin na samu biyan buƙatar zuciya ta amman kuma raina baya taba amincewa da hakan na tabbatar da cewa ba zan taba iya hakan ba duk sona da yi, kiyi hakuri ki ga kudi nan ki dauka ki tafi kawai.”

Rike masa kafafu ta yi ta ce, “Na ji na yarda zan tafi, zan kuma danne dukkan abun da ke taso mun a yanzu amman kamun alkawarin cewa zaka aure ni.”

“Aure? .” Ya yi shiru for some seconds kafin ya ce, “Ba matsala kije yanzu zamu yi magana inna samu nutsuwa.”

Haka ta tashi ta maida kayanta ba don ta so ba har taje kofa zata fita ta ce, “Kar ka manta Please, zan yi zaman jiranka har karshen rayuwata.”

Bai ce mata komai ba har ta tafi.

Wanka ya yi, kafin ya kwanta sai da ya dunga nafiloli da addu’o’i yana hamdala da Ubangiji da yake karesa daga sharrin zuciya aduk da lokacin da kwadaita masa aikata zina.

Sai wajen karfe uku kafin ya kwanta, yana kwanciya kuwa barci ya kwashesa.

“Kai an Ishka mai katuwar Jela ka tashi ko in kara marinka kuma Aradun Allah har jelar nan da ka turamun jikina sai na mareta mugu mai kan agwagwa, ni to ma ina ruwana da kai, kai kana ishkanci da mugunta Abokina ba ya yi shi kam, ba za ka tashi ba ko? In mareka ka kara maidani wancen dakin duhun, ji indon shi wani abun tsoro, ga kai kamar na agwagwa, au na gano ashe hiyasa kake sa wando mai nafkin saboda wannan ƙatuwar jelar taka ko? Aiko yanzu zanyi maganinta.” Ta karasa maganar tana kokarin sa masa hannu.

“Zizi Please Stop it…”

Adeel ya farka daga mafarkin da yake yana rike mararsa.

Bude idon da zaiyi ya ga ba Gaaji bare alamarta.

Tsaki ya yi kawai ya gyara kwanciya ya ci gaba da barcinsa.

“Kar ka kara mun Don Allah, ka barni, bana son wannan abun naka, kar ka samun, zan cije ka, Aradun Allah zan cijeka, na ce kar ka samun.” Tana magana tana hawaye tare da tare gabanta da hannayenta.

Wani irin gigitaccen kallo ya bita da shi yana cire hannayen nata, Gaaji ta ce, “Na rokeka Don Allah, Aradu har yanzu wajen zafi yake yi mun zaka yaga ni , Shikenan yagewa zan yi in mutu in ka kara samun abunnan, Baffa na kazo, ka ganshi ko, mai Idon Mage, Wayyo Allah na na shiga uku sau goma shike nan.”

Ko daga ido ya kalleta bai kara yi ba.

Ganin da haske fa yake shigarta zai kara yi ba fashi Gaaji ta kwallara ihu tana kai bakinta kirjinsa.

“Nace maka ka barni, ka barni nace , mugu An Ishka mai kama da kashin shanuwa ,kanka kamar alade ka barni mai sa nafkin kawai, Baffana sai ya harbeka inya dawo wallahi Allah sai na fada masa inya dawo kai mugune mai kama da awakai ni bana sonka, na tsaneka na tsaneka Aradun Allah.”

Tana gantsara masa cizo a kirji yana kokarin shige mata.

Zai shige kenan ya kara farkawa.

Wata irin zuface mai dumi ke keto masa a jiki, laluban gadon ya fara.

Bai ga Gaaji ba duk abunnan, cike da takaici ya tashi ya zauna yana dafe kansa, “wai sha’awar yarinyar nan baza ta barni haka ba? Kai oh my God.” Tashi ya yi ya ,ya yi wanka sannan ya zauna ya yi tagumi.

Ranar dai kam Prince Adeel bai iya kara rintsawa ba yadda ya ga safiya haka ya ga dare.

