Skip to content
Part 1 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

A guje ta shigo dakin ta tana kuwwar fadin,

“Wayyo Allah Munawwa yanzu ya kirani ya kusa karasowa” tana maganar tana tube kayan jikinta ta fad’a toilet jikinta sai rawa yake saboda doki, wadda aka kira da suna Munawwa ta bita kallo a cike da mamakin rawar jikin da takeyi akan zuwan wannan guy, duk da tasan yanda Munara take bala’in son shi amman dai duk da haka taga rawar jikin tayi yawa, idan kuma tayi duba da wannan ce had’uwar da zasuyi ta farko, dole ne tayiwa ‘yar uwarta uzuri don ko ita kanta guy d’in yan ma burgeta sosai.

A cikin kuzari ta tashi ta bud’a wardrobe d’insu ta zab’owa munara wata had’ad’d’iyar doguwar riga ta shadda coffee color , wadda aka tanada domin wannan ranar kawai, sannan ta d’auko mata wata sark’a da ‘yan kunnenta wad’anda zasuyi matching daidai da color d’in stone work din da aka yiwa shaddar, gyale ma kanshi mahad’in shaddar ta ajiye mata akan gado tareda talkaminta.

Sannan ta sami gefen gadonsu ta zauna tareda janyo wayarta ta fara chatt, a cikin sauri munara ta fito toilet d’in sai tsallen jin dad’i takeyi, ganin kayan dake kan gadon yasa tayi turus tareda b’ata fuska, a cikin fushi ta fara fad’a tana cewa, “Hajiya wa kika fitowa da wad’annan karikitan haukar? Da fatar dai ke zaki saka ba ni ba?”

Munawwara ta kai dubanta a gareta a cikin sanyin muryarta tace, “Ni dad’i na dake ba’a yimaki gwaninta, sannan halan kin manta mummy tace dole ne ki saka daya daga cikin kayan da aka dinko muna?”

Munara tayi zaune akan stool ta fara shafa mayuka a jikinta tana mere tace, “Nifa bana son shishigi malama ku barni da ra’ayina, kowa yayi abunda yaga zai fidda shi yanzu ke ubanwa yake hanaki saka dogayen rigunan da kike faman zunbulawa a jikinki?, sai NI za’a takura to wallahi bazan saka kayan ba kinji kuma na rantse.”

Sanin halinta yasa munawwara taja bakinta tayi shiru taci gaba da chatting din da takeyi, munara ta kare shafe shafenta da ba wani cika kwalliya a fuska takeyi ba, taje ta bud’a wardrobe ta jawo wasu kananan kaya riga da wando sababbi k’al ta saka, sun bala’in kamata tsan tsan a jiki ta dubi kanta a standing mirror tayi murmushi har sai da dimple d’inta duka biyu suka lotsa, taje ta janyo wasu talkama masu bala’in tsini ta fara sakawa, sai ga kira a wayarta ya shigo a cikin zumud’i ta d’auki wayar tace, ” hy honey.” sannan tayi shiru na d’an lokaci sannan tace, “Eh gidan ne k’araso kawai yanzu gani nan fitowa.”

Tana kare maganar tayi saurin jawo wata after dress sharara baka mai hula tareda adon duwatsu a saman hular da gaban rigar, bayan ta saka taje ta fara bulbula turaruka sunfi kala biyar, kowane da kalar k’amshinshi inda suka had’u suka bada wani kalar k’amshin da duk kwakuwar mutum bazai tab’a tantance wane kalar turare ne ta fesa ba, tana k’ara gyara fuskarta tace da munawwara, “malama ke nike jira fa.?”

Munawwara tayi kamar bata ji taba taci gaba da latsar wayarta saboda haushin k’in bin umurnin mahaifiyarsu da tayi, aiko munara taji haushin k’yaletan da tayi a zuciye tace,

“Kada ALLAH yasa kije daman ni ba wanin son kije nikeyi ba don dai kawai bak’in fad’an da ake saka mutum ayi ta yimasa ne, shiyasa nace dake muje tare huta da wani shan k’amshi.”

