Skip to content

Bakon Yanayi 2

Tayi wata kara tace, “Yeeee amman don Allah honey kar in zo banganka ba ka kawo man wani uzuri.”

Kai tsaye yace,.

“Ki zo kawai at the right the time din da na fada maki I will surprise you.”

Tace ” I love you so so much, honey” yace “me too” tace “Ok bye bye.”

Ta kashe wayar sai faman Murmushin jin dad’i take yi, Munawwa da ke zaune gefen gadon tana duba litrafanta ta ajiye littafin ta kalleta cikin jin haushin wannan azarbabi nata akan Namji ta Kira sunanta a hankali tace,

“MUNARA yanzu ribar me kikaci da kika yi masa karya? Ai da kin sanar dashi gaskiyar cewa Saurayinki ne yazo don ya gano cewa ba shi kad’ai ne Mai sonki ba, sannan abun haushi abun takaici wai yanzu ke zaki cira k’afa kije wajenshi, yanzu ke ko a hakan ai yakamata ki gano cewa ba son tsakani da ALLAH yake maki ba, tunda har yaki bayyana gidanku iyayenki su San dashi, to Wallahi kika je sai na fad’awa Mummy tunda ke kullum sai kin bata Mata Rai kike jin dad’i”

MUNARA Kam Baki sake take kallonta har ta k’are sannan tace,. “Ni mamakina da wasu a kullum shine shiga sharu ba shanu ba’a kasa da mutum ba amman yace shi Dole sai ya kwasa, to bud’e kunnuwanki da kyau kiji WALLAHI tunda na yi niyyar fitar nan sai na fita sai dai idan na dawo a sakani tukunya a dafani”

Tana kare maganar ta buga mata wani uban tsaki ta maka mata wata harara ta shige toilet, Munawwa ta bita da kallo ranta a zagule tace

“ALLAH ya ganar da ke gaskiya amman muddin kika je wajenshi sai na sanarwa Mummy tunda ke baki San ciyon kanki ba”

Munara ta lek’o kanta daga toilet d’in tace

“Idan naje ki tanadi ki wuk’a a ajiye idan na dawo a kasheni kar a barni da raina”

Munawwa ta girgiza Kai tace,. “ALLAH ya kyauta”

Haka suka kwana kowa baya kula Dan uwanshi.

*****

Ko da safiya ta waye Munara cike da d’okin zuwa inda suka yi zasu had’u take, tun safe har zuwa k’arfe uku da rabi, tana bugawa dam ta fad’a wanka a gurguje ta fito ta fara shiryawa cikin farin ciki , amman ta b’oyewa Mummy bata sanar da ita ba, Munawwa ce ta san da tafiyar kuma tun da taga tana ta faman shirin fitar, a cikin mamaki tace da ita,

“Wai yanzu kina nufin da gaske ba zai zo gidannan ba kece zaki fita kije ku had’u a wani gun.? ” Munara tayi mata wani kallon renin wayo tace, “Ko zaki hana NI fitar ne uwata.?”

Munawwa ta galla mata katuwar harara tace, “zan dai fad’awa mummy ta hana ki fitar, idan ni ban isa hanaki ba ai ita ta’isa dake ko. ? “

Munara ta buga wani uban tsaki sannan ta ci gaba da shirinta har sai da ta gama zanzarewa cikin shigarta ta k’ananan kaya, wad’anda suka kama ta tsantsan ko ina ya yaji, breast sun fito tamkar su tsone idanuwan mai kallonsu, d’uwawu sun fito bumbum masha ALLAH, sannan ta d’auko d’an k’aramin gyale ta yafa a kanta ta kalli munawwa tace, “To ni zan fece idan na dawo kice kar a barni da rai na.”

Munawwa ta kalleta sama da k’asa sannan tayi tagumi tace, “ALLAH ya shiryeki Munara tunda ke a kullum idan baki b’atawa Mummy rai ba bakya jin dad’i.”

Tana k’are maganar ta bud’e d’akin ta fita Munara ta bita da harara tace, “kije da munafuccinki fita dai ce sai nayi.”

Aiko da sauri ta d’auko makullin motarsu da ta sato d’akin Mummy, ta saka talkaminta masu tsinin gaske ta k’wama wani k’aton glass bak’i, da sand’a ta fito cikin gidan ta fad’a mota tareda bata wuta sai dai tashin motarta su Mummy suka jiyo, a tsiyace ta taci ribas mai gadi ya wangale mata get ta fice kamar wadda zata tashi sama sai taunar cingom dinta takeyi.

