Skip to content
Part 48 of 52 in the Series Mijin Ta Ce by Hafsat C. Sodangi

Na daga ido na kalle shi cikin natsuwa, na tambaye shi wani abu ya faru ne? ya ce me kika gani? Na ce uh’uh nayi shiru naci gaba da abinda nake yi, shima ya kashe wayoyin nashi ya kara gyarawa Baba Yahya jinginon da yayi a jikinshi yana bacci wai don ya kara jin dadi.

Jimawa can sai naji ya ce min ke a rayuwari ai ke ‘yar gata ce Humairah nayi maza na ce mishi da aka yi me? ya ce to kin rayu tare da uwa da uba da Kakanni na bangaren uwa da uba.

Ki duba kiga Hajiyar Giyade irin yawan ran da baiwar Allahn nan tayi, bara ne fa ta rasu. Nayi maza na ce mishi eh, ai daga rasuwar tata ne ma na kara tsorata da rashin lafiyar Mallam.

Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min, to ki kara tsorata Humairah, Mallam zai yi ta zama a duniya ne, jikokinshi na farko-farkon fa sa’o’in Gambo ne, mutumin da yayi irin wannan yawan ran ya bar zuriya mai albarka irin ta Malla ya’ya da jikoki da ya’yan jikoki ba a san yawansu ba.

Su Nusaiba nan duk ba yawan ranne yasa suka san shi ba, ke kina zama kiyi nazari da tunani kan ya’ yan da suka rayu rayuwa irin tawa Humairah?

Nayi maza na daga ido na kalle shi ya ce, ni kam ai maraya ne Humaira, tunda ban san mahaifiyata ba.

Babana ya rasu tun ban isa komai ba, a haka na taso a tsakanin gidajen ‘yan uwa da makwabta babu wani tsayayyen da za ka gani a tsaye akan al’amarinka, haka nayi ta dibi-dibin da nayi karatun primary da secondary a lalace.

Saboda ina ganin wasu yaran unguwar yan kadan suna zuwa a irin wannan lokacin ne fa Mama tazo ta tafi dani, kafin zuwana hannun Mama ban taba dandanar wani abu mai sunan dadi ba.

To ke fa ? A cikin gatanki ki ka rayu mutanen da suke sonki suna kewaye dake, don haka kar muje gida ki samu jikinshi yayi tsanani kice zaki yi ta rusa kuka wannan al’ada ce ta jahiliyya wacce kuma aka hanata.

Cikin natsuwa da sanyin jiki na kalle shi na ce jikin nashi yayi tsanani kenan ko? Bai yi musu ba ya ce eh, gaba daya muka kama bakunanmu muka yi shiru, sai addu’a kawai muke yi.

Mun isa Bauchi wajen sha daya da rabi ne na safe saboda samnmakon da muka yi, ga kuma mota lafiyayya uwa uba kuma shi ne mun godewa Ubangiji ya tsare mana hanyar.

Tun daga karya kwanan layin runfuna ne a kakkafe, Jama’aa ciccike har lokacin kuma Jama’a isowa suke tayi, jikina ya dauki rawa kar-kar-kar. Ado ya kama ni ya rike a jikinshi.

Kiyi hakuri Humairah, tun a hanya an gaya min Mallam lokacin shi ya yi, ban gaya miki ba ne don kar tafiyar ta zamo mana mai tsanani da yawa, kiyi kuka ta hanyar zubar da hawaye ba laifi ba ne, amma kar kiyi wani abinda ya sabawa Shari’a.

Tunda kullum a cikin karatu ki ke, karatu na addini. To shi karatu da ki ke ganinshi yadda duk ya kai da yawa to bai da wani amfani matukar mai shi din ba zai yi aiki da abinda ya sani ba.

Shi yasa ma sai aka ce mana babu wani sani sai wanda aka yi aiki dashi. Ado yana yi min wadanan baya nan tuni ni kam hawaye da majina zuba kawai suke yi min.

