Mummunar Ƙaddara
Ruwa ake tsugagawa kamar da bakin ƙwarya. Ko’ina mutum ya duba ruwa ne ke gudu kwararo-kwararo yana wucewa. Inda bai samu hanya ba kuma sai ya samar wa kanshi da ƙarfin tsiya.
Tun bayan La’asar aka fara wannan ruwa, gashi har goma da rabi na dare ba a daina ba. Tafe Zubairu yake a cikin wannan ruwa ruwa da ake ta tsugagawa, a zuciyarshi yana addu’ar Allah ya kawo mishi mai abin hawan da zai ɗauke shi ko nawa ne ya biya.
Ya yi duk iya ƙoƙarin da zai iya yi wajen ganin ya samu abin hawa amma bai samu ba. Ko da yake masu ababen hawa da yawa na wucewa ta hanyar, duk wanda ya sa wa hannu da nufin ya tsaya sai dai ka ga ya wuce fuuu! Ba tare ya kula da ko inda yake ba. Wasu ma har ruwan da ke gudu akan titin sukan watsa mishi yayin da suka bi ta ciki da ababen hawan nasu.
Babban abin da ya fi tayar mishi shi ne irin halin da ya baro iyalansa a ciki. Ya san yanzu haka suna can sun baza idanu suna jiran su ga dawowar shi gida. Domin ko ƙwayar hatsi bai bar musu a gidan ba. Matuƙar ba matarshi Suwaiba ta yi musu wata dabara irin tasu ta mata ba, to ya tabbatar yanzun haka yaran na can na kukan yunwa.
A duniya babu abinda Zubairu ya tsana sama da ganin hawayen ‘ya’yansa. Zai iya yin komai domin ganin murmushi a fuskokinsu. Yanzu haka ma ji yake kamar ya yi fuffuke ya gan shi a gida kusa da su. Abubuwan da ya siyo musu na tsaraba cike da baƙar leda ya ƙara gyara wa zama a hannunsa na dama sannan ya ci gaba da tafiya a cikin ruwan. Ba tare da tausayin halin da yake ciki ba kuwa, ruwan ya ci gaba da dukan shi babu ƙaƙƙautawa.
Bayan ya shafe kusan awanni uku yana tafiya ne, sai ya iso wani wuri da ake yi wa laƙabi da ‘Kai Ka Kai Kanka’ dama tuni yake tunanin yadda za a yi ya wuce wannan wuri lafiya. Saboda wuri ne mai hatsarin gaske. Wuri ne da mugaye ke yawan zama saboda yanayinsa. Tun daga ‘yan shaye-shaye, ɓarayi, ‘yan daba kai har da ‘yan fashi ma an ce suna ɓoyewa a wurin. Babban abin da ya ke ba kowa mamaki shi ne, har yanzu an kasa yin kome game da wurin. Sai dai yau a kawo sumame a kama na kamawa a kashe na kashewa, wani lokacin ma a sake yin haka. Wato dai masu laifi sun kasa hana jami’ai zuwa wurin, suma sun kasa tashin su daga wurin.
Haka dai Zubairu ya ci gaba da tafiya zuciyar shi na ɗar-ɗar kamar za ta fasa ƙirjinshi ta fito. Ko da ya zo dadai inda wani tsohon gini yake kawai sai gani ya yi ƙarata sanye da baƙaƙen kaya, kowannensu na riƙe da makami. Wasu adda, wasu gariyo, wasu kuma bindigogi suke riƙe da su. Kafin ka ce kwabo sun zagaye shi. Basu ce da shi komai ba, sai ɗaya daga cikinsu kawai da ya miƙo mai hannu da alamar ya miƙo musu abin da ke hannun shi. Jikin Zubairu na karkarwa ya miƙa musu. Ɓarawon ya kai hannu kenan zai karɓa, kwatsam ba zato ba tsammani sai ganin motocin ‘Yansanda guda huɗu suka yi sun danno wurin. Ba tare da wani ɓata lokaci ba kuma suka fara sakarwa waɗannan ɓarayin wuta. Nan fa su ma suka fara mayar da martani. A cikin wannan yanayi na musayar wuta ne wani harsashi da aka harbo ya nutse a ƙirjin Zubairu, nan take ya faɗi matacce ba tare da ya shura ba. Tunanin iyalansa ne abu na ƙarshe da ya zo masa a rai kafin ransa ya fita daga gangar jikinsa.