Ta mik’i hanya tareda k’ule volume na wakar dj Ab sai biyar wak’ar takeyi tana kad’a kai, duk inda ta zo wucewa sai an kalleta saboda kid’an da ke tashi , ita kam ko a jikinta domin in da sabo ma ta saba da irin wannan kallon a duk lokacin da take driving, saboda banzar shigar da takeyi sannan uwa uba kid’an da take kur’e volume ko’ina sai ansan da zuwanta, shiyasa mummy take hanata tuk’i saboda labarin abunda takeyi yazo kunnuwanta, dalilin da yasa take b’oye makullin kenan amman duk da haka idan taso fitar, tasan hanyoyin da zata bi sai ta fita da motar, domin kuwa wani zubin ma daddy take rok’a ya karb’o mata key d’in idan ta kasa gano inda Mummy ta ajiye shi, aiko da yake baya son ganin b’acin ranta sai yasa mummy dole sai ta bata makullin.

Tana tafe tana duba agogo ganin k’arfe hud’u har ta gota, yasa ta k’ara gudu a cikin minti biyar ta isa zambia Park, tana ajiye motar inda ake parking ta fito ta tsaya a jikin motar, tareda jawo wayarta ta fara kiran number’r honey’nta, yana d’agawa yace da ita ta k’araso gashi yana jiranta, tareda yimata kwatancen inda zata sameshi, a cikin takunta na k’asaita wanda tsinin takalmanta ya k’ara taimakonta wajen taya ta rangwad’a, sai taunar cingom takeyi tana kad’a key a sama sai wani shan k’amshi takeyi, tana daf da kai wurin da yayi mata kwatancen ne aka kirata a waya, tana k’ok’arin dauka taci karo da wani har sai da wayar ta fad’i a k’asa, gaba d’aya ta tarwatse a cikin masifa ta d’ago fuskarta, karaf idanuwanta suka sauka akan fuskar mutuminta wanda ta kira da mai fuskar shanu, a razane taja baya tareda nunashi tace, “You again?”

Shi ko sai murmushinshi yakeyi mai kama da yak’e cikin sanyin muryarshi yace, “Munara ko.?”

Munara a cikin tsantsar tashin hankali take kallonsa, sannan da bak’in cikin wayarta da yayi sanadin tarwatsewarta a daidai lokacin da tafi buk’atar ta, da kuma takaicin ko inkular da ya nuna akan b’arnar da yayi mata bale ya bata hak’uri taji sanyi, k’arin haushinta kuma sunanta da taji ya kira a bakinshi, cikin zafin nama ta d’aga hannu ta kai masa mari har biyu, sannan ta d’aga murya tace, “kai wanene da har zaka fashe man waya ka kasa bani hak’uri?, sannan kazo da wani banzan bakinka ka kira sunana.”

Jikin mutumin yana rawa ya duk’a ya tarkato mata wayar, sannan ya mik’ata mata yana cewa, “Don ALLAH kiyi hak’uri ba da gangan nayi maki ba, na amince duk hukuncin da kika ga ya dace dani ki yanke man kawai, idan dai har zaki fuce ki yafe mani.”

Munara tayi masa wani banzan kallo tareda buga masa tsaki, ba tareda ta karb’i wayar ba ta saka hannu ta zaro Sim card’s d’inta sannan ta k’ara buga masa wata harara tace, “Me zanyi da wayar da ka rarratse kai ne matsiyaci kaje da ita ka gyara na barmaka, don bazan tab’a had’a hannuna da na kutare irinka ba, masu saka safa hannu da k’afa don salon cuta su shafawa mutane kuturta,amman tunda har neman gidan aiki kakeyi to ai kasan gidanmu ka zo gobe zan samar maka aikin yi, koda zaka sami kud’in da zaka sayi maganin sauk’in kuturtar ka daina saka safa.”

Har k’asa yakai yana yimata godiya ta saka k’afa ta ture shi ya fad’i ta tafi tana warar idanuwan ta inda zata hango honey’nta, amma kash duk inda ta kurd’a lungu da sak’o bata hango ko mai kama dashi ba, a dole ta koma gida zuciyarta cike da bak’in cikin rashin had’uwarsu, sai tsinewa mai fuskar shanu ta keyi tareda k’udurta irin wulakantashin, da zatayi idan har ya kuskura yazo gidansu da sunan d’an aiki.

