Skip to content
Part 6 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

Tana tsaye tana danna wa honey’nta kira har suka zagayo suka dawo, amma wayar tak’i shiga. BASARAKE ya tsaya da motar a bakin titin yana jiran ta k’araso, a hankali ta tako har zuwa wurin idanuwanta a kan wayar ta shiga motar, ba shiri ta zabga tsaki saboda jin haushin rashin samun honey’n da ba ta yi ba, tsakin da ta yi ya sa dukansu suka waiwayo suka kalle ta, Basarake ya janye idon shi daga kanta ya fara tafiya cikin k’warewa. Munara ta d’aga murya cike d jin haushin rashin samun wayarsa da ba ta yi ba ta ce,

“Wayyo honey rashin jin ka yana saka ni damuwa, ban san me ya sa kake jin dad’in rufe waya ba a kwanannan.”

Munawawa ta tab’e baki ta juya kanta tana kallon gefen titi tare da cewa,

“ISKA yana wahalar da mai kayan kara.”

Basarake yayi murmushi yaci gaba da tuk’insa hankali kwance, Munara kuwa da daman can jiraye take da Munawwa, ta zak’alk’alo mata da fad’a tana cewa,
“Shi dai wanda ALLAH ya d’ora wa shisshigi bai ji dad’in rayuwarsa ba wallahi, ba a kasa da mutum ba amma ya ce zai kwasa. Ai ke ce iska ke wahalarwa, ke da kika rasa wanda kike so har yanzu, tun zamanin k’urciyar har izuwa yanzu mutum biyar bai bud’a baki ya ce yana son ki ba. Ni ko fa! Ke shaida ce masoya har sai na ture saboda tsabar farinjinin da ALLAH ya yi mini. Don ni ko yanzu kasuwa ta watse naci ribar had’uwa da honeyna, d’aya tamkar da million a cikin mazaje, idan kuma kinyi zuciya ki samo irin shi idan kin isa.”

Munawwa ta yi dariya mai sauti sannan ta ce, “Ai ba’a zuciya a cikin lamarin Ubangiji, ki sani abin rabo ne budurwa da jika. Idan ya raba ya bai wa mutum kaf duniya babu mai k’watar masa, don haka ki kiyayi gori ga abin da kika san ALLAH ne ke badawa. Don zai iya bai wa wanda ya so, kuma a lokacin da ya ga dama.”

Ta k’are maganar a cikin muryar kuka, saboda ta ji haushin gorin da Munara ta yi mata. Munara ta buga wani uban tsaki sannan ta ce,

“Kanki ake ji.”

Basarake dai tuk’in kawai yake yi ba tare da ya kalli ɗayarsu ba, amman fa zuciyar shi cike take fam da tausayin Munawwa. Saboda ganin tana sharar hawaye a fakaice, kamar ba ta son ya gano tana kuka. Har suka je makarantar, babu wanda ya sake magana face kwatancen hanyar da Munawwa take yi masa.

Suna zuwa Munara ta b’alle murfin motar ta fito, ko kallon su ba ta sake yi ba ta tafiyarta. Munawwa ta fito ita ma ranta a jagule tareda rungumo littafanta a ƙirji ta ce dashi

“Mun gode fa!”

Basarake ya yi murmushi sannan ya ce,

“Ni ne da godiya, zan bar maku motar a nan, ko kuwa da ita za a koma idan kun tashi na dawo na d’auke ku.?”

Munawwa ta kawar da kanta gefe sannan ta ce,
“Ka tafi abinka kawai, idan muka tashi za mu dawo da kanmu.”

Ta fara taku a hankali za ta bar wurin ya yi hanzarin d’aga murya ya kira sunanta. Cak ta tsaya saboda jin sunanta a bakin shi ya fito rad’am tamkar a don shi aka halicci sunan. Saboda yadda ta ji sunan ya yi dad’in fad’a a bakin nasa, cikin takunsa na k’asaita ya isa gabanta ya ce,

“Kin manta da makullin ko duk saurin ne.?”

Munawwa ta d’ago fuskarta ta kalle shi da idanuwanta da suka yi ja saboda kukan da take yi, gaban Basarake ya fad’i saboda har cikin ran shi ya ji zafin ganin ta cikin yanayin. A hankali ya ce da ita,

“Ki yi hak’uri kin ji, da sannu alkhairinki zai zo har gida ya same ki.”

