Skip to content
Part 3 of 23 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Boss ya dafe kumatu yana runtse idanu saboda jin karar marin da Nadiya ta fuskawa kaisar tamkar shi ta mara.

Tero da shima idon shi yake tar akan Nadiya da kuma gayen da ta mara ya juyo don ya nunawa Boss marar kunyar yarinyar nan sai yaga idon Boss din a kan su yana dafe da kumatu.

“Kai? jar Uba ! Ashe yarinyar Nan bata da mutunci boss? mari fa? dubi haduwar gayen nan amma ta maska mishi mari ko don ta gan shi dan kad’an? amma ba karya ya hadu kuma ya iya wanka .

“Baka ji yadda naji marin nan kamar a jiki na ba Tero? Anya idan ni yarinyar nan tayiwa wannan wulakancin ba zata janyowa duk ahalin su janhurun masifa ba? na rantse maka idan ni tayiwa haka har numfashin ta sai ya yanke.

“Ba zai yanke ba Boss sai ka kwana kan shegiya don kayi kaca kaca da abinda take takama dashi don babar babar ta. suka mayar da kallon su ga Nadiya da kaisar wanda take ta zubawa ruwan tijara tamkar zata make shi.

“Da Allah dube ka tamkar kwado  ? In ma na yarda na so ka ni kuwa ka bani me? dukkan ka baka wuce saka ledar Viva da wannan yar halittar take kake tunanin nufa ta? Ta fada tana tuna kas’an shi.

ta wuce tana masifa yayin da king kuma ya ji wata muzanta da bai tab’a ji ba . domin kuwa kaisar bako ne a garin bauci ba kumata yayi ace ya shaida karamcin mutanen bauci ba rashin kirki irin wannan ba? .

kan king a k’asa Yana Jin kunyar hada ido da kaisar sai ji yayi kaisar din ya dafa shi yana fadin

“King ina son yarinyar nan da gaske wallahi har raina.

dukkan abinda ta fada min sai naji su tamkar taki a shuka .

“Kayi hakuri kaisar. wallahi banji dadin hakan ba naso ace a yau ka shaida karamcin mutanen bauci ba rashin kirki da rashin tarbiar yarinyar nan ba.

“Kar fa ka damu king sai kace baka San soyayya ba? ai yafi ne a soyayya ko kayi nasara akan sa ko shi yayi akan ka. ni kuma sau dayawa ina saka tabbacci da hakikar samun abunda nake so ban tab’a sarewa ko kasawa akan cikar buri ba   haka kuma Inaji a jiki na sai na auri yarinyar nan king . kaine dan gari ina so mubi bayan ta don gano gidan su  zan zama irin mijin da zan burge ta har ta yarda ba kowane namiji ne yafi ni ba.

“Da zaka yarda kaisar sai nace ka hakura da yarinyar nan mu nemi wata kawai tunda gasu nan kamar jamfar jos.

“Forget about king be a man mana sai da faduwa ake nasara idan babu faduwa ba zamu gane girman nasara ba kai dai taya ni da ADDU A ai na fada maka naji a jiki na I will winer .

Ya kama hannun king suka rufawa Nadiya baya inda yan matan da samari suke ta rawa da rungume rungume wasu ma har da sumbar baki salon iskanci dai kala kala

Keena da idon ta ke kan su kaisar har zuwa inda ta kwada mishi mari duk akan idon keena wacce Bata ji dadi ba duk da saurayin ta war boy da ya iso yana ta mata zuba amma sam hankalin ta yana can ga kaisar har taga abinda ya faru.

“Amma gaskiya baki da kirki Nadiya. yanzu ke baki ji komai ba ki cira hannu ki fallawa namiji mari?

cewar keena da ta tarbi Nadiya da wannan maganar.

“Ina namijin yake? wancan kayan banzan? Wancan ai yafi kama da dan taure ba namiji ba.

Safina da lubabatu suka kyalkyale da dariya suna fadin

“Barta keena lokacin ta ne gayun ne sai da haka baki san babban goro sai  magogin karfe ba? Kowane namiji ne daidai Nadiya saboda Allah?.

“don Allah manta da ita luba da inna da baba zaiji ko kuwa da kanshi bare ya tuna dani?.

haka sukayi ta magana har zuwa hall din inda Nadiya kamar ance ta juyo sai taga kaisar a dab da ita.

