“Wai yaya Mukhtar me yasa ka faye neman fitina ne don Allah? kana babba amma kana zama karamin mutum? Ni fa Ina dadewa wallahi banji yaya Sufi yayi maganar ka ba in ma yayi to ba aibun ka zai fada ba amma kai har gobe ka kasa mantawa da abinda ya faru? To don Allah kar ka zo din ni dai a cikin yan uwa na Babu wanda Ban gayyata ba kuma bana Rike da kowa don haka yaya Sufi da abubakar duk zasu zo in baka zo ba za a fasa ne ? ni wallahi ka ishe ni da wannan neman janhurun masifar taka haba da Allah mutum sai kace kafuri kai ba a yi maka kuskure ka kawar da Kai sai ka nemi fitina da jidali? to na gayyato Yaya Sufi tunda ma kana da uzuri kaje na yafe maka da na san Marcos zaka fada min maganar Nan wallahi da ban kira ba . gaba kuma kayi ta da Sufi ai ka san hukuncin wanda ya mutu da gaba ko? To ko Kai ko Sufi wallahi sai daya ya tsinci mutuwar daya in kaje gaban Allah sai kayi mishi bayani ai.
Ya tsinke wayar shi ya bar distinguish Mukhtar da sakakken Baki don ya jima da sanin tijarar Usman kar dai a taba shi don abinda yayiwa Sufi aka kwashe kalau da Usman ne da ba ayi hakan ba .
A fusace ya mayar da Kiran ga wayar usman Yana fadin
“Usman dama ka Shirya fada min magana ne shiyasa ka Kira Ni?.
“Da na kira ka nayi maka maganar Sufi ne? Ina ce Kai ka kawo maganar shi kace I zai zo ba zaka zo ba? tun ranar da na nemi sulhu daga gareka kace ba zaka shirya da shi ba na kuma yi maka maganar shi ? Ba barin ka nayi da Allah ba? to don menene zaka ke fada min wannan maganar? ka manta Sufi Dan Uwa na ne da har kake fadan min ko ladar shi zata zamo daya ya Shiga Aljanna ba zaka bashi ba Ni kake fadawa Haka? Don ban fada maka irin zafin da naji ba ne kake Fadin na Gaya maka magana? To Yaya Mukhtar ka hada ni Ni da Sufi ka tsane mu Gaba Daya in kayi hakan ma bakayi laifi ba taro Kar ka zo na San ko taron auren Ya’ya na na gayyato ka ba zaka zo sai menene? Ai Haka dama duniyar ta koma zumuncin Kuma ya Zama.
Ya kashe wayar shi ya bar Distinguish da Mamakin Usman Dan ta kife ne na karshe shiyasa ma Yake tsoron Haye mishi Amma da abubakar ne yayi mishi wannan wulakancin da ya ji shi Amma Usman Kam yaci ya cinye ba Kuma abinda za ayi.
Ranar Daurin aure taro sosai don anyi gayya kuma an Amsa inda Usman Yake ta Shiga Yana fita har aka daura auren Wanda abokin Usman din faruku shima sai hidima Yake inda aka daura sigar auren tsakanin Usman da abubakar wanda suke waliyyan ma auratan don haka dandazon Al ummar suna ta zuwa fatan alheri wa Usman da abubakar inda Mukhtar ya iso Amma sai ya tsaya daga Baki Baki Yana Kiran abubakar yazo suna tsaye yayin da Usman Kuma ya ke tsaye da Sufi da faruku sai ya hango Mukhtar can tsaye tare da abubaka Yana Kuma kallon su Amma Bai zo inda suke ba har Sufi Yana Shirin zuwa wurin sa Amma usman ya Hana shi yace
“Kyale shi tukun Sufi wancan mutumin sai an biyo mishi ta Bayan gida ko zai koma Kan Doka da order.
Haka Mukhtar ya shige motar shi ya wuce Bai ko bi ta Kan su Usman ba
Taro ya tashi inda Usman na Fadin
“Kiran yaron Nan zamuyi Sufi don mu sanar da shi Halin da ake ciki kafin Uban sa ya Rikita Mana Al Amarin.