Munawwa ta d’aga kai tana yi masa kallon mamaki, ya d’aga mata kai alamar tabbatarwa sannan ya mik’a mata key d’in motar ya wuce. Ta bi bayan shi da kallo kamar wata sakarya, har sai da idanuwanta suka daina ganin shi sannan ta ja k’afafunta ta shiga class zuciyarta sai maimaita kalamanshi take yi tamkar bitar karatu .

Da k’arfe biyu dam Basarake da Malam Isah suna zaune suna bi suka ji horn d’in motarsu Munara, Malam isah jikinshi yana rawa har yana tuntub’e ya je ya wangale musu gate, abun Mamaki sai ga Munara ita kad’ai ta dawo, tana ajiye motar ta yi fuuuu ta shige cikin gidan ranta a b’ace.
Basarake ya yi mamakin rashin dawowar Munawwa tareda Munara, zuciyar shi kitsa masa ‘wata k’ila ita ba ta k’are abin da take yi bane shiyasa.’
Malam isa ya dawo saman bencin da suke zaune suka ci gaba da hirarsu, sai ga Munawwa ta shigo tana sauri ta yi cikin gidan, Malam isah ya lek’a wajen gidan yana cewa,
“Ita kuma wannan yarinya me ya kai ta dawowa cikin adaidaitasahu? Bayan yanzu ‘yar uwarta ta dawo ita ma. Ko dai fad’an ne aka k’ara yi a can makarantar?Tun da ita wannan masifaffar ba ta bari a zauna lafiya koyaushe.”

Basarake ya lek’a shima yana ganin Napep d’in waje tana jira, ya fito ya ce da mai napep,

“Nawa ne kud’in?”

Yana fad’i Basarake ya ciro 1k ya ba shi sannan ya ce da shi ya je kawai. Yana k’ok’arin tashi sai ga Munawwa ta fito da kud’i a hannunta, kafin ta k’araso ya cilla kan napep d’in shi ya tafiyar shi, ta kalli Basarake cike da jin nauyinsa ta ce,

“Ga kud’inka da ka bayar, ina ta sauri kada ya ga na tsaida shi.”

Basarake yayi murmushi sannan ya ce,

“Kije kawai babu komai.”

Munawwa ta tsareshi da idanuwanta sannan ta ce,
“Karb’i kawai wallahi babu komai, ba na so na d’ora maka nauyi kai ma kana fama da kanka.”

Basarake ya b’ata fuska yana cewa,

“Ba kya son na sami ladar ne?”

A cikin sanyi jiki ta ce,

“Ina so, amman ba na son na takura ka don Allah ka yi hak’uri ka karb’a.”

Basarake ya rungume hannuwansa a k’irji ya ce,
“Ya aka yi ba ku dawo tare ba?”

Nan take fuskarta ta canza zuwa b’acin rai kagin ta ce,
“‘yar matsala ce a tsakaninmu, amman komai ya wuce yanzu.”

Ya tsare ta da idanuwan shi masu saka ta shiga wani yanayi ya ce,
“Ki dad’a hak’uri kin ji, in sha ALLAHU za ki ci ribar kykkyawan halayenki.”

Munawwa ta ce masa, “Nagode da fatan alkhairin da kake ta yi mini koyaushe.”

Ta fara tafiya za ta shiga gidan ya d’aga murya ya kira sunanta, ba shiri ta waigo saboda kiran sunanta da ya yi ya ratsa dukkan gangar jikinta, a hankali ya ce,

“zan iya samun lambar wayarki?”

Munawwa ta yi saurin kallon shi cike da mamaki ta ce,
“Me za ka yi da lambata.?”

Ya tako a hankali har ya kai kusa da ita, sannan ya tsura mata kallon shi mai birkita lissafinta ya ce,
“Me ake yi da lambar waya idan an karb’a? “

Munawwa a tak’aice ta ce,

“Kira ko sak’o”

Ya yi murmushi mai sauti sannan ya ce da ita
“To aciki ke wanne kika fi so na yi miki? ko bakya son mu k’ulla zumunci ne?”

Munawwa tayi murmushi sannan ta ce,

“Me zai hana?”

Ya ce, “OK to ki ba ni lambar.”

Munawwaa ta fara karanto masa duka layinta biyu yana saka wa a k’aramar wayarsa da ko murfi babu. Tana k’are fad’a masa ta ce
“Zan iya shiga gida ko akwai wani abin da kake buƙata?”