Jama’a suka tartaso don ganin isowar Ado, suna yi mishi sannu da zuwa Alhaji, barka da isowa, abin da suke fada mishi kenan yana amsawa, amma hankalinshi yana kaina, na yadda zan yi in wuce cincirindon Jama’ar da ke zaune in shiga gida.

Rike Mamanku Nusaiba, tayi maza ta kama ni ta rike ungo jakar nan Hindatu, itama ta karba, to maza Umamatu kuje. Haka muke wuce in na wuce inda maza suke ‘yan uwana suka tare ni don an riga an ji isowata.

Muna shiga gida na saka kuka sosai sai dai ban yi ihu ko wani abin da ya saba ba, na riga na sani ihu ko sabo ba zai dawo min dashi ba, ba zai amfanar da mu da komai ba šai dai ma ya zame mana wani sanadi. Ubangiji ya gafarta mana.

“Sannu da zuwa Hajiya.” Mafi yawan mutane abinda suke fadi kenan, ina amsawa. Manya kuma da suka fi kowa sanin abinda ke tsakanina da mai babban allo suna ganina cewa suke yi.

Uh uhun, sai hakuri Humairah, yau kin rasa Mallam, wannan maganar ita ce tafi komai tayarmin da hankali ta karyar min da zuciya gabadaya gidan a cike yake har tsakar gida babu masaka tsinke.

Tabarmi ake ta shisshimfidawa saboda iyali sun riga sun hadu. Amma kowa yana cikin natsuwarshi babu koke-koke, babu maganganu a koma gefe ana ta hira ana ba da labari a gidan mutuwa.

Kowa cikin natsuwarshi yake, in ma yana istigifari ko salatin Manzo ko kuma yana zaune cikin jimami saboda yasan tilas watarana shima zata zo kanshi.

Dakin Hajiya ‘yar dubu na fara shiga can kusa da ita naje na zauna saboda tana hango ni ta shiga kokarin samar min wurin zama a kusa da ita din, kama ni tayi ta rungume a jikinta tana fadin sai hakuri, sai hakuri sai hakuri. Bar kukan haka kuyi tayi mishi addu’a,.

Ina share hawaye ina ce mata ban gan shi ba ne Hajiya da na ganshi watakila da ya gaya min wani abu, ta ce da kin ganshin ma maganar guda daya ce, ita yayi ta nanatawa kuyi hakuri da gidajen aurenku, kuyi bakuri da zumuncinku, bai fadi komai ba bayan wannan.

Ranar da mijinki yazo kuwa lafiyar shi kałau sun kai awa biyu a falon shi su biyu ya hana a shiga, bayan tafiyar nashi ne ya soma kukan ciwon kai ashe tafiya ce tazo ban cewa Hajiya ‘yar dubu ban san Ado yazo wurin mai babban allo ba, shiru kawai nayi.

Yan uwa suka yi ta baro in da suke suna zuwa yi min ta’aziyya da na natsa nima sai na mike naje na yi wa wadanda suke gaba dani lokacin ne naga inda su Nusaiba suka yi masauki, wurin Hajiya Kubrah.

Anyi zaman makoki kwana uku amma Jama’a sai tururuwa suke yi suna ta isowa a cikin gida ana ganin kamar za a kara zuwa bakwai sai kawai Alhaji Maikudi ya shigo ya kara gaida Jama’a ya ce to yau kowacce ta shirya ta tafi dakinta ya isa haka.

Duk inda muke ba zamu fasa yiwa Mallam addu’a ba, har sai ranar da tamu tazo ta same mu, muka ce haka ne.

Muka tashi daga gidan rasuwa muka bi Gambo zuwa gidanmu, can ma gida yayi matukar cika saboda su Bala da yara sun iso har iyayen Balan ma sun zowa Ado ta’aziyya, ga Yaya Ibrahim da iyalanshi gaba daya, ga su Ruwailah har da su Baba Tanimu.

Ga mutanen arziki kawayena da a yanzu nake mu’amallah dasu matan abokan Ado, Babana ba shiga dawainiya da Jama’a, Zubaida ma haka, tun da ita kam Sa’a can dakinta ma ta sauka gaba daya.