Masarautar Benoni

Gaaji kowanni motsi ta tuna Yareema sai ta gama tsine masa a zuciyarta musamman in taje tsarki don ya ji mata ciwo sosai tana sa ruwa zata yi tsarki sai zafi, wanka kuwa sam taki yarda Uwar Soro ta mata sai ta ce zata yi da kanta.

Kwanciya tazo yi tayi wani irin wawan kwanciya tuni ta hade kafa tana, “Mugu kawai mai kama bunsuru yazo yasa na koma tafiya irin ta agwagwa gashi ba abun in wangale kafa sosai ba in kara yagewa daman duk ya gama ya ga mun duwawuna don mugunta, Aradun Allah sai na rama kuma.”

Zaune suke suna breakfast da Uwar soro ta ce, “Baba kin ga Wancen mugun ya hana mun abokina zuwa ko?”

Uwar Soro ta ce, “Aa zai zo yana can yana lura da baffanki ne ya kusan dawowa.”

Gaaji ta washe baki, “yana dawowa za a muna auren mu da shi wancen mugun ya sakeni ko? Ya dunga goyani muna fita anguwa yana bani tatsuniya ina jin dadi.”

Girgiza mata kai kawai Uwar Soro ta yi.

*****

Mai Martaba ne zaune shi da Fulani Babba da Kilishi suna tattaunawa.

Mai Martaba ya yi gyaran Murya kafin ya ce, “Fulani ince dai kin yi magana da Uwar Goyon Yareema kan batun Khaleesan mu ji ta bakinsu.”

Fulani Babba ta ce, “Aa Ranka Ya dade tukunna dai kam yau nake son zuwa bangaren nata mu tattauna na shedawa Jakadiya kan cewa taje ta sanar mata da cewa ina nan tafe In Sha Allah.”

Mai Martaba ya ce, “Shikenan , amman zan yi matukar Farinciki da hakan in har ya tabbata.”

“Sosai ma gaskiya ni kaina na ji dadin hakan Allah dai ya tabbatar mana da alkairi.” Fulani Babba ta fada.

Sai a lokacin Fulani Kilishi ta yi magana ta ce, “Ranka Ya dade wannan hadin fa akwai Matsala ina jiye mana abun da zai je ya dawo, inda hali a kara jan lokaci tukun gaskiya.”

Mai Martaba ya ce, “To fa! Ko dai kina tunanin akwai wata Matsala ne?”

Murmushi Fulani Kilishi ta yi kafin ta ce, “Aa sam sam Mai Martaba , amman dai kasancewar Yareema wanda ba mai cika son shiga harkar mata ba, kada ayi gaggawan hakan a yanzu shawara ce Amman Allah yasa banyi kuskure ba.”

Mai Martaba ya ce, “A’a amman dai yanzu Fulani ta tuntubi Uwar goyon nasa muji ta bakinta tukunna kafin aiwatar da komai.”

Zuciyar Fulani Kilishi bata so hakan ba,ta so ace tun yanzu ta samu mafitar da zata ja batun auren har ya kai ga ta aiwatar da muradin dake zuciyar ta.

Murmushin dole ta sake a zahiri ba don ta so ba.

*****

Jakadiya kuwa tun ranar da tayi gamo da Aljanu a gun Uwar Soro take matukar tsoron kara shiga, ko da taje kofar bangaren tsayawa ta yi ta tura wata baiwa ta sheda mata cewa gata a bakin kofa.

Uwar Soro ta fito tana, “Ah yau ma Jakadiya ce ta kawo mana ziyara? Bismillah mana ki shigo ciki.” Ta fada tana kokarin komawa.

Murya na rawa Jakadiya ta ce, “Aa aa sakone kawai daman zan fada miki,ina Ni ina kara shiga wannan bangaren naki, ranar ko da na koma gida banyi barci ba kona fara razana nake , Yanzu kam inna kara yin wani gamon ai na san ba shakka mutuwa zan sai lahira.”

