Skip to content
Part 3 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

Munara tayi masa wani kallo mai had’e da harara tace, “Kaci nasara an d’auke ka aikin amma ka sani misbehave kad’an zai sa ka bar gidannan a wulak’ance, yanzu ka jirani inzo aikinka zai fara.”

Bayan shigarta gida da minti biyar sai gata ta fito da kaya dunk’ule a hijabinta, tana zuwa ta watsa masa a fuska tace

“Gasu kaje ka wanke man yanzunnan.”

Da sauri ya kai kallonshi a k’asa inda kayan suke watse, aikuwa sai ga bra ta kai goma zube k’asa yana k’are masu kallo d’aya bayan d’aya.

*****

Shin wai wanene basarake? Honey’n Munara, kuma mutuminta mai fuskar shanu.

Aliyu Haidar shine ainahin sunanshi, wanda ya kasance d’a a wurin Alhaji Dikko mai gwalagwalai, wanda mutane suke yiwa lak’abi da sunan Dikko mai Gwal.

Dikko mai gwal mai arzik’i ne sosai wanda duniyar masu kud’i kanta tasan da zamanshi, siyar da Gwalagwalai itace sana’ar da ya rik’a kuma ta zamo silar arzik’inshi, wanda ta k’ark’ashinshi mutane da dama suke cin abinci har suma suyi wa wasu hanyar samu, kasancewar shi mutum ne shi da baya son tauyewa na k’asa dashi hanyar hak’k’insu, baya bak’in cikin ta sanadinshi kai ma ka zamo wani abu, saboda ALLAH ya azurtashi da kyakkyawar zuciya da d’inbin arzik’i, wanda shi kanshi bai san iya adadin dukiyar da ya mallaka ba,ta sanadin wannan sana’ar da ya gada a wurin mahaifinshi.

A yanzu haka Matanshi hud’u amma babu wadda ALLAH ya baiwa haifuwa dashi sai mahaifiyar Aliyu Haidar, wanda ake yiwa lak’abi da suna *Basarake*, wadda ta kasance matarsa ta farko a yanzu, duk da ainahi cen ba itace matarshi ta farko ba, saboda bai aure ta ba har sai da Matarshi ta farkon ta rasu, wadda suka yi are irin na saurayi da budurwa amma har ta kwanta dama ALLAH bai bata haihuwa da shi ba, kuma bai yi sha’awar k’arin aure ba har sai bayan rasuwarta.

Wata rana yana tafe a kan hanya sun kawo wurin wata roundabout, inda danja ta tsayar dasu mutane suka yi cincirindo da ababen hawansu, suna jiran lokacin da za’a basu damar da za su wuce, Alhaji Dikko yana duba wata jaridar dake hannunshi sai ga wata ‘yar matashiyar budurwa irin sadakar yalla d’innan, sai k’wank’wasa masa glass d’in mota takeyi wadda alamu suka nuna mabaraciya ce, saboda yanda take nuna masa hannu alamar rok’o, da fuskarta da ta zama kalar tausayi idanuwanta sunyi ja wadda a duba na farko zaka gano kukan da tasha, a lokaci d’aya Alhajin yaji ta bashi tausayi sosai duba da yanayinta da ya gani, direban har ya fara yimata fad’a yana korarta, Alhaji ya sauke glass da niyyar yaji k’orafinta aiko sai ga muryarta tar tar tana fad’in, “Don ALLAH Alhaji ka taimakeni mahaifiyata bata da lafiya, in sami abunda zan siyo mata magani.”

Alhajin ya ciro kud’in da shi kanshi baisan ko nawa bane ya mik’a mata, jikinta yana rawa ta zuro hannu ta karb’e tareda barin wajen da gudu ta nufi wata ‘yar hanya har ta shige lungun yana kallonta, haka kawai Alhaji yaji yana sha’awar ya sani shin da gaske mahaifiyarta ce ba lafiyar ko kuma k’arya ce takeyi irin ta mabaratan, a take yace da direban idan sun fita ya samu guri ya tsaya subi yarinyar cen, aiko ana basu hannu suka fito cincirindon ababen hawar dake wurin suka sami wani wuri suka tsaya, Alhajin ya fito tareda direban suka bi hanyar da suka ga tabi, abin mamaki suna shiga lungun suka hango taron mutane suna ta kallon wani abu, koda suka isa wurin sai suka ga ashe yarinyar ce rungume da wata mata sai magagin mutuwa take yi, wadda a duba d’aya zaka gano mahaifiyarta ce saboda kamar da suke yi da juna sosai,yarinyar sai kuka take yi tausayinsu ya kama Alhaji matuk’a saboda ganin ba wanda yayi yunk’urin taimaka masu a wurin, shiyasa ba wani b’ata lokaci yace a d’aukota suje asibiti, aiko matan da ke wurin suna kallo suka talallabo ta yarinyar tana biye dasu tana kuka aka saka ta mota tareda d’iyarta, Alhajin yace da direban yayi sauri su je asibiti saboda matar tana cikin mawuyacin hali.

