Skip to content
Part 5 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

“Honey ga ni na shigo a ina zan same ka?”

Sadauki ya yi mata kwatance inda yake sannan ta kashe wayar ta fara taku k’wask’was da takalminta masu bala’in tsini, tafe take tana yauk’i yayin da idanuwa da yawa suka lalace wajen kallonta,a hankali take taku tana rausaya har ta kai inda Basaraken yayi mata kwatance, amman abun mamaki tun daga nesa ta hango kamar shine rungume da wata tana yi masu selfie, duk da bata tabbatar shine d’in ko ba shi ba ne ba amman ranta yayi matuk’ar b’aci sosai , a cikin sauri ta fara taku kamar wadda zata tashi sama haka take tafiya har ta isa wurin, mezata gani ashe Honey’nta ne rungume da macen ba wani dogon tunani da tayi bale jinkiri kawai ta saka hannu ta wanka mata mari, sannan ta jawota k’iiiii ta jefata cikin ruwan swimming fool d’in tana huci tareda nuna ta da d’an yatsa tace, “Babban kuskuren da zaki tafka a rayuwarki shine in k’ara ganin kin rab’i honeyna, domin akan hakan wallahi babu kalar matakin da bazan iya d’auka a, kanki ba, ke akan ma duk wata shegiyar macen da tsautsayi zai biyo kanta, idan kuma kina da ja a zancen nawa k’addara ta aike ki ki k’ara kwatanta abunda kika yi.”

Tana k’are maganar tayi fuu zata bar wajen mutanen da ke zagaye da wurin suka fara sowa suna tafi tareda jinjina mata, matar da ta jefa a ruwan kuwa ba k’aramin tsoro fuskar Munara da kalamanta suka bata ba, duk da kasancewarta tsohuwar ‘yar bariki saboda a zatonta Munara matarsa ce, shiyasa ta fito da kunyarta tsamo tsamo ta bar wajen.

Munara kuwa ko kallon Basarake bata YI ba ta juya ta fara tafiya zata bar wurin, aikuwa sai gashi da sauri ya biyo bayanta yana kiran sunanta, tayi banza dashi ta ci gaba da tafiyarta a cikin zafin nama ya ci gabanta tareda rik’o hannunta, ba shiri Munara ta fashe da kuka basarake ya fara magana damuwa shinfid’e akan fuskarshi kamar da gaske yace, “Haba baby cooling down plss.”

Munara ta d’ora idanuwanta cikin nashi tace, “Ba wani cool dawn da zanyi ashe daman ka kira ni ne domin ka tozartani?, to na gani sai me kuma kake so in k’ara sani? Wallahi nayi danasanin zuwana wajenka, ina d’okin zan sami farin ciki a raina amman sai gashi bak’in ciki ya kawo man ziyarar bazata, ni kam wannan rana ta zame mani bak’ar rana mai cike da d’inbin takaici.”

Ta k’are maganar a cikin wani sabon kuka Basarake yayi murmushi yace, “Duk wannan kishin ni kad’ai wow ashe haka nike da babban matsayi a gunki baby?Alhmdllh naji dad’i sosai babyna tana kishina kiyi hak’uri kinji wallahi nayi ne kawai don na gwadaki, amman wallahi ba halina kenan ba trust to me my sunshine baby.”

Munara ta d’ago fuska tareda galla masa hararar soyayya tace, “Kaji dad’i ka sanya ni kuka a had’uwarmu ta farko.”

Basarake ya rik’e kunnuwanshi duka biyu yace “Am sorry.”
Tareda jifarta da wani irin masifaffen kallo har sai da taji tsikarta tayi yarr, sannan tayi murmushi tareda gyara tsayuwarta tace,

“Ai shikenan kuma tunda munga juna ni zan wuce gida.”

Basarake ya yi saurin fad’in, “Ai baki isa ba har sai kinzo mun zauna mun gaisa a tsanaki, don haka zo muje mu d’an zanta in k’ara bada hak’uri.”

Munara tayi murmushi wanda ya kasa b’oye farincikin da take ciki, saboda ba k’aramin dad’i taji ba da ganin Honey’nta wanda a zuciyata sai fad’in take yi, “Ashe ma Honeyna yafi kyau a fili.”