Uwar Soro ta yi Murmushi tana , ” aiko da ranar tsautsayi ne amman yanzu ku zo muje ki huta naga sai Haki kike kamar wacce aka biyota da gudu.”

Jakadiya ta rike habar baki, “Ni jikar Amadu , rufamun Asiri in mutu maza su kaini ba mata ba, kin ga Fulani Babba ce ta ce in sanar sake tana nan zuwa gareki akwai maganar da zaku tattauna ina ga amman fa ban san mene ne ba ko ke kin sani?”

Uwar Soro ta ce , “Aa sai dai tazo din.”

Jakadiya ta ce , “To shikenan nikam dai kin ga tafiya ta.”

Har ta juya kuma ta juyo tana, “Umm niko nace Yareema na kasar nan kuwa?”

Uwar Soro ta ce, “Yana nan mana ko ance miki baya nan ne?”

Jakadiya ta ce, “Aa kawai dai na tambayane, sai Anjima.” Ta fada tana tafiya.

Tana cikin tafiya ta gamu da Hajiya Rabi ta fito kenan daga ɓangarenta ga dukkan alamu anguwa zata da sauri ta karasa gareta tana, “Hajiya ka da fa ka a rangwanta akan lamuran batun auren nan domin Yanzu Fulani Babba na daf da zuwa Gun Uwar goyon Yareema a tattauna sunyi zama da Mai Martaba daga nan yanzu zata su tattauna da Uwar goyon sa kin ga kuwa na san indai uwar goyon yareema ta amince komai zai tafi dai-dai.”

Hajiya Rabi ta ce, “Karki damu kice fitar tawa tazo adaidai kenan daman fitar da zanyi gun malam na nufa.” Ta ƙarasa maganar tana tafiya.

Jakadiya ta ce , “Hajiya tsaya mana,gun wani malamin? Fada mun tukun.”

Hajiya Rabi ta tafi tana, “Ke dai bari kawai sai na dawo mayi tafiya.”

Tsaki Jakadiya ta yi tana, “duk dai kwayi kwa gama kuna a tafin hannuna.”

Uwar Soro na komawa ta cewa Gaaji ta zauna a dakinta kar ta kuskura ta fito zata yi baki, kuma indai ta bari suka ganta zasu sa akaita dakin duhune.

Gaaji ta ce, “Cab wannan dakin da mugun Yareeman nan ya kaini ai bazan kara bari akaini ba nikam ma wasa na zanyi.”

Uwar Soro ta fice ba jimawa Fulani Babba ta karaso.

Su ka shiga Daki domin tattaunawa.

Nan take wani irin hadari ya rufe garin ba jimawa ruwa ya sauko da karfinsa.

Akwai baranda agefen dakin da Gaaji take tana ganin ruwa ta birkice tsuminta ya tashi, ba abun da take so arayuwarts irin shiga cikin ruwan sama tana tsalle-tsallenta.

Tuni ta jefar da hijabin dake jikinta ta bude kofa ta shiga tana yan wake-wakenta tana tsalle da wasa cikin ruwan.

Sai da ruwa ya dauke FULANI babba sun gama tattaunawa da Uwar soro kafin ta koma cikin Masarauta.

Kwalawa Gaaji kira take akan tazo sunyi kan cewa yau zata mata kitso taji shiru, ta shiga dakin ba Gaaji, toilet ma ba kowa,har zata fita sai ta ga dayar kofar abude da sauri Uwar soro ta bi, tana zuwa ta ga Gaaji kwance a kasa tana fidda numfashi sama-sama.

Cikin damuwa da ɗimuwa Uwar Soro ta dauki Gaaji ta maidata ciki, kayan jikinta ta fara cire mata da sauri ta goge mata ruwan da ke jikinta sannan tasa mata wasu kayan.

Gaaji kuwa Numfashinta kamar ana kara fisgarsa yana kokarin subuce mata.

Gabadaya Jakadiya ta birkice duk wata dabara ta, ta da take tunanin zata yi aiki ta gwada amman lamarin ya citura.