Da zuwansu asibitin aka karb’e ta likitoci suka rufu a kanta, bayan d’an lokaci da shigarta ne wani likita ya fito yace da Alhaji su shiga matar tana son ganinsu shi da ‘yarta, jikin Alhajin a mace ya nufi d’akin da aka shiga da matar yarinyar tana biye dashi sai sharb’ar kuka take yi.

Koda suka shiga yanayin da ya ga matar a ciki ne yasa jikinshi ya k’ara yin sanyi k’alau, matar sai kiran sunan ‘yarta take mai suna Mu’azatu, da sauri yarinyar taje wurinta tana kuka gwanin ban tausayi, mahaifiyar ta fara magana kamar haka, “Alhaji duk da bansanka ba amma yanayinka ya nuna kai mutumin kirki ne, na baka amanar ‘yata don ni nasan tawa ta k’are mu ‘yan k’asar agadas ne idan ‘yata ta nemi sanin danginmu duk suna cen gidan sarkin agadas, da kaje kace innayo ni kad’ai ce a duk familynmu, Allah ya taya ka rik’on mu’azatu na baka amanarta ko bayan raina bance ka baiwa kowa ita ba kai naba ita halas malas, mu’azatu kiyi hak’uri kiyi hak’uri ALLAH yayi maki albarka da ke da zuri’arki gaba d’aya idan kin had’u da iyayena kice su yafeman laifin da nayi masu don ALLAH su yafe ma….. .”

Daga nan kuka yaci k’arfinta numfashinta ya sark’e ta fara shak’uwa, likitoci suka yo kanka duk iya k’ok’arinsu basu hana mata amsa kiran Ubangiji ba, mu’azatu kam tana tabbatar da mahaifiyarta ta rasu sai gata a k’asa ta fad’i somammiya, hankalin Alhaji ya k’ara tashi da sauri aka bata gado bayan an samu ta farfad’o aka yi mata allurar bacci, har aka je aka rufe mahaifiyarta bata sani ba, sai bayan ta tashi ne, Alhaji yayi mata bayani tareda bata hak’uri, sannan ya kwasheta yakai gidanshi yana bata kulawa tamkar wata k’anwarshi ta wadda suka fito ciki d’aya, bayan wasu ‘yan kwanaki yayi masu shirin zuwa k’asar agadas suka lula.

*****

Basu sha wahala ba wajen gano ahalin innayo ba, kasancewar gidan sarkin Agadas suka nema kai tsaye, ALLAH ya taimakesu suka sami ganin sarkin ba tareda sun sha wata wahala ba, saboda kamar da mu’azatu take yi da familyn gidan jalaludden jamil sarkin agadas tsoho mai ran k’arfe, wanda yaci lokacinshi kuma ya ke cin na wasu, don a lokacin shekarunshi zasu kai saba’in amman kar yake ba wani alamun mugun tsufa da ya bayyana a jikinshi.

Bayan sun kai gaisuwa a wurin sarkin ne kafin ma Alhaji yayi bayanin abunda yazo dasu ne, sarkin ya k’urawa mu’azatu idanuwa a cikin muryarshi mai cike da tak’ama yace, “Duk inda wannan yarinyar ta fito tabbas jinin jalaludden ce.”

Alhaji wani farinciki ya lullub’e shi saboda ganin komi zai zo masa da sauk’i a cikin kwantar da murya ya fara bayani kamar haka, “Tabbas wannan yarinya ‘ya ce a wurin ‘yarka Innayo.”

Ba shiri sarkin ya fara zubar hawaye cikin muryar kuka yace, “Ina kuka baro man ‘yata innayo? duk girman laifin da tayi mani na yafe mata duniya da lahira, ‘ya mai ladabi da biyayya amma saboda soyayya ta zab’i ta rabu da ahalinta, don ALLAH ku sanar dani ina ‘yata innayo?saboda ina son in nemi yafiyar ‘yata”

Mu’azatu ta fashe da kuka Alhaji ya sunkuyar da kai a cikin damuwa yace, “Sai dai ku bita da addu’a domin innayo ta rigamu gidan gaskiya.”

