Skip to content
Part 4 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

Munara ta bi kayan da kallo zuciyarta a cike da jin zafin abunda Munawwa tayi mata a gaban Mummy, don tasan daman tayi ne don Mummyn rayi mata fad’a, shiyasa tayi banza da ita bata ce da ita k’anzil ba taci gaba da cin abuncinta, Mummy ta kalli Mubawwa fuskarta cike da mamaki tace, “Me ke faruwa ne? daga ina wad’anan ababen suka fito ne.”

Munawwa ta tashi zata bar falon tace da Mummy, “Ga mai kayan nan Mummy nima bansan ya aka YI ta fidda su ba.”

Tana k’are maganar ta shige d’akinsu saboda har cikin zuciyarta taji zafin abunda Munara tayi wa wannan bawan ALLAH, bayan shigewarta d’aki Mummy ta kai kallonta ga Munara tace, “Wai meke faruwa ne bansani ba?”

Munara tana murmushin yak’e tace,

“Mai aikin da nace maki Daddy yace a d’auka ne na kaiwa ya wanke mani, to shine Munawwa taje ta kwaso wai ba mutuncinmu bane, to ni banga aibun wannan aikin da na saka shi ba, daman tayi ne don kawai kiyi man fad’a don ALLAH Mummy ki fita iskanta, kar ki biyeta kice zaki yiman fad’a don Allah.”

Ta k’are maganar a cikin marairecewa tamkar tayi kuka, ganin haka yasa Mummyn tayi murmushi tace, “Bazan yi fad’a ba amman ki kiyaye ba kowane aiki ne ake baiwa mai aiki ba, musamman ma Namiji banga abunda zai had’a shi da wankin wad’anan kayan ba, saboda haka ki kiyaye a gaba.”

Munara tace, “Zan kiyaye gaba.”

Sannan ta kwashi kayanta ta shige d’aki tana shiga ta jefawa Munawwa a fuska tana huci tace, “Tunda kin hana a wanke to ke gasu nan ki tashi k’i wanke man, ni wallahi bana son shishigi da sa’ido miye naki a ciki ne da zaki shiga abunda ba’a kasa dake ba?, wai harda k’ok’arin had’ani da Mummy don saboda tayi man fad’a, to ta ALLAH ba taki ba don ba’a YI abunda kike so ayi ba wallahi an dai ji kunya.”

Ta k’are maganar ta shiga had’o wani wankin wasu ma duk wankakki ne, haka ta had’o su tareda bugawa Munawwa tsaki ta fice d’akin, tana fita falon taga Mummy ta tashi aiko da sauri ta fice harabar gidan.

Basarake kuwa lokacin da Munawwa ta wuce ya bita da kallo, saboda zuciyarshi ta tabbatar masa da Munara da gangan ta aikata Munawwa ta dai kareta ne, haka kawai yaji ya yaba da hankalinta tareda nutsuwarta, saboda a gani biyu da yayi mata dukansu fuskarta k’unshe da murmushi, abu na biyu kirkinta ya burgeshi, shiyasa ya bita da kallo har ta shige sannan yayi murmushi, ya koma wurin Isah mai gadi ya zauna kasancewar Isah mutum ne shi mai surutu, shiyasa ya fara koro masa labarai duk da basarake ba magana ta dameshi ba, amman a haka ya biye Isah suka yi ta fira suna dariya.

Suna cikin firar ne suka hango Munara ta nufo su kamar wata kububuwa, tana zuwa ta tule kayan wankin a k’asa tareda nuna Basarake da hannu tace, “this is the first and last da zan baka aiki kak’i aikatawa, kasani yin hakan daidai yake da korarka a gidannan idan kunne yaji jiki ya tsira.”