*****

Tana cinno kan motar cikin gidansu taji gabanta ya fad’i, saboda tuno irin artabun da zasuyi ita da Mummy idan ta shiga gidan, cikin rawar jiki ta samu ta ajiye motar sannan ta fito ta nufi cikin gidan, sai da ta fara lek’e lek’e ta tabbatar bata hango Mummy ba, aiko afujajan ta bazama da gudu ta fad’a d’akinsu tareda murza key ta rufe, hannunta a gaba ta sauke ajiyar zuciyar cin nasara, juyawar da zatayi tayi arba da Mummy dake zaune tana kallonta fuska tamau ba alamun sassauci, aiko Munara ta gwalalo idanuwa tareda juyawa tana k’ok’arin bud’e d’akin ta fita, bulalar da taji ta sauka a bayanta ne yasa ta daina yunk’urin bud’e d’akin, ta fara kururuwar kiran sunan Daddy ya zo ya taimaketa, Mummy ko ta saki k’wanji tayi ta jibgarta da dorina, sai ga Daddy cikin tashin hankali yana kiran sunan Mummy yana mata kashedi akan kada ta kuskura ta sake dukanta har da yin ratsuwa, cak Mummy ta tsaya saboda jin rantsuwar da yayi tana huci ta bud’e d’akin ta fice, Daddy jikinshi yana rawa yaje ya ri’ko Munara suka fito falo sai gunjin kuka takeyi, Daddy ranshi a b’ace ya fara zubawa Mummy fad’a har da ik’irarin duk ta sake dukan Munara to a bakin igiyarta d’aya ta saki.

Ba Mummyn da Munawwa ba har ita kanta Munara lafazin ya girgizata, saboda tun da suke makamancin hakan bai tab’a faruwa a gabansu ba, wasu hawayen takaici suka saukowa Munawwa a fuska cikin zuciyarta tana nemarwa ‘yar uwarta shiriya, saboda abunda takeyi ya shalle tunaninta duk da kasancewarsu ‘yan biyun da suka fito ciki d’aya, amman halayensu sunsha bambam da juna matuk’a gaya.

Munawwara Hasana da Munara Husaina ‘yan biyu ne masu kama da juna sak,wanda a duba d’aya baza iya tantance wannan itace hasana ko hussaina ba, sai dai halayyarsu ce kawai take banbance su saboda Hasana wadda ake yiwa lak’abi da suna Munawwara ALLAH ya yota mai sanyin hali da gudun zuciyar iyayensu, yayin da Hussaina Munara ita kam tijararra ce tun tana ‘yar karamarta, Munawwara tasha matuk’ar wahala wurinta a zamanin k’urciyarsu, wanda har izuwa wannan lokaci bata shan inuwa d’aya da ita, duk da kasancewarsu ‘yan biyu saboda Munara bata raga mata ko kad’an, duk fad’a da dukan da Mummy zata yi mata a banza sai dai idan bata yi niyyar aikatawa ba, sai ta k’are sannan ta dawo tana jin tsoron hukuncin da za’a yi mata, Munawwara komi nata mai sanyi NE kamar yanda halayenta suke sauk’ak’a, sab’anin Munara da komi girman mutum bata shayin sakin jiki ta karta masa rashin mutunci, da bakin tsiwarta tsaf zata wanke mutum da soso da sabulu sai dai in bai shigo gonarta ba.

*****

Yinin ranar cur wurin lallashin Munara Daddy ya lalace, don ko abinci da Mummy ta kawo masa bar mata kayanta yayi bai ci ba, saboda kawai an tab’a masa shalelenshi Munara ‘yar gaban goshin Daddy.

Koda dare yayi suka shiga bacci daga Munara har Munawwara ba wanda yace da wani k’anzil, amma Munawwara da takaicin Munara ta kwanta cikin zuciyarta, saboda taji haushi sosai wai ace sanadiyyarta Daddy yake yi wa Mummy barazana da saki, sai juye juye takeyi ta kasa bacci, sab’anin Munara da take ta baccinta hankali kwance.

Munawwara ta tashi zaune tareda kunna ‘yar k’aramar fitilar dake rage duhun d’akin, tareda bubbuga MUNAra ta fara kiran sunanta a hankali tun tana baccin har ta jiyo sautin kiran sunanta da Munawwa takeyi, a hasale ta d’ago fuskarta tana yiwa Munawwa kallon tuhuma a cike da jin zafin tada ita daga baccin da tayi, Munawwa ta had’e fuska tace, “Ki tashi akwai maganar da zamuyi.”