Daga nan ya kwashe abunda ya sani ya sanar da sarki, sarki da sauran masu ruwa aji na fadar sai taya sarki kukan rasuwar ‘yarshi sukeyi, sarki ya taso da kanshi ya ri’ko hannun mu’azatu suka shiga cikin gida, kai tsaye d’akin mahaifiyar innayo ya kaita, bayan yayi mata bayanin abunda yake faruwa kafin kace me gidan sarki ya runtume da koke koken kukan rasuwar innayo, saboda innayo ‘yace wadda ta taso mai farinjini da tsantsar ladabi da biyayya ga kowa, innayo ta zuba lokaci a zamani k’urciyarta har zuwa lokacin aurenta, inda sarakuna da manyan attajirai suka yi ta rubibin aurenta, amman zuwan wani bak’on Nigeria gidan sarkin ya hargitsa kwakwalwar innayo, wanda akanshi ne ta zab’i ta bar mahaifarta da ahalinta, saboda nacewar da tayi akan soyayyarshi shine yayi silar rabuwarta da danginta bayan an d’aura masu aure, amman da sharad’in bata ba ahalinta kuma duk taji ta amince ta biyo angonta zuwa k’asar Nigeria.

Wanda shi kuma ya kasa rik’on amanar innayo ya dinga gasa mata aya a hannu har lokacin da ALLAH ya azurta ta da haihuwar mu’azatu, uk’uba babu wadda bata sha ba a hannunshi abinci ma sai wanda yaga ALLAH ya taimako ta dashi sannan take ci, batasan kowa ba sai ALLAH sai shi shiyasa lokacin da ya saketa tayi ta tanb’ele ita da ‘yarta, rayuwa tayi masu tsanani basu wannan gida aikatau basu wancen, daga baya dai suka fad’a sana’ar bara bak’in ciki yayi mata yawa ta fara ciyo a tsaye wanda shine yayi silar kwantar da ita magashiyyan, wanda a sanadinshi ne suka had’u da ALHAJI Dikko har zuwa lokacin ajalinta.

Alhaji Dikko bai baro k’asar ba har sai da aka d’aura masa aure da mu’azatu, saboda a cikawa innayo wasiyyarta, bayan an sanar da dangin baban mu’azatun inda d’aya daga cikinsu ya wakilci aurenta, haka Alhaji ya tattaro amaryarsa tareda rakiyar dangin mahaifiyarta zuwa gidanshi.

Shekara d’aya da aurensu mu’azatu ta haifi santalelen d’anta, mai kama da ahalin gidan sarki jalaludden sak!, Alhaji da danginshi sunyi farin ciki sosai da wannan haihuwa, rana ta zagayo aka sawa yaro suna ALIYU HAIDAR, fad’in shagalin da aka yi a wannan lokaci ba b’ata baki ne, domin kuwa nera tasha kashi sosai marok’a da makad’a sun tabbatar da lalle wannan yaro d’an gata ne, Aliyu haidar ya taso a cikin kula da tattali na mutane da yawa, ta b’angaren uwa da uba kowa sai sam barka musamman mahaifinshi Alhaji Dikko da yake ji dashi tamkar tsoka d’aya a miya.

Aliyu har ya kai shekara goma amma ko b’atan wata mu’azatu bata sake yi ba, ganin haka ne Alhajin Dikko yayi sha’awar k’ara aure koda ALLAH zai sa ya sake samun wata haihuwar, sai gashi itama matar da ya auro har tayi shekara biyu shiru, aka bashi shawarar ya sake wani auren koda rabon a cen yake, aiko baiyi k’asa a gwiwa ba ya sake wani auren itama dai haka tabi sahun ‘yar uwarta shiru ba wani labari, Alhaji bai yi k’asa a gwiwa ba ya k’ara murzo sabuwar amaryarshi sabuwa dal a kwali, sai gashi ita d’in dai ba wani alamun haihuwar har tsawon shekara, daga nan Alhaji yayi saranda ya garzaya asibitoci domin a binciki lafiyarshi, binciken farko aka gano matsalar daga gareshi ne, aka had’o shi da magunguna ya dinga sha amma har izuwa wannan lokaci ba canji.