“Bakaji abinda na fada maka ba kenan? yasin na kuma ganin keyar ka a kusa dani sai na saka an kama min kai nonsense kawai.

taja hannun luba suka bar wurin.

Tero ya dubi Boss yana fadin

“kar kaje inda yarinyar nan take boss don zata kuma baka mamaki ne ka barta kawai in nemi Killin ya zo ya sano mana ita.

“Ba dai a nan ba Tero ai aikin mu zai kwana ne don idanun mutane yayi yawa .

Boss ya fada yana barin wurin da nufin zuwa inda yaga nadiya ta nufa.

“Nifa na rasa abinda Boss ya gani  a wurin yarinyar nan har ya nace mata haka tana wulakanta shi.

cewar tsagera.

“Kai fa ai babu ranar da zaka ga kyan mace shege in dai ba giya ba sai ko kwaya anya ma kuwa tsagera kai namiji ne? sai dai ko mata maza.

“Uban ka ne mata maza dan ta shegiya me kake nufi dani ne?.

Tero ya kyalkyale da dariya yana fadin

“To ai ni ban ga alamar maza a tare da kai ba.

suka fito motar suka rufawa boss baya inda yake dab da su Nadiya.

Sallama yayi musu safina ta juyo da sauri tana fadin

“Sai boss hadari Mai zubar da ruwan dalolin amurka Allah ya Kare maka sherri.

yazaro dala dubu ya mikawa safina ta cabe tana godiya yayin da Nadiya ta ja tsaki tana mishi kallon uku saura kwata.

“Safina ina son kawar ki amma me nayi mata take wahalar da Ni?

da sauri safina tace

“Wace kake so Boss? duk ma wacce kake so na baka ita Yasin.

ya nuna mata Nadiya yana fadin

“Gata a nan safina wai ban hadu bane? ko kuwa ban iya wanka bane? bani da kyau ne ?.

“Ai karya ne ace mace tace bata son ka Boss ko baka da kyau ai akwai kudi a gidan ku ko da ake cewa gidan su Nadiya GIDAN KUDI kuma naku gidan gidan daloIi ne wallahi masu kyauta da dalar amurka a wannan Nigeria.

“Gara da kika gane GIDAN mu GIDAN KUDI ne ta Yaya wani makaryaci wanda na tabbatar da baban sa bai wuce mai wankewa Daddy na mota ba zai zo da wata argar motor da aka gama yayi tun 199D yace min yana sona? Ai sai dai ko baban sa amma shi kam nafi karfin talaka irin shi irin baban sa.

“Babana ne takala? .

“To nawa ne da shi a account? kazo gidan mu na baka sadaka ka Kai mishi ta fada tana mishi wani mugun kallo tana .

da sauri boss ya riko hannun rigar ta tana shirin wucewa a fussce yana fadin

“Kar ki kuma fusata zuciya ta a karo na uku don wallahi zaki yi nadama marar adadi a rayuwar ki don cin mutuncin ki har ya wuce kaina yaje ga mahaifi na?.

da sauri Nadiya ta fincike hannun rigar ta ta kuma kifa mishi mari kafin ta sake tofawa fuskar shi yawu tana fadin.

“Uban uban naka na zage shi  inga abinda zakayi?.

da wani irin sauri Tero ya daga hannu yana shirin maska mata mari amma boss ya rike hannun Yana duban fuskar Nadiya yana murmushi.

“Barni na yaga shegiyar yarinyar nan boss Uban ta ita da kowaye Uban ta sunci gindin babar su.

Nadiya ta juyo tana kallon Tero da yake auna mata ashar.

“Ni ka zaga?

Ta fada da mamaki a fuskar ta don ba a taba yi mata zagin rashin kirki irin wannan ba.

“Gindin babar ki yar ta shegiya ya fada yana son Kai hannu a jikin ta da son ya make ta .

cewar Tero da yake son kwacewa daga rukon da boss yayi mishi da son ya isa ga Nadiya ya kwakkwada mata mari.

“Tero yarinyar da nake so kake zagi?

cewar Boss

“Kar ka kuma zagin ta don zan baka mamaki.