Tana kare maganar ta fice kamar zata tashi sama minti biyu a tsakani sai gata ta tadawo da aguje ta shige toilet d’insu, munawwa ta bita da kallo wanda ko tantama batayi Mummy ce take yiwa wannan b’oyon, aikuwa sai ga mummyn ta bud’e k’ofar d’akin nasu ta shigo, idanuwanta suna kai kan kayan dake zube a saman gadon tace da munawwara, “idan ta fito wankan ki tabbatar ta saka kayan.”

Munawwara tayi murmushi tace “to mummy amman ai tana jinki ma.”

Mummy tace, “to ai ta fito ta saka kafin inje in dawo. ” tana fita munawwara ta sauke ajiyar zuciya taci gaba da latsar wayarta, munara dake lab’e a jikin k’ofar toilet d’in tana jin mummy ta fita, ta fito da sauri zata fice d’akin, munawwa ta kai kallonta gareta tareda d’aga murya tace, “bakiji abunda mummy ta fad’a bane halan.?”

Munara ta juyo tare da galla mata wata jar harara ta fice d’akin da sauri, munawwa ta ajiye wayar tareda yin tagumi tace, “Ya ALLAH.”

Sannan ta tashi ta jawo d’ankwalin doguwar rigar dake sanye a jikinta ta yafa, sannan ta saki wasu talkami plat a kafarta ta fice tabi bayan ‘yar uwarta.

Munara ko da sand’a ta fito d’akinsu ta lek’a bata hango mummyn ba aiko da sauri ta fice , abun mamaki koda taje tazo harabar filin gidansu bata ga kowa ba aiko jikinta yana rawa ta lek’a har wajen get d’insu, a nan ma bata ga kowa ba, sai wani mutumi dake zaune a kan wasu manyan duwatsuna dake gefen k’ofar gidan nasu, wannan mutumin ko yana hango fuskarta ta lek’o ya fad’ad’a fuskarshi da murmushi mai kama da yak’e, saboda yanayin fuskarshi da ke tattakure alamun yunwa k’arara sun bayyana a jikinta, sannan ga wani bak’i da fuskar take dashi tamkar anyi masa fenti, sai dai kuma sock’s farare k’al dake sanye a tafin hannunshi dana k’afafuwanshi.

Munara tayi mashi kallon sama da k’asa sannan tayi tsaki tana waige waigen ta inda bak’onta zai b’ullowa, shi kuwa ganin yanayin kallon da tayi masa yayi murmushi tareda yunk’urawa ya tashi daga kan dutsin da yake kai, ya fara taku a hankali zuwa wurinta, ganin yana nufota munara tayi baya da sauri zuciyarta a cike da mamakin zuwanshi wurinta.

Ba shiri tayi saurin rufo ‘yar k’aramar k’ofar get d’insu, wanda yayi daidai da zuwan munawwara tana tambayarta baizo bane? Munara ta gwalalo mata idanuwa tareda nuna mata k’ofar, a cikin mamaki munawwa ta bud’e k’ofar ta lek’a aiko itama tayi arba da wannan mutumin, duk da ta d’an so taji tsoro amma dai ta dake tama k’arasa fitowa duka, sannan ta fara gaidashi a mutunce don ita mace ce wadda tasan darajar d’an adam, tana girmama duk matsayin da taga wani a ciki, mutumin yaji dad’in gaisuwar da munawwara tayi masa sannan a cikin muryarshi tattausa yace da ita, “wurin ‘yar uwarki nazo amma naga ita kamar ma tsorona takeji.”

Munawwa tayi murmushi tace, “A’a ba wani tsoro kawai dai don bata sanka bane ba amma yanzu bari inje inyi mata bayani kayi hak’uri kaji.”

