“Ke bashi da zuciya fa keena komai nayi mishi baya kulawa kuma al amarin nashi kamar ba haka nan yake ba.
“Baki jaraba wannan ba ne ai ko bashi da zuciya yana da kishi yaga wani Kato a gidan sa hat ma in son samu ne kuke dan kashe fitila ta yadda zai fahimci kuna zagawa ai zaki ga bacin ranshi ke dai bani lambar Wayar shi da ta motar shi.
“Me zai hada ni da lambar shi keena?wallahi ban ma san kalar lambar shi ba sai dai ko muje parking space na nuna miki ta motar shi.
“Nafi son ta wayar shi don kar aiki na ya kuma kwana ki kira wani mana ya turo miki?.
“Babu wanda zan kira fa keena . ko kawo wayar ki na kira mama ta tura min lambar tashi. Ta karbi wayar keena ta kira Haj Aliya tace a tura mata lambar Kaisar ai kuwa babu shayin komai Haj Aliya ta tura mata lambar tashi keena tayi murmushi tana fadin
“Muje na dauki ta motar itama ai umma bibbiyu tafi guda.
suka futo amma basu ga motar ba don da ita ya tafi gombe.
“Babu komai tunda na sami wannan sai ki daura damarar yi mishi rashin kirki mai daraja wacce zata gajiyar da shi har ya sallame ki salin alim.
“Yanzu dai je ki studion show ki karbo min wayar sai su luba su jira ki har ki dawo.
Haka kuwa akayi kena ta fice ta karbo waya yayin da safina da luba suke ta zaga gidan Nadiya suna yaba tsarin sa da haduwar sa
Da zasu tafi ma sai da keena ta kebe Nadiya tana kara ingiza ta ga yiwa Kaisar rashin mutunci ta yadda zai sallamo ta duk wani sbu da ta dan baya so sai da tace tayi mishi.
“Keena kenan Ni fa na ma gama tsara yadda zanyi da gayen nan wallahi gawa dubu zan aunawa shege yaci ya mace .
“A a kar muyi haka da ke mana in kika kashe shi ni kuma kiyi yaya dani ? kawai dai tunda baki so ni ina so ki samu ki fice ni kuma na shigo zan kuma kawo show don zuwan shi gidan ki yana da muhimmanci gareki da ni don shine zai kawo mana karshen komai . tun batayi nasarar dora Nadiya ba har tayi nasarar dora ta ta kuma hau ta zauna.
Sukayi mata sallama suka fice yayin da suka zube mata yan biyu da sukayi bacci suna tsotson yatsun hannun su don yunwa suke ji in har ka ga suna shan hannu to dama can uwa ba damuwa tayi da su ba bare kuma kawayen ta sun ziyarce ta.
Ta mike da wani irin makirci wanda ta shirya na hada girki wanda tunda tazo gidan bata yi shi ba in ma tayi nata ne ita kadai amma a yau da yake tayi nufin mugunta da manuba sai ta shirya girki na garari wai da sunan tarba.
Karfe shida da rabi motar shi ta shigo gidan ya faka yana fitowa da tsaraba irin ta nono da man shanu zabbi da kwayayen su malam Ango ya taya shi dauka suka shiga sashin mama ta tarbe shi yana ta wara ido don ya ga su sha aban don hankalinsa kaf yana Kan yaran don ya san matukar dai ba wurin mama suke ba to suna can cikin garari.
Haj Aliya tana mishi sannu da zuwa ya aje mata tsarabar da su Baddo da kawu yayari suka hado musu ya juya ya fice yana rike da madara sabuwar tatsa da ya ruko wa yan biyu.
Nadiya tayi kwalliya ta shirya yan biyu wanda suke sanye da hannu a baki amma abin mamaki uwar su bata san shan hannun su alama ce ta yunwa ba da yake suna da hakuri basuyu kuka ba tayi musu wanka ta sake musu kaya tana cikin shirya su ne Kaisar ya shigo yayin da yaran suka soma daga hannu Alamar zasu zo wurin shi ya dauko su yana shafa sumar kansu yana sambatar su kallo daya ya gane suna cike da yunwa don haka ya juye madarar da yazo da ita ya soma basu suka yi kat .
Nadiya ta soma sauke mishi kayan girkin abinda yayi matukar bashi mamaki don bata tab’a jaraba hakan ba sai ya tuna da maganar da dattijon nan ya fada mishi na tana can tana shirya yadda zata kashe shi. Tayi murmushi tana zuba abincin da ta zabgawa gawa dubu tana zubawa ta aje mishi gaban shi ta kuma zuba kayan sanyin suma ta dire mishi tana mishi murmushin mugunta.
Yaja abincin ya yi bismillah ya soma ci ya kuma ji dadin abincin sosai ya gama yana duban ta yana fadin
“Ko ke fa sweetie? Yanzu ba gashi kin sami lada ta ba ? Mu je ki karasa ladar ki ina son zanyi wanka kafin na dan ganki ko?.