Abdulhameed kuwa da ya Yankee shawarar zuwa ya sanat da Baffa Alkali Yana son aje mishi neman auren Nadiya don ya San zai fahimce shi a yanzu don dukkan su Yan uwan Uban nashi Baffa alkali ne Mai saukin fahimta don Haka sai ya tuna da abinda ya faru a Baya Wanda son zuciya ya Hana ya Gane gaskiyar Baffa alkali Amma a yanzu ya fahimta kuma ya San shi baya Rike da komai sai alheri don Haka ya shiga mota don zuwa gidan
Yana Kan hanya wayar shi tayi Kara Amma Bai dauka ba sai da yaji ana ta faman Kiran shi don Haka Yana dab da isa gidan Baffa Alkali ganin Kiran sai shigowa yake yass ya dauki wayar sai yaga Baffa Usman ne da sauri ya dauka Yana gaishe shi Yana Fadin
“Wallahi ban San Kai bane Baffa ayi mini afuwa.
“Ba komai Abdulhameed kana Ina ne?
“Gani Nan Nazo gidan Baffa Alkali saboda yarinyar da nake so ne nake son kuje min tambayar auren ta Baffa.
Gaban Usman ya bada dass amma sai yace
“To jira mu gamu Nan zuwa gidan
Ya sauke wayar Yana Fadin
“Kunji yaron nan gashi a gidan Sufi Wai yana so muje mishi tambayar aure? amma muje gidan kawai Ni na san yadda zanyi mishi.
Suka shiga motocin su suka nufi gidan Sufi
Abdulhameed Zaune a gaban haj Safiya suna gaisawa ta kawo mishi Ruwa yayin da abdurrahaman ya fito Yana Fadin
“Wai Boss dama kana Nigeria? Ina mutanen suke ne Tero da Tsageran Nigeria.
Suka cafke suna Dariya suka Shiga fira
Sumayya ta fito suka Dubi juna ita da abdulhameed kafin sukayi dariya yana fadin
“Amma dai ke baki da kirki wallahi yanzu sshe kin dawo Nigeria Amma ko ki neme Ni?
Ta zauna tana fadin
“Momy bata fada maka naje ba?
Ya kada kanshi Yana Fadin
“Da yake ban cika zama gidan ba wata kil kuma ta manta ne.
Shigowar su Baffa alkali ne yasa suka mike don nuna girmamawa garesu
Sun gaishe su ne zasu wuce usman ya tsayar da abdulhameed sumayya da abdurrahaman suka fice suka barsu
Ya zauna a k’asa su kuma suna kan kujera y sake gaishe su Usman ya dube shi Yana Fadin
“Abdulhameed kace tambayar aure za a je maka?
Ya sunkuyar da kanshi Yana Fadin
“Eh Baffa akwai wata yarinya da Baffa Alkali ya San labarin ta Yar gidan Alh iro ce to yanzu dai mun gama daidaituwa shine baban ta yace na fito.
“Masha Allah abdulhameed nayi murna sai dai wani hanzari ba gudu ba kana ji?
Ya dago yana kallon Baffa Usman din jin Yana ambatar wani hanzari ba gudu ba.
“Abdulhameed ka san abinda yake faruwa tsakanin Mukhtar da Sufi?
Ya gyada kanshi Alamar ya Sani.
“To gaskiya Mukhtar yayi nisa a lamarin sa har Yana neman ya Bata mana zumunci abinda Kuma ba zamu tab’a yarda ba Kai ka Sani mu biyar iyayen mu suka Bari Kuma har Allah yayi musu cikawa abdulhameed ban tab’a Jin iyaye na sun samu matsala da Yan uwan su da dangin su ba. To in Sha Allah muma Haka zamu Tafi kafin ku maye gurbin mu . Ka San ko ta wace hanya zamu kawo gyaran Nan ? Ya kada kanshi.
“Ta hanyar ku abdulhameed Kai da sumayya kume kawai zaku kawo Mana daidaituwa har Yaya Mukhtar ya yarda Sufi Dan Uwan sa ne Kuma baiyi abinda yayi don ya tozarta Mukhtar ba gaskiya itace abinda ta kawo Sufi a yau wallahi tallahi da Sufi Yana a yadda Mukhtar Yake kallon sa wallahi da Bai kawo a yau ba Kuma shi kanshi Mukhtar din da bau Zauna lafiya ba Don Haka alhakin gyara zumuncin iyayen ku Yana Nan a Hannun ki Kai da sumayya.
Abubakar ya muskuta Yana Fadin
“Kiran sumayya za ayi Yaya Usman don itama taji da su ne muke son gyara tsakanin Yan uwan mu idan sun bamu goyon baya zamuyi alfahari da haihuwar su idan Kuma Basu bada goyon baya ba to sune suka lalata Mana zumunci Kuma da su zamuyi kuka.