Sannan ta buga masa tsaki mai sauti ta shige cikin gida, Isah ya kalli Basarake yana Murmushi yace dashi,

“Aiki fa ya sameka don wannan yarinya da kake gani akanta sai ka rasa aikinka wallahi, batada kirki ko kad’an amman maigida ji yake yi da ita bata laifi a wurinshi Mummynsu kawai ke taka mata birki, don ita bata d’aukar mata shagwab’ar da take yiwa maigida, da ka ganta ka kiyaye abunda zata k’ulla maka sharri, amman kaga ‘yar uwarta tawainiya halinta daban da nata shiyasa ba sa jituwa da juna, kamar ba ciki d’aya suka fito, yarinyar tasan mutuncin babba ko ni nan tsakaninta dani gaisuwa ce, sab’anin waccen mai bakin tsiwar da ita ko marina zata iya yi idan ta kama, shiyasa nike takatsantsan da ita don kar tayi man sanadin da zan rasa aikina da nike d’aukar nauyin iyalina, har ma da ‘yan uwa idan ta doro.”

Basarake ya yi murmushi ba tareda yayi magana ba, ya tashi tsam ya nufi bayan gidan inda Munara ta nuna masa d’azu, ya zube kayan yayi zaune yana kallonsu zuciyarshi sai sak’e sak’e take yi masa, akan yayi ko kar yayi saboda rabonshi da wanki a hannunshi har ya manta, amman wai yau gashi zai yiwa budurwa wanki, yana nan zaune ya fara jin motsin tafiya, da sauri ya tashi ya fara tara ruwa a famfo yana tsaye yana jiran ruwan su cika ne, sai ga Munawwa tafe fuskarta d’auke da damuwa, tana zuwa tayi tsaye tana kallon shi tareda rungume hannuwanta a k’irji.

Basarake yayi kamar baisan tana wurin ba yaci gaba da had’a ruwan wankinshi suna kumfa, ya saka hannu ya jawo wata t. Shirt ya saka zai fara wankawa, Munawwa ta k’araso wurin da sauri ta rik’e rigar ba shiri Basarake ya kai kallon shi gareta, idanuwansu suka had’u daga shi har ita ba wanda baiji wani sign a jikinshi ba, Munawwa ta kasa d’auke idanuwanta a kanshi, saboda wani sak’o da idanuwan suke aika mata a dukkan gangar jikinta, da sauri ya janye idanuwanshi saboda yanayin da yaga ta shiga, wanda shima kanshi jarumta ce kawai yayi amman tabbas idanuwanta sun sakar masa dafi wanda ya sami masauki a cikin zuciyarshi ya zauna, a cikin dakiya ya fara magana kamar haka,

“Kiyi hak’uri ranki ya dad’e na tsaya tara ruwan ne shiyasa ban fara da wuri ba, amman yanzu zanyi a yiman uzuri.”

Sautin muryarshi ta k’ara narkar da Zuciyar Munawwa, shiyasa ta kasa d’auke idanuwanta akanshi tana kallon bakinshi da ke furzo Lafuzza tamkar ba a cikin bakin suke fitowa ba, saboda muryarshi ta k’ara dulmiyar da ita a cikin yanayin da batasan ko na minene ba, a cikin sanyin jiki tace, “baka yi laifi ba ai daman nazo ne na taya ka wankin saboda gudun ka fama ciwonka.”

Basarake ya kai kallonshi akanta a cikin mamakin maganarta yace, “Ki barshi kawai zan iya ai ko gida ma lallab’awa nike yi idan zan yi, ko yanzu ma haka zanyi a hankali har na k’are.”

Munawwa ta fisge rigar a hannunshi sannan tace dashi, “Zauna abunka ni zan wanke kayan sai kayi shanya, ko baka son in sami ladar taimako ne?.”

Basarake yayi sakato yana kallonta zuciyarshi cike da mamakin girman mutuncin Munawwa,a lokaci d’aya yaji jikinshi yayi sanyi k’alau ba musu yaja gefe ya tsaya, idanuwanshi akanta tana wankin har aka zo kan shanya, a hankali yake d’aukar kayan d’aya bayan d’aya yana shanyawa har suka kusa k’are wankin saura k’iris, sannan Munawwa ta d’auraye hannunta da jikinta tace, “Ka k’arasa sauran bari inje in dawo.”

Ya kalleta yana murmushinshi mai kama da yak’e yace, “Nagode ranki ya dad’e ALLAH ya saka maki da gidan aljannah.”

Munawwa tana tafiya tace, “Ameen”

Har ta k’ule Basarake bai d’auke idanuwanshi a kanta, saboda ba k’aramin mamaki ta bashi ba a zuciyarshi yace, “Daman akwai ire irenki masu jink’an mutane a cikin mata?”