Yace “ba damuwa nagode da kulawarki”

Munawwa ta shige get d’in inda ta iske munara sai faman kiran wayar honey d’inta takeyi, amma wayar tak’i shiga hankalinta a tashe sai kai da komo takeyi tana yarfa hannu tareda buga k’afafuwa tamkar wata ‘yar yarinya, wanda anan take hawaye suka taru a k’wayar idanuwanta saboda damuwa, munawwa ta kalleta taso tayi dariya amma ta mazge tace,

“Wannan mutumin fa wajenki yazo kije kiji me ya kawoshi.”

Munara ta galla mata wata k’atuwar harara tace, “Wallahi da kin k’ara yiman maganarshi sai mun dambace dake yanzu a nan wurin .”

Munawwa ta zaro idanuwa a waje tace,

“Hajiyar honey ba ni na kar zomon ba don ko rataya ma ni ba’a bani ba.”

Ta k’are maganar tana dariya ta shige cikin gidansu ta barta anan cikin takaici, munara ko da taga wayar tak’i shiga ba shiri sai ga hawaye sharrr suna gudana akan fuskarta, a zabure ta fito k’ofar get d’insu tareda taku kamar hud’u zuwa biyar tana lek’a dama da hagu, tana so taga ta inda motar honey’n nata zata b’ullo, wannan mutumin yana tsaye yana kallonta ganin ta nuna kamar bata san dashi a wurin ba, yasa yayo tattaki ya k’araso inda take tareda yimata sallama a cikin sanyayyiyar muryarshi.

Munara tayi saurin juyowa ta galla masa harara bata jira taji abunda zai fad’a ba ma, ta fara balbaleshi da ruwan masifa tana cewa, “Wai kai wani irin kulafuci ne wannan?, miye tsakanina da kai ne da kake so ka shiga rayuwata ne?, a’ina ka sanni ma wai da har ka wanke k’afa kazo gidanmu?, ka kalleni dakyau ka kalli kanka baka ji kunyar zuwa wurina ba? kai kanka kasan ni ba sa’ar ka bace, don ALLAH ka tafi ni ko fuskarka ma bana son gani, idan kuma naci ne sana’arka to ka jira kad’an zaka ga irin wad’anda suke daidai dani ba kai ba mai fuskar kashin shanu.”

Mutumin yayi murmushi kamar baiji zafin maganganunta ba yace, “Yanzu don nazo in nuna maki irin son da nake yimaki laifi ne?”

Munara tayi saurin ja da baya nesa dashi tace, “so? Wa kake so d’in ni din?cab! Lalle k’wak’walwarka kanka ta toshe, kuma notukan saman kanka duka sun kwance amma wallahi kama rena ni. “

Mutumin ya k’ara matsowa a kusa da ita yana murmushinshin shi mai kama da yak’e yace, “Tun da na d’ora idanuwa na akanki naji ba wadda nike so irinki, don ALLAH ki daure ki soni koda kad’an ne kinji.?”

Aiko a zabure munara ta d’aga hannu ta wanka mashi wani haukataccen mari tareda da nuna shi da d’an yatsa tace, “Ko a unguwar nan ka sake na k’ara ganin k’afarka sai ka yabawa aya zak’inta.”

Tana k’are maganar hawayen bak’in ciki suna zuba ta shige gidansu tareda bugo k’ofar get d’in da k’arfi tace garammmm!!!!.

Mutumin ya bita da kallon mamaki yayi murmushi yace, “sweetyna ce ta d’aga hannu ta mareni a zuwana na farko a gidansu.”