Yayi murmushin shi sanna ya ce,
“Na gode sosai da lokacinki da kika ba ni, ALLAH ya hutar da gajiya.”

Munara ta shige ya bi ta da kallo ransa fari k’al saboda samun lambarta da ya yi, sannan ya shiga ya iske Isah yana gyangyad’i. Tsaye ya yi yana kallon shi sai ya yi luu ya dawo, tausayin shi ya kama shi matuk’a, a haka ya fito gidan ya zauna bisa kan wani dutsin, sannan ya danna kiran wayar Kakale suka sha yi. Bayan sun k’are ya kira Abbu yana sanar da shi halin da ake ciki akan business d’in da yake k’ullawa da wani company a kadunar.

Munawwa kuwa koda ta shiga babban falonsu ta tarar da Mummy tana ta yi wa Munara fad’a, a kan baro ta da ta yi a ta yo gida. Ta cika tayi fam saboda jin haushin fad’an da aka yi mata a kan Munawwa, a cikin muryar kuka ta ce,
“Sai da fa na ce ta zo mu je ta tsaya hira da k’awayenta, ni kuma na ji haushi na fisge key d’in na tafo, tun da na ga ita ba ta tashi zuwa gidan ba.”

Munawwa ta katse ta ta ce,
“Ke dai kin ji haushin sallamar bawanki da na yi, tun da bai zauna zaman jiran mu har mu tashi dawowa ba,don na ce ya dawo za mu zo da kanmu shi ne ta dinga ciman zarafi a gaban mutane.”

Mummy ta nuna ta da yatsa ta ce,
“Don ubanki nawa kika saka kika siye shi? Da zai ta zaman jiran ki tun safe har biyu a makaranta? wallahi Munara ki canza hali saboda ko kad’an ba kya kyauta wa kanki da ‘yar uwarki. Ke kullum abu kad’an idan ta yi miki sai kin zuk’ule? Shin waye ba ya da zuciya a kirjinsa? Ko ke ba kya ganin abin da kike yi mata? Kuma a haka kullum tana hak’uri da halinki, to idan kika kawo iskanci, wallahi sai a bar mata motar ita kad’ai ke ki je ki ji da bak’in halinki da ke kullum sai an tada jijiyoyin wuya a kanki.”

Munara ta tashi fuu ta shige d’akinsu tana gunguni, Mummy ta bi ta da kallo rik’e da baki ta ce,
“Ubangiji ya shirye ki Munara.”

***
Tana shiga d’aki ta fad’a kan gadonsu ta fashe da kuka, saboda jin haushin fad’an da Mummy ta yi mata a kan wannan shegen kuturun mutumin.

Basarake kuwa yana gidan har marece sannan ya yi sallama da su ya yi masaukin shi. Bayan ya k’are kimtsa kansa ya fara tura wa Munawwa zazzafan saƙo a cikin harshen turanci. Wanda ya tura mata da wani layinsa daban, kuma na musamman ba tare da ya bayyana mata kansa ba. Sannan ya jawo wayarsa ya kira Ummi har suka k’are gaisawa Munawwa ba ta mayar masa da reply ba. Ya yi wani kayataccen murmushi sannan ya d’auko ‘yar makararriyar wayar da ko murfi babu ya danna mata kira da d’ayan layinta, saɓanin wanda ya tura mata saƙo da shi. Saboda ya sa a ransa zai yi wasa da hankalinta har sai ya kama ta a hannu sannan ya bayyana mata kansa. Ai kuwa kira d’aya biyu ta d’aga saboda saƙon da ta gani ya ba ta mamaki sosai, don da kalaman soyayya masu zafi aka yi amfani da su, duk da ba ta san mai saƙo ba, amman hak’ik’a ya burge ta sosai. Zuciyarta tana ta wasiwasin anya wannan saƙon d’an aikinsu ne ya turo shi kuwa? shi yasa da taga kira da new number ta yi saurin d’auka domin ta tabbatar da gaskiya. A cikin sanyin jiki ta yi masa sallama shi ma ya amsa cikin daddad’an muryarshi mai sakata nutsuwa, bayan sun gaisa Munawwa ta ce,

“Ban fa gane ba.”