Yana nan tsaye cike da mamakinta har ta dawo bai k’arasa wankin ba, tayi murmushi ta ajiye kular abincin da ta kawo masa tace, “Gashi nan idan ka k’are sai kaci abincin.”

Har k’asa ya durk’usa yana yimata godiya Munawwa tace dashi,

“Ba komi ai yiwa kai ne.”

Sannan ta juya ta bar wurin zuciyarta a cike da mamakin abunda ta hango a cikin k’wayar idanuwashi,ta tambayi kanta tace, “shin me hakan yake nufi ne? ba dai wannan mutumin zuciyata zata rikito mani ba?, ina in possible.”

Har taje d’akinsu ta fad’a kan gadonsu bata ma san ta kai ba saboda tsananin tunanin abunda ya gallabi zuciyarta, Munara dake ta gwada kiran wayar honey’nta, ganin yanayin da ta shigo ne yasa ta kai kallonta gareta, ba shiri ta tab’e baki tace, “cen ga su gada.”

Munawwa ta kalleta bata ce da ita k’anzil ba, illah tashi tsam ta tub’e kayanta ta shige toilet abinta, Munara ta buga wani k’aton tsaki ta k’ara gyara kwanciyarta akan gadon, sai faman gwada buga wayar takeyi, amman duk bugun number’r honey’n da takeyi magana d’aya ce ake fad’a mata wato, a kashe take amma ta kasa hak’ura sai kira takeyi wani bayan wani, inda tayi kira yafI hamsin amma kuma maganar d’aya ce, a cikin bak’in ciki ta jefar da wayar tareda fashewa da kuka tana fad’in, “Honey ina ka shiga ne? ka barni da kewarka gashi rashin jinka ya sakani a damuwa wayyo ALLAH honey kazo kewarka zata kashe ni, don ALLAH kazo nayi marmarin jin muryarka.”

Ta k’are maganar tareda fashewa da wani irin kuka mai tsanani.

Da sauri Munawwa ta fito toilet jikinta da kumfa saboda kukan da Munara take yi ya d’aga mata hankali, ganinta kwance tana ta sanbatun kiran sunan Honey ne yasa ta buga mata wani uban tsaki tace “Wallahi kin d’auki alhakina haka kawai kin tada wa mutane hankali saboda wani banza cen.”

Cikin fushi ta komawarta toilet abinta tareda bugo k’ofar da k’arfi, saboda taji haushin ganin wai akan Namiji take wannan hauka, Munara ta kai kallonta gareta a cikin k’ufula tace, “Gara ni ai ina da farin jinin a ganni a ce ana so, ke fa da har yanzu saboda bak’in jini irin naki ko a school baki da saurayi ko d’aya, an dai sha haushi ko ‘yan talla ba zasu rasa masoya ba amman ke gaki da ajin da komai amma wayam ake.”

Munawwa tana jinta amma tayi banza da ita har ta k’are wankanta ta fito, tana tsane jikinta tace da ita “a dai rage wani rawar kai hajiya irinku ne suke jawa mata ana yi masu kud’in goro.”

Munara da ke kwance tana faman kiran wayar Basarake har a lokacin, ta tashi zaune fuska a d’aure tace, “Mazan ma ai kala kala ne hajiya don ke kanki kinsan Honeyna, ba irin Namijin da mace zata juya masa baya bane, saboda haka bana son shishigi a daina saka man na mujiya a barni in sha iska.”

Munawwa tayi murmushi mai sauti tace, “Iska yana wahalar da mai kayan kara, a dai rage son maso wani hakanan don son da kike yi masa, shi nasan rabinshi baya yi maki don da ace da gaske yake yi da ya tako k’afarshi cikin gidannan, a k’alla yanzu kunfi wata hud’u da had’uwa to me zai hana yazo wurinki in har da gaske yakeyi”

Munara tayi saurin fad’in, “Ranar da duk ya zo da wane idon zaki kalleshi? bayan kin gama zaginshi a bayan idanunshi.”

