Munara tayi masa wani kallo mai had'e da harara tace, "Kaci nasara an d'auke ka aikin amma ka sani misbehave kad'an zai sa ka bar gidannan a wulak'ance, yanzu ka jirani inzo aikinka zai fara."
Bayan shigarta gida da minti biyar sai gata ta fito da kaya dunk'ule a hijabinta, tana zuwa ta watsa masa a fuska tace
"Gasu kaje ka wanke man yanzunnan."
Da sauri ya kai kallonshi a k'asa inda kayan suke watse, aikuwa sai ga bra ta kai goma zube k'asa yana k'are masu kallo d'aya bayan d. . .