Skip to content
Part 15 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Garar Amarya

Zaune amaryar take akan tafkeken gadonta tana murmushi, a can ƙarƙashin zuciyarta kuma tana mai ƙara godewa Allah bisa cika mata burinta da ya yi. Shekaru shida kenan suna soyayya da mijin nata, amma sai Juma’ar da ta gabata Allah ya nufa aka ɗaura musu aure. Babu irin surutun da ba a yi akan auren ba, amma Allah ya nufa dai sai an yi.

Daga mijin har danginsa sun yi matuƙar ƙoƙari wajen yin hidima a lokacin wannan biki. Iyayen amaryar kuwa, ba a cewa komai. Irin garar da suka kawo wa ɗiyar tasu, rabon da ka ji irin haka an manta ma. Manja galan huɗu suka kawo mata manya, haka ma man gyaɗa, kai hatta man shahu shima sai da suka kawo galan biyu manya. Shinkafa buhu biyar suka kawo, masara kuwa buhu goma cur suka kawo. Maiwa da dauro da ibaro da dawa buhu uku-uku suka kawo. Gurjiya da gyaɗa buhu ɗaya ɗaya suka kawo, barkono ma buhu suka kawo mata. Kai in taƙaice maka labari dai, kusan komai buhu buhu suka kawo. Hatta citta, ƙaramin buhu suka ciko da ita. Albasa kuwa kwando biyar suka zo mata da shi. A lissafi dai, kayan garar da iyayen yarinyar nan suka haɗa mata, in dai Allah ya ba su rabo da wuri, to har bayan suna ma ba lallai ne mijin ya yi wata siyayya game da kayan abinci ba.

Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba. Domin kuwa duk wanda ya zo sai ya yaba. Kuma ta san iyayenta sun fitar da ita kunya a wurin dangin miji da maƙwafta. Balle kuma shi mijin, wanda aka yi wa babban taimako.

Satin su guda kenan da yin aure. Komai na tafiya musu daidai. Inda suke babu wata hayaniya saboda sabon wuri ne, kuma G.R.A ne ba damuwa kowa ya yi da kowa ba. Kuma da yake ba ta fara girki ba, bata da wani aiki face bacci. Yanzu haka ma baccin take ji, ganin mijin nata ya tafi masallacin juma’a kuma daga can zai wuce wani wajen ba dawowa zai yi da wuri ba ya sa ta kwanciya. Nan take kuwa baccin ya kwashe ta. Ba Ita ta farka ba sai kusan la’asar.

Ko da ta farka, sallah kawai ta yi ta nufi kitchen da nufin ta samu abin da za ta zuba a cikinta. Domin da wata irin yunwa ta farka kamar za ta ci babu. Shigar ta kitchen ke da wuya sai ta yi turus! Domin wayam ta ga ɗakin girkin. Babu ko guda ɗaya. A’aha, me ke faruwa to? Ta duba duk wani wuri da ta san sun ɗan ajiye kayan maƙulashe amma shiru ba ta ga komai ba. Cikin hanzari ta nufi store domin ta duba kayan garar da aka kawo mata. Me za ta gani? Babu ko ƙwayar hatsi a store ɗin. Galan-galan ɗin man gyaɗa da na ja da na shanun duk babu ko ɗaya.

Nan fa amarya ta fito tsakar gida a rikice tana hawayen takaici da tashin hankali. Kafin wani lokaci duk ta fita hayyacinta, yunwar da take ji kanta ta neme ta ta rasa. Dama gidan basu sa mai gadi ba tukunna saboda basu samu irin wanda suke so ba. Don haka sai ta yi hanzari ta yi bakin ƙofa ko za ta ga wani. Ai kuwa sai ta ga gate a wangame. Nan fa ta ruga a guje ta yi waje kai ba ko ɗankwali amma ba ta ga kowa ba. Fitowar ta ke da wuya ta ci karo da angon nata ya dawo. Nan fa ta fara zayyana mishi abinda ke faruwa. Shi kuwa ya yi ƙememe akan lallai da haɗin bakinta hakan ya faru. Abu dai kamar wasa har ya kai su ga zage-zage, daga ƙarshe ma dai ya sake ta ta koma gidansu.

<< Bakar Kaddara 14Bakar Kaddara 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.