Munawwa tayi wani mere tareda Mik’ewa tsaye ta nufi wardrobe d’in kayansu ta bud’a tareda ciro kayan da zata saka, tana k’ok’arin sanyawa a jikinta ne tace, “ni dai shawarar da zan baki ki daina rud’ar kanki kina sauraren k’aryar da yake shirga maki a banza, Namiji D’an kunama ne ranar da duk ya halbeki zaki gano gaskiyar magana ta.”

Tana k’are saka kayan ta fesa turare sama sama sannan ta fice d’akin, ta bar Munara da takaicin maganganun da ta datsa mata, saboda maganganun sun shigeta sosai zuciyarta ta fara hasaso mata alk’awali biyu da ya sab’a mata, na farko yace zai zo gidansu amma baizo ba, da tayi masa magana yace ya zo ya ganta da wani shiyasa ya koma, to ai in da gaske ne ko da wanin ai sai yazo ko gaisawa ce suyi, sai dai in daman bai zo d’in ba to amma kuma in bai zo ba taya yasan wani yazo wurinta?,,sannan na biyu yace su had’u Zambia Park taje tayi ta bulayin nemansa bata ganshi ba, idan har da gaske yaje me yahana su had’u, shin me hakan yake nufi ta k’are nazarin da tambayar kanta, a fili ta furta cewa “anya ba yaudarata Haidar yake so ya yi ba?”

Wata zuciyar tace da ita,, “Kin manta irin son da yake yi maki ne.?”

Tace “to me hakan yake nufi nikam gashi nayi ta kiran wayoyinshi a rufe.”

Ta k’are maganar a cikin damuwa ta jawo wayarta ta fara jera masa text wani bayan wani, a zuwan da ya bud’a wayarshi ya gansu domin ya gano irin kewar da tayi tashi yaji tausayinta.

Munawwa ko tana falo tana kallo ne Isah maigadi ya yi sallama a bakin falon, Munawwa ta taso ta zo wurinshi tace, “Baba Isah ya aka yi ne.?”

Isah ya d’an rusuna yana ‘yar dariya yace, “Mutuminku ne yace a tambayo masa ba wani aiki saboda yana so yaje gida.”

Sai a lokacin Mutumin ya fad’owa Munawwa a rai tace, “ALLAH sarki kace ya tafi kawai sai gobe, duk da dai bansani ba ko akwai wani abunda zai yi, amman dai yaje kawai ba damuwa.”

Tana cikin maganar ne sai ga Basarake da tulin kayan wankin Munara ya goge su tas ya nufo wurin, da sauri Munawwa ta fito taje ta zura hannu zata karb’i kayan ne suka k’ara yin four eye’s dashi, aikuwa da sauri ta karb’i kayan har hannunta ya zoji nashi hannu da ke k’unshe cikin safa, abun mamaki taji yatsunshi a mik’e gar ba alamun kuturta ko kad’an,kanta a k’asa tace dashi, “Angode sosai fa kasha aiki sannu da k’ok’ari.”

Basarake yayi murmushi kawai ba tareda yayi magana ba, ya rungume hannuwanshi a k’irji yana kallonta har ta kai k’ofa zata shige,ta waigo ganin yana kallonta tayi masa murmushi shima ya mayar mata da nashi mai kama da yak’e sannan ta shige abinta.

Basarake kuwa ya d’auki minti biyu tsaye wurin idanuwanshi a kan k’ofar, sannan ya juya yana yiwa Isah maigadi sallama har ya bud’a ‘yar k’aramar k’ofar get d’in gidan zai fita Isah yace dashi, “Kar fa ka mance da wuri zaka fito gobe.”

Basarake yayi masa murmushi yace, “zan zo da wuri insha Allah sai goben.”

Sannan ya fice ya bar maigadi yana kamo tashar da yake so ya saurara da tsohon radio’nshi.