Fita tayi ta shiga bangaren Prince Adeel ta tarar baya nan, shamaki ta kira ta tambayesa ko yasan inda yake, nan yake tabbatar mata da cewa kusan Kwana Hudu kenan ai Adeel baya ma kasar.

Haka ta koma bangarenta da sauri ta , tana shiga ta ga abun ya kara tsamari numfashi sama-sama ga shi jikinta ban da rawa ba abun da yake yi, tsabar yadda jikinta ke rawa shi kansa gadon motsawa yake.

Wayarta ta dauka ta danna Number Adeel sam kiran baya tafiya ,ganin bata da wata mafita ga yar mutane na shirin mutuwa kawai ta danna kiran Adnan.

“Adnan ka zo yanzu Please, Gaaaji ba…”

Bata karasa ba ta katse wayar ta nufi kan Gaaji, dagata tayi ta riketa tana jijjigata.

Prince Adeel na sauka a mota daidai kofar get dinsa gabansa ya yi wata irin mummunan faduwa, har zaiyi bangaren sa sai kuma zuciyarsa ta raya masa cewa ya yi bangaren Uwar Soro, Yana zuwa kofar Part din Ya ci karo da Adnan yana kokarin shigewa cikin sauri damuwa ta bayyana a fuskarsa.

Hada ido suka yi da juna, Adnan ya yi saurin kawar da kai yana shigewa.

Bin bayansa Adeel ya yi yana mamakin me ya kawo Adnan wannan Part din cikin wani yanayi bayan kuma sunyi da shi cewa ba shi ba gaji har sai WATA BAKWAI ya cika.

A fusace ya shige ciki, Adnan na shiga ya ce, “Subhanallahi Me ya sameta?”

Cikin Muryar damuwa Uwar Soro ta kalli Gaaji tana fadin, “Fulani Babba ta zo muna tattaunawa na sheda mata kada ta fito nayi bakuwa, tafiyar Fulani Babba ke da wuya na shigo na tarar da ita ta bude kofar baya ta shiga cikin ruwa ga dukkan alamu wannan ruwan gabadayansa akanta ya sauka tun tana Numfashi sama-sama har yanzu ta fara gagara yi.”

Daidai da shigowar Prince Adeel.

Jikin Adnan na rawa ya ce, “Ok bara na kira Doctor Jawad ya zo yanzu.

Tsayawa kallonsu kawai Adeel ya yi ba tare da ya ce komai ba, ya zura idanunsa kan Gaaji, a hankali ya karasa inda take, ya dan tsaya for some seconds sannan ya mika hannunsa ya karbeta daga jikin Uwar Soro, ya kwantar da ita akan gadon sannan shi ma ya haura kanta

A hankali ya kai fuskarsa daidai ta,ta.

Adnan ya gama kiran Doctor Jawad tsayawa ya yi kawai yana kallon Prince tare da rashin fahimtar me yake shirin aikatawa haka.

Uwar Soro ma binsa kawai tayi da kallo tana mamakin anya kuwa lafiyar Prince kalau?

Cikin Nutsuwa yasa hannayensa ya tallafo bayanta, sannan yasa bakinsa kan nata , Numfashi ya fara bata ta baki a hankali.

Numfashinta ne fara dawowa kadan kadan sai da ya dauki wajen Minti Uku yana kokarin dawo da ita hayyacinta Doctor Jawad na shigowa ya gyara mata kwanciya yana lulubeta da blanket sannan ya fice daga dakin Ba tare da ya ce masu komai ba Part dinsa ya shiga.

Dubata Doctor Jawad ya shiga yi don duk da numfashinta ya dawo amman har a lokacin bata dawo hayyacinta ba.

Sai da gwada mata b.p da duk wani gwaje-gwaje sannan ya mata allura don yanayin da take ko an bata magana da kyar zai iya yin aiki.

Adnan ya ce, “Dr Ya dai? Ina fatan ba wata babbar matsala bace dai?”