Shigowa nayi wurin Gambo na samu Kawu Ado da abokinshi na tuntuni, Mallam Umar wanda yanzu shi da Gambo babu wanda yasan tsakaninsu, saboda mu’amallar dukiyar da suke yi.

Suna zaune kan shimfida a kasa su biyun ita kuma Gambo tana daga can cikin daki kusa da bakin kofar dakin tana rike da labulen don ta rinka hangen su don suji dadin maganar da suke yi.

To mutuwa kam ba an riga an yi ta ba, Mallam Umar sai yasa a fasa abin da aka sa a gaba? Ya ce a’a Gambo a dai bar shi a hakan kawai na juya na fita na basu wuri cikin zuciyata dai ina mamakin abinda aka sanya da ya sanya Gambo fadin mutuwar Mallam ba za ta bana ayi ba. Nasan lalle yana da muhimmancia wurinta.

Kwana na biyu a gida na kwashe iyalina muka koma gida muka je muka samu Mama wacce ba sai na tsaya fadin mutuwar Mallam tayi matukar faranta mata rai ba, a zuciyata na ce uhun murnar mutuwa kam ma ai murnar banza ce, tunda kai ma mai murnar ba ka tsira ba, wani naka ma bai tsira ba.

Kwananmu biyu da komawa, Ado yayi tafiyarshi wacce dama zai yi rasuwar Mallam tasa ya daga, ni kam ina gida tare da iyalina tunda Mallam ya rasu na kara maida komai ba komai ba.

Kullum sai na tuna shi, na tuna kalamanshi musamman nasihohinshi da mafi yawancin lokaci yake yawan nanatawa, wannan duniyar ai ba komai ba ne, dan dadinta kuma takaitacce ne. Su al’amuran cikinta kuwa in har kana da hankali to na tsoratarwa ne, ina iyayenmu suke? Ai muna kallonsu suka kare ba mu yi komai ba don ba mu da ikon yin to haka randa tazo kanmu to gashi kuwa tazo din yau baya nan.

Duk yawan iyalinshi kuma taruwa kawai muka yi muka yi kuka muka tashi wannan kadai ya ishi bawa tsoro.

Sati biyu da tafiyar Ado ya dawo ya kwana a gida gari ya waye daga ni har shi ga dukkan alamu muna cikin jimami don ‘yan abubuwan da suka gudana a tsakaninmu duka babu wani matsanancin nishadi a ciki.

Tun kwanaki fa naso muyi wata yar magana da ke rasuwar da aka yi ne yasa na dakatar da al’amuran zuwa wannan lokacin.

Na zuba mishi ido ina kallonshi cikin natsuwa da sauraro. Sai naji ya ce min kin san abokina na ruwan bungo da matanshi da iyalinshi duka, na ce mishi eh, ya ce ke da kanki ne kike gaya min cewar suna da kokari wajen kula da tarbiyar ‘ya’yansu, na ce haka ne.

Ya sake kallona cikin natsuwa ya ce min, to tun kwanakin baya kamar sati shida da suka wuce nayi mishi waya na ce mishi in akwai yarinya budurwa a gidanshi ina so.

Abinda naji a zuciyata yafi karfin a kira shi faduwar gaba, na dai daure kawai na zuba mishi ido ina kallonshi cikin wani yanayi da ban tabbatar ba a-farke nake ko a mafarki nake oho?

Ni da ke muna da fahintar juna, kanmu a hade yake bamu da wata matsala a tsakaninmu, yarinyar da zan kawo ba wata yarinya ba ce da ba kinsan tarbiyarta ba, kinsan iyayenta kin san komai dinsu, har ma kuna mutunci ke da su.

Yar wajen Hannatu ce, ba na so ki dauki wani abu da tsanani ko kiyi tunanin saboda wani zan yi musamman da yake na sha gaya miki cewar ina son mata biyu amma ba zan yi ba, sai adaidai lokacin da ke da kanki za ki shaida cewar nayi miki adalci.