Ko da ya fito bakin titi ya tari acab’a ya kai shi inda ya ajiye motarshi, yana zuwa ya sallami mai shagon da ke wurin wanda ya bari ya kula masa da motar, sannan ya shige ya nufi hotel d’in da ya sauka bayan ya cire sabuwar fuskar da ya saka sannan ya cire safunan, yana tafe yana murmushi har ya kai hotel d’in yana yin parking motarshi, a gajiye lik’is ya shiga masaukinshi tun a k’ofa ya fara cire kayanshi ya nufi toilet, ya dad’e yana watsawa jikinshi ruwa sannan ya fito yana tsane jikinshi da towel, ya jawo wayoyinshi ya kunna yayi order’r abincin da zai ci, bayan an kawo masa ne yana cin abincin yana duba wayoyinshi domin yaga me ke going, ai kuwa sai ga text’s d’in Munara sunata shigowa d’aya bayan d’aya har guda goma sha biyu, ya fara dubawa yana murmushin mugunta, bayan ya kammala cin abincin ne ya shirya a cikin wasu k’ananan kaya, sunyi masa kyau sosai sannan ya jawo wayarshi ya na k’ok’arin kiran Munara sai ga wayar Mahaifiyarshi ta shigo, nan take wani farinciki ya bayyana akan fuskarshi, yana murmushi mai sauti ya bari har sai da wayar ta tsinke sannan ya bi da nashi kiran, bugu d’aya biyu ta d’auka bayan ta sauke k’atuwar ajiyar zuciya tace, “Me ya sameka ne da kake kama waya ka rufe ayi ta nemanka ba’a samu.?”

Basarake yana murmushi yace, “Kaina bisa wuya Ummi wani meeting ne muka shiga tun safe sai yanzu muka fito, shiyasa kika Ji wayar a rufe amman insha ALLAH ba zan sake rufe wayar ba kiyi hak’uri kinji. “

Hajiya Mu’azatu tayi murmushinsu na manya tace, “Yafi dai gashi kasa Hajiya ta d’agawa kowa hankali saboda tayita kiran wayarka bata samu ba.”

Basarake yayi dariya yace, “K’yaleta Ummi rikicin tsufa ne kawai yake damunta.”

Hajiya Mu’azatu tana yar dariya tace, “Ungo naka d’an agadas Hajiyar ce ka ke cewa haka?, ka fa san duk yanda bata son kayi nisa da gida, don haka ka kirata yanzu ka kwantar mata da hankali Abbunka ma yayi ta neman wayarka bai samu ba, don ALLAH ka daina rufe wayar kaji, tukunna ma wai yaushe zaka dawo ne?.”

Basarake ya sosa k’eya yace, “Eh to sai yanda kwanakin suka bada amman ina sa ran inyi sati d’aya anan d’in kafin in zo in ganku in dawo, don aikin zai d’auki sati hud’u kafin mu k’are.”

A cikin damuwa Ummi tace, “ALLAH ubangiji ya taimakeka ya baka nasarar duk abunda kaje nema, ALLAH ya tsare muna kai ka dawo cikin aminci”

Basarake yana murmushin jin dad’i yace, “Ameeñ Ummi nagode, bari in kira kakale yanzu inji ya zan kwashe da rigimarta.”

Bayan ya yi sallama da Ummi a cikin shauk’in so irin na d’a da uwa tareda kewar juna, sannan ya danna kiran wayar Kakale,a nan ya shiririce suna ta buga dirama da kakele, yana tsokanarta yace sai yayi wata bai dawo ba aiko sai ga kakale har da su kuka, jikinshi yana rawa ya fara bata hak’uri yace da ita nan da sati d’aya zai zo don ya ganta kawai, sannan suka rabu da ita lafiya, yana k’are wayar ya jefa wayoyinshi a aljihu ya fito harabar hotel d’in, inda yaje bakin swimming fool ya zauna, tareda aza k’afa d’aya akan d’aya yana kallon kowa d’ai d’ai, musamman wasu ‘yan iskan mata da samarinsu da suke ta tanbad’ewa, basa kunyar idanuwan kowa sharholiyarsu kawai suke yi.

Saboda takaicin da suka bashi ranshi a b’ace ya jawo wayarshi ya dannawa Munara kira, kira d’aya tayi caraf ta d’auka tareda buga uwar Kuwwa, wadda tayi sanadin shigowar Mummy da Munawwa a guje cikin d’akin, ganinta a kan gado tana ta birgima ne yasa suka yi tsaye suna kallonta, wurin turje turjen ne duk ta watse wankin da gugar da Basaraken yayi mata, duk suka watse wasu a k’asa wasu akan gadon saboda murna ta ma kasa d’aukar wayar har ta katse sai birgimarta jin dad’i takeyi saman gadon.