Dr Jawad ya cire Glass dinsa yana maidawa aljihu ya ce, “Ehto ku san hakan za ace, Alhmdu Lillah amman da ace Prince bai bata taimakon gaggawa ba ta dau lokaci bata wannan numfashin gaskiya da an samu matsala Sosai,

Amman yanzu kuma damuwar lta ce jikinta ya yi sanyi gabadaya ta ko ina ba dumi ko kadan, wanda hakan illa ce babba musamman ga lafiyar mace, duk da na mata allura kuma an lullubeta yadda dumin jikinta zai iya dawowa amman akwai bukatar ana shafa mata tafin kafarta da hannu na yan wasu lokuta domin suma suyi gaggawan dawowa da ɗuminsu, ta shiga ruwa sosai wanda ya zarce kimar yadda jikinta zai iya dauka, don haka kafin ta dawo daidai za a iya daukan time.”

Adnan ya ce, “Lokaci kuma? Kamar har yaushe?”

Dr Jawad ya ce, “I can’t Says Saboda yanayin yadda jikinta ya bada hadin kaine, don ka ga sanyi ya shigeta Sosai jinya biyu za ayi atakaice ga sanyin jiki ga kuma mura wacce ta zam dole, sai dai ana kiyayewa da abun da zata ci ko zata sha sosai ganin an kauracewa abubuwa masu sanyi, sannan ta daina zama a waje mai sanyi ko iska, kayan da zata sa ma a jikinta yana covaring ko ina na jikinta.”

Uwar Soro ta ce, “Ba matsala In Sha Allah za a kiyaye.”

Tare da Doctor Jawad Adnan suka fita zai je ya karbo magungunan da za ana bawa Gaaji inta farka.

Prince Adeel na zuwa daki ya zauna kan 2sita ji yayi dukkan wani gabobi na jikinsa na ciwo,hakan yasa ya tashi ya je ya yi Wanka yana yin wanka ya sa gajeran wandonsa da rigar shan iska yana zaune yana hutawa.

Zuciyarsa na masa ƙuna yana jin cewa kamar ya koma ya tambayi Adnan shin me ya kawowa bayan deal dinsu bai kammala ba?

Tsaki ya yi ya dauki Drinks dinsa da ke cikin glass cup yana sha cikin Nutsuwa tare da kokarin danne zuciyarsa.

Ya gagara ban da tsaki ba bu abun da yake.

Wani irin tashi ya yi a fusace sai da glass cup din ya fashe, ya fice cikin sauri.

Yana shiga Part Din, Uwar Soro na Shafawa Gaaji kafa kamar yadda Dr Jawad ya umarta, Adnan ma zama ya yi daf da ita yana kokarin ciro hannunta cikin bargon, cikin wata gigitacciyar murya Adeel ya ce, “Wait…”

Adnan ya dago yana kallonsa sai da karaso garesa kafin ya ce, “What about Our Deal? Ka manta da cewa ba ruwanka da yarinyar nan har sai ranar da na sallameta?”

Adnan ya tashi yana fadin , “And So? Ai a yanzun kamar kanwa take gareni don haka ina da damar kula da lafiyarta, tsaya ma! Ka damu da ita zaka tafi wata kasar ka banzantar da ita? Adeel lamuranka tun suna bani mamaki har na daina, na rasa me wannan yarinyar ta tare ma a rayuwarka ka ke da burin galabaitar da rayuwarta.”

Kan Adeel na kasa ya ce, “Ina ruwanka? Ince yanzu dai a karkashina take ba naka ba? So zai fi kyau in ka tsaya daidai gurbinka don in har ka kuskura ka shiga gurbin da ba naka ba za ka sha mamaki.” Ya ƙarasa maganar yana dagowa tare da nunawa Adnan yatsa.

Tsaki Adnan ya yi ya ce, “karkashinka take tabbas amman hakan ba zai hanani taimaka mata ba muddin tana da bukata.”