Ban san yanda aka yi ba, sai kawai na tambayi Ado to adalcin me kayi min a yau da zaka kawo min ita? Ban san shi ba in kuma akwai shi nuna min shi.

Shiru yayi yana kallona, bai tanka ba, tuni naji, wani abu yana motsi cikin Jikina daya sani shure mishi abin karyawan nashi da kafata na mike tsaye ina fadin, ai tuni nasan abotarka da Mallam Haruna in ba sa’a nayi ba tsiya zata zame min.

Ba ka da hira sai ta ya yanshi ni ina nasan su balle in san wata tarbiyar su da ka ke cewa na gaya maka? Ina ruwana da su, Mama ce ta saka kayi aure don burinta ya cika ba kuma zai cikan ba a haka zata mutu.

Kar ki zagi Mama Humairah, saboda bana so kiyi sanadin da maganar zata lalace a tsakaninmu, kar ki neme ni da fitina tunda ni ba ita nake nema da ke ba.

Ki bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda muka saba yi saboda yaran nan sun riga sun fara wayo bana so su shaida wani sabani a tsakaninmu.

Na mulmulo wani irin mahaukacin ashar irin wanda ban taba ba na antakawa yaran na ce su sheda komai, saboda ka shirya cutata wannan mutuwar tsohuwar tasa ka kayi aure mugu…caraf yayi ya kama min baki ya rike, yana sakin bakin kuma ya faska mini mari.

Kafin ta sa ni auren wata ai ta sani aurenki, kenan ba yau na fara yi mata biyayya akan aure ba. Hannu biyu na saka na kama rigar Ado na rike na ce to a saken kawai tunda ai bayan umarnin aurena ta baka umarnin sakina sake ni kawai a yau kowa ya huta.

Kama hannayená nayi yá tattara su wuri daya ya hada su a jikina, ya hankada ni nayi tsalle na kife can gefe. Ya kama hanya yayi tafiyarshi.

Ana cikin haka sai ga su Ruwailah sun iso da su Furerah, Jama’ar cikin gida gaba daya sai ‘yan kadanne ba su zo ba, gaba daya labarin auren Ado ya bazu ko’ina.

Don haka suka zo su jajanta min al’amarin tunda su din a yau nawa ne a bangarena suke.

Muna zazzaune jungum-jungum gaba daya mun buga uban tagumi, kowa da lissafin da zuciyarshi take yi, na hanyoyin da zamu bi auren ya wargaje kafin ranar daura shi.

Sai da Sa’adatu ta iso tana rike da hannun danta sun sha kwalliya sai walkiya suke yi. Hajiya sannu da zuwa, suka soma gaishe ta tana amsawa a lalace, a wulakance na zuba mata ido ina kallonta.

A zuciyata ina tambayar kaina dama yarinyar nan ta iya yi wa mutane irin wannan wulakancin ni ban sani ba? Wai ita matar me kudi ko? To bari na nutsu,  ana gama gaisuwar ta mike ta nufî can cikin daki ta bar mu, don haka muka ci gaba da tattauna al’amuranmu irin masoya sai gata ta sake fitowa fuskarta a murtuke kai duk ku watse ku bar gidan nan ko kuma in kira Yaya Ado in gaya mishi abinda naji kuna tattaunawa a kai.

A fusace na ce mata, ke Sa’a za ki ci mutuncin mutane nane a gabana? Kina hauka ne? za ki kawo min iskanci ne da rashin kunya? Nan da nan ta kama kuka haba Anti, kishiya musiba ce? Da in za’ ayi miki ita sai ki birkice ki fita hankalinki ki  ara mutanen da zasu yi miki karya?

Su wacece bata da kishiya a cikinsu? In kura tana maganin zawo tayi wa kanta mana, kin san ki ga yawa wani gaskiya ya ji amma in gaskiyar tazo  kanki ba za ki iya aiki da ita ba?

Na wanke Sa’a da mari mai kyau saboda maganganun nata sun zama rashin kunya a wurina.

<< Mijin Ta Ce 47Mijin Ta Ce 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.