Skip to content
Part 4 of 14 in the Series Ba'indiya by Haiman Raees

Ta’aziyyar Dilip Kumar

Da sunan Allahna mai girma

Wannan da ya yo mu mai rahama

A wurinsa gafara muke nema

Mun yarda da kai babu tantama.

Tsira da aminci mai girma

Ga manzon mu mai girma

Wannan da muke yi wa hidima

Duk wanda ya so ba shi nadama.

Kwana dai in har ya ƙare

Tafiya ba wanda zai kare

Ba ‘ya’ya ba matan aure

Hakanan ranka za fa a zare.

Ko ka yo aikin alheri

Ko kuma ka yo na sharri

Hakanan za a saka cikin kabari

Wannan shi ne batu na zahiri.

Dilipu Allah ya jiƙanka

Ya gafarta maka laifinka

Ya shafe maka zunubanka

Ya ƙaro haƙuri ga iyalanka.

Allahu ya sa mutuwa ta zam hutu

Na cutuka da suka yi katutu

Ya zamo tafiya ta zama hutu

Kowa tabbas ai za ya mutu.

Allah muna roƙo ka yo rahama

Ga bawan nan naka mai himma

Ka sa ya ruwan ƙorama

Ƙoramar tafki na rahama.

Saura mu ma muna kan hanya

Allahu gare mu Ka yo shiriya

Mu zamo mun zauna kan hanya

Mu daina faɗa ko jayayya.

In lokaci yayi cikin sa’a

Mu tafi muna a cikin sa’a

Bakin mu da sunan Allahna

Da abin sona manzona.

Haimana ne yake yin baiti

Baitin batu da ke kan saiti

Saitin da sam ya fi na titi

Allah tsare mu da yawon dandi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 10

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ba’indiya 3Ba’indiya 5 >>

4 thoughts on “Ba’indiya 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×