“Kafin ka bashi mamaki nice zan fara bashi mamaki wallahi don sai ya gane ya zagi yar GIDAN KUDI wallahi.

cewar Nadiya wacce ta fito da wayar ta tana kira tana fadin a karaso gold and silver.

kan kace me? sai ga motar DSS sun kutso gold and silver inda Nadiya ta fito tana nuna Tero tana fadin a tafi da shi a koya mishi hankali ya zagi Uban ta wanda zai iya siye Uban shi har da zunubin shi.

Ai kuwa sai ga Tero an damuka an wurga mota an wuce da shi inda kuma boss ya bi bayan motar DSS don karbo Tero .

Kaisar ya dubi king suka dubi juna king na fadin

“Kaga gadarar yarinyar nan ko ? ta yaya kake hango tafiyar ku kai da ita kaisar? ba matar kwarai bace wannan yarinyar gara ka barta ka nemi wata.

“Naji na gani king kai dai ADDU A zakayi min amma naji na gani shi fa so makahone baya ji baya gani.

“Naka son ne haka gaskiya ni kam inda ake sona nake bana son da zai zama kurma kuma makaho don zai wfka ni rami ne.

“Na yarda muje kar su gudu ka kasa nemo min gidan su .

Lokacin da suka juyo sai suka ga babu su Nadiya da lubabatu suka shiga nema amma ko mai Kama dasu  basu gani ba  .

cike da tashin hankali kaisar yake duban king Yana fadin

“Kaga sun tafi wurin surutun ka da Allah Ni muje dan iska da kai dama na lura kana min black stomach ne amma in sha sha Allah sai na gano gidan su yarinyar nan matukar dai a cikin bauci take.

ya nufi motar king ya shiga yayin da king ke fadin

“Ai Allah yasa ma rabuwar nan taku itace alheri don ni ban hango wani alheri a tarayyar ku da ita ba in sha sha Allah kuma kun rabu kenan.

Ya shiga motar ya tashe ta suka nufi gidan alh iro wanda akewa lakabi da iro GIDAN KUDI wani shahararren mai kudi a garin bauci wanda kaisar ya sauka bauci zuwa gidan shi daga engila zuwa bauci.

suna karya kwanar unguwar da gidan iro yake kaisar yasha mamaki domin kuwa ya yarda iro yaci sunan sa gidan kudi

motar king ta faka a kofar gidan wanda yake cike da masu tsaro suka kuma taso suna tambayar king waye shi kuma wa yake nema?.

Kaisar ne ya bada amsa da cewa wurin alh iro suka zo .

“Ya san da zuwan ka?

“Eh bari ma na kira shi.

ya soma kiran wayar Kara biyu aka dauka Daddy ya soma fadin

“Kaisar ka iso?

“Eh Daddy gani a kofar gida.

“Ok to Bari nayi magana a barka ka shigo.

ya yanke kiran inda wayar mai musu tambayoyin ta dauki tsuwwa ya duba sai yaga mai gidan ne ya dauka da sauri inda aka bashi umurnin budewa kaisar kofar.

Ai kuwa a guje ya soma tura kofar get din wacce har sashi baya hudawa yace da su kaisar su shigo .

King ya tashi motar suka danna katafaren gidan inda suka hango alh iro yana saukowa daga saman benen da kanshi ya tarbi kaisar da king suka shiga cikin katon gidan Wanda sukayi ta wuce kofofi da faluka kafin suka dire a wani falo mai kama da fadar shugaban k’asa inda haj Aliya ta tarbi kaisar tamkar zata mayar da shi  ciki tana ta mishi sannu da zuwa.

Suka zube a gaban su shi da king suna gaishe su sai tambayar shi hanya suke Yana amsawa da komai lafiya.

Haj Aliya ta mike tana kiran Fati da Nadiya amma Fati ta fito sai taga bak’in da Daddy yake fada zasu zo.

ta duka tana gaishe da su kaisar  wanda tayiwa kallo daya taji wata faduwar gaba mai tsanani Amma ta mike haj Aliya na fadin

“Ina Nadiya kuzo ku dauko kayan abincin Nan .

“Mama ai tun dazu Nadiya ta fice.

“Ina ta tafi?

Haj ta tambaye ta.

“Wai together kawayen ta suka gayyace ta.

“Da kyau zata zo ne ta same ni muje ki dauko kayan abincin.

<< Azurfa Da Zinari 2Azurfa Da Zinari 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×