Tsawar da Mummy ta daka mata ne yasa ta nutsu ba shiri, Mummy ta fara yi mata fad’a kenan sai ga wani kiran ya shigo, da sauri ta d’auka tareda yiwa Mummy alamar tayi hak’uri tayi shiru, sannan ta fad’a toilet da gudunta ta rufo k’ofa.

A cikin zumud’i ta fara magana a cikin shagwab’a tace, “Haba honey haba honey yanzu abunda kayi mani ka kyauta kenan sabida ALLAH?”

Basarake yayi murmushi da gefen bakunshi yace, “Me nayi wa babyna ni kam, baby sai kinyi hak’uri dani fa saboda nayi busy da yawa, lokacin da nayi maki kwatancen inda zaki same ni a zambia park, muna k’are wayar aka yiman kiran gaggawa, nayita kiranki akan ki k’araso mu gaisa ban same ki ba, shiyasa na tafi amman nima banji dad’i ba, naso naga babyna ido da ido domin in banbance fili da photo wanne tafi kyau, duk da jikina yana bani za ki fi kyau a fili.”

Wani farinciki ya lullub’e zuciyar Munara, tayi wani tsallen jin dad’i tace, “To yanzu yaushe zamu koma had’uwa kuma?”

Basarake yayi murmushin mugunta yace, “Yanzu haka ina cikin garinku idan zaki iya zuwa k’ofa a bud’e take sai ki zo mu gaisa.”

Munara tayi hanzarin fad’in “What??? surprise, wayyo ALLAH honey a ina kake? don Allah fad’a mani yanzu yanzunnan zan zo mu gaisa.”

Yana murmushi ya yi mata kwatancen inda zata same shi, a guje ta fito ta jefa wayar kan gado, sannan ta koma toilet d’in ta darzo wanka jikinta yana rawa ta shirya a cikin shigarta ta k’ananan kaya, ta zunbula k’aton hijab d’inta na sallah wanda sallah ce kawai ke sa ta saka su, sannan ta d’auko wata jaka ta tura k’aramin gyalenta, da glass d’inta da turaruka sannan ta rufe jakar ta rataya, ta fito da gudu talkaminta a hannu tace, “Mummy bari inje in karb’o littafina wurin Nucy yanzu nan ma zan dawo minti biyu ma sunyi yawa.”

Tana magana tana tafiya cikin sauri har ta fice, Mummy ta kalli Munawwa tace, “Anya yarinyarnan kanta d’aya kuwa.?”

Sai da ta zagaya ta bayan gidan ta cire hijabin da ta sako sannan ta bud’e jakar ta ciro gyalenta ta yafa, tareda k’wama k’aton glass d’inta bak’i wanda ya k’ara fito da kyawonta, bayan ta feshe jikinta da kalolin turaruka sannan ta fito da sauri ta jefa jakar a mota, ta ja motar da k’arfi ta fice gidan zuciyarta cike da d’okin ganin honey’nta, tafe take akan hanya tana ta wassafa yanda za suyi four eye’s da shi ido cikin ido, zucuyarta lullub’e da farin ciki marar misaltuwa tafe take a kan titi kamar kullum ta saki kid’a sai tashi yakeye, duk da go slow d’in da ke kan titunan amma minti goma kacal suka kaita hotel d’in, saboda yanda take ta zuba gudu abinta sai kace ita kad’ai ce a saman titin.

Bayan tayi parking d’in motar ne ta k’ara jawo turaruka ta bulbulewa jikinta sannan ta fito tana gyara zaman half gawn d’in rigar kantin da ke jikinta,sai yatsine yatsine take yi tana wulla idanuwanta sama da k’asan hotel d’in, a zuciyarta tana ta tunanin ta ina ma zata fara ne?, aikuwa sai ga kiran Basaraken ya shigo wayarta, jikinta yana rawa ta d’auki wayar tareda cewa…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakon Yanayi 3Bakon Yanayi 5 >>

1 thought on “Bakon Yanayi 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×