Duk yadda Prince Adeel ya so da danne bacin ransa ya gagara karasawa gaban Adnan ya yi yana magana cikin zafin rai, “ka fita ka bar dakin nan tun kafin in dau mataki akanka.”

Wani irin Murmushin takaici Adnan ya yi, ya na, “ba zan fita ba in zaka iya ka fidda ni da kanka.”

Prince Adeel bai san lokacin da ya fara kaiwa Adnan hannu ba, nan take suka fara kokuwa.

Uwar Soro da ta zuba masu ido ganin abun bana kare bane ta ce, “haba! Haba Don Allah wai wani lokacin sai kuna abu kamar yara? Ai ido ba mudu ba amman yasan kima ko darajata da nake anan ya ci ace kun gani kun dakata da koma miye ku ajiye wannan zafin zuciyar taku agefe.”

Sake Adnan , Prince Adeel ya yi ya fice cikin sauri yana tafiya zuciyar sa na zafi , bugu kirjinsa yake wanda ke daf da shi zai iya jin sautin.

Yana fita Adnan ya kalli Uwar Soro ya ce, “Na rasa gane me yake nufi da wannan yarinyar wallahi, adazu da ceceta har sanyi na ji araina amman kuma ashe hakan ba har zuci bane.”

Yanzu dai kaje a wanke maka wannan raunin da ka samu.

Adnan ya ce, “To Shikenan zan tafi kila kuma sai zuwa gobe zan zo in duba jikinta kafin ta farfado In Sha Allah.”

Suka yi sallama ya tafi.

*****

Jakadiya ce zaune tare da Fulani Kilishi.

Jakadiya ta ce, “Ina da babbar Jarida na san dole kina da bukatarta, amman wannan karan fa sai kin biya gaskiya.”

FULANI Kilishi ta ce, “ki fada koma mene ne Indai kudine damuwarki kinsan ban da matsalarsu.”

Jakadiya ta gyara zama tana waige-waige murya kasa-kasa ta ce, “Hmm Hajiya Rabi fa ta dage kan dole sai Yareema ya Auri Khalesa,in takaice miki da cewa taje gidan wani Boka ta karbo magani dazu na ji suna magana ta window na laɓe amman babban takaicin shine basu bayyanar mun da inda zasu sa maganin ba, tabbas dai na san sunyi shiri mai girma da zai iya tarwatsa shirin kowa cikin Masarautar nan.”

Fulani Kilishi ta ce, “Au au, ganin duk ina raga masu ne ya janyo hakan ina? Ba matsala yanzu zan aikata abun da kowa da ke cikin Masarautar nan sai ya girgiza.” Ta karasa maganar tana daukan mayafinta.

Jakadiya ta ce, “to ai baki sallameni ba,kuma baki fadamun ina kika nufa ba.”

Ko saurarenta Fulani Kilishi ba tai ba ta fita cikin sauri.

Jakadiya ta yi kwafa tana , “Lallai nima anzo daidai wajen da dole sai na dau mataki.”

Khalesa kuwa Hajiya Rabi ta bata wani kulli kan taje ta sa a kasan kafet din Kofar Part din Princess Adeel yadda yana takawa Shikenan komai zai tafi yadda suke so kuma suka tsara.

Tana sawa ta tafi kenan sai ga Fulani Kilishi ma da nata layace ta shimfidata a ta cen karshen carpet din da Safina tasa.

Dukkaninsu wannan aika-aikar cikin dare suka yi ta.

Kowa ya kwanta da zakuwar ganin safiya da abun da zai faru.

Misalin Karfe Goma na safe Prince Adeel ya fito ya yi wanka cikin shigarsa ta manyan kaya dukkanin abun da ke jikinsa fari ne sol,Yana fara tafiya zai nufi kofa daidai lokacin Gaaaji ta farka a firgice.

Tana farkawa ta fita da gudu, Adeel na sa kafarsa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Auren Wata Bakwai 11Auren Wata Bakwai 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×