Munara ta buga mata wani tsaki sannan ta tashi zaune tana yimata wani kallon up anda Dawn tace,

“Aikin kenan gulma ba aci gaba da yi ai har safiya ta waye, tunda kin yiman munafucci an dake ni to kuma yanzu me kike so kice dani?, inyi hak’uri ko kuma wani tsegumin ne kike so ki kwaso ki sauke shi a kaina, to ni banida lokacinki hajjaju.”

Ta k’are maganar tareda gyara kwanciyarta, Munawwa ranta yayi k’ololuwar b’aci shiyasa ta fara furzo kalamanta kamar haka, “Duk abunda zaki yiman ba zan fasa fad’a maki gaskiya ba, saboda abunda kike aikatawa kwata kwata bakya kyautawa kanki da iyayenm, domin naga abun naki yana so ya wuce makad’i da rawa, wai ace kina ji kina gani kin had’a hasuma tsakanin iyayenki, wai akanki Daddy yake furta datse igiyar aurenshi da Mummy, shin ribar mi kikeci idan kin saka Mummy a damuwa?meyasa kike mance cewa Mummy ce fa ta haifeki ba ke kika haifeta ba, yazama dole a gareki kiyi mata biyayya ko da bakya so, tun kafin fushin ubangiji ya sauka akanki. “

Munara daga kwancen tace, “ALLAHU AKBAR malama tashi kin faye naci.”

Munara daga kwancen tace, “ALLAHU AKBAR malama tashi kin faye naci.”

Munawwara tace, “Kome zaki ce to ki fad’a gaskiya ce dai bazan fasa fad’a maki ba, don haka ki daina yin abunda zai kawo rikici tsakanin iyayenmu.”

Shirun da Munara tayi mata ne yasa ta kwanta itama tun tana tunani har bacci ya yi awon gaba da ita.

*****

Da safe musalin k’arfe goma na safe mai gadi ya zo yana sanar da Mummy wani yazo neman Munara, Mummy ta k’wallawa Munara kira dake kitchen tana dafa indomi ,bayan ta fito ne Mummy take sanar da ita tayi bak’o a waje, a haka da take da ‘yar guntuwar riga mara hannu sai wando three quarter da d’an gyale saman kanta, tazo zata fita Mumm ta maka mata harara sannan taje d’akinsu tana gunguni ta d’auko hijabin sallahrta ta saka, ta fito tana ta Alla Alla a ranta idan mai fuskar shanu ne saboda tanadin rashin mutuncin da tayi masa, a dalilin sanadin da yayi na rashin had’uwarta da honey’nta wadda har a lokacin take cike da jin haushin wayarta da ya fasa.

Tana fita harabar gidan kuwa tayi arba da mutuminta, ta k’ara tamke fuska kamar wadda bata tab’a dariya ba, tazo ta tsaya k’erere a gabanshi jikinshi yana rawa ya risuna yana gaidata, ranta a had’e take amsawa kamar bata so kafin ya k’ara wata magana sai ga Daddy ya fito a cikin shirinshi na fita sai sauri yake zubawa, ya nufi motarshi zai shiga idanunshi suka sauka inda Munara da wannan mutumin suke a tsaye, cikin mamaki yace, “Ya akayi baby? meke faruwa ne?”

Munara ta fara magana cikin shagwab’a tace, “Daddy aiki yake nema shine nake so a taimaka masa.”

Daddy ya washe baki yana dariya yace, “To ki d’auke shi kawai baby tunda kina so.”
Munara tazo da gudu ta rungume shi tace, “Nagode Daddy i love you so much.”

Ta k’are maganar tareda rik’o hannunshi ta yi masa kiss, Daddy yana murmushi yace, “Me too my daughter. take care”

Ya k’are maganar tareda dafa kanta sannan ya shige mota ya bata wuta, suna yiwa juna bye bye har ya fice amma ko kallon mutumin bai yi ba bale ya tsaya su gaisa, duk da yunk’urin gaida shi da mutumin yayi.

Munara daga inda take tayi masa nuni da hannu akan yazo, jiki ba kuzari ya fara taku ya nufi wurinta a cikin girmamaw yace,

“Gani hajiya.”

Munara tayi masa wani kallo mai had’e da harara tace, “Kaci nasara an d’auke ka aikin amma ka sani…

Bookmark
ClosePlease loginn

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.5 / 5. Rating: 2

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

<< Bakon Yanayi 1Bakon Yanayi 3 >>

Drop a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.