Shiyasa ya d’auki son duniya ya d’ora akan Aliyu haidar wanda yanayin yanda yake tafiyar da takunshi a rayuwa yasa ake kiranshi da suna BASARAKE, yayin da matan Alhaji suke neman ina wuta su kad’a shi, saboda bak’in cikin rashin samun haihuwar da basu yi da Alhajin ba, shiyasa dukansu ukun kowace da kalar tuggun da take had’awa tilon d’an Alhaji Dikko wato basarake, wanda ALLAH ya ke ta tsallake shi da sharrinsu, a sanadinsu ne yasa ya shiga tsoron mata da sharroransu, wad’anda yayi karatunsu tun a cikin gidansu kafin shima ya mallaki tashi matar, wadda ta kanta ne ya k’ara sarewa da lamarin mata saboda ko wata biyar ba’a rufa ba auren ya watse, wanda tun daga lokacin ya tsani mata da miyagun halayen wasu daga cikinsu, shiyasa ya yi shiri sosai akan wajen neman auren da yake so yayi a wannan lokaci, wanda mahaifiyarshi da kakarshi wadda ta haifi Alhaji Dikko, suke ta damunsa akan sai ya yi dole, a cewarsu ko don suga irinshi kafin SU bar duniya, musamman dai ita Kakale da a kullum yaje wurinta sai tayi kuka akan rashin aurenshi, wai tana so kafin ta mutu taga ‘ya’yan da zai haifa da idanunta.

BASARAKE ingarman Namiji ne fari dogo son kowa k’in wanda ya rasa, mutum ne shi miskili wanda ko a magana zaka gano miskilancinsa, mutum ne shi wanda baya son hayaniya wanda a komi nashi yana yin shi ne a cikin nutsuwa, ko tafiyar shi a cikin tak’ama yake yinta tun yana d’an yaronshi.

Yayi karatunshi tun daga secondary har zuwa jami’a a k’asar agadas, shiyasa duk wani taku irin na manyan sarakai ya iya,saboda rayuwar da yayi a masarautar, wadda a yanzu haka yayan kakarshi innayo shine akan kujerar mulkin.

Farkon had’uwarshi da Munara a face book inda tayi ta damunshi saboda hotunanshi da ta tab’a gani, wad’anda ta dalilinsu ne Munara ta haukace da son Basarake, tun baya kulata har shima ya fara bata kulawa, sannu a hankali soyayya ta shiga tsakaninsu, inda a kullum suna lik’e da waya suna nunawa junansu k’auna, labarinta kaf babu wanda Munara bata sanar dashi ba, pic’s d’inta a wayarshi ba adadi inda anan ne ya gano Munara da Munawwara ‘yan biyu ne.

Tabbas yana son munara sosai amma rawar kanta da ya fahimta ne yasa ya yanke shawarar ya jarabata kafin ya bayyana kanshi a gidansu sai gashi aka yi rashin sa’a jininta sam bai had’u da bak’on yanayinshi ba.

Wanda ya ajiye ayukanshi kaf ya tare garin kaduna, saboda kawai gayyatar da tayi masa akan aikin da zata bashi gidansu, sunsha dirama sosai da abokinshi Musty kafin ya yi wannan tafiya, wanda shine ya rako shi a lokacin zuwanshi na farko gidansu Munara, saboda ya nuna masa ya rabuda ita kawai ya nemi wata, shi kuma ya nuna sai yaga iya k’arshen gudun ruwanta, ya rok’eshi akan kada ya fad’awa kowa abunda yake kaishi kaduna, saboda yayi wa Alhajinshi k’aryar wata hark’allar kasuwanci ne yake fafutuka a cen, sai gashi aikinshi na farko gidan nasu Munara yaci karo da wankin bra

Ci Gaban Labari

Idanuwan basarake akan bireziyoyin Munara dake zube a k’asa, jikinshi yayi sanyi k’alau a hankali ya d’ago kanshi domin yakai kallonshi a fuskarta, amma wayam ba Munara babu alamunta sai Munawwa da ke k’arasowa wurinshi, fuskarta cike da damuwa saboda jin haushin abunda ‘yar uwarta tayi, saboda gaban idanuwanta Munara ta had’o su ta fito, sai gashi kuma ta ganta ta dawo tana k’unshe dariya a gaban Mummy, shiyasa zuciyarta ta bata ta fito ta ga wace wainar ce take toyawa, aikuwa sai gashi ta hango tulin bireziyoyinta gaban Basarake, ranta ya b’ace sosai tana zuwa ta duk’a ta kwashe su a cikin jin kunyar abunda Munara tayi ta dake kawai ta feshe shi da wani murmushi tace dashi, “Don ALLAH kayi hak’uri bata zaci su ne ta kwaso ba.”

Tana k’are maganar ta shige gida Munara dake falo tare da Mummy tana karyawa, sai ga Munawwara ta shigo da bra’s d’in ta a jiye mata akan kujera, a cikin fushi tace da ita, “Ga kayanki nan ki canza masa wani aikin don wannan ba mutuncin gidanmu ba ne.”

Munara ta bi kayan da kallo zuciyarta a cike da jin zafin abunda Munawwa tayi mata a gaban Mummy, don tasan daman…

<< Bakon Yanayi 2Bakon Yanayi 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×