Yace ta zo su koma cen wurin tace ita sam bazata koma wajen ba saboda hotonshi da na yarinyar ya kasa barin idanuwanta, shiyasa yace da ita tazo su je wani gun, ai kuwa suka jera suna firarsu ta masoya suka nufi wata ‘yar rumfa inda tsirarun mutane ne a ciki, bayan sun zauna ne ya bada odar a kawo mata abun tab’a baki, minti biyu tsakani aka cika d’an table d’in dake tsakiyar kujerun, Basarake ya kalleta yayi murmushi yace,

“Ashe haka kike kishina baby.?”

Munara ta jefe shi da wani kallo tace, “Da kasan yanda sonka yake wahalar da zuciyata da baka yi wannan tambayar ba, Wallahi honey baka ji yanda naji ba lokacin da naga wannan matsiyaciyar a jikinka, ji nayi kamar an watsa mani wani ruwan dalma a jikina, don ALLAH honey ka soni ko da rabin son da ni nike yimaka ne kaji.”

Ta yi maganar cikin sanyin murya tareda zubowar wasu hawaye a kan fuskarta, Basarake ya kalleta sosai tsawon minti biyu saboda ta bashi tausayi sosai, amman tuno halayenta na rashin ganin girman d’an Adam, da tsagwaron rashin mutuncinta ya yi saurin kawar da tausayin yace da ita, “Yanzu a k’addara wani abu ya gifto a tsakaninmu ace ban aure ki ba ya zaki ji kenan.?”

Munara tayi saurin runtse idanuwanta tace, “Ka daina fad’ar wannan magana plss honey wallahi zuciyata zafi take yi, kasani har abada bana fatar abunda zai gifta d’in wanda har zai yi sanadin rashin aurenmu, saboda tabbas ko wacece k’addara ta hau kanta ta aure man kai wallahi zata jefa rayuwarta a cikin gagarumin had’ari, kai bari in ma kai maka k’arshen zance ko Munawwara ce tayi k’ok’arin raba ni da kai, wallahi bazan tab’a barinta taci bulus ba saboda kai nawa ne babu wata shegiyar macen da ta isa ta mallake ka face ni babynka Munara.”

Lafuzzan da ke fita a bakinta sun saka Basarake fad’uwar gaba sosai, musamman Sunan Munawwa da ta ambato ya sanya jikinshi yayi sanyi k’alau, a cikin sanyin Murya yace da ita, “Anya baby wannan zafin kishin naki bai yi yawa ba kuwa?kinsan fa yanzu ba’a son mata su kasance masu zafin kishi sosai, ki rage kinji baby don bana son ki d’aga hankalinki a banza.”

Munara ta harareshi tace, “To ka kiyayi abunda zai jawo kishin shikenan sai a zauna lafiya.”

Basarake yayi murmushi tareda rungume hannuwanshi a k’irji yace, “Rigima baby.”

Munara tayi ‘yar dariya tace, “Ai kai ka jawo komi.”

Basarake yayi murmushi mai sauti yace, “Har marin da kika yiwa ‘yar mutane ni na jawo mata kenan? cab amma kam ta maru gaskiya .”

Munara ta k’yalk’yale da dariya tace, “kad’an ma tagani WALLAHI don bazata iya jurar tanadin balbalin bala’in da nayiwa duk wata ‘yar iska mai son raba ni da kai ba.”

Basarake yayi wani murmushi da shi kad’ai yasan ma’anarshi yace “ko”

Tace “Of course”

A haka dai Basarake ya biyeta, yayi ta janta da fira har ta saki suka ci suka sha suka koma photuna har sai da aka yi magriba sannan ya rakata har bakin motarta, bayan sunyi sallama ya fad’a mata cewa gobe tun da sassafe zai wuce Abuja.

Munara ta dawo gida a cikin shauk’in son Basarake da ya mamaye lungu da sak’o na zuciyarta, ko da ta dawo gida har an fara Isha’i saboda sai da ta biya gidansu Nucyn sannan ta garzayo gida, farinciki fal ranta shiyasa lokacin da ta dawo Isah yana sallah tayi ta horn amman bai zo ya bud’e mata get ba, da kanta ta fito ta wangale get d’in sannan ta shiga da motar ta ajiye, bata bi ta kan Isah’n ba ta shige cikin gida abinta, Isah da har rafkanuwa yayi a cikin sallahr saboda jin tsoron abunda zai je ya dawo, yana ganin ta shige hankalinshi ya kwanta tareda sauke ajiyar Zuciya yace, “cab ALLAH ya soni yau.”

