Skip to content

Bita akan rubutun gajeren labari 3

Ku na iya latsa nan don karanta darsin rana ta biyu

RANA TA UKU

Darasi na 1

Matakan tsara labari

Duk ginin yayi kwari, to wajibi ne a samar da tubala masu inganci sannan a yi masa ginshiki da tanka mai ƙwari. Shi ma labari haka ake yi masa irin wannan shiri domin yayi armashi kuma ya nagarta.

Kowanne marubuci yana samun labarinsa ne ta hanyoyin da suka hada da mafarki ko a fada maka, ko ka gani a talabijin ko a gabanka ko ma ka karanta a littafai da sauransu. Kowacce hanya dai mutum ya samu labarin da zai rubuta, bin matakan sarrafa tun daga tushe yana da muhimmanci.

Da zarar ka samu labarin da kake ganin ya dace ka rubuta, wacce hanya ce ta farko da ta kamata ka yi wa labarinka ginshiki da ita? Wannan dabara ita ake kira Five Finger Pitch.

Five Finger Pitch dabara ce da wani kwararren marubuci mai suna Michael Lengsfield ya samar domin inganta rubutun labarin fim. Sai dai kowanne marubuci yana iya dauka yayi aiki da ita domin samun labari nagartacce.

Ta wannan dabara ana dunkule labarin ne cikin matakai biyar na yatsun hannu, kowanne yatsa yana dauke dunkulallen bayani akan labarin. Watau kamar a ce fuloti ne aka yi zanen gida a takarda kafin a fara ginin.

Da taimakon five finger picth ne ake gane irin armashin labarin ko akasin haka. Waɗannan matakai kuwa su ne:

1. Genre: Ajin da labarin ya fada. Watau misali a ce, labarin soyayya ne, ko ban dariya ko sadaukantaka ko kasada da sauransu.

2. Tauraro: Wanda aka rubuta labarin akansa da takaitaccen bayani game da shi.

3. Goal: Irin burin da tauraron yake da shi da yake son cimmawa

4. Obstacles: Irin matsalolin da tauraron ke gamuwa da su wajen cimma burin nasa

5. What is Important: Abu mafi muhimmanci dangane da labarin. Ko irin darasin da za a koya a cikinsa.

Bari mu dauki kowanne abu mu yi takaitaccen bayani tare da misali.

Darasi na 2

Karin bayani da misalan Five Finger Pitch

1. Genre: Labarin da kake son bayarwa za ka nemo masa matsuguni a cikin rukunan labari kamar yadda na ambata. Misali, soyayya, zaman iyali, siyasa, jarunta, sadaukantaka da sauransu. Ya danganta da irin yadda kake son fassara labarinka yadda mutane za fahimta.

2. Character: Tauraron labarin naka da irin shekarunsa da muhallin da yake zaune. Misali, tauraron littafin Ruwan Bagaja, wani saurayi ne dan shekara 15 zuwa 30. Ya taso a matsayin agola amma ya fi dan gida daraja.
Ko kuwa mu ce, tauraronmu wata bazawara ce da aka mutu aka bar mata yara kanana.
Wani misalin kuma shi ne, wani basarake mai adalci amma mai tsanani ga masu laifi.

Duk dai yadda ka fasalta tauraronka wanda zai ja ragamar labarin.

3. Goal: Burin da tauraro ke da shi a cikin labarin. A gajeren labari ana ba wa tauraro babban buri guda daya rak, wanda a ciki kuma za a iya tara masa wasu bukatun hawa – hawa. Misali anan shi ne, burin Alhaji Imam na Ruwan Bagaja shi ne ya samo ruwan kogin Bagaja domin a yi wa dan sarki magani. A hanyarsa ta zuwa neman ruwan bagaja yayi ta cin karo da abubuwan da dama na dadi da akasinsa.