Kan Abdulhameed ya kulle don ya kasa hango ta yadda shi da sumayya zasu Hadu su kawo gyara .
Sumayya ta shigo da sallama ta Duka a gefen Baffa Usman tana Fadin
“Gani Baffa.
Ya dube ta Yana Fadin
“Sumayya an Sha gwagwarmaya duk da ke bakya Nigeria Amma dai in shot Mukhtar Yana gaba da Sufi abinda muka yi iyakar iyawar mu Amma abin yaci tura sai daga karshe muka Gane kune Zaku kawo Mana gyaran da muka kasa kawowa ke da abdulhameed kin Gane?
Ta kada kanta tana fadin
“Baffa hakika ban San komai ba Amma in Sha Allah dukkan abinda kuke so nayi don na kawo sauyin Nan zanyi shi koma meye ban kuma ji Dadin hakan ba.
“To Alhamdulillahi sumayya Allah yayi miki albarka Abdulhameed kaji abinda sumayya ta fada Kai Kuma Yaya kake Gani?
“Baffa Nima dukkan abinda kuke so nayi don ganin komai ya daidaita zanyi in Sha Allah.
“To fakat Kar na jaku da nisa aure a tsakanin ku shine abinda zai daidaita iyayen ku duk da Yaya Mukhtar shine ya Rike abin da zafi Amma Sufi Bai Rike ba don Haka auren ku ma har daura shi anyi a yau din Nan don Haka halaccin da zaku nuna Mana shine ku Rike juna da mutunci ku Kuma nunawa iyayen ku girman zumuncin da Yake tsakanin ku Kar ku yarda a Raba ku ta Haka Yaya Mukhtar zai yarda shine Yake Shirin barin ahalin sa .
Wani Abu ya Daki abdulhameed yayin da sumayya Kuma ta toshe Baki tana zaro idanu.
Abdulhameed ya Runtse idon shi Yana Jin hajijiya na neman maka shi da k’asa.
Baffa Alkali wanda sai a yanzu ne yayi magana Yana Fadin
“Abdulhameed Kar Wanda ya Boye Mana abinda Yake Ransa duk Wanda yaji kamar an zalunce shi Kai da sumayya yayi magana a nan na tabbatar da Yan Uwa na har shi Yaya Mukhtar din basu da nufin zalunci a gareku idan har kunji zaku cutu kuyi magana Kuma karbar auren sumayya ba Yana nufin haramta maka wacce kake so ba Abdulhameed Ni da kaina ne zanyi maka komai na auren waccen .
“Baffa kunfi karfin komai a gareni Babu Kuma abinda zaku saka Ni na kasa yi muku shi Kar Allah ya kawo wannan Ranar da zaku ce nayi na kasa Baffa Nagode da auren Yar uwa ta da kuka girmama Ni da shi Allah yasa ya zamo silar yauka’k’a zumuncin mu in Sha Allah kuwa zan kasance fiye da yadda kuke zato .
Usman ya Rike kafadun Abdulhameed cike da Jin Dadin kalaman shi Yana Fadin
“Masha Allah Alhamdulillahi abdulhameed hakika ka nuna Mana Kai jinin mutanen kirki ne Kai din Mai albarka ne Kuma kamar yadda Sufi ya fada auren sumayya ba zai haramta maka na waccen ba a yau din ma zamu je maka tambaya Allah ta ala yayiwa Rayuwar ka albarka.
“To bamu ji ta bakin sumayya ba itama a Bata damar ta.
“Namiji ma yayi sadaukarwa abubakar bare mace? .
“A a yaya Sufi hakki ne a Bata nata itama.
“Baffa Ina biyayya a gareku da umurnin ku Allah yasa hakan ya Zama alheri s garemu duka Baki daya.
“Ameen ya hayyu ya qayyum sumayya Allah yayiwa Rayuwar ki albarka ya Baku zuria masu albarka wacce zasu kasance mutanen kirki fiye da ku . Su kasance masu biyayya fiye da ku . Don Haka tashi muje ka kaimu gidan Alh iron a yau din Nan in Sha Allah za ayi komai a Gama .
Daddy Alh iro ya karbi bakuncin Mai Shari a Sufi biro tare da Yan uwan sa ya Kuma karbe su cike da mutuntaww don hakikatan ya yarda ya Amince Sufi mutumin kirki ne wanda Yake tabbatar da gaskiya gurbin ta ba irin Dan Uwan sa distinguish Mukhtar Biro ba.