Munara koda ta shiga Mummy tana d’akinta tana sallahr,kai tsaye ta wuce d’akinsu ta tarar da Munawaa ma sallahr takeyi, itama ta fad’a toilet ta d’oro arwallah ta ranka magriba sannan tayi isha’i, bayan tayi addu’o’inta wad’anda duk na rok’on ALLAH ya k’arawa Honey’nta sonta cikin zuciyarshi ne, sannan ta tashi tsam tareda jefar da hijabin akan gadonsu, sannan itama tayi sufa ta fad’a gadon tana murnar jin dad’in ganin honey’nta da tayi a yau ido da ido, sannan ta jawo wayarta ta fara duba pic’s d’in da suka yi dashi, d’aya bayan d’aya wad’anda duka sunyi kyau masha ALLAH, Munawwa sai kallonta takeyi a cike da mamakin wannan farin cikin da take yi, ganin Munara ta raja’a da kallon wayar ne tana ta murmushi yasa ta lek’o kanta domin taga me take kallo haka, aikuwa sai ga photon Munara da Basarake ya fito b’aro b’aro a kan screen d’in wayar sai kallon juna su ke suna murmushi, ba shiri k’irjin Munawwa ya buga dam! Saboda ita ta rasa me ke saka ta fad’uwar gaba a duk lokacin da taga pic d’in Basarake, tun ranar da ta fara d’ora idanuwanta a photonshi take jin haka, wanda ta rasa gano dalilin da yake saka ta fad’uwar gaban, duk da watarana tana jingina hakan da cewa saboda tsananin kyaun da yake da shi ne.

Munawwa ta shagala da kallon pic’s d’in da Munara ta ke ta bud’awa nasu ita da Basarake, jin numfashin Munawwa a kusa da ita ne yasa ta d’ago fuskarta ta dubeta, da sauri ta tashi zaune tace, “To uwar tsugudidi me ake kallo ne?”

Munawwa tayi dariya sannan tace, “Pic’s dinku na gani kunyi kyau.”

Munara ta galla mata harara tace, “To kije da ALLAH ya isar kallon honeyna da kika yi, don wallahi in dai kinsan kin kallar man shi to ban yafe maki ba.”

Munawwa ta zaro ido a waje tace, “Munara kinsan me kike fad’a kuwa?”

Munara ta harareta tace, “Ciyon hauka ne a kaina.”

Munawwa ta yi mere tace, “Naga alama kam, amman in dai haukar bata duka bace ai da sauki.”

Tana k’are maganar ta fito falo ta bar mata d’akin, Munara ta buga mata wani uban tsaki tace, “Kyaji da shi Uwar tsugudidi wallahi akan honeyna zan iya sab’awa da kowa don bani da aminci da kowace mace akanshi, duk girman kusanci na da mutum kuwa wallahi zan iya yaga masa rigar mutunci .”

Koda dare yayi suka shiga bacci dukansu tunani d’aya ne a cikin zuciyoyinsu, waton tunanin Aliyu haidar mai lak’abi da sunan BASARAKE, domin kuwa Munara tunanin had’uwar da sukayi kawai take yi tana ta wassafo siffarshi a zuciyarta,a cikin shauk’in sonshi da ke ta mamaye dukkanin zuciyarta, saboda jin takeyi kamar tafi kowace mace sa’a kaf a duniya, tunda har tayi gamon katar da samun irin shi.

Munawwa ko da ta tuno fuskarshi musamman pic’s d’in da taga yayi da Munara, sai taji kirjinta ya buga dam! dam! sannan abu na biyu tunanin muryar sabon d’an aikinsu da ya addabeta a zuciya, musamman idan ta tuno k’wayar idaniyarshi da idan suka had’a idanuwa take jinta a cikin wani yanayi, wanda kai tsaye bazata iya fassara abunda take ji ba, uwa uba muryarshi mai dad’i da take ji har cikin kwakwalwarta kanta.