Ya yi murmushi mai sauti sannan ya ce,

“Kina magana da sabon d’an aikin gidanku, da fatar dai baki manta shi ba?”

Munawwa tayi

tareda tashi daga kwancen da take a kan kujera ta zauna, sannan tace, “taya zan manta ka ko?”

Basarake yace, “Daman na kira ki ne kawai mu gaisa na gode sosai da lokacinki da kika ba ni.”

Tace “Ni ma na gode.”

Sannan suka yi sallama, sai bayan sun k’are wayar ne Munawwa ta tuno da sakon ta sake danna masa wani kira, caraf ya d’auka ya yi saurin fad’in,

“Ranki ya dad’e lafiya dai ko?.”

Munawwa tayi k’asa da muryarta sannan ta ce masa,
“Ka yi hak’uri don ALLAH, wani sako ne na gani na zaci kai ka turo shi, amman kuma na ga lambar ba d’aya ba, shi ya sa na shiga kokwanto.”

Ya yi murmushi sannan ya ce,

“Saƙo kuma?”

Ya yi maganar cikin nuna alamun mamaki, munawwa ta yi murmushi sannan ta ce, “Eh shi ko ba kai ka turo ba?”

Ya yi saurin fad’in
“Ba ni ba ne ranki ya dad’e, ni wannan layin ma da kika gani shi ne kad’ai da ni.”

Munawwa ta ce, “OK babu damuwa shi kenan na gode”

Kafin yace wani Abu ta datse kiran, cike da mamakin wane ne mamallakin daddad’an sakon?.

Ba ta koma bi ta kan saƙon ba ta ci gaba da harkokinta har zuwa dare, lokacin da ta zo kwanciya tana duba wayarta ta k’ara ganin wani sabon saƙo ya shigo. wanda yake d’auke da kalaman soyayya masu shiga jiki ana yi mata sai da safe, zuciyarta ta k’ara shiga rud’u duk da ta ji dad’in kalaman ba kad’an ba. shi yasa ta so ta mayar da reply amman ta share kawai a ranta ta ce,

“Sai ka gaji don kanka ka bayyana kanka.”

Ta ajiye wayar ta gyara kwanciyarta idonta ya kai gefen Munara, inda take ta zuba chatting da honey’nta sai k’yalk’yala dariya take yi a cikin jin dad’in hirar da suke yi.

Munawwa ta juya sannan ta yi addu’ar bacci tana jiran ya d’auketa, amman tunanin sabon mai aikinsu da wannan saƙon sun saka ta gaba, abin mamaki kuma da ta rintse idanuwanta fuskar honey’n Munara take gani a cikinsu. Wanda ba kullum ne fuskar ba ta yi mata gizo ba tana fad’o mata a rai ba, sosai lamarin yake damunta matuk’a gaya. Saboda babban abin kunyar da zuciyarta take so ta jawo mata kenan a dunya, tare da hargitsin da take so ta jefa kanta a cikinsa ba ɗan ƙarami ba.

***
Ko da safiya ta waye, tun da safe BASARAKE ya zo gidan. Munara ta saka shi ya wanke mata motarsu bayan ya k’are ya zauna yana hutawa ta fito da shirin zuwa makaranta. Tana zuwa ta jefa masa key ba tare da ta ce da shi komi ba, ya d’ago fuskarsa yana kallonta har ta shige motar ta hakimce tana jiransa. Ƙ’aton glass d’inta bak’i make a kan kyakkyawar fuskarta sai taunar cingom take yi tana hurar hanci. Ya jima yana jiran Munawwa ta fito amman shiru ba ta fito ba, zuciyarsa ta shiga nazarin me ya tsaida ta. A ransa yace, ‘Watakil ita ba za ta je makarantar ba’ Yana k’ok’arin tashi ya ji muryar Munara a kansa tana fad’in,

“Idan aikin ne ka gaji da shi ai sai ka yi bayani a sallameka Malam! Don ni ba na d’aukar k’ananan iskancin masu zuwa cin arzik’i a gidan nan .”

Basarake ya tsura mata idanuwansa sosai ransa a b’ace, tana had’a ido da shi ta ji gabanta ya k’ire ya fad’i babu shiri. Saboda tun da take ba ta tab’a had’a idanuwanta da shi ba sai ranar. Amma ta waske tare da buga masa wani k’aton tsaki ta shige…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakon Yanayi 5Bakon Yanayi 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.