Suka gabatar mishi da abinda ya kawo su a take ya Amsa musu Bayan ya tabbatar musu da komai da ya shafi Rayuwar Nadiya amma dai har gobe Yana nan a matsayin uban ta Kuma zai aurar da ita ne ga abdulhameed ba don Uban sa ba sai don alfarmar Sufi wanda Yake a mutum sak Babu kwana.
Sukayi godiya tare da neman a yanka musu sadaki da komai na aure saboda basa bukatar a ja lokaci.
“Shikenan kuce faduwa tazo daidai da zama nima dama da akwai aure biyu da za a daura karshen watan Nan kunga sai a hade kawai a daura gaba Daya. To Allah yasa alheri muke Shirin kullawa yasa kuma mutuwa ce Rabaww.
Da Haka sukayi sallama da alh iro Wanda ya shiga gida Yana fadawa haj Aliya yadda akayi . Ta Kame Baki tana Fadin
“Allah Mai iko Ashe dai shi Kadai yasan Al Amarin da ya shirya tsakanin sa da yarinyar Nan duk wannan Abu da ya faru Bai ji ya fasa ba,? Lallai so Daya yakewa yarinyar Nan Allah yasa hakan ya zama alheri ai na ga ta shiga taitayin ta har ta San ta tashi ta Kama Aikin gida ba tare da nace tashi kiyi ba? Girkin gidan Nan fa yanzu itace take yin sa ta wanke ta share wani lokacin har tausaya Mata nake Amma da ta tsaya a Haka da yanzy ta wuce Haka Amma Allah ya shirya Mata dama ita duniya maganin Mai kokari take.
“Haka ne amma Aliya Ina ganin kamar alabo fa yana shirin bani kunya har yanzu fa bai je gidan Alh sule ba .
“Ba zai baka kumya ba Daddy bari zan kira shi ai yadda kukayi nufin hada wannan alherin in Sha Allah sai kun cika shi.
Alabo ya dauki wayar mama yana gaishe ta ta Amsa tana tambayar shi yaje kuwa gidan Alh sule?.
“Mama ban je ba gaskiya don Ina ganin kamar ba zan iya yiwa yarinyar nan adalci ba kar nazo na cuce ta .
“Kana nufin zaka zauna a Haka kenan? Kana nufin zaka bawa Daddy kunya baban? dukkan musulmin da yayi I’mani da kaddara fa mika hannu Yake ya Karbe ta ya Kuma gode wata Kil fa Rabo ne ya zo muku da Hakan idan kaki to kana son kayi jayayya da ikon Allah don haka in dai na Isa da kai kaje wurin yarinyar nan ku daidaita da Rabo Mai kashewa gara Mai Rabawa kaji Baban.
“To mama in sha Allah yau zanje kin Isa kiyi komai wallahi damuwa nake da ita ne mama shiyasa kika ga ban kuma bi ta kan yarinyar nan ba ne smma in Sha Allah yau zanje Kuma wata Kil haka Allah ya Shirya mini.
“Yauwa to ka gani ? Allah yayi maka albarka ya yayi maka maganin damuwar ka baban.
Ya Amsa sukayi sallama
A Ranar kuwa ya je gidan Alh sule suka zanta da zainab wacce Bai zaci zai ganta kyakkyawa fiye da zaton shi ba . In Banda hadi ma ai ya san zainab tafi karfin ajin sa Amma sai ya sami kansa da nunawa zainab Yana yin ta itama da Yake mace ce mai saukin fahimta sai suka daidaita har Yana nata kyauta sukayi sallama har da musayar lambar waya sukayi sallama ya wuce Yana tunanin da yayiwa Kansa don Bai tab’a zaton zainab din yarinya ce irin haka ba yayi zaton tunda aka ce jawara ce to cutar sa kawai za ayi a jona mishi lika lika
Sai ga dan bawan Allah yana kiran wayar zainab Yana fada mata abinda yake zuciyar sa da son lallai ta aminta dashi . Zuciyar mace kogin sirri tuni ya mallake ta aka Shiga musayar kalamai har zuwa Ranar da aka daura aure uku a kofar gidan Alh iro. Auren Nadiya da Abdulhameed. Alabo da zainab Fati da Kuma Kaisar bisa wakilcin su Baffa Alkali da yaj Uwan sa Usman da abubakar. Yayin da alh iro ya zama wakilin zainab Alh sule kuma ya zama na Nadiya inda a Ranar Daddy Alh iro yace kowace ta tare a gidan mijin ta amma tace yayi hakuri har zuwa Sati a karasa musu siyayya.