Kamar haɗin baki kuwa, sai ni da Dardira muka sake nufo juna da wani sabon azababben gudu, muka tari juna tare da fara sabuwar fafatawa. Nan fa faɗan ya zamo sabo, ya zamana muna kaiwa juna muggan hare-hare. Sai da muka kwashe sama da daƙiƙa ɗari da sittin muna wannan fafatawa amma Dardira ko lakutar hanci na bata samu damar yi ba, yayinda ni kuma gaba ɗaya na rikitata da duka da sandata. A ƙalla na yi mata ƙwararan bugu guda shida a manyan gaɓoɓin jikinta. Hakan yasa da ƙyar take iya tsayawa. . .
Masha Allah lbr yy Kuma ya bada ma’ana muna maka fatan alkhairi marubuci Allah ya Kara basira Kuma Allah ya daukakaka
Amin. Jazakallah Khair
Aiki mai kyau Allah yataimaka Gaskiyya labarin nan yayiman
Amin. Na gode sosai.
Wow! Allah ya taimaka. Labari kam ya yi dadi. Allah ya ƙara basira.
Ina godiya sosai.
Allah ya sa albarka a cikin wannan aiki naka.
Amin. Jazakallah Khair