Yana k’are maganar ya mik’e wata hanya yana tafiya har yasha kwana, sai naga ya nufi wata kafurar dunkulalliyar mota sai k’yallin sabunta takeyi, ya bud’e ta ya shiga ba shiri na lab’e jikin motar na lek’a, aiko me zan gani sai naga ma ashe akwai wani a cikin motar, yana shiga suka baiwa juna hannu sukayi shaking, sannan d’ayan mutumin ya kalli fuskarshi ya kyalkyale da dariya har da buga hannunshi akan starring motar, a hankali naga wannan bak’in mutumin ya saka hannu ya fara k’ok’arin cire bak’ar fuskar dake manne da tashi, yana sauke bak’ar fuskar naganshi wani had’ad’d’en guy fari sol da sumar kanshi bak’a k’irin hadda wani murd’e murd’e tayi saboda tsananin sulbinta, da hancinshi har baka mai tareda madaidaicin bakinshi mai d’auke da d’an k’aramin gemun da wayayyun samari suke ajiyewa, ga wani bak’in saje da ya kwanta luf luf a gefen fuskarshi.

Ina lab’e ina kallonshi ya cire safar hannunshi mai d’auke da dogayen yatsu farare sol da gashi kwance luf a bayan yatsun shi, ya ciro safar k’afar itama ya had’a su a waje d’aya ya jefa a bayan sit, d’ayan mutumin da suke tare yana dariyar k’eta yace, “haba basarake kayan aikin kake wulak’antawa.?”

Wannan guy d’in da aka kira da Suna basarake, ya galla masa harara yace,

“Me zanyi da kayan da suka janwo aka kwad’a man mari.”

Aiko abokin tafiyar tashi me zaiyi ba dariya ba har ya tada motar suka bar unguwar bai bar dariyar ba.

A cikin wani bajimin kuka munara ta shiga gidansu idonta a rufe taci karo da mummy, wadda daman cen jiran shigowarta takeyi saboda ganin kayan da tace ta saka ajiye akan gadon, aiko a zafafe mummy tayi mata wani rik’o munara tana d’aga ido taga mummy ta fara kukan neman ceto, sai d’aga murya takeyi sai kace wadda za’a cirewa rai tana fad’in,

“Don ALLAH mummy kiyi hak’uri bazan sake ba.”

Kururuwar hak’urin da take baiwa mummy ne yasa Daddy yayi saurin saukowa daga sama, ranshi a b’ace yake kallon mummy tareda yi mata gargad’i da idanuwa akan ta saki munara, mummy ta d’aga hannu zata kaiwa munara duka daddy ya rik’e a hannu a cikin b’acin rai yace, “wai har yaushe zaki barin yarinyarnan ta huta?, a kullum aka jiyo tashin muryarki da ita ne, to ni ban matsa ma yarana ba don haka wallahi bazan zura idanuwa a takurasu ba, sake ta kar ki karya mata hannu.”

Ya k’are maganar tareda fisge munaya da rik’on da mummy tayi mata, mummy ta bishi da kallo baki a sake kamar wata sakarya tace, “Shikenan ni yanzu banda ikon tayi laifi inyi mata hukunci.?”

Daddy ranshi a b’ace yace, “to me tayi maki ne yanzu da zaki yimata hukuncin duka da girmanta?, tunda ta zama sarkin laifi kullum ita kad’ai ce keyi a gidan.”

Mummy tana nunata da d’an yatsa tace, “kika yarda na koma cewa ga abunda zakiyi kika k’i, wallahi sai na karya ki a gidannan ki daina ganin an d’aure maki gindi kina abunda kike so, wallah tsaf zan saka bulala in zaneki ras!”

Daddy ya kai dubanshi ga munara da ta lafe a bayanshi sai muzurai takeyi, yana murmushi yace, “me kika yimata ne? da zaki jawa kanki duka a banza.”

Munara tayi k’wal k’wal da idanuwa tace, “wai don nak’i saka kaya shine.”

Daddy yana dariya yace, “to dole ne saka kayan? tunda ba kyaso ba sai a kyaleki ba, yanzu ina bak’on har ya tafi ne?.”

