Safiyya ta kalli Fatima tace “ ki kwantar da hankalinki ki natsu don yau basuzo makarantaba kuma muna da labarin sai sunyi kwana biyu kafin su dawo don ko tafiya basa iyawa, sodoji mugayene wallahi akwai iya bada horo da duty. Iyayensu sun zo jin ba'asi, aka sanaar dasu ba anan abin ya faru ba can wajene suma malaman basa da masaniya akai, sai iyayen suka ɗaukar masu( fermision) na kwana biyu idon sun warke sai su dawo, haka mukaji abakin malamai.
Wani gwauron lumfashi Fatima ta saukee tare da faɗin "Alhamdulilllah har naji wani daɗi yanzuko zan baku. . .