B’angaren Basarakenma hakan ce ta kasance dashi a lokacin, domin kuwa da tunanin ‘yan biyun ya kwana a zuciyarshi wanda ya kasa tantance me ya dace ya aikata?, saboda tabaas yana son Munara amman tun ranar da ta fara wulak’antashi, tun a ranar yaji ta fita kanshi saboda halinta na rashin girmama d’an adam da yagani, yayinda a gefe d’aya kuma yake ganin girman Munawwara saboda irin tsantsar mutuncin da ya hango take dashi, sannan uwa uba tausayin da ta nuna masa ya saka shi jin wani abu a zuciyarshi dangane da ita, tsawon ranar a duk lokacin da ya tuno ta sai ya tsinci kanshi a cikin mutuwar jiki, tareda wata kasala da take lullub’e masa dukkan sassan jikinshi, a daddafe yaga safiya ta waye bayan ya yi breakfast ne yayi shigarshi ta kullum ya yi tsinke sai inda yake ajiye motarshi, sannan ya hau acab’a yayi unguwarsu Munara, tun a bakin get d’in gidan ya jiyo sautin fad’anta, a gurguje ya biya d’an acabar ya tura ‘yar k’aramar k’ofar a hankali sannan ya shige, Munara tana kallonshi ta yo kanshi tana fad’a kamar wadda zata dake shi tace, “Wai kai wani irin kidahumin mutum ne kai?, da rana d’aya da fara aiki zaka fara baiwa mutanen gida matsala?,to bari kaji idan ka sake ka sake yin latti to ka d’auka ma an sallameka kawai daga aikin, don ba gidan ubanka bane ballantana ka dinga yiwa mutane iko” tana huci ta k’ara cewa ” ka iya driving ? “Basarake yayi saurin d’aga kanshi ba tareda yayi magana ba, a cikin d’aga murya ta k’ara cewa, “To k’adangare Magana zaka yi ba d’aga wa mutane kai ba, karb’i jawo motar mu gani don kar muje ka watsar da mu a saman titi”

Ta k’are maganar tareda wurgo masa key d’in motar, wanda yayi daidai da fitowar Munawwa rungume da littafanta, tana ganin abunda Munara tayi masa a lokaci d’aya taji ranta ya b’aci, da sauri ta k’arasa wurin ta duk’a da niyyar d’auko masa key d’in ne, aka yi dace shima ya duk’a hannunsu ya had’u wuri d’aya, duk da a cikin safa hannunshi yake, amman sai da yaji wani yarr a jikinshi ba shiri ya kai kallonshi gareta, wanda itama ta d’ago ta kai kallonta gareshi a tare zuciyarsu ta buga dam! dam!, da sauri Munawwa ta zare hannunta tareda d’auke idanuwanta akanshi, sannan ta tashi tsaye tana yi masa ina kwana, ya amsa fuskarshi cike da murmushinshin yak’e, sannan ta nufi motarsu inda Munara take tsaye jikin motar tana faman kiran wayar Basarake, Munawwa ta bud’e murfin gaba ta shiga ranta a b’ace tace da Munara , “Yakamata ki rage abunda kike yiwa wannan bawan ALLAH”

Ta k’are maganar ba tareda ta juya ta kalleta ba, Munara tana shirin bud’a baki ne sai gashi ya shigo ya tada motar, yana murmushi yace da Munara “shigo muje ko” tayi masa wani kallon renin wayo sannan ta matsa gefe d’aya tace, “Je dai ka gwado mu gani in ka k’ware wallahi ba zan shiga ka halaka ni ba.”

Basarake yayi murmushi kamar baiji zafi ba yace da Munawwa, “Kema ki fita in jaraba inga ko zan iya.”

Munawwa tayi saurin fad’in, “Muje kawai.”

Basarake yayi saurin kallonta yace, “Ba kya tsoron in watsar dake?kin fa san tuk’in d’an koyo sai a hankali fa.”

Munawwa tayi murmushi mai sauti sannan tace “Ai kaima ran ne da kai kamar kowa, naji na amince duk abunda zai sameka ya same mu a tare, bare ma jikina yana bani kai gwani ne a wurin driving d’in mota.”

Basarake yayi saurin kallonta zuciyarshi ta buga amman ya dake abunshi, ya tada motar a hankali yayi ribas sannan ya fito get d’in gidan, wanda tun kafin su k’araso tuni Isah ya wangaleshi, saboda jin tsoron cin mutuncin ‘yar gaban goshin Daddy wato Munara, bayan ya fito ne ya d’an fara tafiya kan titi Munara tana biye dasu tayi tsaye k’ofar gidan tana kallon yanda yake tuk’a motar, aranta sai jinjina shishigi irin na Munawwa take yi don bala’in haushinta take ji, idan taga tana nuna damuwarta akan wannan bak’in mutumin mai fuskar shanu.

Tana tsaye tana dannawa honey’nta kira har suka zagayo suka dawo amma wayar tak’i shiga, BASARAKE ya tsaya da motar a bakin titin yana jiran ta k’araso, a hankali ta tako har zuwa wurin idanuwanta akan wayar ta shiga…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakon Yanayi 4Bakon Yanayi 6 >>

1 thought on “Bakon Yanayi 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×