Munara ta zunb’uro baki tana hawaye

Mummy saboda haushi kasa magana tayi, tayiwa munara wata k’atuwar k’wafa ta wuce su fuu ta shige kitchen, saboda bata son ta furta kalmar da ba mai kyau ba, don bata son su raba wa kansu abunc kunyar cikin lamarin, don zai ga tayi masa rashin kunya a gaban yayansu.

Daddy Kam zaunar da MUNARA yayi cikin tausasa halshe yayi ta lallashinta har ya samu ta saki sannan yace da ita taje d’akinsu cikin natsuwa taji me ya hanashi zuwan kamar yanda yace.

Ta mike tana dariya tace ,. “Nagode Daddy I love you so much amman don Allah kace kada Mummy ta dakeni kaji?”

Ta k’are maganar cikin shagwaba Daddy yana Murmushi yace,

“Ai ba ma zata fara ba itama tasani jeki abunki”

MUNARA ta shige d’akinsu zuciyarta cike son jin abunda ya hanawa Haidar d’inta zuwa gashi ya janyo garin nemanshi ta had’u da mai fuskar shanu.

Tana shiga d’akin ta fad’a kan gadonsu ta fara dialing numbar Haidar d’in aiko sai gashi an d’auka, cikin zumudi ta tashi zaune tace

“Haba Honey haba Honey shine kace ga ka a unguwarmu kasa na fita bulayin nemanka amman kaki zuwa to ai ba komi ka jirgani kaji dad’i”

Daga cen bangaren ya bata fuska kamar da gaske yace,. “Bayan nazo tun daga nesa na hangoki da bak’o to bana son in takuraki shiyasa na juya abuna”

Munara ta dafe Kai tace, “Oh sheet ba fa bakona bane ba almajiri ne ya zo wajen Daddynmu neman sadaka shine fa na karb’o na kawo masa”

Haidar Kam daga bangarenshi ya kumshe dariyarshi yace, “Au haka ne ai ban sani ba”

MUNARA cikin jin haushi “to yanzu ka sani amman ai da ko kirana ka yi ko daga nesan mun gaisa, to yanzu Ni dai ya kenan gobe zaka dawo ko?”

Yayi yar dariya yace

“A’a bazan dawo ba amman in kina b’ukatar ganina mu had’u a Zambia park gobe da k’arfe hudu da rabi na yamma.”

Munara ta yi tsalle tace, “Serious fa!”

Ya ce, “of course”

Ta.yi juyi akan gadon cike da jin dad’i tace,

“Promise”

Ya ce,

“Promise.”

Bakon Yanayi 2 >>

5 thoughts on “Bakon Yanayi 1”

  1. Masha Allah yakara basira da daukaka managarciyar Marubuciya, hakika ke Marubuciya ce Mai basira wadda ta cancanci yabo madallahi Dake managarciyar.

  2. Littafin bakon yanayi littafi ne da ya kunshi halayen yammatan mu na wannan zamani marubuciyar tayi ammafani da ilimi da Basira gurin rubuta shi madalla da wannan hazikar marubuciya Allah ya Kara basira

  3. Bakon yanayi book mai tafiya da salo na daban da ya tabo bangarori da dama na rayuwa Allah yaqara basira da lafiyar ido my dijah muna yin bakon yanayi over bcoz yana sugar over

    1. Lallai munara kin samu wuri dole kiyi shanya…. Amma ba laifin ki bane laifin daddy ne da ya sangartaki, Mommy kicigaba da yi mata addua Allah ya tarota,,,. Toh saraki kai Kuma da haka kazowa munaran da alama dai jarabata zakayi bankuma ga alamun zata iya cin jarabawar ba,,,, toh ko waye Khaidar Kuma?!

      Mom Allah Kara lafiya da zakin hannu…

  4. Masha Allah hakika bakon yanayi littafine daya tabo rayuwa a mabanbantan yanayi Allah yabaki baiwar rubutu Allah yaqara daukakaki yakara miki lpia amin littafi yayi dadi ahmadulillah

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×