Ya fada yana kama hannun ta ta bishi duk da bata so bin nashi ba don tayi zaton ba zai gama cin abincin lafiya ba zai fara bullayi sai gashi tana gani karrr.
Yayi wanka yafito yana daura alwalar sallar Isha I ya kuma tayar da sallar a gida duk Nadiya na kallon shi ganin babu wani abu da ya nuna.
Ya gama sallar ya koma kan yaran shi su Ramadan da Sha aban yana musu wasa suna dariya tana gefe cike da mamaki har dare ya tura ya kuma nufi dakin ta abinda ya nuna mata manufar sa inda taji a yau kam zai zama marigayi matukar yace dai zai tab’a ta sai dai me? kamar kullum yauma haka taji tamkar an daure ta ta kasa motsi sai da ya nutsa ya sallame ta ne ta ji tana iya wani motsi .
A ranar da keena ta karbi lambar wayar Kaisar a washe gari suka nufi niger ita da luba bayan keena ta kuma karbo kudi hannun shaid’an wanda tace wa rana irin ta yau zata iso jos tare da sak’on sa wato Nadiya saboda saura kiris a kashe Boss.
Shaid’an ya gaggabe da dariya yana fadin idan aka yi sati biyu bai ganta ba zai iso makaranta ya neme ta don ya soma gajiya da jiran ta.
“Bama za a kai ba shaid’an ai na fada maka sauran kiris a kashe Boss din.
Ya tura mata dubu dari biyu yace ta cinye kudin ta saura ita yake jira yanzu
Sun Isa niger ta zubewa ba I’mani kudi ta kuma bashi lambar wayar Kaisar wacce ya soma gabatar da aikin akan ta kamar yadda ya saba sai dai mai makon yaga takardar ta kama da wuta kamar yadda yake ka idar aikin nashi sai yaga takardar tayi k’asan Ruwan da yake cikin kwaryar da take gaban shi .
Ya maka wa ruwan yizgar hannun shi sai yaga kwaryar ta fashe ruwan ya watsu a jikin su ya wanke su .
Karar da ba I’mani ya fasa ce ta amsa amo a dajin sai ga hayaki yana turnike dajin kafin ya soma kururuwa sai ga kwarya dauke da wani ruwan ta bayyana a gaban shi ya kuma mika hannu sama sai ga takardar da keena ta bashi ta lambar wayar Kaisar ya kuma jefa ta cikin ruwan a wanna karon sai ta kama da wuta tana ci saman ruwan da yake cikin kwaryar kuma wai ruwan bai hana wutar ci ba.
Ba I’mani ya gaggabe da dariya yana fadin, “Karya ne a lalata min sharri babu I’mani ne nan dole ma a bar ni na yi yadda nake so karya ne karya ne.
Ya dubi keena wacce ya soma dibar ruwan yana kwara mata a jiki har yayi mata sharkaf ya kuma fincike mata kayan jikin ta kafin ya daka tsalle ya afka mata .
*****
Daddy Alh iro ya iso misau gidan dan uwan shi halilu inda fati ta tarbe shi tana mishi oyoyo yaya Hajara ma ta soma fiddo abinci daga madafi na tarbar iro na iro kamar yadda take ce mishi.
Yaya halilu ya fito yana mishi barka da zuwa ya sauke shi a falon shi fati na ta sauke mishi kayan tarba.
Bayan sun gaisa ne alh iro yake duban yayan shi yana fadin, yaya halilu uba na ya same ni da magana na kuma ji dadi dama tunda nayiwa Nadiya aure hankali na ya koma kan fati abinda yasa ban yi wani motsi ba don ban san ya take a nan ba tunda naji kana fadar yaro likita wanda yake son ta amma ni a yadda na tsara uba na shi na zubawa fati sai dai ban fidda maganar ba sai gashi Allah ya fiddo ta. to abinda nake gani yaya kawai ka fada mata an fidda mata miji amma kar ta san waye mijin don in ta sani to maganar da bana so ta fita zata fita don haka Yaya halilu yaya kake gani?.
Yaya halilu ya sauke ajiyar zuciya yana fadin, ‘Haka yayi iro amma fa barin kashi a ciki baya maganin yunwa maganar da bama son ta fito dole ne fa zata fita amma kuma nayi maka uzuri don haka yadda kayi din nan yayi Allah ta ala ya saka mu shaidu ya kuma tabbatar da alheri ka bani aikin yiwa ya ta karya iro duk da na san komai amma zan rufe mata kawai dai zan kira ta na fada mata kazo ka same ni kace kayi mata miji in kuma tana da wanda take so fa iro dole dan ka yayi hakuri amma in babu zan ce mata Kaine ni a wurin biyayya dole tabi abinda kake so. To hakan ma yayi yaya Allah ya tabbatar da alherin ciki kuma ni da zaka biye ni da nace kar ka bata wani zabi akwai wata mace da zata ce bata son uba na ne? Da me aka fishi,?
“A a fa iro shi don me zakayi mishi yadda yake so sai itace ba za ayi mata yadda take so ba? Idan dai bata da wanda take so ne zan yarda da tsarin ku amma in tana da shi zan bata damar ta.