4. Obstacle: Watau irin tangarda da fadi tashin da tauraronka ke gamuwa da su wajen cimma bukatarsa. Ba a so marubuci ya zamana ya nuna son kai tauraronsa. Duk yadda za ka cunkusa cikin matsala da yadda zai fita duk ka bayar. Domin yawan rikicin da tauraron ya shiga shi ne yawan jan hankali da labarin zai yi. Misali, muna da tauraro mai zawarci da aka bar mata ‘ya’ya mijinta ya rasu. Kalubalen da ke gaban ta shi ne irin tarbiyyar da za ta ba wa ‘ya’yanta har su girma su zama mutane. Ana so marubuci ya zo da matsaloli ta fuskar da ba a yi zato ba.

Ita wannan bazawara mun san za ta iya gamuwa da zaluncin dangin miji da rigimar gado da tozarta yaranta da fafutukar neman abinci da sauransu. Yana da kyau ta zama jaruma mai karfin halin fuskantar duk kalubalen da ya taso mata. Kada ka sa ta zamana kullum cikin kuka da salla da jan carbi. Wannan dabi’a ce mai kyau amma ba za ta ja hankalin mai karatu ba.

5. What is Important: Darasi ko abin lura da ke cikin labarin. Ba a so labari ya zamana na bara na ci wake ko na ji gardin aya da sauransu. Ana so kowanne labari ya zama mai isar da wani sako. Za ka fadi irin abu mai muhimmanci da kake ganin labarin naka na dauke da shi. Sai dai fa ka sani, marubuci na iya fadin sakon da ke cikin labari amma ya zamana makaranci ko manazarci ya ga sabanin haka.

A littafin Sara da Sassaka na Bala Anas Babinlata, muhimmin abu da ke kunshe cikin labarin shi ne gwagwarmayar kwatar ‘yanci daga turawan mulkin mallaka da kuma tasirin soyayya a cikin sha’anin mulki.

Darasi na gaba za mu kawo hanyoyin da ake rubuta Five Finger Pitch yadda tubalan labarinka za su yi karfi.

Darasi na 3

Misali na 1

Genre: Zamantakewa

Character: Matashin saurayin wanda mahaifinsa ya rasu ya bar masa babban kanti mai cike da rudanin lissafi

Goal: Tattara kan dukiyarsa domin sanin adadin mutanen da suke bin mahaifinsa da wadanda yake bi bashi.

Obstacle: Rashin cikakkiyar shaida yadda za a iya gane gaskiyar masu da’awa da kuma wadanda ake bi bashi. Saurayin ya gamu da matsaloli da yawa har ya kusa rasa rayuwarsa.

What is Important: Labarin na nuna yadda zamantakewar ‘yan kasuwa take wajen rashin adana lissafi da yadda suke fadawa rikicin bashi basu ji ba basu gani ba saboda rashin ajiyar bayanai

Misali na 2

Genre: Laifi

Character: Tsohon maaikacin tsaro da yayi ritaya aka masa laifin kisan wani dan siyasa da yake yi wa aiki
Goal: Kokarin gano wanda ya kulla masa sharri kuma ya wanke kansa
Obstacle: Yana buya kada jami’an tsaro su kama shi ko wadanda suka kulla masa sharrin su nuna inda yake.

Important: Aiki da tunani da kokarin tunkarar matsala da karfin hali.

Misali na 3

Labarin wata yarinya da ta kamu da son wani Kirista alhali ta san ba za a bari ta aure shi ba a gidansu saboda sabanin addini. Burin ta shi ne ta musuluntar da shi cikin ruwan sanyi. Matsalar bata san yadda ake wa’azi da daawa ba. Babban abin lura shi ne tasirin soyayya da yadda ake maganin magulmata.

AIKIN GIDA

Ina so Marubuta mabiya wannan bita kowa ya tsara labarinsa ya dora su a matakin Five Finger Pitch kamar yadda na kawo misali.

Ana iya amfani da kowanne salo a cikin ukun nan da na kawo.

Kada ya wuce gobe Alhamis ko Juma’a da safe.

Wannan ma yana cikin sharuddan satifiket.

Mu kwana nan.

Wassalam

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page