“To yaya halilu duk yadda akayi yayi daidai komai ya zamo dai alheri muke fatan ya tabbata mu da su.
“To Allah ya sa hakan mu da su din aminci mara yankewa duniya da lahira.
Har yamma daddy Alh iro yana tare da dan uwan sa suna firar zumunci kafin yayi mishi sallama yayin da fati ta bada sako a kawowa mama da Nadiya har ma da su twins.
A ranar Baffa halilu bai ma fati maganar ba sai washe gari ya kira ta ta iso ta zube a gaban shi tana fadin “gani Baffa.
“Yauwa binta jiya Baffan ku yaxo mini da wata magana ya kuma ce a tambaye ki idan kina da wanda kike so ki fiddo shi don shi kam yayi shirin auren ki don tare yaso hada ku da Nadiya to ita al amarin nata yaxo ne da wani salo shiyasa amma ke a yanzu yace in akwai wanda kike so ki fito da shi shine xan tambaye ki akwai wani ne ? ni dai na san akwai yarinya Nan likita da har zan gabatar mishi da shi sai na tuna ban sani ba ko baku daidai ta ba.
Wata irin faduwar gaba ta riske ta jin ana mata maganar aure sai taji koma waye ya samu zata karbe shi tunda muradin zuciyar ta dai ya zama mafarki smma kuma bata jin zata iya karbar likitan da Baffa yake magana don yana ganin kamar alfarma ma yayi mata.
“Yaya ne binta? kar ki matsawa kanki ki nutsu sosai ba garaje ba ki duba wani daga cikin maneman ki in kuma babu dama shi yace ya zaba miki miji ne don kar ya shiga hakkin ki in babu ne xai baki wanda ya zaba miki in kuma kina da shi ki kawo.
Ta sauke ajiyar zuciya tana fadin, “Baffa kai da daddy kun Isa kuyi mini hukunci kowane iri ne idan har daddy ya zaba min miji ina godiya in kuma kai ka zaba min Baffa duka ina godiya saboda ko babu komai zabin ku alheri ne a gareni Kuma Ni dama Babu wani db na aje magana da shi wanda kuka zartas min yayi Baffa.
“To alhamdulillahi binta nima da na so hada ki da likitan nan amma sai na barku in kuka daidai ta kanku zanji to sai Kuma ga Baffan ku yaxo shi jiya da maganar yayi miki miji amma nace sai anji in baki da wani tunda kuma kin zama yar halal in sha Allah zakiga amincin da Ubangiji zaiyi miki Allah ya daukaka rayuwar ki ya baki Ya’ya na kwarai wanda zasu biki kinji binta? ta amsa da ameen Baffa. Sai ta shiga fargabar wane irin miji ne daddy ya zaba mata,? ko itama cikin su maccid’o ne ? Oho smma dai abinda ta yarjewa kanta shine koma waye daddy ya zaba mata zata karbe shi da fatan ya zamo Mata alheri.
Yaya Hajara kam tayi murna matuka gaya sai dai Baffa yace kar a bari ta sani alabo ne mijin in sun hadu can sa kwashe ta in yaso ma a fada musu gaskiya kawai.
Yaya halilu ya kira wayar daddy ya fada mishi yadda sukayi da fati wacce ta bar musu wuka da nama. daddy ya sakawa fati albarka fiye da yawan shekarun ta inda mama ma tayi mata ADDU AR samun rabon duniya da lahira.
Su keena da suka taho ba I’mani yan cewa zaizo neman ta koma ta iske shi a kofar gidan Yana jiran ta kamar yadda malam Ango yayi don haka bayan ya sallame su suka taho keena na kokawa skan yadda ba I’mani ya haike mata da yadda warin jikin shi ya ishe ta smma kuma luba na tuna mata suna zuwa zata iske Kaisar yana jiran ta sai tayi murmushi tana fadin
“Ki bari kawai luba ai akwai aiki a gaba na muje dai zuwa ko da Nadiya tana son zaman auren gayen nan sai na fidda ta yasin sai kuma akayi sa a bata ma so .
Da haka suka iso bauci kai tsaye suka wuce makaranta da fatan su sami ganin Kaisar.
Nadiya kam ta rasa yadda zatayi da Kaisar wanda ya mayar da ita gona duk wani kokari da yinkuri baya tasiri sai ya gama abunda Yake so da ita duk da a ranta bata ji zata iys giving up ba. Sai dai kuma ta kasa wani kokari yayin da Kaiser da yan biyu basu da matsala shi dai kam sai wani shining yake Yana Yar kiba yayin da Nadiya kuma ta soma rama kan kace me,? sai ga zazzafan zazzabi ya na damun ta al amarin da ya tuna mata da lokacin bullar cikin yan biyu abinda take ji a yanzu shine yake shirin tabbatar mata da an kuma duk da zuwa yanzu twins watan su biyar suna cikin na shida amma kuwa da akwai tsiya da tashin hankali idan har ya zama ciki ne da ita kamar yadda take tunani.